NOVELSUncategorized

A GIDANA 28

#OneLove❣

{28}


 Khalid ya daure tsananin mamakinsa yace “kana nufin kanwarta ce kenan?”

 Mutumin ya matso cikin rada da gulma yace “bawan Allah shawara zan baka ka tafi dan mu kanmu yanzu ba wanda yake kula zuri’ar gidansu.”


 Idanu ya dago ya kalleshi yace “mene?”

 Ya kara matsowa har mamaki ya kama Khalid yace “babbar ta rasu, karamar ce Raziyar in santa kake ma ka koma dan…..”
Sai kuma yai shiru yace “baruwana jeka kawai.”

 Khalid ne ya kalleshi, yace “menene dan Allah?”

 Kamar zaiyi magana sai yace “ni dai ba ruwana nayi nan.” Kafin Khalid ya sake magana yayi gaba.”

 Duk yanda yaso ya shirya tunanin dake yawo akansa ya kasa hadashi yanda ya kamata, duk da Adam ace ya yaudari yayarta ne ya auri Zainab baici ace taje gidan matarsa daukan fansa ba, to yayar ma ta rasu? Garin ya?

 Ganin ya kasa gani komai ga haushin baije test din ba kawai yasashi ya juyo dan takaici.

 Zama yai a cikin mota yasa hannunsa akan goshinsa.

Wayarsa ce tai kara alamar text yana dubawa yaga kudi ne yaga ya shigo 20k, ganin sunan Zainab yasa ya fahimci itace.

******

 Shiru tai bayan ta dawo office dinta, gaba daya kalaman Khalid ke yawo a kanta suna kara kona mata rai, meyasa ya raina Adam ne?
 Wani karamin tsaki taja kafin ta ajiye wayarta data turamai kudi tana cewa in bazai iyaba ya ajiye aikin ai ba dole.

*******

 Da kyar takecin soyayyan doya da kwai data gama yanzu, kana kallanta kasan cusawa kawai takeyi bawai dan tanajin dadin sa ba.

 Tv din ma dake gabanta tana kallo ne amma yau batajin shaukin kallan yanda ta saba, ajiye zuciya tai tare da shan tea, tana dagowa daga ajiye cup din taga an kashe socket din tv din.
Sannan tazo gabanta tasa hannu ta dauke plate din datake cin abincin.

 Goggo ta kalleta, Sadiya tace “zubomin nawa sai ki zo ki dau naki.”

 Goggo cikin kufula tace “da alama bakisan me ake kira da tarbiyar na gaba ba ko dayake ke da kika zo daga taimako kina neman ruguza……..”

 Yanda Goggo taga tana kumbura ne yasata yin shiru, bansan tarbiyar ba?
Da sauri Goggo tace “haka nace? Gaskiya bakiji da kyau ba.”

 Sum sum Goggo ta rabe ta gudu ta wuce kitchen tana cewa “kamar zata daken?”
Abincin ta zubo mata sannan ta fito, gani tai ta saki abincin goggon a kasa, baki Goggo ta saki ta matso da sauri.

 Oh zubarwa nai? Bansani ba, ta fada tare da amshe nata.

 Daki ta wuce rai a bace, Goggo ta sake baki gaba daya itakam da alama tazama ita ake taimako a gidan ba sadiya ba.

 Kallan dakin su Zainab tai rai a bace ta nufi dakin, Adamu na kwance yana bacci rub da ciki, haushi ne ya kara tike ta.
 Filo ta dauka ta dada mai, farkawa yai da sauri ya kalleta.
Cikin tsananin takaici da fada tace “har kana iya bacci bayan abinda kaja mana? Ko ince kake neman ja mana? Ka tashi ka kori waccen kedarar ko kuwa?”

 Adam ya kalleta yace “wani bacci bayan sai yanzu ne na samu ina ta tunani?”

 Baki ta tabe tace “tashi maza ka korerta tun kafin ta kashemu da ran mu.”

 Mikewa yai ya shigs toilet tsaki tai cikin takaici ta fito.

Adam yana fitowa daga toilet ya nufi kofar dakinta, hannu yasa a jikin kofar sai dai fargaba ya hanashi budewa, dakyar ya daure ya murda kofar tare da turata.

