NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 27

_NO. 27_*

   …………“Wai lafiya kaketa zabgamin harara Ajiwa? Naga kaika ɗaga wayarnan da hannunka bani na bakaba, to miye laifina da zakaita
watsamin waɗannan mayun idanun damin tsoki?”.
       Yanzunma tsakin yaja tareda ɗauke itanunsa daga kan Attahir, takardun gabansa ya tattara waje ɗaya yamike ya fice daga Office ɗin.
     Da kallo Attahir ya bisa yana dariya ƙasa-ƙasa.
     Dukda yaji dariyar ta Attahir bai kulasaba ya fice abinsa yana jin wani irin takaicin da baisan daliliba.
          Sosai Attahir ya kwashe da dariya yana dukan tebir ɗin gabansa, “Ajiwa manyan ƙasa”. Ya faɗa  Shima tare da miƙewa ya fice abinsa.

       Koda ya koma gida har dare abu kamar wasa yaƙi barin ransa, duk yanda yaso yakice muryar yarinyar aransa ya kasa, wannan wace irin masifa ce haka, Bily da aka haifa a gabansu itace har take neman zamema ransa matsala (duk ɗaukarsa bily ce), “Mtsoww anyama banzannan Attahir bashi ya shirya ba?”. Yay maganar a fili cike da takaici.
       Tun fa yana ɗaukar lamarin da sauƙi harya zame masa abin tunani lokaci-lokaci, harma zuciyarsa na buƙatar sakejin muryarta, sai dai tsabar baƙin miskilanci yahana koda a fuska ya nunama wani.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        Ɓangaren Ummukulsoom kam tuni tama manta da wani batun wayar da sukayi, dan karatunta taci gaba dayi harsu Bily suka shigo, sun ɗan taɓa hirarsu daga nan suka kwanta.

★★★★

          Su Ummukulsoom sun cigaba da Exam cikin aminci da fatan nasara, kulum cikin kaima ALLAH kukansu suke tareda ƙwazo a exam ɗin, ahaka suka kwashe watanni har yau gasu ALLAH ya kaisu ga nasarar gamawa, ranar Ummu tasha kukan daɗi, duk da dai tanada sauran karatu na shekara ɗaya a gabanta kafin tazama Barrister ta gaskiya.
        Ansha shagalin bikin yaye ɗalibai, wanda ya kayatar ya ajiye tarihi, Ummukulsoom tana ɗaya daga cikin ɗaliban dasuka sami ƙyauta aword na ɗalibai mafi ƙwazo, hakanne yasaka Dad matuƙar jin farin ciki, dan shida Abba da Ummi yaya Attahir, Yaya Zaid, maman Ahmad suka halarci taron, kowa yanata saka musu albarka tareda taya murna.
       Aranar suka baro port harcourt cikeda kewar su Peace wadda taita kuka, dan ba ƙaramar shaƙuwa bace mai yawa ta shiga tsakanin wannan ahali dasu Ummukulsoom, shiyyasa bazasu taɓa mantawa da suba, dolene su dinga kawo ziyara a kai akai kamar yanda suma sukayi alƙawarin kawo musu.
     
     Koda suka dawo KD ma wata ƴar kwarƙwaryar walima Abba da Dad suka shiryama su Ummukulsoom bayan sati biyu da dawowarsu, bawani uwar gayya akaiba, maƙwaftane sai kuma makusantansu da dai wanda baza’a tasaba.
         Tun safe su Ummi basu zaunaba, dan shirye-shiye suketayi na abincin da za’aci da sauran kayan maƙulashe Zuwa ƙarfe biyu na rana iya waɗanda aka gayyata suka fara isowa, harda Hajiya Momcy itada Buhayyah da tazo hutu, yaukuma shine karon farko da zasu haɗu da Ummukulsoom a gidan, dan duk zamanta a gidan hajiya jamila bata taɓa zuwa ta isketaba.
       Zuwa kusan Uku saiga Inna harira tare da Aziza, sam Momcy bata wayi Aziza ba, kasancewar itama ta kara girma yanzu, sannan ko acan da bawani farin sani Momcy tai mataba, tunda kota shiga gidan wajen Ummu ba sakar musu fuska takeba.
      Aziza ɗakin su Ummu ta shige inda mai ƙwalliya take shiryasu.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

