NOVELSUncategorized

A GIDANA 1

In the name of Allah the most Beneficent the most merciful.
Praise be to Allah lord of the words.
The beneficent the Merciful.
Master of the Day of judgement.
Alone we worship;Alone we ask for help.
Show us the straight way
The way of those on whom Thou has bestowed the Grace, those whose portion
Is not wrath, and who do not go astray.聽聽 Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku daukacin masoyana, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yana lafiya, musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, masu ciki Allah ya saukesu lafiya, wadanda ke neman haihuwa Allah ya basu, masu neman aikin yi Allah ya taimakesu yasa su samu Ameen suma Ameen.
 _Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen….. lol duk da nasan ke ko kai ka fada………._

  Dafatan za’amin uzurin jina shiru da akai馃槃

_Sai dai dan Allah inaso mai karatu yamin uzuri akan wannan littafin bazan samu damar yin posting kullum ba saboda wasu dalilai._

Nagode馃グ

馃崁 *A GIDANA*馃崁

*_Na Ayusher Muhd_*

 *Shafi na Farko*

Da sauri ta gama shafa hoda sannan ta dau dankwalinta ta daura, agoggo ta kalla sannan ta jawo jakarta da sauri, ta bude wardrobe ta dauko mayafinta ta rike a hannu ta fito.

 Kitchen ta nufa dan tasan yana ciki, tana shiga ya juyo ya kalleta yace “Honey an fito?”

 Rugumeshi ta matso tai tace “Yau wani irin bacci ne ya kammani dakyar ma bude idona.”

 Murmushi ya mata sannan ya sumbaci kuncinta yace “your tea.”

 Dauka tai ta kalleshi sannan ta sumbaceshi itama tace “Thanks love.”

“Kin manta ni zan kaiki?”
“Oh! Ashe fa na sallameshi.”

 Kai ya girgiza yace “Honey a rage fada, dan Allah drivers nawa kika kora?”

 “Ka zauna zani da kaina.” Ta fada tare da juyowa, da sauri ya riko hannunta yace “na manta sune basaji.”

 Harararsa tai tace “wato ni uwar fada ko?”

 “Nooo inji wa? Yanzu na dau mataki?”

 Murmushi tai tace “ni ka bari na tafi da kaina yafi sauki.”

 Key dinsa ya dauko wanda ke saman fridge yace “muje.”

 Falo suka fito hannunsu rike da juna, Goggo suka gani zaune tana kallo a falan.

 Kusa da ita ta karasa tace “Goggo ina kwanan mu?”

 Goggo ta kalleta tace “ni jiya mantawa kikai kince zaki bani kudin anko?”

“Oh na manta, amma ni Goggo wai wani anko ne ku manya daku?”

 Fuska ta hade tace “ba sai kin fadamin magana ba, in bazaki bani ba kawai kice bazaki ban ba, fadar maganar na menene?”

 Kallan agogo tai ganin lokaci na wucewa tace “zan bashi sai ya kawo miki.”

 Da sauri tai gaba “ke wlh Goggo, ina laifin ki bari sai ta dawo? Bayan na fiki bukatar kudi yanzu.”

Harara ta maka mai tace “wannan damuwarka ce, kuma wlh ka kawon kudina yanda aka baka.”

 Binta yai da gudu, tana tsaye gaban motarshi yai saurin bude mata sannan ya zagaya ya shiga gun driver.

 Yana zama ya tada motar yaja suka bar gidan.

 Mai gadin daya bude ta kalla tace “zan turama kudi kaba mai gadi nashi naga wata yazo karshe, sai kaba Goggo na ankon, dan ko tambayarta ban ba nawa ne.”

 Yai saurin cewa to, kallansa tai tace “ka cinye kudinka ne?”

 Kallanta yai sannan yadan sosa keya, ajiyr zuciya tai sannan tace “zan turoma dan dama anyi albashi, sai dai Honey plz adan rage kashe kudi.”

 Kallar tausayi yai yace ” sry Honey.”

 Murmushi tai ta riko hannunsa da hannunta dayan hannun koma ta dan kurbi tea dinta sannan ta sakeshi ta zuge jakarta ta dauko wasu takardu tana dubawa.

 Kallanta yai yace “in kaka nustu kina aiki you look soo……”

 Kallan data masa ne yasashi yin dariya ba tare da ya karasa ba, tace “Honey a nemo wani driver din.”

 Ajiyar zuciya yai yace “wannan karan bari muga wanda zamu samo wata nawa zaiyi.”

 Kallansa tai tace “zaka fara ko? Wannan sai ya shekara 2 zuwa 3”

 Dariya yasa yace “muna fata, amma indai wannan Honey dince hmmm.”

 Takardun hannunta ta cigaba da dubawa hakan yasashi yin shiru.

