NOVELSUncategorized

A GIDANA 19

Page 19


 Wani wahalalen kuka ne ya kubce mata toshe bakinta tai tanayinsa, ta dade a cikin dakin nan ba tare da ko fitila ta kunna ba, a hankalu ta taso ta turo kofar dakin ta fito.


 Ba kowa a falan da alama sun shiga yin sallah ne, bangarenta ta wuce tana zuwa itama ta shiga toilet tai alwala.

 Adam ne ya shigo tana kokarin tada sallah, Honey?
Juyowa tai ta kalleshi tare da yin murmushi, takowa yai a hankali zuwa inda take sannan yace “menene?”
Kai ta girgiza alamar ba komai, a hankali yasa hannunsa zai dauka a kan fusksrta, kauds fuskarta tai da sauri tace “ka dawo?”
Hannunsa ya maida ya sauke sannan yace “eh.”
Hijab din ta karasa sawa sannan ta tada sallah, ta dade tana tasbihi kafin ta mike, kan gadonta hau ta kwanta.

 Adam ya kashe laptop din ya matso yace “Honey kuka kikai?”
Bata juyo ba tace “a’a”
Ajiyar zuciya yai sannan ya fara danna mata kafafunta yana cewa “kinci abinci ne?”
Juyowa tai saitinshi a hankali tai wani lalaussn murmushi ta zubamai ido.

 Kwanciya yai daf da ita suna kallan juna yace “Honey?”
Uhmmm

Shiru yai yana tunanin kalaman Sadiya, kallan Zainab yai yace “yaushe kika fara sona? Na dade inasan naji.”
 Murmushi tai har hakoranta suka fito tace “abinda yazo ma kenan?”

Kai ya daga alamar eh shiru tai tana tunani kafin tace “sanda kacemin ka fara sona saboda kudina?”

 Dariya yai sosai harda mikewa ya zauna, tace “Da gaske nake.”
Tsagaitawa da dariya yai sannan yace “yaushe na fadi haka?”

Tace “ka manta? Zuwanka station dinmu na hudu?”
Fuska ya rufe yana dariya yace “lalai Honey, wai dagaske lokacin kika fara sona?”

 Tace “eh”
“Na dauka fa fada zakimin lokacin kinsan a rana kika fara min murmushi?”

 Dariya tadanyi tace “am serious lokacin na fara maida hankali kanka, at least u are honest, nasan bazaka taba yaudara ta ba.”

 Jawota yai ya rungume a jikinsa, murmushi tai tace “kace Sadiya ta koma dakinsu Nabila.”

 Dagota yai ya kalleta, tace “badai ce mata zakai ta tafi gobe ba ko?”

 Shiru yai yana kallanta fuskarsa dauke da nuna jin dadi, tace “ka barta tai 2weeks kaga dai bata taba zuwa ba.”

Murmushi yai cikin gamsuwa…….

************


聽 Fitowa falo yai ya zuba mata abinci, Goggo dake xaune ita ma tana cin abinci ta bishi a harara sannan tace “batada hannu ne?”
 Cikin falan ya shigo rike da plate, Sadiya dake zaune tayi shiru ya kalla sannan ya ce “Goggo to nawa ne.”
Kaine zaka zubo abinci dan haka? Kadaiji kiki gaba gaba ma a kitchen zan ganka kana tuka tuwo.”

 Alama yamata datai shiru yana nuna mata Sadiya, baki ta tabe tace “kunya kake ko me?”

 Haushi ne ya kamashi ya kalli Sadiya yace “Ki koma Dakinsu Nabila da kwana.”
Da sauri ta kalleshi sannan tace “Yaya.”
Goggo ya kalla wacce ke zabgamai Harara kamar idanta zai fado yace “badai ni nace ba Zainab ce.”

 Juyawa yai da sauri, Goggo ta kalleta tace “kikace gobe zaki tafi? Idanunta ne suka ciciko tace “kiyi hakuri Goggo nima goben naso tafiya amma bangama registration dina bane.”

