A GIDANA 24
{24}
Gabanta ne ya shiga dukan uku uku, nutsuwarta ta tattaro ta kalleshi.
Idanunsa haryanzu yana kanta yana jiran yaji me zatace.
Nutsuwarta ta daidaita sannan ta kalleshi tace “Barka, au ina wuni?”
Khalid yace “Sadiya me kike anan?”
Murmushin yake tamai sannan tace “naje yin registration ne shine naji yunwa nazo nan.”
Yanda yake kallanta ne tasan tabbas bai amince ba, idanunta ne suka ciciko tace “Dan uwanane shi bari yazo kaji.”
Tana neman sake tambaya ya bude motar ba tare da ya kula da Khalid ba yace “Raziyyah sorry na koma siyo abu ne.”
Kafa tasa ta haureshi kallanta yai zai sake magana ya hango mutum a jikin window.
Kallanta yai sannan ya kara cuso kansa dan ganin waye.
Khalid na tsaye yana kallansa, Raziyyah hankalinta ne ya kara tashi ta kalli Khalid zatai magana ya juya ya bar gun.
Kallan Jameel tai cikin takaici ta kwadamai jakar hannunta tai cikin takaici ta bar mota.
Raziyyah lemon fa?
Ko bi takanshi batai ba ta nufi motar Zainab hankalinta a tashe.
Ya tada mota yana neman tafiya kawai ta bude gefen driver ta shiga.
Kallanta Khalid yai cikin mamaki fuskarsa a murtuke yace “Get Out!”
Kallansa tai tace “zan fita amma sai na fadi abinda ke raina.”
Khalid bai kalleta ba sai dai yayi shiru.
Hawayenta ta goge tace “Bada wata manufar mukai karya ba na shiga wani haline na neman taimako.”
Ganin bashida niyyar kulata tace “shine Ya Adam ya taimakeni, na tabbatar baka tunanin ni nakai kaina gidan a matsayin kanwarsa ko?”
Dan Allah kayi hakuri Wlh bada wata manufa nazo ba.
Shiru tadanyi a ranta tana cewa wannan dan banzan ko uban me ya kawoshi? Gashi da alama bashida yadda.
Khalid ne ya kalleta yace “am in hurry can you get out?”
Wani takaici ne ya kamata, ta share kwallarta sannan ta kalleshi fuskarta ta canza daga alamar tausayin datai tace “badai Zainab kake neman fadawa ba ko?”
Kallanta yai sannan yai murmushi yace “Oh this is your true self?”
Tace “koma menene banaji kanada hurumi a ciki, mijinta ne ya kawoni dan haka duk abinda ya faru tsakaninmu ne banaji mai tuka mota ya isa yai wani abin, kowa ya…………”
Yanda ya juyo ya buga mata wani kallo ne yasa tai shiru, kasa karasawa tai gani tai ya bude inda yake zaune yazo kofar datake ya bude ya mata alamar da ta fita.
Mikewa tai cikin kufula ta bar gun.
Khalid yaja yabar gun ransa a bace.
Me Adam yake tunani? Me ya faru harya yaudari matarsa ta aure akan ta?
Raziyya kam ranta ne yi dubu gun bacu, cikin kufula tace “wlh baka isa hanani yin abinda na taso domin shi ba, tarwatsa rayuwar Adam dashi kadai na taso har nakai wannan lokacin.
Jameel ta kalla wanda ya fito yana kallanta.
Karasowa tai cikin jin haushi ta mai wani mugun kallo tace “kunyi magana ne a shagon?”
Yace “Razy shiya tambayeni ni bankawo komai a raina ba wlh.”
Kallansa tai tace “bana key din karamin gidan dakai.”
Karamin gida? Cikin mamaki ya tambaya, wani banzan kallo tamai yasa hannu ya ciro yace “me zakiyi?”
Amsa tai tace “ka aikon da takardun gidan, na dau kasona.”
Kasanki? Cikin mamaki.
Tace “mungama daga yau ni dakai.”
Ta juya zata fita, da sauri ya riko hannunta yace “Razy me kike shirin yi? Kinfi kowa sanin bazan iya rayuwa bake ba, sannan sirrinki fa duk na sani.”