 Tana zaune daga ita sai vest sai dai yau vest dinma ta dageta sama duk cikinfa a waje yake, wani abu ya hadiya sannan ya kauda kansa gefe.

 Kallansa tai sannan ta dauke kanta ta cigaba da danne dannenta a waya, shiru yai yana nazarin kafin yace “Hmm Sadiya….”

 Bata kalleshi ba hakan yasa ya kara tattaro dauriyarsa yace “dan Allah kiyi hakuri kizo ki tafi.”

 Abincinta kawai takeci kafin ta ajiye plate din ta kalleshi, shakewa nake hadomin tea.

 Kamar zai musa sai kuma ya juya, Goggo na zaune yazo ya wuce da tea, yana bata ta kalleshi tace “fita.”

 Juyawa yai sum sum ya bar dakin.

 Goggo ta kalleshi tace “zata tafin?”

 A hasale yace “tace na fita, duk ba ke kika ja komai ba? Da kin barni na lalabata ai da ba haka ba, amma duk nunawar da kikai kinji me aka ce ba duk shi ya ja halin da muka shiga ba.”

 Mene mene? Wato laifina ne kenan? To ai ni na kawota ba dole ba? Ko kunya bakaji, ni Allah yasa ma baka karasa can ba?”

 Kallanta yai kawai cikin takaici ya juya yabar gidan ma.

 Ranta yakai kololuwa gun baci.


**********

 Idanun Khalid a runtse yaji an bude kofar motar, shigowa tai fuska a daure tamau ta zauna, bai kalleta ba shima sannan baice komai ba ya ja motar suka fara tafiya.

 “Naga kudi sun shigo dazu? “
Hmm
“Thanks.”
Yau har suka isa ba wanda ya tanka, tana isa ta fita daga motar tare da bugo kofa da karfi.

 Fitowa yai ya zubawa gidan kallo yana nazarin meke faruwa a cikin gidan nan?
Jakarsa ya dauka ya fita, yana hanyar danbatta ne ya kira Adam sai dai duk yanda ya kirashi bai dauka ba, hakan yasa ya ajiye wayar.

 Mamaki ya kama Zainab dataga Goggo bata falan, dakin Goggon ta nufa tana kwance cikin kunar rai.

 Zainab ta bude kofar tace “Goggo!”

Goggo ta dago da sauri tace “Zainab kin dawo?”

 Jikin ne?

Tai saurin cewa “a’a kawai banajin zaman falan ne, tun azahar na shigo.”

 Ba karamin mamaki Zainab tai dajin hakan ba, kafin tace “tunda dai lafiya ai Alhamdulila”

Juyawa tai ta fita.

 Dakin Sadiya ta kalla, kawai ta nufi daki, budewa tai.

 Sadiya dake zaune tana waya, tana ganin Zainab ta gyara zamanta tare da kashe wayar.

 Zainab ta kalli yanda take zaune daga vest sai dan wando, daurewa tai tace “Sadiya kina nan ashe?”

 Cikin sanyin murya tace “eh yanzu na shigo, da muna hira da Goggo a falo.”

Kallanta tai cikin alamar zargi, suna hira? Bayan Goggo tace tun azahar take daki? Sannan ita tunda take ma bata taba ganinsu suna hira ba yanda dai yaci ace uwa da ‘ya nayi.

Okay kawai tace ta ja kofar ta koma daki.

 Adam yau ma bainan, gashi jiya taji haushin tana mai magana baimassn tanayi ba, kuma haryanzu baiko kira yabata hakuri ba yanda ya saba.

 Kayanta ta ajiye ta nufi toilet.

******
Sai wajen goma sha daya yauma Adam ya dawo, tana zaune daram akan gado ta cika ta batse dan bazata dauki wannan halin banzan ba.

 Adam ne ya shigo sum sum ya bude kofar daki, ganin Zainab a zaune ne yasa gabanshi ya fadi, baki na rawa yace “Honey!”

 Kallansa tai sannan tace “daga ina?”

 Yana yar dariyar waskewa ya nufota, hannu tasa ta dakatashi daga tabata tace “daga ina?”

 Nadan fita ne neman aiki.
Neman aiki?
Da sauri yace akwai wani baban abokina dayace na kawo takarduna.

 Shine sai dare ka dawo? A wani garin suke?

 Shiru yai kafin yace “Honey!”
Tace “jiya ma ba sai 11 ka dawo ba?”

