NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 53-54

???????? *’YAR SADAKA..*????????

5⃣4⃣&5⃣5⃣


Cikin kuka da tashin hankali mummy ke magana”Shikenan auta kajamana abun kunya’ mezan gani a gidana ni hauwa?
Da gudu ta qarasa dakin mashkur Bako sallama tana surutai marasa Kan gado.ita ta manta da ciwan kafanta sabida tsabar tashin hankali datake ciki.


Maryam ko ta duqufa gurin yiwa nijlah sannu tare da qoqarin yadda Zata gyara Mata jiki,,sedai duk yadda maryam taso taba nijlah’ nijlah taqi bata dama..
Banda kuka da Kiran Kaka babu abinda nijlah take tana riqe mara yayinda taqi Bari Maryam ta taimaka Mata.

Mummy na zuwa ta fara bin jikin nijlah da kallo tana hawaye’  turus tayi ganin jinin dake bin kafan nijlah” haushine ya kama mummy  tayi kukan kura ta chafki wuyanta tare da zubamata rankwashi akai’
Dan ubanki haka Ake Bari zaki dagamin hankali,shegiyar yarinyar kawai me suffar aljanu.

Turo Baki nijlah tayi,,cikin kuka tafara magana,Allah Baba Bari nayi ki tambaya kado ai dai yace Nima Zan haihu gashi kuma cikin ya zube ta fada tana sakin wani kuka danma zuwa yanzu ciwan maran yafara sakinta.

Saketa mummy tayi tana tsaki’ aikin banza yarinya qarama dako kanta bata Gama sani ba yaje ya daukowa mutane wahala,,to wallahi zanga me gyara Miki jiki a gidan nan sedai ki rufe a haka,,Nina godema Allah dayasa bakimin wannan qazantar a falo ba..

Kuka nijlah tasa tana cewa” Dan Baba ki wankemin wallahi bazan iyaba.

Ke Maryam tashi kifita anan kije ki cigaba da aikin Dana saki’
Maryam da karkarwa tace to mummy’
Nan ta fita tana tausan nijlah sedai bata da yadda zatayi,,tana fita ta fada kitchen ta cigaba da aikin ta..

Maryam na fita mummy ta maida hankalinta ga nijlah tana cewa’ to ke kuma me Bari saiki jira Wanda yamiki cikin yadawo kinga Saiya wanke miki,, kafin nijlah tayi magana mummy ta fita tana murmushi.

Falo ta dawo ta zauna Kan kujera  ta dora qafa daya Kan daya tana dariya Saida tayi me isarta kafin tace’ hmmmm gaskiya yaro yarone Banda haka ina wannan yarinyar ta isa ciki har zatayi bari’ Banda hauka irin nata’ to nidai me aikina bazata taba wannan jinin me shegen qarni ba we dai ta jira idan ya dawo yasan yadda zeyi da ita.

Tinda mummy ta fita nijlah ta kife cikin jinin tana kuka,,Banda karkarwa babu abinda jikinta yake’ hakoranta sai haduwa suke da juna suna bada qara kaf kaf kaf,,lokaci guda zazzabi ya sauka a jikinta me zafin gaske….


Gyara Zama mashkur yayi cike da San Jin shawaran da jabeer ze bashi yace’ Uhmn jabeer kenan bazaka gane ba’
Haba mashkur kaima kasani dole ran mummy ya baci kama ci sa’a mummy na Sanka na tabbata da kB ne da tintini mummy ta koreshi a gidanta gaba daya..

Ajiyar zuciya mashkur ya safke Yana cewa’ jabeer nasan da haka Amma yakamata ace kaima Ka fuskanceni’ be kamata mummy tariqayin haka ba duba da yanayin nijlah’ yarinyace qarama idan tana Abu zaka fuskanci batasan komai na raguwa ba Amma duk da rashin wayanta Saida ta gane irin qiyayyar da mummy take Mata’ wallahi jabeer ina tsaran girman nijlah batare da mummy ta chanza Hali ba, ya qare maganar idansa cike da hawaye..