 Shiru Goggo tai kamar bazatai magana ba ta zuba maga ido sai cewa tai “badai bakyasan tafiya bako?”

 Da sauri ta kalleta tace “Goggo!”

 A’a inba haka bane bar maganar, karki faramin wannan hawayen.

 Sadiya tai kasa dakai tana share hawayen.
Mikewa tai ta dauko yar jakarta tayima Goggo sai da safe ta shiga dakinsu Nabila, tana shiga ta cilar jakar kan gado sannan tabi kofar dakin da harara, wannan mata…. tai kwafa.

 Wayarta babba ta dauko ta fara dane danen ta tana chatting…..

 Wajen karfe 12 na dare Zainab na bacci yaji wayarsa tai kara alamar text.
Idanunsa ya bude sannan ya jawo wayarsa, Yaya….
Abinda kawai ya gani kenan, number ya kalla, baisanta ba hakan yasa yai duba log din sa, ganin ya kira wayar yasa ya mike da sauri ya fito.

 Knocking din dakin Sadiya yai a tsorace yana fatan Allah yasa ba ciwo bane ya kamata har ta kasa rubuta mai text.
Nishi yaji daga ciki wanda ya sashi hanzarin bude kofar, tana kwance da vest a jikinta da skirt din dazu, tanata murkusus akan gado.

 Da sauri ya karasa yace “Sadiya lafiya? Meya sameki haka?”

Yai maganar cikin tashin hankali, Bayana yaya bayana zai balle, tana fada tana kuka cikin tsananin ciwo.

 Sadiya tashi kisa riga muje asibiti, dan dagowa tai gaba daya rabin kirjinta ya fito, da sauri ya dauke聽 idansa daga kanta, ya hadiye yawo yace “daure ki tashi muje asibiti.”

Mikewa ya nemi yi da sauri ta sa hannu ta kamoshi, juyowa yai da sauri, tace “yaya ka tausayamun.”

 Yanda idanunta sukai jaa yanayinta duk ya canza ga hawaye datake yi yasa tausayinta ya kamashi? Tace “dan Allah yaya ka bubugamin tsakiyar bayana, dan Allah kafin na mutu.”

 Baya? Ya fada cikin mamaki, luuu tai da idanunta kamar mai shirin suma ta fara wani farfar da idanunta kamar mai aljanu, Adam baisan sanda ya fara bibaga mata bayan ba.

 Can ta saki wani nannauyan ajiyar zuciya, sannan ta rike hannunshi dake bubugawa.

 A hankali ya zare hannunsa sannan ya mike tsaye yace “ya daina?”

 Ta daga kai tace “nagode Yaya.”

 Shiru yai yana kallanta, tace “ya akai?”
“Bakomai” yace sannan ya mike da sauri yace “ki huta.”
Nagode yaya ta fada tare da kara dagowa kirjinta ya kara bayyana.

 Da sauri ya fita daga dakin, yana fita ya furzar da wani iska tare da ajiyar zuciya, shiru yai.

“Ya Adam ina asibiti ciwon baya nane ya tashi.”

 Shiru yai bayan ya tuno wannan kalmar, da sauri ya girgiza kai tare da komawa dakinsu.

 Yana fita Sadiya ta kwanta sosai tare da yin dan tsaki, sannan ta kira saurayinta video call.


*************


 A daidai station dinsu yai parking, kallanshi tai kafin ta fita tace “yamai jikin?”
“Da sauki”

Okay, kawai tace tai shiru dan so take taji ko an sallameshi tunda bai fada mata ba ta ina zata kara tambaya?

 Harta bude kofa yace “yana asibiti, mungode sosai.”

 Juyowa tai ta kalleshi sannan tace “to.”

 Kayanta ta kwasa tai waje.

 Tana shiga taga Ramlatu a bakin kofar office dinta, bata ce mata komai ba ta bude ta shiga, knocking tai sannan tadan tura kofar a tsorace.

 Zainab na zaune tana duba abu a computer din dake gabanta, tea dinta ta kurba sannan ta kalli Ramlatu kadan.