“Sorry Honey zan dinga dawowa da wuri.”

 Matsowa yai ya xauna kusa da ita yace “sorry kinji na daina.”

 Kai ta daga alama to sannan tace “to.”

 Kwanciya tai ya zauna a kusa da ita yana shafa bayanta kamar yarinya hartai bacci.

 Shiru yai yana tunani, a hankali ya mike ya cire kaya sannan yazo ya kwanta.

 Juye kawai yakeyi ya kasa bacci, dazu yana ganin kiran Khalid yaki dauka, tsoro ma yake karya kara jin wani abin.

 “Kazo dakina”
Text din daya shigo wayar sa kenan, kallan Zainab yai ganin tana bacci sosai yasa ya mike a hankali ya fito.

 Dole yaje ya lalabata ta tafi, da wannan tunanin ya murda kofar dakin.

 Tana kwance rub da ciki ya shiga, bata juyo ba tamai  alama dayazo ya zauna a gefenta.

 Karasawa yai ya zauna, tadan kalleshi tace “Dan bugamim bayama Yaya.”

 Kallanta yai sannan yace “ciwon yake?” Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana tuno Baby wato Fiddausi wace ke yawan ciwoka ciki kuwa harda ciwon baya wanda yafi matsa mata.

 Shiru yai yana kallan Sadiya gabansa na faduwa, tace “bugamim.”

 Hannu yasa yana buga mata sai dai kalaman Khalid ne ke dawomai, ganin da alama tunani yakeyi yasa ta juyo tare da bude hannayenta.

 Kallan kirjinta yai wanda duk rabi a waje yake sannan ya kalli fuskarta, tace “na bata ma rai kwana biyu ko?”

 Shiru yai sai dunkule hannunsa dayake yana neman kin amincewa, tace “yahkuri yaya kasan na fadama inada lalura.”

 Ido ya kura mata yana kokarin danne sha’awar dake taso mai.

 Hannu tasa ta jawo rigarsa ya fada kanta, a hankali ta dagoshi ta sa bakinta cikin nasa.

 Yanda kasan jira yakeyi nan Adam ya birkice ya na neman fita hayyacinsa.

 Sun riga sun shiga wani yanayi, nishi kawai kakeji dan yau har rigar jikinta sai daya cire.

 Yoo abinda yake kwana yake yini dashi yau ya samu.

Zainab wacce ke rike da wayarta saboda kiranta da akai ta dauka takejin duk abinda yake faruwa.

 Sakar wayarta tai ta fadi kasa, gaba daya jikinta rawa yakeyi neman mikewa take sai dai kafafunta sun kasa daukanta, da kama bango haka ta bi har dakin Sadiya.

 Idanunta kumshewa kawai suke kamar mai shirin suma, handa takejin nishin Adam tana tsaye a jikin kofa ne yasa taji gaba daya tana neman zubewa kasa.

 Da kyar ta iya sa hannu ta bude kofar.

 Adam wanda gaba daya ya zauce da sha’awa har ya fara kokarin aikata aika aika, dan har kayanshi duka da nata ya cire ya cilar.

 Tana bude dakin taga abinda ke faruwa kawai ta zube a kasa ta suma.

 Adam wanda ana bude kofar ya dago cikin tsananin tashin hankali.

 Sadiya kam ko nace Razy ta kalleshi sannan ta kalli Zainab, bataso tarwatsa komai cikin sauri ba sai dai tasan in ta bari waccen dan iskan kyankyasan ya cigaba da shiga abinda bai dameshi ba komai xai wargaje ne ba tare da tayi abinda ta dade shekaru tana jira ba.

Zainab na kalla wace ke sheme kasa a sume.

Goggo wacce ta kasa bacci saboda tsoron abinds kuliya zata aikata yasa ko abinci bataci ba sai yanzu da yunwa ta hanata sukuni ta fito shan dan tea.

 Ganin kofar dakin a bude yasa tai ciki.

 Zainab ta gani a yashe a bakin kofar a sume.
Ga Adam a kan gado gaba daya ya kame ya kasa ko motsin sa sutura.

 Wani kwalelen ihu data saki ne ya razanani, sai da wayata da nake typing ta subuci????


Hmmmm anzo gurin inji mai tsoron wanka????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button