Ido jabeer ya zuba mashkur Yana nazarinsa kafin ya bude baki a hankali yace’ dadina dakai wallahi ragwanta kama mace’ Dan Allah duba yadda Ka bude baki kana kuka saikace mace’ nifa bawai bangane abinda kake nufiba,,na gane sosai sedai in tambayeka?

Inajinka cewar mashkur’ yafada cike dasan tsayar da kukansa!

Yanzu Dama Kai Baka shirya daukar irin wannan tashin hankali ba kaje Ka auro jinsin dakasan mahaifiyarka bata so?

Oh God’ jabeer nasani dole mummy tayi fishi Amma yakamata ta sauko haka sabida nabata hakuri’ to shikenan kacigaba da rarrashinta Zata hakura cewan jabeer.

Ajiyar zuciya mashkur ya safke Yana cewa’ jabeer nifa ba wannan me damuna ba!

Menene kuma cewan jabeer Yana kallan mashkur cike da tausayawa?
Jabeer Yasmeen ce’ narasa yadda zanyi na ajiye soyayyanta na hukuntata akan abinda ta aikata’ dariya jabeer yasa Yana cewa ai bazaka iyaba,,abokina nasankafa dasan Yasmeen har tinani nake akan soyayyarku’ sedai yanzu na kama bakina na rufe tinda gashi kayimata kafi kishiya’ Duka mashkur yakai masa Yana cewa’ pls jabeer muyi magana Ka ajiye zancen wasa’ wallahi Nima banso hakan ba naso raguwa da Yasmeen ita daya kamar yadda take a cikin gidansu sedai kash qaddara ta Riga fata..

Dariya jabeer yayi Yana cewa hhhhhh daga Baya kenan angon nijlah’ murmushi mashkur yayi bece komaiba jabeer ya cigaba da magana” abokina abinda kayi kayi daidai Dan be kamata Ka hukunta Yasmeen da hukunci me tsauri ba,,duba da yadda akayimata kishiya tinkafin ta shigo Dan ma kishiyar kwailace.

Murmushi mashkur yayi Yana cewa eh nidai nace yanzu ya zaayi da maganar nijlah?

Shiru jabeer yayi Yana tinani kafin yace’ mashkur inaga kawai a nemi makaranta me kyau asakata ciki islamiyya da boko..
Girgiza Kai mashkur yayi’ nan jabeer ya Tabe Baki Yana cewa Kai nifa banasan iskanci yazaayi muna magana ta Riga Bani amsa da Kai,, sorry jabeer a gaskiya banasan nijlah tafara haduwa da wasu kawaye tana cikin wannan hali,,nafiso saita fara wayewa kafin ta Shiga cikin mutane’
Sabida me mashkur jabeer ya tambaya?
Sabida ina gudun su hure Mata kunne..

To shikenan kaima kayi magana’ toga shawara ta biyu’ meze Hana mu kaita makarantar matan aure taje can ta koya Zama da mutane tare da wayewa da girki Kai hadda Kula da miji za’akoyamata a ciki.

Murmushi mashkur yayi yace hakan yayi Amma kafin nan Nima inasanta akusa Dani sedai bayan kwana biyu Zata iya tafiya kaga lokacin Nima na Samu sai kuma yakasa qarasawa.

Baki jabeer ya riqe Yana cewa wai kana nufin har rage zafi kake da wannan yar yarinyar’ dasauri mashkur ya zaro Ido waje’ Yana cewa’ ah haba kaga niba haka nake nufiba nafi so Ka samamin malama dazata riqa zuwa har gida tana koyamata kafin biki kaga da an Gama biki saita wuce makaranta.

Murmushi jabeer yayi Dan ya Riga ya harbo jirgin mashkur yace’ to shikenan kwana nawane biki.