               “Attahir ka takurama rayuwata fa da yawa”.
      “kaine kaja na takura makan ai Ajiwa, katashi ka shirya Please, 4pm fa za’a fara walimar nan, gashi kuma har 3:12pm yaushe ka gama shirinka har muka tafi dan ALLAH,  a dai gaban Abba ka amsa zakaje balle yauma ka shikama mutane rashin arziƙinka daka iya  kaƙi zuwa”.
      Banza yay masa yaƙi amsawa, shi yama rasa wane abune ya shiga kansa harya amsa zuwa kd a weekend ɗinnan, da ba’a takura masa da wannan kayan takaicinba.
      Miƙewa yay yashige bedroom ɗinsa yabar Attahir kaɗai a falo.
     Gwalo Attahir yayma bayan Amaan yana faɗin ɗan rainim wayo sai kaje dai insha ALLAH.
      Shidai baisan yanaiba, kasancewar bai wani jima da wankaba yasashi ƙokarin shiryawa, harya ɗakko ƙananun kaya saikuma ya maida yana jan ƙaramin tsoki, Dad yasha masa gargaɗi saka manyan kaya a duk lokacin da irin wannan abun ya taso, kansa ya dafe yana mai tsirama kayansa idanu, shi yama manta rabon da yasakama jikinsa manyan kaya, dama sai in zaije Ajiwa ne kokuma ranar juma’a, saiko in tafiya ta haɗashi da Dad dole, yana shiri yana kuma ɓata fuska saikace dole.

       Kamshin mayen  turarensa ne ya saka Attahir ɗagowa ya kallesa, a hankali ya furta “Masha ALLAH a saman laɓansa saboda ganin ƙyawun da Yaa Amaan yay masa, yau dai kam ya fito a asalin bahaushensa ɗan asali ba sojan Nigeria ba.
      Sanye yake cikin shadda gizna ƴar gaske kalar bulu mai duhu, ɗinkin zamani dogon wando da riga mai gajeren hannu, kasan cewarta babu wani tsawo, kaɗan rigar ta wuce ɗuwawunsa, ɗinkin ya zauna masa ɗas dai-dai da halittarsa, yayin da ƙyawun haiba da kwarjinin musulinci ke yawo bisa kamilalliyar fuskarsa ma’abociya tsare gida.
     Hularsa zanna ce a hannunsa ko kari bai mataba, sai agogon fata baƙi da yake koƙarin ɗaurama tsintsiyar hannunsa, ya sake tsuƙe fuska saboda kar Attahir ya tasashi gaba da tsiya kamar yanda ya saba idan yaga yasa manyan kaya.
       Fahimtar hakan da Attahir yayine yasashi yin ƴar dariya yana mikewa, “Oh ALLAH, Ajiwa ina roƙon ALLAH yasa kar wankannan naka ya tafi a banza, ALLAH yasa yau dai kayi kasuwa wata ta kyasa, mun gaji da zawarcin dakakeyi wlhy”.
       Idanunsa ya lumshe ya buɗe akan Attahir tareda ciza lip nashi alamar zan kamakane.
      Attahir yakuma sanya dariya, “To miye na fusatar?, kowadai yasan kai bazawarine yanzu wlhy tunda ka taɓa aure malam”.
      Ƙin kulasa yay ya nufi hanyar fita yana gyara karin hularsa, Attahir ya kwashe da dariya, yasan ya kaisa maƙura shiyyasa yagaza bashi amsa, shika ɗaine ke iya taɓa Ajiwa fiyema da haka a zauna lafiya, dan suna matuƙar ƙaunar juna, shikaɗai yake iya sanin damuwar Ajiwa ko sirrinsa, kamar shima Ajiwan ne kawai ke iya sanin nasa sirrin da damuwar.
     Fitowa yay shima dan yasan yanda yakaisa bango kaɗan daga aikinsa ya tafi ya barsa a gidan. Ilai kuwa, iskewa yay isa na ƙokarin buɗe masa mazaunin driver alamar shinema da kansa yau zai tuƙa motar, abinda kakan daɗe bakaga yayiba.
     Buɗe gefensa yay da sauri ya shiga.
    Amaan ya Kashe Motar yana kallon Attahir cikin harara, “Malam kasanifa bazan tuƙa ƙaton banza ba”.
       “Kam bala’i Ajiwa wai nine ƙaton banza?”.
      “Inba ƙaton banzaba uwar miye? Dalla fitarmin a mota kaje ka hau taka da kazo a ciki”.
      “Anƙi a fitan, idan kaga dama ka zubar dani a hanya bazawari kawa…..”
     Naushin ya kawoma fuskar Attahir yay saurin kaucewa yana dariya, “Tab yi haƙuri mazan fama, miyay zafi zaka juye fushin gwairantakar ka a fuskata kaima matata asara da amaryar dazan ƙaro”.
      “Mtsoww banza na mamajo”. Amaan yafaɗa yana tada motar.”
         “Uhm babu komai, nadai fi bazawari tuzuru mara aure mai kwannan shago da filo a ƙirji”.
      Wani lalataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, Attahir na latsasa yanda yaso, shi kaɗaine kemasa irin hakan baiji komaiba, saboda tsantsar ƙaunar da yake masa a rayuwa, bai sake kulashiba har suka ɗau hanyar gidansu Attahir ɗin, saima karatun Qur’an daya sanya a motar.
    Hakanne yasaka Attahir shima yaja bakinsa yay shiru yana sauraren karatun.
     Har suka iso gidan bakinsu bai saɓaba, kasancewar harabar gidan babbabace sai basu ajiye motar a wajeba suka shige ciki…

