NOVELSUncategorized

A GIDANA 27

{27}


 Adam ya kalleta cikin tsoro yace “Sadiya.”

 “Tsi tsi tsi ni kanka ne baya aiki ko haka Allah ya halliceka? Har a wannan yanayin Sadiya zakace?”

Adam ya matso kusa da ita da sauri ya zube a kasa yace “na sani bake bace dan akwai abubuwa da dama da kike aikatawa ba a hayyacinki ba, taya daga taimako na taimakeki zaki…….”


“Taimako?” Wata dariya ta sheke dashi sannan ta sa hannu a wuyansa sumbatar sa tai a bakinsa sannan tace ” kule?”

 Kallanta yai yaga hoton da aka dauka ta kalleshi tace “in tura mata?”

 Da sauri ya mike zai warci wayar, mikamai tai tace “ba sai ka fadi ba.”

 Adam gaba daya sai ya kasa komai, Goggo dake wajen kofa ne taji kamar kanta baya aiki saboda abinda kunnenta ke juyo mata, baya tai tara dayin kara wayyoooo Allah.

 Da sauri Adam ya bude kofa Zainab dake kan Sallaya ta idar da sallah kenan ita ma ta fito.

 Zainab ta kalleshi ganin ya fito daga dakin Sadiya, sai dai bata kawo komai ba ta wuce gun Goggo tace “Goggo lafiya? Faduwa kikai?”

 Kallan Zainab tai sannan ta kalli Adam tace “wayyo Allah na faduwa nai!”

 Sannu, Sadiya ce ta fito ta tsaya a bakin kofa tana kallanta, Adam wanda gaba daya tsoro ya kamashi ya kalli Zainab yace ” bari na kaita ciki.”

 Ta kalli Goggo tace “ba sai munje asibiti ba dai ko?”

 Goggo ta zubawa Sadiya ido, kallan Sadiya, Zainab din tai, suna hada ido da Zainab ta fara matsar kwallar tace “sannu Goggona, tsoron matsuwa ma nake.”

 Adam ne ya taimaketa ta mike sukai daki, sai da taga sun shiga daki sannan ta shiga kitchen ta duba flask, ganin taliya yasa ta zuba a plate ta wuce daki.

 Suna shiga daki Goggo ta kwace hannunta sannan ta dada mai wani dundu wanda sai dayai kasa.
Zubewa tai a kasa itama tana kara dukansa tana cewa “wannan wannan ka gama dani ka gama cutata, duk uban kudin dakaci kana makaranta gun sake jarabawa da wahalar da ka samu ban taba jin haushi ba saboda ina ganin ai kayi dacen mata wanda zan fanshe wahalata, yanzu dan hauka ka yadda wannan kuliyar ta kamaka a tafin hannunta.”

 “Wayyo na shiga uku wannan yaron shi zainkarasani lahira.”

Adamu yai shiru yana zube a kasa, idanunsa yana neman kawo ruwa.

 Goggo tace tashi ka kirata tazo ta bar gidan nan yanzu kafin rayuwarmu ta kare dan wallahi bazan koma kauye ba kafi kowa sannin matar nan taka in taji ko minti daya bazamu sake a gidan nan ba.

Adam ya mike jiki a sanyeye duk zafin dukan nan bakai zafin abinda ke ransa ba, dan har ga Allah yana san Sadiya a kasan ransa, yana san ya kasance da ita, yaushe yasan yaudararsa take?

Kallanta yai tana zaune akan kujera abinda kullum a kasa take zama yace “kizo inji Goggo.”

 Wani banzan kallo tamai tace “kace tazo in jini.”

 Baki ya bude yace “mene?”

 Kallansa tai sannan ta nunamai tv, tace “ba a gaban tv take wuni ba? Kace tazo ina kiranta.”

 Tsayawa yai ya kasa ko motsi.

 Zainab ce ta fito deban ruwa, kallansa tai a tsaye sololo.
Matsuwa tai tace “Honey!”

 Kallanta yai yace “Hmm.”

 Ya akai? Jikin Goggon ne?”

