NOVELSUncategorized

A GIDANA 13

Haske Writers Association馃挕

Shafi na Goma Sha Uku
*Jinjina Gaisuwa tare da Fatan Alkairi a Duk Inda Kuke Billy Galadanci da BillynAbdul….May Allah Always Help and Bless You馃グ馃グ馃グ馃グMuch Love*


聽 Cikin mamaki Adam ya kalleta yanda take hawaye ne ya bashi tausayi, yace “Sadiya?”

 Hawayenta ta share tace “Yaya bansan meke damuna ba wannan larura tawa ni kaina na kasa ganeta.”

 Larura?

 Ta kalleshi, zatai magana kenan sukaji alamun bude kofa, da sauri ta ja hannunshi suka bar kitchen din. Store ta turashi, sannan ta shiga tare da barin kofar a bude kadan tana lekawa.
Kuna wutar falan da akai ne yasa ta fahimci wacece, matsowa yai yace ” wacece?”

 Nunamai Nabila dake kale kalan falan tai, yace “to me muke anan? Laifin me mukai muke boyewa?”

Nabila ta kalla wacce ta shiga kitchen nan ma taga ba kowa, tabbas taji alamun magana tana bacci, ganin bakowa ne yasa ta koma daki, tana rufewa Adam ya kalli Sadiya wacce tace “yaya yahkuri ina tsoron me zatace ne in ta ganmu muna magana tsakar dare mu biyu.”

 Yace “ni dake a matsayin jini daya muke ko kin manta ne?”

 Kanta ta saukar kasa tace “na manta yaya, yahkuri.”

 Murmushi yai yace “bakomai, jeki kwanta dare yayi sosai.”

 Kai ta daga alamar to sannan ta juya ta fita, tana fita ya fito ya nufi kitchen ya hau kwankwadar ruwa sannan ya juya ya shige daki ya kwanta.

 Sadiya kam a hankali ta shiga dakin, Goggo nata jan uban munsharin bacci, ta kwanta a inda take kwanciya wato kasa.

 Shiru tai tana tunani, kafin bacci ya dauketa.

 Kamar yanda ta saba karfe bakwai ta gama shiryawa, Adam dake kwance yana bacci ta kalla sannan ta sunkuyo ta sumbaci kuncinsa, bargon ta gyaramai sannan ta dau kayanta ta fito daga dakin.

Sadiya ta gani tana ta wanke wanke tare da gyare gyare a kitchen.

 Cikin mamaki tace “Sadiya me kike haka da safen nan?”

 Nan ta tsugunna har kasa ta gaisheta, Zainab ta amsa tace “amma ke da zaki kwanta ki huta me kike a nan?”

 Murmushi tai tace “Auntu kawai sai na hau kwanciya? Gwara dai na taimaka da wani abin.”

 Zainab ta fara hada tea dinta tana cewa “da sai ki bari in an tashi amma ba da sassafe haka ba.”

 Sadiya tai kasa dakai alamar kunya, Zainab cikin jin dadi tace “nagode.”

 Sadiya tace nice da godiya Aunty.
Zainab ta dau tea dinta ta fita.

 A waje ta ganshi yana goge motar, karasawa tai gun, ganin bai ganta ba yasa ta danyi motsi da kafarta.

 Khalid ya juyo ya kalleta tare da cewa “oh bansan kin fito ba.”

 Inda aka bigeshi jiya ta kalla sannan tace “hannuna.”
 Da sauri ya bude motar sannan ta sasu a ciki, shiga tai ciki ta zauna, sannan ya shiga shima.

 Harya tada mota sai ji tai ance “Ina kwana?”

 Mamaki ne ya kamata wanda har saida tace “dani kake?”

 Baice komai ba ya fita da motar, kallansa tai sannan tace “daga jiya zuwa yau ka canza yanayin da kake kallo na ne?”

 Cikin mamaki yace “name kenan?”

 Tace “gaisuwar ta mecece? Ko dan abinda ya faru jiya yasa ka fara daukata abar tausayi?”

 Jiyai baisan me ma zai ce mata ba hakan yasa yai shiru bai ce komai ba, dauke kai itama tai ta cigaba da dube dubem takardarta.

 Yana san yaji ko number ta sake kiranta amma baisan ta yanda zaice ba, hakan yasashi yai shiru, dan jiya baccin dayai kalilan ne, yana ta mamakin wannan lamari, wato dan ankori mai laifi sai ya nemi lalata ma matar aure rayuwa saboda kawai cikar burinsa na daukan fansa? Lalai bata san me mugun nan ya shirya a kanta ba da……..”

 Jin wayarta na kara ne yasa ya kalleta ta glass din mota, jiyai tace “Nabila!”

 Hakan yasa ya maida kansa titi, daga can Nabila tace “wai Aunty harkin tafi?”
Tace “eh da wani abin ne?”

 Cikin shagwaba Nabila tace “yaufa zamu tafi.”

 Oh my Gosh!

 Abinda ta fada kenan sannan tacigaba ” wajen nawane?”

Tace “bansani ba wlh amma nasan bai wuce rana.”

 Zainab tace “ba matsala zan dawo lokacin lunch sai muyi sallama na koma.”

 Nabila tace “okay in naga an kusa lunch da kaina zan kiraki, nasan inkika shiga aiki mantawa zakiyi.”