 Suna isa yai parking, kallansa tai tace “bari na turama yanzu yanda zaka cirar mata nata dana mai gadin.”

 Yace to.

 Nan ta dau waya ta tura mai kudi sannan ta dau jakarta ta fito, harta kusa shiga taji ya kirata, juyowa tai ya taho da sauri rike da tea dinta ya mika mata, thanks ta fada tare da nuna cup din alama ta amsa ta gode.

Ciki ta shiga, tana shiga cikin bakin kofar ta hade fuska tamau, duk inda ta wuce gaisheta sukeyi tana amsawa tana wucewa.

 Tana shiga office dinta ta ajiye jakarta da tea din sannan ta juyo ta fito, gun program din ta fara shiga, kallan masu aikin gun tai wadanda ke kokarin ganin komai ya tafi daidai tai tace ” acanza wannan background din is too light.”

 Da sauri yace “okay.”

 Kallan jikin camera’s din tai kafin tace “meye hakan? Sau nawa zance a rage contrasts din nan?”

 Da sauri yace “am sorry, yanzu zan gyara.”

 Dan ajiyar zuciya tai sannan ta duduba hasken light din gun sai da ta tabbatar komai yayi ta kalli agoggo sannan tace “is live so you have to be extra careful.”

 Da sauri sukace okay.*********

聽 Da sauri ya fito daga soronsa ya fita waje, dan yanda ake kwalla sallama sannan daga jin muryar ya fahimci wanene.

 Dan dattijon na ganinsa ya murtuke fuska tamau ya kalleshi rai a bace yace “Khalid karka batamin rai kar kuma ka bata min lokaci bani kudina.”

 Khalid ne ya kalleshi yace “Malam Mamman dan Allah kayi hakuri, ga dubu daya dazun nan aka biyani kudin fenti, gobe insha Allah…….”

 Dubu dayar ya amsa yace “karfa ka maidani dan iska, nan nan ubanka yai hatsari kazo kamar zakai min kuka na ara maka dubu goma ka kaishi asibiti yau wata hudu kenan amma haryanzu dubu biyar ka bani da wannan ta yau kenan, nifa shi yasa banasan harka da matsiyata wlh, ubanka yaki barinka kai aikin noma wai shi a dole sai kayi boko, to dakagama bokon uban me ka tsinana? Uban me kake dashi? Dubu goma ta gagareka biya a wata hudu? To wlh ni bazan dauki iskanci ba.”

 Khalid yace “kayi hakuri insha Allah zuwa karshen watan nan zan hada maka.”

 Tsaki yaja sannan ya wuce yana tafe yana masifa.

 Shiru khalid yai sannan ya wuce ciki.

 Mahaifiyarsa na tsaye a tsakar gida yana shigowa ta matso tace “Malam Mamman ne ko?”

 Murmushi yai yace “eh amma bakomai Umma, ina Asiya? Ta biya kudin makarantar dana bata jiya?”

 Tace “ta biya, haryanzu ba labari?”

 Yace “Karki damu Umma insha Allah zan samu aiki.”
 Idanunta ne suka ciciko tace “shekara 4 kenan da gama karatunka, sai dai haryau babu labari sai uban wahalar siyan form kake kana zuwa yin jarabawa.”

 Murmushi yai sannan ya danyi gaba yace “kiyi tamin addu’a, lokaci ne.”

 Kallan tausayi tamai, ciki ya shiga inda mahaifinsa ke kwance ba lafiya, saboda hatsarin motar dayai wanda yasa kafarsa daya ta samu matsala, ya dade yana sana’ar tokin mota sai dai lokaci daya tsautsayi ya hau kanshi komai ya zama labari.

聽 Kusa dashi yaje yace “Abba kanasan wani abu ne? Dan zan wuce gun sana’ar mu ne.”

 Hannunsa ya riko yace “Allah ya taimaka, in inasan wani abu zan sanar da mamanka.”

 To saina dawo.
 Abinda ya fada kenan ya mike.

 Abba yace “adawo lafiya Khalid.”

 Fitowa yai daga dakin ya kalli Umma yace “na wuce.”

 Wayarsa ce tai kara ya dauka da sauri, Salmanu! Ya?”

 “Kana ina?”
聽 “Ina danbatta ya akai?”

Salmanu yace “zaka samu zuwa kano yanzu? Dan wlh wani aiki ne muka samu gidan akwai maiko, kai sauri kazo.”

 Da sauri Khalid yace “turomin address din gani nan zuwa.”

 Nan ya kashe wayar yao waje da sauri.

 Jakarsa kawai ya dauka a soro ya fita, yana zuwa ya samu mota ya hau ya nufi kano.


