NOVELSUncategorized

A GIDANA 29

{29}


 Goggo a rikice ta kalli Zainab, wacce ke sume sannan ta kalli Adam wanda da alama shima suman zaune yai, takaici ne ya kara kamata ganin sa zir ba ko kaya.

 Idanu ta runtse cikin tsananin bakin ciki ta kalli Sadiya wacce ke kwance kan filo, tana kallan abinda ke faruwa.


 Hankali a tashe ta garzayo kusa da Adam ta tsinkamai wani mari, a gigice ya farfado ya kalleta yace “Goggo!”

 “Ka tashi ka sa kaya ko sai na guntile abin?”

 Sai a lokacin hankalinsa ya dawo akan abinda ke faruwa, hankalinsa  a matukar tashe ya zabura yaja bargon da Sadiya ta luluba, kallan Zainab yai dake kwance duk jikinsa rawa yake ya kalli Goggo hannu tasa ta hankadashi ya zauna kan gado dabas tace “wannan wannan…..”

 Sai kuma tai shiru tsabagen tashin hankali da rasa bakin ma magana.

 Tama rasa me zatamai ta huce, kallan Zainab tai sannan ta karasa tana neman dagata.

 Adam ta kalla tace “kazo ka kamata mun kaita asibiti ko kuwa?”

 Gaba daya a rikice ya matso kallansa tai tace wannan ma ina zai iya tuki?

 Yau itakan wani mumunan mafarki takeyi haka?

 Muryar Sadiya taji tace “in kun fita ku ja min kofar?”

 Cikin tsananin kumburin fuska Goggo ta kalleta tace “in kofar gidan ubanki ce sai ki sani na kule tsinaniya mai sufar mayu.”

 Haka suka fita da Zainab Goggo tace mukaita daki.

 Nan sukai daki da ita, kallan Adam tai cikin takaici kawai tasa hannu biyu tana dukanshi ta ko ina, shi kanshi kuka kawai yakeyi yana cewa “dakeni Goggo.”

 Sai da hannunta taji ya fara xafi sannan ta kalleshi cikin tsananin takaici sannan a zuciye ta fito daga dakin.

 Zainab ya kalla, hannunta ya kamo kawai yana kuka, dan shi kansa baisan meya shiga kansa ba, dan ya tabbatar a yanda yajishi dazu da ba kowa ba abinda bazai aikata ba.

 Kukan da yake ne ruwan ya diga a kan fuskarta, a hankali yatsun kafarta sukai motsi.

 “Honey? Ki yafemin bansan meya shiga jikina ba wlh…..”

 Wadannan kalaman nasa ne suka doki kunuwanta, kanta taji yayi wani uban sarawa, mumunan a binda ta gani ta tuno.

 A zabure da firgici ta bude idanunta tare da jan wani dogon mugun numfashi taja, bakinta da gaba daya jikinta suka hau rawa daga kwance.

 Adam dake rude lulube da bargo ne ya kalleta, ganin yanda jikinta ke rawa, ga bakinta ya kara daga mai hankali, hankalinsa ne yai mumunan tashi ya matso yace “Honey Honey.”

 Gaba daya ya gama tsorata a rikice ya zura riga ya fito dan kiran Goggo.

 ******

Goggo wace tana ajiye Zainab ta shigo dakin Sadiya cikin tashin hankali da rikecewa ne ta kalli Sadiya dake kwance bayan ta maida kayanta ta kwanta kamar mai bacci.

 Goggo ta yaye zanin gadon data luluba dashi tace “kin tashi kin bar gidan nan ko sai na gwaraku da bango kanki ya fashi? “

 Sadiya ce ta juyo ta kalleta tace “idan kin isa kenan?”

 “In na isa?” Goggo ta tambaya.

 Sadiya tace “zan zauna harsai sirikarki ta dawo daga mutuwar wucin gadi datai na bata amsoshin tambayoyim da zata tambayen sannan na fita.”