 Hannunta ya kama da sauri yace “ba shi bane muje.”

 Dariya tai tace “ruwa zan deba.”

 Shiga daki zan kawo miki ba’asan ana cin abinci ana tashi.”
Murmushi tai cikin jin dadi, Sadiya ce ta kalleta tace “Aunty Yaya na kula dake sosai, irin su Yaya basa cin amanar matansu.”

Zainab ta kalli Adam sannan tace “Shiyasa nake ji dashi ai.”

 Nan ta shiga daki, juyowa yai ya kalleta.

 Kallansa tai tace “wuce ka kiramin Goggo ko kuma Allah yanzu na tura.”

 Juyawa yai sololo ya nufi dakin Goggo ya sanar da ita aiken Sadiya.

 Baki ta bude tace “inzo?” Cikin bacin rai ta mike ta nufi falo zatai masifa.

 A gaban tv ta ganta tana juna wayarta a jiki.

 Cikin zuciya Goggo tace “ke dan ubanki bakiji ina kiranki ba? Yr banza karuwa, wuce ki hada kayanki kafin naci ubanki a gidan nan.”

Bata kula Goggo ba sai data gama hadawa remote ta dauka ta zauna a kan kujera sannan ta danna video dinsu, baka gani sosai saboda da alama a jikin tv stand tasa wayar kafin ya ankara sai dai ga muryarshi nan sannan sanda yana tsaye fuskarsa ta fito, ga nishi da alama ya fada.

Jikin Goggo ne ya hau rawa, hotonsu ta bude inda ya rungumeta a mota.

Bakin Goggo na rawa ta kalleta.

 Adam kam gaba daya ya sandare kai kace itace ne a gun.

 Da sauri Goggo ta kashe socket sannan ta kalleta tace “meya hakan?”

 Sadiya tace “in kika kara cemin karuwa ko kuma nabar gidan nan tabbas zaki tsinci wannan abin a wayar sirikarki.”

 Goggo idanunta ne suka fito cikin takaici ta kara mangare Adam wanda yakeji kamar yai kuka, meye laifina? Daga taimako? Ya fada tare da sa kuka.

 Zainab ce ganin bai kawo ruwan ba yasa ta fito.

 Kallan mamaki ta musu ganin Goggo da Adam a tsaye carko carko ga Sadiya a zaune, sannan Adam
Sai goge fuskarsa yake kamar mai kuka.

 Cikin alamar Zargi tace “lafiya?”

 Adam ya juya da sauri ya nufi kofar fita yai waje.

 Goggo ce ta kalleta tace “fada nake mai ya nemi aiki wannan zaman ya isa.”

 Zainab tace “ai yace yana nema, komai sai Allah yayi, sannan shi kinsan baisan aiki irin namu ko na wahala.”

 Goggo tace “Hmm.”

Wucewa tai ta debo ruwanta sannan ta wuce ciki, sai dai sam tana ganin akwai wani abin bayan fadan aiki, haka kawai Adam bazaiyi kuka saboda maganar aiki ba.

Sadiya ce ta kalli Goggo tace “nima bani ruwa nasha.”

Wa? Ni?

Sadiya tace “me kike a gidan nan banda kallo? Bani ruwa tun kafin na tura.”

 Da sauri Goggo tai kitchen ta dauko ruwa kamar mai shirin kuka, yau meke faruwa da ita? Itakam da alama rayuwarta ta kare.

******

 Duk yanda ya tambaya bai samu ansar komai ba a Naibawa, ganin haka yasa ya fito, ga dare yayi dole sai gidan Kawu ya nufa.
 Shiru yai yana tunanin abinda ke faruwa kafin ya tambayi kansa, ni me nene nawa a ciki? Meye nawa na damuwa? Rayuwarsu ce sun san abinda ya kamata ai ba yara bane su.

 Sai dai sam ya kasa bacci sai juye yakeyi, can yace taimakon datai na Abba na zan rama mata.

 Da sassafe yana sallar asuba ya kara komawa can, sai dai yanzu ma ba wani labari.

