NOVELSUncategorized

A GIDANA 26

{26}


 Goggo ta mike cikin mamaki ta murda kofar, sai dai tajita a kulle, bubuga kofar tai tace “Ke fito!”

 Daga ciki Razy tana jinta batada alamar mikewa, Adam dake daki ne ya fito jin yanda ake buga kofa.


 “Goggo lafiya?l

 Kallansa tai sannan tace “so nake yarinyar nan ta maimaita metacemin.”
Metace?”
Ranta a bace tace “kazo ka tattara yarinyar nan tabar gidan nan ko sai ranka ya baci?”

 Kallanta yai yace “zan mata magana gobe ta tafi.”

 Tsaki tai cikin kuluwa sannan tace “kai dai kam wlh anyi soko, yarinya karama ka kasa sallamarta, naga uban abinda kake rikewa.”

Juyawa tai ta koma ta zauna ta dau remote, shiru yai yana nazari kafin ya dau key yai hanyar waje.
Aikin kenan.
Ta fada rai a bace.

 Adam na fita ya kira Ziyad, kana ina?
Ziyad yace “ina gida anjima zan tafi.”

 Nan yace ganinan zuwa.

Gun Ziyad yaje suka fara hira, can cikin hira Ziyad yace “oh ni kwaro ya kiran yana tambayata budurwarka ta da.”

Budurwara? 

“Eh ka manta? Fiddausi.”

 Idanu Adam yadan fito dasu dan sam ya manta da ita, sai an dade in ba da wani dalili bama baya tuna ta.

 Meyace?
Nan Ziyad ya fadamai yanda sukai.

Adam cikin rashin kulawa ya cigaba da hirarsa.

***********
Washegari.

 Sun taho a hanya suna tafe tana waya, daga yanda take wayar zakasan da mahaifinta ne, cikin jin dadi take wayar.

 Khalid dake kallan glass din motarsa ta baya yana kara tantance mai motar dake biya dasu, wayarsa ce tadan yi kara, dauka yai a hankali yace “ka dubo?”
 Salmanu yace “wanda kace na tambaya baisan gidansu ba shima.”

 Cikin rashin jin dadi Khalid yace “okay nagode.”
Kashe wayar yai sannan ya kara kallan motar bayansu, parking yai yana shan kwana, motar daga dan baya itama tai parking.
 Zainab wacce ta gama waya yanzu tace “ina zaka?”
Yace “yanzu zan dawo am sorry.”
Fita yai tabishi da kallo tana leken abinda yakeyi.

 Knocking din glass din motar yai, Bash daya waske dashan ruwa ya bude yana cewa “Ya akai?”

 Khalid ya kalleshi yace “me kake?”

 Bash yai dariya yace “ruwa nake sha.”

 Khalid ya kalli cikin motar sannan ya kalli wayarsa dake gefe camerar wayar a bude take, yace “dan mikon wayar ka.”

Bash ya rufe ruwan yace “yanzu bawan Allah haka kawai ina tafiya kace in baka wayata? In baka kayi me?”

 Khalid ya kalleshi yace “zaka bani ko sai na kira wacce ta saka?” Ya fadi hakan yana fatan bugar cikinsa.
 Bash ya kalleshi yace “Ba ita ta sani ba ni na sa kaina.”

 Kenan sashi akai? Ita? Wacece kenan? Badai wata kuma Zainab ta sakema Laifi ba?

Daurewa yai ya kalleshi yace “bani wayarka.”
Bash yace “wai a kan me zan baka wayata?” Yai maganar yana rike wayarsa.
Khalid ya zagay daya bangaren kafin Bash ya kulle ya shige.

 Wayr ya amshe daga hannunsa sannan ya duba calls.
Razy yaga ansa, mamaki ne karara ya bayyana a idan Khalid cikin tsananin mamaki yai saurin duba photo ganin a camera wayar take da alama hoto aka gama dauka.

