NOVELSUncategorized

A GIDANA 25

{25}

 Duk yanda Khalid yaso yai bacci ya kasa, can ya tashi ya zauna yana nazarin wannan abu dake faruwa, shi kallo daya yana yarinyar nan ya fahimci ba yar arziki bace, ya akai gaba daya idansu ya rufe suka kasa gane wa? Me Adam yake tunani dahar zai kaita gidansa a matsayin kanwarsa? Indai akace kanwarsa kenan mahaifiyarsa da yaji tana gidan itama da ita aka hada baki kenan?


 Haka yai ta saka da warwara haryai bacci, ya fito da safe Umma ta nufo asibitin.
A waje suka tsaya suka gaisa tace “zaka wuce?” Yace “eh.”
Tace “Jiya nida naji kunya? Matarnan daga kai waina sai data sako min dubu biyu a cikin flask din? Ita haka akeyi? Muna godiya ana sake mana abin alkairi.”

 Khalid yace “dubu biyu?”
Tace “eh wlh, dama nasan baka sani ba, ka mata godiya dan Allah, ina ma tsoron sake msta wani abin kar ta sake sako wani.”

To Umma. Haka yace ya fito.
Ya iso da wuri yana fatan ganin Adam dan jin wannan abin.
 Sai dai ba kowa a wajen, Bala ya kalla yace “yaushe Mai gidan yake fitowa?”
Bala yai dariya yace ” ai Alhaji sai azahar daka ganshi inhar ba da dalili ba.”
Khalid yai shiru tare da shiga ciki, Zainab tana gama shiryawa ta fito ta nufi kitchen, tea dinta ta hada yanda ta saba sannan ta fito falo.

 Goggo na zaune tana kallo hannunta rike da cup din tea.
Zainab ta gaisheta, Goggo ta amsa tace “Sadiya yau zata tafi.”
Cikin mamaki Zainab tace “yau kuma? Jiya Honey yace zata sake sati daya.”
A gidan ubanwa zata sake?
Goggo tai subutan baki gun fadar haka, Zainab fuskarta dauke da mamaki tace “Goggo!”
 Murmushi Goggo tai cikin dan dabara tace “a’a gani nai wai ba amfani tanada harkar karatu tazo ta tare anan.”

 Zainab tace “inya tashi duk yanda kukai ya kirani a waya ina sauri ne.”

 Goggo ta dan tabe baki a ranta tace ai kullum cikin sauri kike indai kece.

Zainab ce ta fito dauke da kayanta, sannan ta shiga ta ajiye, ta zauna.

 Ana fita daga gate din gidan text na shigowa wayarta “A haka in aka ganki sai a dauka kinada nazari amma yanzu na san bakidashi, na fada miki abu kinyi watsi dashi ko?”

 Mekenan? Tai maganar a fili.
Khalid ne yace ” mutumin rannan ne?”

 Ya fada hankalinsa adan tashe, a’a bansan waye wannan ba kuma.
 Ta fada tana kallansa, dan parking yai da motar sannan yace “zan iya gani?”

 Shiru tai tana nazari, yace “in baki yadda na gani ba shikenan mu tafi kawai.”
Mikamai wayar tai batace komai ba.
Tundaga text din farko zuwa na yau ya karanta, sannan yai shiru ya dau number ya mika mata.
Kallansa tai tace “bansan waye wannan ba amma nasan komenene sharri yake shirin yi, nasan Adam nasan abinda zaiyi da wanda bazaiyi ba.”

 Khalid ne ya kalleta yana tuno waccen rainin wayan da aka mata.
Kallansa tai tace “me? Baka yadda ba? Abokinka ne barshi dai da san jikinsa amma bashi da wata matsala.”

 Khalid ya juya ya tada mota yace “hakan ake fata.”

 Kalmar tadan tsaya mata sai dai bata sake tambaya ba, har suka isa.

 Tana shiga yai shiru yana nazarin sakon nan da kuma yarinyar nan, tabbas ko za’ace yayi shishigi sai yasan me take a gidan nan.
Number daya dauka ya kira, yayi mamaki dayaji number tana aiki, kenan Zainab bata ko gwada kiran number ba? harta kusa katsewa sannan aka daga.