Juyowa tai ta kalleshi, tace “danka san sirrina sai akai me? Ni wanda na sani naka fa? Na fadama karna sake ganin ko missed call dinka.” Tana kaiwa nan ta fita daga motar.
Da gudu y fito yace “in na kawo mana wata mafitar fa? Ni inaga ba lalai sai ta hanyar Adam zaki tarwatsa farincikinsa ba, me zai hana mubi tagun matarsa?”
Kallansa tai tace “koma menene ba ruwanka a ciki.”
Adaidaitar datazo wucewa ta shige tai gaba tana maimaita kalaman Jameel, ta hanyar Zainab? Da sauri ta girgiza kai tace mutanen dake karkashinta uban me zasu tsinana.
***************
Haka ya cike application din aikin amma gaba daya hankalinsa na kan abinda ke faruwa, taya Adam zai dauko mace ya kawota?
A haka ya dawo Tv station din.
Lokacin tashinta nayi ta fito rike da kayanta, Ramatu na biye da ita tana bata hakuri tare da cewa “Dan Allah Aunty kiyi hakuri wlh wannan karan ba’a san raina bane, bansan yanda abin yake bane, dan Allah kiyi hakuri, Allah zan sake wani.”
Ko kallanta Zainab batai ba, tunda ta fito yake kallansu, ko ba a gun yake ba kana gani Ramatu zakasan rokonta take, kai ya dauke cikin mamakin wannan hali.
Harta shiga mota Ramatu na bata hakuri amma ko kalla batace mata ba.
Kallan Khalid tai jiki a sanyaye sannan ta share kwallar da ta zubo mata, Zainab ce tace “mu wuce.”
Shiru yai ba kuma alamar tada mota a tattare dashi.
Kallansa ta sakeyi tace “muje nace.”
Kallanta yai sannan yace “magana ake miki, inkin gama sai mu wuce.”
Ranta a bace tace “in banida ra’ayi fa?”
Baice komai ba haka kuma bai tada motar ba, Ramatu ce ta zuro report din cikin motar ta window tace “Aunty plz ki duba wannan.”
Ta juya tare da cewa Nagode.
Tana tafiya Zainab ta hade fuska tamau tace “Umarnina ba umarni bane ko me kake neman maidani.”
Tafiya ya farayi sannan yace garin irin wannan hali gashi can mijinki na miki karya, ya dauka a zuciyarsa yai maganar sai jiyai tace “me kace?”
Kallanta yai ta mirror yace “Sorry.”
Wani takaicine ya kara kamata, sorry? Cikin jin haushi tace “Zagi na kai hala?”
Baice komai ba dan baima san me zai ce ba, ranta a bace tace “Banajin zagi sannan bana shakkar abinda wani yake tunani akaina.”
Tana kai nan ta dauke kai ta maida kanta jikin tablet dinta.
Khalid baice komai ba suka cigaba da tafiya
**********
Motar Adam ta bude ta shiga, zama tai jiki a sanyaye ta kalleshi.
Bai kalleta ba sai dai ya rasa meyasa yake san ya kalleta.
Atishawa tai tare da sa hannunta kan cinyarsa.
Kallanta yai sai dai yakasa zare hannun nata, cikin kulawa yace “bakyajin dadi ne?”
Kallansa tai idanunta ya ciciko tace “ina tunanin tafiya ne da wannan hade ran da kakemin.”
Kallanta yai jikinsa yai sanyi, murmushi tai tare da cewa “bansan me yasameni ba, sai dai da alama na jawoma bakin ciki.”
Da sauri yace “A’a Sadiya, nine zan baki hakuri.”
Hawayenta ta share tace “kai zan ba hakuri yaya nama kiss bada saninka ba.”
Shiru yai ya kasa cewa komai, sai dai gaba daya ganin tana hawaye hasa jikinsa yin sanyi.
Share hawayenta tai tace “can you hug me na karshe?”
Jiyai bazai iya musa mata ba a hankali ya dan matso, jawoshi tai ta rungume tare da sa kuka.
A hankali ya shiga shafa bayanta alamar lalashi, kallan wani a wajen motar tai wanda ke rike da waya da alama hoto yake dauka, Adam ne ya dagota yace “nagode Sadiya, sannan ki yafemin.”
Ajiyar zuciya tai sannan ta kalleshi tace “banasan tafiya yaya ka bari na kara sati daya, ba abinda zanma kallan ka kawai nakesan na dinga yi.”