**********

A bangaren Adamu kuwa yana ajiyeta yai wata yar kara tare da duba account dinsa, gani kudi yasashi yar taka karamar rawa daga zaune, da sauri ya juya kan mota ya nufi Atm, yana zuwa yaciri kudin Goggo da za鈥檃 bata dana mai gadi, sannan ya ciri dubo goma yasa a aljihu, kida ya saka a motar yana tafe yana kada kai, yau akwai jin dadi a majalisa.

  Jin dadin yanayi yasashi kawai yai ta dan yawo a gari, nishadi kawai yakeyi ji yake duk duniya ba wanda ya kaishi jin dadi.

 Tsayawa yai yana kallan wanda ke kokarin tsalaka titi.

 Fuskar sa ya kara kallo sai dai ya tsallaka titi, da sauri yaja mota ya nufi gefen titi yana binshi.

  Horn din motar dayajine ya sashi dakatawa, juyowa yai cikin mamaki dan dai ba tare hanya yai ba.

 Juyawa yai zai cigaba da tafiyar sa yaji ance 鈥淒anbatta.鈥�

 Cikin mamaki ya juyo, bai gane mai maganar ba hakan yasa ya dan matso kadan.

 Hannu ya daga mai tare da nunashi yace 鈥淒anbatta kaine wlh.鈥�

 Khalid ya kalleshi yanzu kam ya ganeshi cikin mamaki yace 鈥淎dam?鈥�

 Dariya Adam yai yace 鈥淒anbatta cinye duu daga ina haka?鈥�

 Yace 鈥渄aga danbatta saukata kenan.鈥�

 Shigo na karasa dakai.

 Kallansa yace 鈥渒arka damu yanzu zan nemi taxi ko bus.鈥�


 Dariyar dake neman kofcemai ya kara dannewa yace 鈥渟higo dalla.鈥�

 Ganin suna bata lokaci yasashi zagayowa ya shiga.

 Adam ya kalleshi yace 鈥渋kon Allah, kwaro ashe da raban zan ganka.鈥�

 Ran Khalid yadan soso sai dai bai nuna ba yace 鈥渋nasu Zakar?鈥�

 鈥淪una nan lfy, sai dai duk yanzu kowa hidimar gabansa yakeyi, kasan yanzu Zakar yana aiki a kaduna, Mansir kuma yana aiki a Abuja.鈥�

 Khalid yai yake 鈥渕asha Allah.鈥�

 Adamu ya kara kallan jikinsa yace 鈥渒waro ya? Kaifa? An fara aiki? A wani asibitin ko babban company?鈥�

 Khalid ya kalleshi yace 鈥渕e kake nufi?鈥�

 Adamu yai dariya yace 鈥渕e nake nufi kuwa? Kawai dai naga ne kai jarabawarka bazata wahalar dakai ba, duk fa shekararmu kai kadai ne ka fita da A class kaga kuwa ai kai sai babban company.鈥�

  Adamu ransa ya baci, kallansa yai yace 鈥渁i ba wannan bane hujja komai lokaci ne.鈥�

 Kai ya jinjina yace 鈥渉aka.鈥�

 Sannan ya ja mota, shiru sukai kafin Adamu yace 鈥測anzu dai ba aiki kenan kake san cewa ko me?鈥�

 鈥淓h.鈥�
鈥淥h Allah kenan yanda kaci karatu waya taba kawo haka?鈥�
 Kallansa yai yace 鈥渟aukeni anan, anan zan sauka.鈥�

 Nan?

Khalid yace 鈥渆h.鈥�

 Adam yai parking sannan yace 鈥渢o ya? Ko na samoma aiki? Dan ni bana aiki kasan ni banasan wahala sannan jarabawa ta ma dai to, sai a hankali, sai dai matata akwai kudi, tana neman driver ko kana sha鈥檃wa na samoma?鈥�

 Kallanshi Khalid yai cikin mamaki, Adam yace 鈥測a? Baka yarda bane? Wlh bana aiki, sai dai ta ko ina a jiki nake.鈥�

 Khalid yace 鈥渂a laifi.鈥�

 Har ya bude motar zai sauka Adam ya zaro kudi yace 鈥済a wannan.鈥�

 Khalid ya kalleshi yace 鈥渘o, karka damu.鈥�

 鈥淣a manta ashe Mr Right ne, nasan bazaka amsa ba, amma ga numberta in kanasan aikin kamin magana.鈥�

 Numbersa ya rubuta a jikin paper ya bashi.

 Khalid ya amsa kawai ya fita rai a bace.

Adam yana ganin ya fita ya tuntsire da wata muguwar dariya, da sauri ya kira Zakari.

 Nan ya fesa mai, ya kira Mansir shima ya fesa mai.

 Dariya kam yashata har cikinsa sai daya amsa, sai a lokacin ya tuna ashefa baici abincin safe ba……

 Khalid kam yana sauka ya nemi taxi ya karasa inda zaije.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button