 Hello!
Jin muryar mace ne yasa ya danne zuciyarsa tare da gwada sa’arsa yace “Razy?”
Number tadan kalla, tana mamaki dan sim din a wayarta yake amma ba kowa yasan dashi ba tace “Yes? Waye?”

 Khalid mamaki ya kamashi yace “me kike tunani kikeyi?”
Sake kallan number tai sannan tace “waye?”
Kashe wayar yai tare da yin shiru yana tunanin abinda ke faruwa,
Raziyya tai shiru tana kallan wayar, wanene?

********
Goggo Zainab na fita ta nufi dakinsu Zainab.
Budewa tai kai tsaye, Adam na kwance rungume da pillow yana sharar bacci.
Dayan pillow din ta dauka ta makamai, a zabude ya farka, kallanta yai yace “Goggo lafiya? Mekike anan?”

“Me kake nufi da kuliyarcan?”
Me nake nufi kamar ya?
Kace bazata tafi yau ba? Uban me zata zauna tama?
Adam ya kalleta yace “zata tafi amma wai ba yau ba.”
Cikin masifa tace “kai bansan iskanci, uban me zata zauna tama? Badai wani abin ya faru tsakaninku ba?”

 Goggo tai tambayar a tsorace, kallanta yai yace “me zai faru?”
Yanda ya bada ansar ne ya kara tsoratata tace “kai bansan iskanci, tashi ka sallameta ta tafi, sam hankalina ya kasa kwanciya.”

 Adam yace ‘naji dan Allah jeki.”
Fita tai ranta a bace sosai.

******

Juya motar yai ya nufi gidan, daga waje ya ya tsaya sannan ya daga waya ya kira Adam.

Adam dake kwance yana nazarin yanda zai sallameta ne sako ya shigo mai, Yaya dan Allah charge nake so kamin ina kitchen.”

 Mikewa yai ya fito, Goggo bata falan da alama wanka ta shiga, kitchen ya nufa ya tsaya a bakin kofa tana fere dankali, yace “ya akai wayar taki ba charge? Ko bakida charger ne?”

 Hannu tasa bayan ta matso ta jawo rigarsa ya karaso cikin kitchen din, rungumeshi tai tare da sakin wata ajiyar zuciya tace “har hankalina ya kwanta, dazu gaba daya battery na yayi low.”

 Dagota yai yace “kar Goggo ta fito.”

 Kiss tamai a baki sannan tai murmushi, duk da gabansa dake faduwa.
Sake mai kiss tai tana neman shiga canciki wayartai kara.
Matsawa yai tareda daukan wayar, yana gyara sautin muryarsa.
Khalid yace “Adam ina waje inba damuwa kazo zamuyi magana.”
Adam cikin mamaki yace “magana? Wacce?”
Khalid yace “saika zo.”
Adam cikin mamaki yace “Khalid?”
Kallansa tai jin sunan daya ambata, hankalinta a dan tashe tace “Khalid?”
Yace “eh wai magana yakeso muyi.”

 Yawo ta hadiya sannan tace “kaje ka shirya bari na kai mai ruwa nace kana zuwa.”

 Kallan mamaki ya mata yace “ruwa?”
Tace “eh wai karyaga ka dade.”

 To shikenan, ya fada sannan ya wuce daki.
Fitowa tai ta dakko wayarta ta nufi waje.

 Khalid dake zaune yana jiran Adam ya hangota ta fito.

 Tana zuwa ta bude gaban motarsa ta shiga.
Khalid bai kalleta ba ya dan duba agoggon wayarsa.

 Kallansa tai tace “me zaka cewa yaya?”
Bai tanka ta ba sannan bashima da alamar kulata, tace “wai dan Allah kai da kake driver meye naka na shiga hurumin dabe shafeka ba?”

 Yanzu kam Khalid ya kalleta, wayarsa ya dauka yai dialing  din  numberta.
Wayarta dake saman skirt dinta ne tai vibration.
Khalid ya kashe sannan ya sake kiranta, kallansa tai hankalinta a tashe, yace “kome kike shirin yi ki dakata dashi, ki koma inda kika fito.”

 Kallansa tai tace “bazan dakata ba wlh harsai naga rayuwar Adam ta salwanta.”

 Kallanta yai kamar zai kulata sai kuma ya fasa, dauke kai yai wanda hakan ya sake bata mata rai, kallansa tai tace “Zainab ce ta saka ka bincika? Me kake tunani in na tura mata wannan video din?”