3 weeks ya rage Insha Allah’ Allah ya kaimu jabeer yafada Yana tsokalan mashkur.

Harsun Gama hira mashkur yace’ kaga abokina wai kuwa ina Shi Nasir Ka Bani wayansa inasan magana dashi?

Hannu biyu mashkur yasa ya dafe kansa Yana cewa’ Kai Amma ban kyautaba’ wallahi jabeer tin bayan dawowana ban qara waya da Nasir ba.
Nasan yanzu hankalinsa a tashe yake’

Tab Amma wannan iyayenta ba qaramin kasada sukayi ba,,wai kana nufin daga Kai sai nijlah kuka Baro kauyen kankan?
Dariya mashkur yayi Yana cewa da Bello suka hadoni Niko na korashi sabida banaso yazo yaga tashin hankalin da mummy Zata man,,Amma yanzu Zan dauko SIM card Dina nasan Nasir duk inda yake hankalinsa a tashe yake’.

Gaskiya Ka gaggauta kiransa Dan Baka kyautaba’ hakane jabeer Nima banso daukan lokaci me tsayi har hakaba,,abubuwane kawai da suka sha kaina gashi itama yarinyar ta cika rigima’ Kai wallahi har kash…..sai kuma yakasa qarasawa Yana Sosa Kai..

Daga nan suka Dan taba hira mashkur yace’ nizan wuce kaga lokaci Yaja gashi nabar nijlah a daki,,sabida nasan Zan Dade shiyasa ban kaita saban gidaba na kaita gidan mummy…

Gidan mummy fa kace mashkur?
Eh wallahi jabeer can na kaita shiyasa kaga inata sauri ban saki jiki na zauna ba ,,yanzu ma sabida dolene zuwan.

Hakane yanzu dai kayi saurin tafiya sauran bayanin Zan Kira Ka sai muyi a waya.
To shikenan jabeer nagode nan ya miqa masa hannu sukayi musabaha,, har mota jabeer ya raka mashkur Yana daga masa hannu…

Sosai Mashkur ya saki gudu a mota Yana yi Yana adduan samun ta lafiya sedai tindaga bakin get yake jiyo hayaniyar mummy..
Dasauri ya fito a motan ko parking ne Ida gyarawaba ya Shiga ciki,,

Assalamu alaikum

Yauwa sannu da zuwa’ angon nijlah saika qarasa Shiga ciki,ga matarkacan tayi Bari.

Bari kuma mummy mashkur ya tambaya?

Dan gidanku tambayana kakeyi’ Ka wuce kaje Ka gyaramin gida kafin nayi Baki warin jini ya hanasu zama’

Be tsaya jin qarashen zancen ba ya Shiga dakinsa da gudu Yana kwala Kiran nijlah.

Ke Maryam qaramin turaran wuta a dakinan Dan gaskiya yau bazan kwana a wannan gidan ba..

Yana Shiga ya ganta kwance cikin toilet tana fidda numfashi a hankali’ dasauri yaqarasa kusa da ita Yana cewa’ke nijlah meke damunki.

Bata iya magana ba yasa hannu ya dagota jikinshi Yana kallan fuskanta’
Langwabewa tayi a jikinsa shiko ya rumgumeta Yana shafa bayanta, beko damu da jinin daya bata Mata jiki ba,,seda yaji tafara sauke ajiyar zuciya yasa hannu ya dago kanta..

Murmushi yayi yace’Dama kin tabayi ko wannan ne na farko?

Cikin kuka nijlah tace Allah bantabayin Bari ba,,kamanta yammata basa Bari sai matan aure.

Mtssss wai Dan Allah yaushe zaki hankali nijlah?
Dasauri nijlah tace gobe..

Bata qarasa rufe bakiba mashkur yasa hannu ya bige bakin Yana cewa’ Bana Hana idan ina magana kinayi ba,,koni sa’ankine???

Comment & share


*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button