 Shigowa tai jiki a sanyeye tace “Na gama.”

 Zainab ta mata alama data ajiye ta fita ba tare da ta ce mata komai ba.”

 Jiki a sanyeye ta ajiye ta fita, waya ce ta shigo ta dauka, director ne yace “ya maganar daukan staffs din nan? Kinsan na fadamiki zamuyi transfer din wasu zuwa kaduna.”

 Tace “wannan karan ni zan dauki ma’aikata dakaina ranka ya dade, in kuma baka aminceba bazansa baki ba kowa ka kawo.”

 Haushi ne ya kamashi, dan dai duk wani hanyar samun kudi itace ta kawo musu idea din kuma ita ke wucewa gaba amma da tuni ya kori yar rainin hankalin nan.
Zainab cikin gadara tace “mekace?”
Dariya yasa yace shikenan ai yanda kikace hakan za’ai, tace “zan ware wadanda za’akai kaduna.”

 “Ha’a shima ke xakiyi? Wannan ki barshi ni xan ware dakaina.”

Kamar zata ce a’a sai kuma tace “okay.”
Ta kashe wayarta.

 Aikinta ta cigaba dayi ta fito tana duduba programs, editing da sauransu.

Khalid dake zaune ne ya kalli wayarsa, fitowa yai ya nufi cafe, yana shiga ya duba aikin da aka turo, shiru yai yana tunanin yaje test din? Dan yasan koyaje ma ba samu zaiyi ba, sai dai kasan ransa na bashi yakimin ya sake gwadawa komai na Allah ne.


Wata babbar mota wacce kallo daya zaka mata kasan ta jika da kudi ne tai parking ata gefensa kadan, da sauri driver din ya zuge glass din mota yace “bawan Allah a aina gidan Tv din Muryar Arewa yake?”

 Khalid yace gashi can, ya matso yana nuna musu, driver din yace dan Allah in ba damuwa ko zaka rakamu?”

 Am sorry gaba zakai sai kai kwana zakaga sign dinsu.

 Mungode.

 Ya koma yaja motar.

 Mutumin dake zaune a baya ne yai shiru, babban mutum ne, ya rasa meyasa kwanan nan mafarkinta kawai yakeyi, yana tunanin lalai lokacin da zai daidaita tsakaninsu yayi, koda bazata yarda dashi ba yana ganin dolene ya nemi yafiyarta, shiyasa ya nemi su Nabila su dawo dan yana tunanin ganinta, dan mafarkin dayai jiya ya tada mai hankalin sosai wanda yasa yau da dsssafe ya nufo garin na kano.

 Sun isa suka tsaya driver din yace “a aika tazo?”

 Yace “a’a kabarta ta fito naga sun kuds tashi.”

 Hango Khalid sukai ya nufo gun, cikin mamaki driver din yace “Ashe anan yake aiki.”

 Khalid ya wuce ba tare da yace musu komai ba, sai data gama tsara takardar Application na daukan ma’aikata da zasuyi sannan ta fito.

Tana fitowa ta nufi motarta ta shiga, tana rufe kofa driver din nan ya kwankwasa.

 Kallansa tai cikin mamaki tace “Mamman?”

 Da sauri ya gaisheta yana dariya, Khalid ya kalleshi ya dauke kai.

 Mamman yace “Tare muke da Yallabai!”

Yallabai? Tai tambayar jinta banbarakwai.

 Yace “eh yau haka kawai yace muzo yanasan magana dake.”
Juyawa tai ta kalli motar, sannan tace “in aiki ne ya kawoku ku gams ku tafi Allah ya kiyaye hanya.”

 Ta rufe kofa tace “muje.”

 Khalid yaja mota cikin mamakin abinda ke faruwa, suna gaba suna binsu a baya, Khalid yace “koma wanene tunda ya taso yazo ki tsaya ku gaisa ma……..”

 Cikin fada tace “a matsayinka na wa?”