 Ta fada bayan ta zaro wayarta ta dana video din, bata nuna mai wayar ba sai dai ga nishi nan na an fada kogi ita da namiji, sannan ta dakko pic din da suke rungume a mota ta nuna mai tace “ko na hada mata da wannan?”

 Duk yanda Khalid yaso ya danne abin baisan sanda ya wanka mata mari ba, ransa a matukar bace ya kalleta, itama kallansa tai ranta a bace, zatai magana Adam ya bude kofa cikin mamaki yace “Khalid meta maka zaka mareta?”

 Kallansa Khalid yai sannan ya kalleta wacce ta fashe da koka tare da rike hannun Adam, tace “ya zamuyi yaya? Ya san niba kanwarka bace shine ya maren.”

 Adam ya kalleshi yace “koma menene baikai harka mareta ba, akan wani dalili?”

 Kallansa kawai Khalid yake kafin yace “nasan ko a skul kwakwalwarka bataja sosai amma banyi tunanin toshewar kwakwalwarka takai haka ba.”

 Adam ransa ya baci balle haushin an gwaba mai magana a gaban Sadiya, yace “mene?”

 Khalid yace “da nazo muyi magana ne amma yanzu na fahimci maganar batada amfani, ya tada mota tare da jawo kofar motar ya tafi.

 Adam baki a sake ya bishi da kallo, yace “sai kace motar ubansa.”

 Sadiya ce ta kalleshi tace “Ya Adam garin ya ka dakko shi a matsayin driver? Ko Aunty ce ta dakko shi?”

Yace “nine wlh.”
Tace “Yaya ina ganin kamar…..”
Sai kuma tai shiru, kamar me?”

 Kallansa tai tace “ni farkon zuwana dana gansu a mota ma na dauka mata da miji ne, yaya ina ganin kamar akwai abu tsakani……….”

Wani mugun kishi ne ya fito karara a idan Adam, yace “me kike san cewa? Kinsan Zainab kuwa? Tafi karfin tai abind kike tunani.”

 Ya juya ciki a kufule.
Yana shiga ta daga waya ta kira number “Bash ina san amin photoshop na wasu.”
Turo hoton na gani, tace “kai zaka dauki hoton, zan saita lokacin da zan nemeka.”

 Yace okay.

 Kashe wayar tai sannan ta shiga ciki.

 Goggo na zaune suka shigo kallanta tai tace “ke zoki hada kayanki ki bar gidan nan in ba gidan tsohonki bane.”

 Sadiya ta kalleta tace “ba gidan tsoho na bane ba kuma mai fitar dani.”
Ta shige daki.

 Galala Goggo tai da baki tana kallanta, fuskarta ta girgiza da sauri anya ba mafarki take ba? Meya faru yanzu??

Nace oho ????


*********

Ran Khalid yakai matuka sosai gun baci, meke faruwa? Wacece yayarta? Shiru yai kafin ya dau waya ya kira Salmanu.
Salmanu dan Allah dan jeka gida, akwai littafin da nake rubuta numbers ka dubomin number wani Ziyad a turon.

 Salmanu yace to.

 Wajen minti talatin Salmanu ya turo mai, Khalid ya kira number.

 Ziyad ya dauka daga can bangaren.

“Khalid ne.”

Kwaro? Ziyad yai tambayar cikin mamaki.

 Khalid yace “eh, nace dan Allah da Adam yana budurwane kafin yai aure? Watace tace ta santa shine nake so naji ko karya take.”

 Dariya Ziyad yai yace “saboda haka ka kirani?”

Khalid yace “yahkuri.”

 Ziyad yace “yana da ita, Baby ni yama sunanta na gaskiya???”

 Can yace ahhh Fiddausi, budurwarsa ce sosai, dan tun tana junior akeshan love, waya taba tunanin bazai aureta ba?”

 Khalid yace “ohh ba itan bace.”
Ziyad yace “ita wannan tana da sikila.”

 Khalid yace ayya, Ziyad yai dariya yace “ashe driver man ka koma?”
Wata dariya yasa yace “Adam ya fada mana, waya taba tunanin kwaro zai kare a tukin mota?”

 Kashe wayar sa Khalid yai sannan yace “Sikila? Fiddausi?

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button