NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 31 to 40

Sai shima a nan ne ya gane abinda ya aikata, yayi saurin saka hannu yana sosa kai cike da murmushi a face ɗin sa yace, “I’m so sorry Ƙanwata, wlh na manta ne”.

Murmushi tayi kawai tana kallon sa, sai kuma ta gyaɗa masa kai

Hakan sai yasa yaji daɗi sosai, don be yi tunani hakan daga gare ta ba, a kullum faɗa masa take yi ba ta ƙaunar irin wannan rayuwan, duk da shi a wajen sa ya saba sosai ga friends ɗin sa da yayi school tare da su, irin wannan rayuwan wayewan shi ne Baffa ya taso dashi, babu ruwan sa don ya rungume mace, amma tun sanda Ɗahira ta soma taka masa birki shima ya rage yi, duk wani halayen sa mara su kyau da yasan za su ɓata mata rai, ya dena su, duk sabida farin cikin ta, shiyasa a kullum sake ji yake yi ƙaunar ta na ƙara wanzuwa a cikin ƙalbin sa, idan har ya same ta a matsayin matar sa kuwa; to, tabbas ya gama dace a rayuwan sa, ita ɗin haske ne cikin rayuwan sa, zai so ya kasance da ita har abada a duniyar sa..

“Yaya mu je kar muyi late”. Tayi maganar tana kallon Wrest watch ɗin dake ɗaure a hannun ta

Murmushi yayi kafin yace, “tom dear”.

A tare suka fita daga gidan.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

        Washe gari aka wayi gari Kaka be da lafiya, zazzafan zazzaɓi ya tashi dashi, sosai hankalin iyalan gidan ya tashi, nan da nan aka ɗunguma aka yi asibiti dashi

Su Ɗahira suna can labari ya riske su, ai nan ko wannen su ya kiɗime, domin ba ƙaramin ƙaunar Kaka suke yi ba, ko kaɗan ba sa son abinda zai taɓa sa, duk da kuwa ya tsufa amma suna matuƙar ƙaunar sa; ba sa son su rasa sa, ga shi be cika ciwo ba shiyasa hankalin su ya tashi da ganin yanda jikin sa yayi mugun zafi.

    Gaba ɗaya iyalan gidan sun hallara a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Kaka, kowa hankalin sa a matuƙar tashe, da yawan su sun kasa zama sai zagaye suke yi, irin su Ɗahira kuwa sun kasa jure wa sai sharan hawaye suke yi.

    Su Abbu na ciki su ne masu duba shi, su kansu hankalin su ya gaza kwanciya, sabida halin da suka ga Kaka ya shiga, sun kasa shawo matsalar sai faman zufa suke yi.

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button