★★★★★

        Su Ummukulsoom kam suna ɗakinsu, duk hidimar tarbar zuwan baƙin da akeyi basu fitoba, sunsha ƙyau itada Bily cikin golden color ɗin gown ta Material, ɗinkin ya zauna musu a jiki ƙwarai da gaske, ɗan kwalinma da aka naɗa musu akai golden, kai komai nasu kalar golden ne, danma ƙiri-ƙiri Ummukulsoom ta hana ai mata kwalliya mai yawa a fuska, hakan yasaka itama Bily cewa ai mata ƴar dai-dai, amma hakan bai hanasu yin ƙyawuba sosai.
          Ƙyawun dasuka shane ya sanya Aziza dagewa tanata zuba musu hotuna a waya dukda Ummukulsoom nata kaucewa bataso.
        “Waike Ummu mike damun kankine? Dalla malama ki tsaya na ɗauki hotuna son raina?”.
     Harara Ummukulsoom ta zuba mata, taja gyale zata yafa Bily ta riƙe, “Malama wlhy baki isaba, dagani harke babu wanda zai saka wani gyale”.
        “Amma dai bily sanin kankine bazan iya fita hakaba ko?”.
      “To sannu matar liman, aiko dole ki iya, naga bawani taron maza bane balle kice, daga iyayenmu sai yayyenmu sai ƙanne da ƙawaye…….”
      Kafin Ummu ta bata amsa tajiyo Ummi na kiranta, dan haka ta sakarma Bily gyalen tarefa yin ƙwafa ta fita tana amsawa.
       “Woow autata kece haka kamar zan kaiku gidan aure?”.
     Hannu Ummukulsoom tasa ta rufe fuska tana faɗin “Kai Ummi”.
      “ALLAH kuwa kin ganki kuwa kamar na sace na ɓoye”.
     Kuma rufe fuskar tayi tana dariya ƙasa-ƙasa, Ummi ta rungumeta tana kuma yaba ƙyawun da Ummukulsoom ɗin tayi, yarinyar akwai sura mai ƙyau, hannunta ta kama suka nufi ɗakinta.
     Sarƙoƙine masu ƙyau da abin hannu guda biyu a kan gadon da Ummi ta ajiye, ta zaunar da Ummukulsoom gefe tana nuna mata, “Ummuna zaɓi wadda tai miki anan”.
    Cike da tsatsan so da ƙauna Ummukulsoom ta kalleta, tuni wasu hawayen farin ciki sun taru mata cikin fararen idanunta, a hankali tace, “Ummi mizan saka muku dashi ku tabbatar daku na dabanne a zuciyata da rayuwata, Um……”
     Cikin ƙatseta Ummi ta ɗaga mata hannu, “Ki ɗaukemu matsayin iyaye kawai ya wadatar damu Ummukulsoom, karna sake jin makamancin wannan a gareki kinji, inajinki araina kamar yanda nakejin su Bily, inhar bazasuyi tunanin mana ramako da haihuwarsuba kema karki taɓa tunanin yin hakan, tsakanin iyaye da ƴaƴa babu ramako sai jinƙai”.
     “Hakane Ummi, ALLAH yay muku sakamako da Aljannah, yabamu ikon muku biyyaya da jin ƙanku”.
     “Amin ya rabbi dear, wacce kika ɗauka na saka miki?”.
      Ta gabanta kawai ta nuna, dan sarƙokin duk sun haɗu, babu wacce tafi wata.
    Ummi da kanta ta sakama Ummukulsoom sannan ta fita ta kira Bily itama, tuni suka ƙara haskawa da wani mugun kyau, ga turare da Ummu ta kuma feshesu dashi tana ƙara gwarzanta ƙyawun da sukayi.
     Hanasu fita Ummi tayi tace su zauna a ɗakinta tana zuwa.
    Da to suka amsa mata, suka zauna suna ƴar hirarsu da Peace a waya suna bata labarin abinda ke faruwa, itako sai jaddada musu take ai mata video ɗin komai a tura mata.
   Sunata mata dariya kuwa.