 Za kuwa ki farka ki ganki a kabari wlh, wannan yarinya ban taba ganin tsinaniya irin ki ba, wlh ko ki tashi ki bar gidan nan ko kuma wlh ki ziyarci lahira.”

 Sadiya ta ja zanin gadon tace “ko zan tafi sai da safe ba uban da zai fitar dani a daren nan.”

 Goggo ta fizgota da hannu tana neman jawota ne Adam ya shigo a rikice yana kiranta.

 Saketa tai ta fito da gudu tana cewa “menene?”

 “Zai zainab”
 A rikice sukai dakin da take, hanyarzu jikinta a rikice yake , hankali a tashe tace “mu tafi asibiti.”

 Nan suka kinkimeta sukai waje.

 Asibitin Standard suka nufa, gaba daya dan Allah yasa gari bai waye bane sam babu motoci a hanya da lalai sai dai wani ikon Allah amma yanda Adam ke tuki, da kyar ya kaisu cikin asibitin.

 Zainab gaba daya haryanzu ta kasa saita tunaninta, abinda ta gani ne yake dawo mata kawai ta ko ina jikinta rawa yakeyi.

 Haka aka shiga da ita suka kwantar da ita wata nirse tazo dubata.

 Adam zaune a waje shida Goggo sunyi tsuru tsuru, Goggo in ta kalleshi sai taji kamar ta rufeshi da duka, shikam sai matsar kwalla yake, can yace “Goggo ya zamuyi?”

 Tambaya kake? Tambaya kake? Banda hauka da rashin tunani sau nawa ina fadama ka shiga hankalinka da wannan yarinyar? Tun farko ma uban wa yace ka tsintota?”

 Adam ya share kwallar sa yace “na shiga uku Goggo, Zainab bazata taba yafemin ba, Goggo na shiga uku.”

 Haushi ne ya kara kamata ta runtse idanunta cikin takaici.

 Wajen awa daya sannan nurse din ta fito ta kallesu tace “shock ne amma yanzu mun mata allurar baci so in ta tashi muna sa ran komai ya dawo daidai, da alama shock din  data shiga babba ne.”

 Adam yai shiru yana tausayin abinda zai faru.

Haka sukai Jugum a asibiti, harara kawai Goggo ke zabgamai tana neman mafita da yanda zatai kwacesu, dan itakam im Zainab ta koresu shikenan rayuwarta ta kare dan batasan yanda zata cigaba da rayuwa ba.

Kallan kafarta tai ashe ko takalmi bata sa ba, Adam ta kalla shima haka, tace Allah yasa ka sa wando ba rigar ka zura ba sokon banza.”

 Kasa yai dakai cikin tsoron halin da suke ciki.

 Tunowa datai sun bar Sadiya a can ita kadai ne yasa ta kara shiga wani hali.


 Kallan Adam tai tace “inaji dole naje na kuri tsinaniyar can kafin ta farka mu koma ta kulla ma sharri.”

 A tsorace ya riketa yace “Goggo ki taimaken karki tafi ki barni in Zainab ta tashi banssn yanda zanyi ba.”

 Cikin takaici ta bige hanunsa tace “kasan kana tsoranta ka aikata?”

 Kasa yai dakai cikin tashin hankali, ya zatai da tsinaniyar can?

Haka har gari ya waye suna zaune, sai da Goggo tace “tashi ni kaje kai sallah zan daure in shiga gunta kafin ka dawo.”

 Mikewa yai yace “in na dawo zan tsaya a waje.”

Kallan takaici tamai kawai ta wuce ciki.

A hankali ta bude kofar, sai data tabbatar tana bacci sannan ta shiga.

 Zainab dake bacci ta kalla, tabbas tasan akwai tashin hankali mai karfi in Zainab ta farka, lalai ko za’a mutu haka zatai ta bata hakuri, itakam bazata iya rayuwa ba a gidan Zainab ba wlh.

 Tana idar da sallah ta fito dan itakam inba korar magen can tai ba bazata taba samun nutsuwa ba.