 Mamaki ne ya kamashi ya juyo da sauri yace “me?”

 Tace “amatsayinka nawa kake neman sani abu? Aikinka tuka mota kai abinda ya dameka, tunda shi kazo yi.”

 Wannan kalmar ba karamin batama Khalid rai tai ba, mutuncin abinda tamai ne yasa ya daure sai dai ya juyo ya mata wani kallo.

 Tace “me? Dan mahaifina yazo ganina sai ya zama dole sai naje?”

 Mahaifi? Abinda ya maimaita kenan, cikin bacin rai yai parking.

 A zuciye ya bude mota ya fito ya bude kofar inda take zaune yai wani murmushin bakinciki, ya kauda kai yace “da na dauka nine ban fahimci kyawawan halayenki ba. Tuki nake?”

 Ajiye key din hannunsa yai yace “gashi nan, sai ki nemi wani mai tuken, dan banaji zan iya tuka wacce batasan darajar mahaifinta ba.”

 Ranta ne yakai kololuwa gun baci fitowa tai ta tsaya tace mene?

 Bai tanka mata ba sai gaban mota daya bude ya dau jakarsa, kudin aiki na danai zan turama Adam account number dina.

 Da sauri tace “Dawo nan.”

 Kallanta yai rai a bace ya nufi motar dake gefe zai wuce wanda suma sukai parking.
 Da sauri Dady ya fito ya tsaya gabansa yace “ya akai?”

 Khalid yace “bakomai ina wuni?”

 Dady ya amsa sannan yace “naga ka barta a hanya ne.”

 Kallansa khalid yai tare da yin kasa dakai, Dady cikin sanyin jiki yace “kayi hakuri dan Allah, da alama saboda ni ka ajiyeta, ka tsaya anan zan mata magana, amma dan Allah kar saboda ni ka ajiye aikinka.”

 Shiru Khalid yai jikinsa yai sanyi, haushin Zainab ya kara kamashi.

 Dady yai murmushi yace “na mata laifi ne shiyasa take haka, karka damu.”

 Khalid yai shiru yana kallan Dady ya nufi motar.

 Zainab na ganinshi ta shige cikin mota, zuciyarta cike da al’amari kala kala.

 Bude bayan motar ta daya gefen da take zaune yai.

 Kanta na jikin window bata juyoba.

 Zainab!

 Sunanta Dady ya kira wanda yasa idanunta yin rawa suna neman yin rauni.

 Zainab!

 Juyowa tai cikin fada kasa magana tai sai motsa baki kawai datake yi idanunta suka ciciko….


***************
Goggo ke zaune tana hada jaka, sai zuba kaya take kai kace wani gari zataje.

Sadiya dake gefenta a daki tace “ni goggo sati zakiyi acan ne?”

 Sati kuma? Gobe zanje da safe in dawo da yamma sai kuma jibi muje dinner

 Sadiya cikin dabara tace “ki kwana acan Goggo kinsan kwana da biki yafi komai dadi.”

 Goggo ta kalleta tace “da gaske?”
“Ku zauna kusha hira sannan ku shirya daga can kuje dinner kinga da daddare sai ki dawo.”

 Kallan mamaki Goggo ta mata tace ” ke da bakya magana yau bayanin na menene?”

Sadiya tai kasa dakai tai shiru, Goggo ta kalleta tace “ni lalen da yan mata keyi manya bamayi ko?”

 Sadiya a ranta tace wannan mata, amma a fili tace “sunayi amma sai dai jaa.”

 Goggo tace “to ni ina zani ma gidan lalai babba dani.”

“Indai lale kikeso na iya sai dai ba sosai ba.”

 Cikin jin dadi Goggo tace “haba?”

Eh bandai iya sosai ba amma lokacin a gida ina yima Yayata…….
Ta kai karshen maganar cikin wani yanayi na damuwa.

 Goggo ta kalleta tace “ya akai ta rasu ne?”

 Da sauri Sadiya ta mike tace “Bari na shiga toilet.”

Ta fito daga dakin………

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button