*******

Wajen karfe 11 na dare Adam ya dawo, sum ya shige daki ya tura a hankali, ganin Zainab na bacci yasa ya lalaba ya kwanta cikin takaici da dana sanin abinda ke faruwa wanda tunda ya fita yake dana sani.

 Hana kwanciya yaji ta rikoshi, a hankali tace “Honey ka dawo? Ina kaje kai da baka san fitar dare?”

 Idanunsa ya runtse cikin takaicin abinda ke faruwa yace “na fita kawai yawo ne.”
Murmushi tai tace “nace abokinka yai applying din aikinmu, kai haryanzu baka san aikin zirga zirgar?”

 Yace “a’a.” Shiru yai saboda gaba daya bai san magana.

 Kara kwanciya tai a kafadarsa tace “Honey!”

 A hankali yace “Hmm”
Tace “mun shirya da Dady.”

 Baisan abinda take cewa sosai ba kawai yace “Uhm Hmm.”

 Mamaki ne ya kamata, matsawa tai daga jikinsa sannan tace “abinda zakace kenan?”

 “Me nace?”

 Cikin bacin rai tace “bashi.”
Jan bargo tai ta kwanta, Hm hm? Wani ya maidata makauniya mijinta kuma tana fadamai abinda ta matso ta fadamai shine zaice Uhm Hm?

Da safe tana tashi ta fita, tayi mamaki dataga yau Goggo bata fito kallo falo ba.

 Mota ta shiga fuskarta a hade sosai.

 Shikam ko a jikinsa dan gani yake duk matsalar tata ce wani irin rashin kula ne zaice ace bakisan kanwar mijinki ba? Shekara ba daya ba ba biyu ba da aure?


*****

Yau ba wanda yama wani magana har suka kusa isa, haushi ya kara kamata dan ta dauka zai bata hakuri.

Sai da suka kusa isa cikin bacin rai tace “kacemin makauniya sannan bazaka dau lefen ka ba?”

 Khalid na tukinsa kamar bazai magana ba sai yace “in bakyasan ace miki haka ki sa ido a Gidanki.”

A Gidana? Kai waye da zaka ce na sa ido a gidana? 

Khalid yace “niba kowa bane sai dai duk abinda ya faru kisan kece kashi 60 na matsalar.”

 Ranta a matukar bace tace “da alama ka gaji da aikinka”

 Shiru yai bai tanka mata ba.

 Haushi ne ya kamata suna isa ta fita ta banko kofar da karfin tsiya.

 Binta yai da kallo kafin yai ajiyar zuciya, meyasa yake saurin yin fada in tamai magana? 

 Sam ya rasa me yasa ransa ke saurin baci da yanayin yanda take magana, bayan yasan a karkashinta yake sannan ta taimakeshi.

 Idanunsa ya runtse kafin ya ajiye motar ya fito dan komawa Naibawa.

 Yanzun ma baisamu kowa ba yana kokarin juyawa ne ya kalli wayarsa, ganin date din yau ne yasa ya zaro ido da sauri, hannu yasa a kansa cikin dana sani yace “Oh God ashe yaune test din?” Sam ya manta da wanda aka turomai kwanaki.

 Cikin rashin jin dadi ya juya, wanni magidancinya gani kamar bazai tambayeshi ba sai yaje gunsa yace “dan Allah bawan Allah kasan wata Fiddausai?”
Fiddausi? Ya tambayeshi.

Khalid yace “eh tanada Sikila sannan mahaifinta sunan mahaiginta Basiru.”

Shiru yai kafin yace “Tanada kanwa Raziya?”

 Idanu Khalid ya bude kafin yace “kanwa?”

Mutumin yace “ita?”

Da sauri Khalid yace “eh.”

Mutumin yace “shiyasa baza’a gane ba da kace gidansu Raziya ne zasu gane, ita Fiddausin ai ta dan kwana biyu da rasuwa.”

 Kallansa Khalid yai yace “ta rasu?”

 Eh baka sani ba?

Idanun Khalid ne suka fito sosai…….

Ni kaina idona sai da suka fito????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button