 Zainab ce lokacin da take komarin bude mota, mamaki ne ya kamashi ya kalleshi da sauri yace “me kake shirin yi?”

 Bash ya kalleshi yace “me kuwa? Ba abinda nake shirin yi.”

 Shiru Khalid yai ganin Zainab na zaune yasa ya kalleshi yace “koma me kake shirin yi karka kuskura na kamaka kana bina, inba haka ba duk abinda ya biyo baya kaika sani.” Goge hoton yai sannan ya ajiye mai.


Ya bude motar yana tafiya zuwa taso motar yana tunanin meyasa bai goge hoton dake wayar Razy ba? Ko dayake inhar sharrinta ya kai haka ya tabbatar ta ajiye wani hoton a wani gun, meya faru haka? Wacece rayuwarta ta salwanta akan Adam?

 Bude motar yai gaba daya yana tunani, Zainab wacce gaba daya tunda ya fita hankalinta ya tashi ne ta kalleshi tace “wanene? Turoshi akai?”

Kallanta yai kadan me kikeyi gidanki ya zama haka?
Ganin baice komai ba yasa tace “Magana nake.”

 Kallanta ya sakeyi yace “Will you please keep your eyes open?”

 Mene?
Ta tambaya cikin bacin rai, makauniya ce ni ko me?

 Kallanta yai kamar zai sake magana sai yaga in har baisan komai ba yai magana kamar yana neman raba aure ne.

 Ranta a bace tace “uban waye a motar da har zaka fadamin magana?”

Khalid yace “am sorry.”
Ya tada motar, bayan yaga waccen motar tabar gun.

 Ran Zainab yakai kololuwa gun baci dan bakin ciki ya isheta da har ta kasa magana, wannan dan rainin hankali ita zaicewa makauniya ko me?

Da bakin ciki suka isa gida, yana parking ta fito a zuciye ta wuce ciki, ya sani sarai taji haushin abinda yace “amma garin ya suka bar yarinya karama take juyasu haka?”

 Waya ya dauka ya kira number Adam.

 Adam ne ya dauka yace “ya akai?”
Yanda yai maganar ne yasa Khalid yace “ka fito.” Ya kashe wayar.

 Adam ya kalle wayar yace “ka fito?” Sai kace wani danka? Har zai ci gaba da kallan ball dinsa sai kuma ya mike dan yana san jin meya kawo zancen Fiddausi.

 Zainab ce ke gaida Goggo da gida fuskarta a hade, kallan Adam tai batace komai ba ta wuce ciki.

 Gaban Adam ne ya fadi, meya faru? Honey? Sannu da dawowa.
Yauwa Honey kawai tace ta shiga daki.

Goggo ta tabe baki tace “oh ni!”

Kallan Goggo yai tace “ka gama boyewar? Kasan Allah kazo ka kuri magen nan? Dan gulma yau ko ganinta banyi ba daga kai har ita.

Adam yace “ina zuwa.”

 Fita yai tace “au kaima ka iya rainin wayan?”

Adam ya fita Khalid na tsaye a waje.

 Kusa dashi ya karasa fuskarsa a hade, Khalid ko damuwa dashi baiyi ba ya kalleshi yace “Adam bakada hankali ne?”

“Banda hankali?” Adam ya tambaya ransa a matukar bace.

 Khalid ya kare tamke fuska yace “wannan yarinyar daka dauko ka tabbatar ka sallameta yanzun nan in ba so kake ta tarwatsa maka rayuwarka ba gaba daya.”

 Adam a kufule ya kalli Khalid jinyake kamar ya makeshi, mene? Kai wanene da zakace inyi abu inyi? In taimakeka in baka aiki ka nemi maidani karamin mutun?

 Ran Khalid ne ya baci cikin kufula yace “wato kai bakada hankali ko? Banda hauka uban waye zainkawo yarinya gida yacewa matarsa wai kanwarsa ce? Banda hauka da rashin tunani? In kanwarka tazo fa? Taya ma daga ganin yarinya zaka kawota gidanka?”