      Duk wanda ya dace ya iso yazo, gidan yacika da ƴar hayaniya kaɗan musamman ta ƙananun yara dake wasa.
   Hakan ne yasaka Amaan jin bazai iya zama ba a wajen taronba, dama tunda suka iso yana falon Attahir zaune, sai yanzune suka fito, dukda kowa ya nemi mazauni fitowarsu Ummukulsoom kawai ake jira dasu Dad sai yaki zama.
       
     Ummi da kanta tazo ta fita dasu Ummukulsoom, nanfa kallo ya koma sama, kowa sai maimaita masha ALLAH yake a ransa, Momcy da zuciyarta ta gama narkewa akana ƴammatan da suka gama haɗuwa ayyanawa take a ranta lallaifa Fodion ta ya samu matar aure acikin waɗannan carkwaɗa-carkwaɗan ƴaƴan, yanzune zatai masa cikakken aure na ƙwarya tabi ƙwarya tamkar yanda mahaifinsa yay mata gatse.
      Inda aka tanada dominsu suka zauna.
     Zaid daya cika fam da kishi akan Ummukulsoom ne yay addu’ar buɗe taro, yau itace ranar da yaci burin sanarma Ummukulsoom sirrin zuciyarsa na tsawon shekaru biyar da wasu watanni da yaketa dako.
       Ita kanta Ummukulsoom jitai dukta takura saboda kallon da samarin abokan su Yaa Zaid ɗin ke musu na ƙurulla, sai faman bankama duk wanda suka haɗa ido harara takeyi, itafa gaba ɗaya harkar soyayya ko samari haushi suke bata yanzun.
     Aziza ce ta taso a nutse ta kawo mata waya da Baba yay kira, danshi bai samu zuwaba yana ɗilau.
    Karɓa Ummukulsoom tayi ta miƙe domin keɓewa gefe guda ta amsa.
      Tacan baya sashen Yaya Attahir ta nufa, dan daga canne kawai bazaka iya jin hayaniyarba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button