 Adam ta gani xai shigo ita kuma zata fita, da gudu ya karasa yace “Goggo ina zaki?”

 Wani banzan kallo tamai tace “ban sani ba.”

 Tai wucewarta.

 Tana fita taga adaidata ta shiga.******

Karfe bakwai da rabi Khalid ya iso gidan, Bala ne ya kalleshi yace “ranka ya dade basa nan dukansu.”

 “Basa nan? Lafiya dai ko?

 Bala yace “Hajiyarce ba lafiya suna asibiti.”

 Shiru yai yana tunanin ya tambaya yaji sosai ne? Amma yana ganin ba huruminsa banr hakan yasa ya juya.

 Ya juya kenan Goggo na sauka a adaidaita, mai adaidaitan ta kalla tace “in dako ma kudin ka.”

 Kallanta yai yace “gaskiya Baba kiyi sauri.”

 Tace to.
Khalid ta kalla cikin alamar tambaya tace “wa?”

 Gaisheta yai sannan yace “Khalid ne, wanda ke kaita gun aiki.”

 Oh matuki?
Yace eh, kafarta ya kalla ba ko takalmi, tace “an fadama batada lfy ko?”

“Eh, Allah ya kara sauki.”
Tace amin, sallama ya mata ya juya.

Ciki ta shiga taba Bala kudin adaidaita sannan ta nade hannun rigarta kai kace mai shirin dambe ce ta nufi dakin Sadiya.

 Cikin masifa ta bude kofar, a rikice ta kara kallan dakin, ba kowa a ciki sannan bako kayanta a ciki, hankali a tashe ta fara leleka dakunan gidan, sai dai ba ita ba labarinta, sai wayar zainab dake ta kara.

 Daukan wayar tai ta dau takalmi ta fito.

 Dawowa tai asibitin, a waje taga Adam, yi tai kamar bata ganshi ba tai hanyar ciki.
Da gudu ya taso yace “Goggo kin dawo?”

 Tace “uban me kake anan? Kai da zakaje kusa da ita tana tashi ka nemi yafitarta?”

 Shiru yai shidai kam yasan Zainab.

 A hankali Goggo ta tura kofar daki, ajiye wayar Zainab tai a gefe ta ma Adam alama daya shigo, yana sa kafa cikin dakin Zainab ta mike ta zaune, kai kace mikar da ita akai.

 A tare suka kalleta gaba dayansu hankulansu a tashe, kallan asibitin tai, sannan ta kalli Adam wanda ke makale a bakin kofa, Goggo ta kalla idanunta sunyi jaaa sosai ko dan bacci tasha?

 Bakinta kawai take motsawa tana san magana amma ji take wani abu ya tokare a kirjinta, har makoshinta.”

 Ganin maganar bazata yiwu ba ta mike ta zo kusa da Goggo hanyar waje ta nuna mata, da sauri Goggo tace “Zainab kin farfado? Sannu kinji.”

 Idanunta ta runtse da karfi, Adam ta hango akan gado ba kaya shida Sadiya gaba daya sun fita hayyacinsu.

 Da sauri ta bude idanunta, sannan ta nunawa Goggo hanyar waje.

 Goggo tace “ya akai? Abu kike so?”

 Zainab rai a bace ta kara nuna mata hanyar waje, sarai Goggo ta san me take nufi amma tace “Zainab?”

 Bakin kofa ta nufa wanda Adam na ganin ta nufoshi ya zube a kasa yai kneel down tare da daga hannunsa  yace “Honey!”  

 Ko kallansa batai ba ta kara kallan Goggo ta nuna mata waje.

 Goggo sum sum ta zo ta fice, suna fita ta rufe kofa ta sa key.

 Sulalewa tai a jikin kofar ta zauna, gaba daya ta rasa meke faruwa, inama mafarki takeyi? Meke faruwa da rayuwarta.

 Wayarta dake kara ta kalla, da kyar ta mike taje ta dauka, ganin gun aike ne yasa ta ajiye har ta katse.