Adam ne ya dunkule hannunsa cikin kumbura fuska yake kallansa.

 Khalid yace “Fiddausi, a ina gidansu yake?”

Fiddausi? Adam ya tambaya.

 Khalid yace “ita kadaice ko tanada kanwa?”

 Adam ya hade fuska yadan harareshi yace “meya kawo wannan zancen?”

 Khalid cikin takaici yace “ban san Fiddausin ba balle nasan kamanninta amma ka tabbatar bata kama da waccen yarinyar?”

 Hankalin Adam ne ya tashi ya kalli Khalid da sauri yace “me?”

 Khalid yace “bansan wacece ba bakuma ni da masaniya akan meya kawota amma ka bala’in shiga hankalinka, har hotonka rungume ta tana dashi.”

 Idanun Adam ne suka fifito bakinsa na rawa yace “mene?”

 Khalid yamai wani kallo yace “banda rashin tunani taya zaka nemi yin alfasha a gidan auranka? Dan hauka kuma da yarinyar da baka sani ba?”

 Adam cikin tsoro yace “banyi zina da ita ba, tace ba zina bane.”

Wani kallan takaici Khalid yamai yace “da alama kana bukatar komawa islamiya.”

 Harya dau jakarsa zai fita yace “a wace unguwa take? Fiddausin nake nufi.”
Sunan babanta fa?

Adam baki na rawa yace “Basiru.”


 Adam hankalinsa a tashe yace “Naibawa suke yar lemo.” Yanda yai maganar kadai zaka san hankalinsa baya jikinsa.

 Fita Khalid yai ya bar gidan, direct Naibawa ya wuce yar lemo.

 Gaba daya hankalin Adam ya gama tashi dan da kyar ya iya takawa zuwa ciki, dakin Sadiya ya bude.

Goggo ta mike da sauri tace “ina zaka?”

Shiga yai ya rufe kofar.

 Hankalin Goggo a tashe ta sa bakinta jikin kofar tace “Adam ka fito ko sai kaci gidanku anan gun.”

Sadiya dake waya da babbar wayarta shigowar Adam ne yasa ta dan zaro ido.

 Kallanta yai yace “Me Khalid yake cemin?”

Mikewa tai tace “me yacema Yaya?”

Ta matso tana neman kamo hannunsa, hannunsa ya matsar sannan yace “hoton me kika dauka?”

 Ganin tasan kwanan zancen yasa ta ja baya ta zauna akan gado.

 Dama tana jin haushin Bash yace mata bazaiyi abinda ta sashi ba yanzu kuma nan ya bulo? Lalai Kwaro yake ko khalid? To ko kyankyaso ne sai ta saita mai kansa.

 Adam ta kalla wanda yace “waccen wayar fa?”

 Murmushi tai tace “ahhh am so tired! Na gaji da sa mask din da bai dace da ni ba.”

Mask! Ya tambaya yana kallanta.

 Fuskarta ta hade tace “me? Yanzu kana so ka koreni ne bayan kaji abinda yace?”

 Kallanta Adam yai yanda take magana ne sam kamar ba Sadiyan daya sani ba.

 Kallansa tai sannan ta dakko wayarta ta nunamai pic din da video din tace “inka isa kace na bar gidan nan, wlh kana fada ina turawa matarka, tasan wanene kai.”

Gaba daya hankalin Adam ne ya tashi.

Mikewa tai ta zo kusa dashi ta sumbace shi, hannu tasa tana yawo dashi kan kirjinsa tace “in maye yaci ya manta uwar da bazata taba mantawa ba.”

 Gaba daya zufa ce ke zubowa Adam, yace “me kike nemana dashi.”

 Hannu tasa ta shafi fuskarsa tace “kana iya baccin yanzu? Na tabbatar sha’awa bata barinka kayi sosai.”

Adam zufa ke zubo mai gaba daya kansa ya dau wani irin zafi……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button