 Zainab tai dariya sannan tace “to ki tabbatar kin kira.”
Nan sukai sallama ta kashe wayar, harta danyi shiru sai tace “wajen 12:30 zaka dan maidani gida.”

 Okay!
Abinda yace kenan, shiru tai, har suka isa.

 Suna isa ta fita tai ciki, juyawa yai da motar ya nufi police station, duk da dai yasan a banza zashi amma yana fatan y hadu da nagari.

 Bayan ya shiga ciki ne ya sanar da su wata number yake so su bincika suga na wanene, officer din ya tambayeshi number wacece? Matarka ce ko mamanka? Ko kuma Yayarka ko kanwarka?

 Kallansa yai yace “kanwatace.”

 Yace “wanene ke kiranta?”

 Khalid ya kalleshi cikin jin haushin tambayar ya kai da aka fadama ana san ka taimaka ka nemi me number zaka tambaya wai number waye?

 Ganin yanda Khalid ya ke kallansa ne yasa yace “oh ashe fa haka kace ko?”

 Ran Khalid ya fara baci, daurewa yai yace “eh ga number.”

 Sai da ya gama karantawa sannan yace ” yauwa meye sunansa ma? Sannan a ina zamu nemeshi?”

 Khalid ya kalleshi yace “barshi kawai, dan da alama ba a nan ka dace ba.”

 Ya juya a kufule ya bar gun, Officer ya bishi da zage yana cewa a gidan uwarka na dace? Dan************

 Khalid ya shiga mota rai a bace yaja ya bar gun, waya ya daga ya kira Salmanu, daga can ya daga yace “Khalid.”

 Khalid yace “Salmanu kasan wani a police station? Number nakeso amin tracking.”

 Salmanu yace “bansan kowa ba wlh sai yayan waccen.”

 Khalid yace “wanda suka yaudareka? Basu indai sune.”

 Nan ya kashe wayar ya juya can tv station din, yana isa ana turomai text na interview yana karantawa ya kifa wayar dan yanzu yama daina sa rai.

**************


聽 Goggo tana zaune akan kujera tanacin soyayyen dankali da kwai da Nusaiba ta soya musu, tana ci tana kallanta a tv.

Ita kadai ce a falan dansu Nabila na daki suna hada kaya, Sadiya kuma na wanka.

 Fitowa yai daga daki yana mika, alamar yanzu ya tashi, Goggo ta kalleshi ta tabe baki tare da shan shayinta ta cigaba da cin dankalinta

 Kallanta yai yace “Hajiya Goggo abinci akeci ne?”

Kallansa tai sannan tace “wai kai bakajin kunyar rayuwarka?”

 Kallanta yai yace “me kuma nai?”

 Tace “kalli karfe nawa? Ka baje kana uban baci kamar kasa, ko kunya ma bakaji.”

 Agoggo ya kalla karfe sha daya da kwata yace “to wai Goggo menene dan nai bacci? Kemafa kallan ki kike, kici kisha ki kwanta.”

 Ta harareshi tace “can ta matsema, nidai ina tuna ma ran asabar zaka kaini biki ran lahadi kuma za’ai dinner da daddare.”

 Wata dariya ya saka kafin yace “wai da gaske dinner din zakuyi?”

 Tace “mu kawayen uwar amarya ne meye in munje?”

 Yace bakomai Allah ya taimaka.

 Tace “waccen magen daka kwaso yaushe zaka kaita makarantar ta gama ta tafi? Nifa kasan bansan a takuramin a dakina.”

 Yace “Zainab tace ta zauna adakinsu Nabila insun wuce yau.”

 Goggo ta kalleshi cikin zargi tace “ita da saka sallama gobe meye naka nacewa ta koma can?”

 Yace “bani na fadaba Zainab ce tace saboda ke.”

 Goggo tace “to koma menene ka tabbatar ka sallemeta gobe.”

 Yace to naji, tana ina?

 Tana daki.

 Ta cigaba da cin abincinta.
 Dakin ya nufa ya kwankwasa, daga ciki ta bude.

 Kallanta yai yace “inkinshirya ki fito kici abinci kafin na shirya sai muje.”

 Tace “kai kaci abinci?”
Yace “ba matsala muje ko acan na samu wani abin.”

 Tace “to.”

 Fitowa tai sanye da kayan Goggo wanda sun mata yawa, yace “ina zuwa.”

 Sa sauri ya nufi dakinsu, Goggo ta bishi da ido.
Yana zuwa ya bude drawer din kayan Zainab, kayan da ta dade batasa ba ya dauko guda biyu sannan ya dawo da sauri聽 Goggo ta kara binshi da kallo.

 A bakin kofa ya tadda ita ya mika mata, kallansa tai tace “na waye?”

 Yace “kayan Zainab ne bata sashi saboda ya mata kadan,ki gwada ko zai miki”

 Ta amsa idanunta suka ciciko yace “kar ki fara kukan nan naki.”

 Ta kalleshi tace “Yaya nagode.”

 Juyawa yai da sauri dan shiryawa.

***********

 Bayanta tadan mike saboda dan gajiyar data taso mata sannan ta kalli agoggon hannunta, ganin lokacin ya kusa yasa ta jawo drawer din kusa da ita hoton dake ciki ta ciro, a hankali tasa hannunta ta goge sannan ta kura wa hoton ido, idanunta ne suka fara canza kala da sauri ta maida hoton ta rufe.

 Sannan ta mike da dau wayarta.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button