 Wayar ta kalla gaba daya ta kasa kuka, ta kasa ko magana, number Dady ta scrolling har tana shirin yin dialling ta tuna abinda tamai akan san zuciya irin tata, Ummy!!!
Abinda zuciyarta ta kira kenan, idanunta ta runtse, Alhakin Dady ne bina Ummy? Ummy Adam…..

 Abinda zuciyarta ke fada cikin kukan zuci wanda ta kasa zubar dashi a kwayar idanunta.

Number kanwar mamanta tai scrolling, tunowa da yanda Aunty batajin dadi sosai itama gun mijinta wanda harda bakin cikin hakan yasa ta gaji da zaman gidanta yasa ta ajiye wayar ta kifata.

 Nabila! Kina ina??? Rayuwata da alama tazo karshe……

 Asibitin ta kalla sannan ta kara daukan wayar, number Khalid ta lalubo tamai text.

 “Kace Bala ya dako ma key ka zo ka dauken a asibiti”

 Khalid na kokarin shiga cafe ne wannan sakon ya shigo wayarsa, kallan sakon ya sakeyi shidai ya rasa meyasa yake tunanin gagarumin abu ya faru a jiya, daga yanda Zainab uwar san aiki da kuma yaga sirikarta ba takalmi.

 Juyawa yai ya koma gidan.

 Jin sakonta yasa Bala cikin rashin yadda yace “gaskiya ina tsoro.

Khalid ya nuna mai sakon, Bala yai shiru yana tunani, ganin Khalid abokin Adam ne a cewarsu sannan ga daga yanayin Khalid yana ganin ba mutumin banza bane yasa yai shahada ya dako mai spire key din da take ajiye gunsa.

 Khalid ya hau ya nufi asibitin.

“Na iso?”

“Ka shigo ina sama”

 Ciki ya shiga, Adam da Goggo na zaune jugum Goggo ji take kamar tasa kafa taita makawa Adam.

 Ganin Khalid yasa Adam ya mike da sauri ya nufoshi.

 Khalid cikin mamaki  ya kalleshe yace “Adam?”

Adam ya kamo hannunsa yace “Khalid na shiga uku na……..”

Adam..
Kiran da Goggo tamai ne yasashi yin shiru, Khalid yai shiru yana kara tabbatar da zarginsa.

 Kamar tasan ya iso kawai ta fito ita da nurse, wacce take binta tana ce mata ta dawo ta zauna ko dan rashin maganar da takeyi. 

 Ko kallansu batai ba har Khalid din tai gaba.

Gaba daya ta canza, kafafunta ba takalmi bako mayafi a jikinta, rigace doguwa zuwa gwiwa ta bacci, da wando, sai hula a kanta.

Da alama halin da take ciki ma baisa tasan abinda ke sanye a jikinta ba.

 Juyawa yai ya nufi inda take yace “an baki sallama ne?”

 Bata ko kalleshi ba ta sauka har kasa, mota ta nufa ta kalleshi ta mai alama da ya bude.

Yana budewa ta shiga ciki ta zauna.

 Kallan Adam da Goggo dake tsaye a bakin kofar asibitin yai sannan ya bude motar ya shiga.

 Tafiya suka fara tana kallan motocin dake wucewa, Khalid yai shiru shidai yana tuki amma gaba daya zuciyarshi na tsoron kardai wannan yarinyar tayi wani abin?


Zainab a hankali wani zazzafan hawaye ya zubo mata, tunda ya sako kamar an koro kuka, duk yanda taso ta dane kukan ji tai ta fashe da wani wahalalen kuka mai matukar ratsa zuciya.

 Ba karamin tashin hankali Khalid ya fuskanta ba, gefen titi ya gangara, sannan ya ajiye tissue a gefenta ya bude motar ya fita ya tsaya a jikin kofa, sai dai gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, tsananin tausayinta ne ya kamashi.

Kuka take iya karfinta, wanda ni kaina sai danaji hawaye????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button