Kallanta yai hankalinsa a tashe yace “a ina?”
Tace a gidan Aunty.
Gaba daya hankalinsa ne ya tashi karara yace “A gidana?”
Tace “Gidan Aunty.”
Yanda take maganar ne yasashi kallanta cikin mamaki yanda take maganar ba kamar dazu ba.
Kallansa tai tace “am sorry Ya Adam amma bazan iya barinka da gidan ku ba, ko sati sai na kara a ciki.”
Baki ya sake yana kallan ikon Allah, anya Sadiya ce?”
Yace “bangane ba.”
Tace “kasan yaushe rabona da bacci? Kullum mafarkinka nakeyi, ta ina zan iya tafiya da wannan abin? Kabarni na zauna ko na sati daya ne kafin nan na saita kaina sai na tafi.”
Shima gaskiya abinda ke damunsa kenan, ya kasa cireta a ransa, tsantsar sha’awa ce ke yawo dashi.
Hannu tasa akan cinyarsa tace “kaima nasan abinda ke damuna yana damunaka Yaya.”
Shiru yai yana kallanta, tace “bamuyi zina ba yaya, junanmu kawai zamu ragewa sha’awa dan Allah ka barni na kara sati.”
Samun kansa yai da cewa “ba zina bace?”
Da sauri tace “ai baka kusanceni ba”
Kallanta yai tare da dan fito da harshensa kadan.
Murmushi tai ganin komai na zuwa da sauki, gaba daya wasan ya daina birgeta, anya bazata canza sali ba kuwa? Tabi shawarar Jameel.
To amma Zainab ta ina?
Khalid ne ya fado mata arai, tai dan kwafa ganin irin wulakantata dayai………
A haka suka isa gida ko kunya Hannunta nakan cinyarsa shi kuma ya kasa cirewa sai dan sanyi da yakeji.
Suna isa gida motarsu Khalid na shigowa.
Khalid yai parking ya zuba mata ido daga cikin mota ba tare da ya fito ba.
Itama kallansa tai sannan ta dauke kai, da sauri ta taho inda Zainab take ta bude mata tace “Aunty sannu da dawowa.
Kallanta tai tace “Sadiya an kammala?”
Cikin jin dadi tace “Eh Aunty na gode sosai.”
Khalid yana jinta yanzu kam ya tabbatar yarinyar nan yar banza ce, tasan yasan komai amma ko kallansa batai ba?
Adam ne ya karaso inda Khalid yake, Zainab ta kalleshi tace “Honey!”
Cikin sanyin jiki yace “Honey sannu da dawowa.”
Tare suka shiga itada Sadiya.
Khalid ya fito suka gaisa da Khalid, ya amshi account number dinshi, yace “kwaro zan shiga ciki gaba daya banajin daidai.”
Khalid ne yace “Sadiya!”
Juyowa Adam yai da sauri yace me?
Khalid yace “a’a kawai ina mamakin girmanta ne, kasan a skul ka taba zuwa da hotonta kai da ita kana tsokanar Ziyd a class akan matar da zaka bashi ce.”
Adam cikin tsoro da neman waskewa yace “Oh baka manta ba? Ni na manta anyi haka ma wlh.”
Khalid ya kalleshi, Adam yace “ta kara girma da kyau ko?”
Khalid gani yai ma bata lokaci ne sake mai magana kawai ya dau jakarsa da ledar da Zainab ta ajiye dan haushi ko duba cikinta baiba yai sallama da Adam yabar gun….
Suna shiga falo suka taradda Goggo a zaune tana waya da alama cikin fishi take magana.
Yoo dole ki kira ki lalemeni, sanda kuka sa aka hanamu shiga gun rawa fa? Sannan me kika cemin? Cemin kikai mune manya manya, amma meya faru?
Ganin su Zainab yasa tace “na kiraki.”
Kallansu tai tace “kun dawo? Ya naganku tare?”
Ta fada tana hararar Sadiya ta gefe.
Zainab ta gaisheta da gida kawai ta wuce ciki.
Kallan banza ta bita dashi tace “kullum a turbune ake dawowa.”
Raziyya ta kalleta a ranta tace “ko kunya?”
(Nima nace kema ko kunya? Kina mace馃檮 kina abu kamar馃槖)