A GIDANA 31
{31}
Kallansa tai sannan ta dauke idanta tace ” akwai inda zani acan”
Bai tada motar ba sai dai yana nazari, kallansa tai tace “muje!”
Motar ya tada suka fara tafiya, hannunta rike da wayarta tana kallan sunan Dady, can ta danna kira.
Ringing uku aka dauka, sai dai me? Jitai muryar mace, Basma daga can take “Zainab?”
Da sauri Zainab ta kalli wayar wani abu ya tokareta, Basma tace “yahkuri na daga wayar, yanzu ya dawo break daga gun aiki ya shiga toilet ne.”
Kashe watarta Zainab tai sannan ta rufe idanunta kamar mai bacci.
Har suka shiga danbatta bata bude idanta ba da alama daga tunane tunane bacci yayi gaba da ita, suna kan titin shiga danbatta ne yace “ina ne unguwar?”
Shiru yaji hakan yasa ya duba mirror din gabar motar, ganin tana bacci yasa yace “Hello!”
Zai sake magana yaga ta farka a zabure, tana Inalilahi wa Inalilahi Raji’un.
Idanunta ta bude a tsorace, tana maida numfashi, Khalid ya gangara gefen titi.
Kallansa tai ta tana jin haushin yanda yake gaminta yanayin da bata san kowa ya sameta a ciki.
Daurewa tai tace “muje.”
Yace “inane?”
Kallan garin tai sannan tace “I don’t know.”
Juyowa yai ya kalleta yace “You don’t know?”
“Hmm yafi shekara biyar dana zo i can’t remember.”
Baisan sanda wata dariyr rainin hankali ba, haushi ya kamashi yace “then ki kira kaninta muji.”
Wayarta ta dauka ta kirashi, daga can yace “Zee kece?”
Tace ” Sabir Aunty na nan kuwa?”
Aunty Amina?
Eh
Yace “mijinta ya koma Abuja da aiki ya akai?”
Okay shikenan, kafin ya sake magana ta kashe wayarta.
Khalid ta kalla tace “batanan.”
Baki yadan bude yana kallanta kafin ya danyi wani abu daga cikin kirjinsa zuwa bakinsa, yace “yanzu ya za’ayi?”
Oho!
Fuskarsa ya hade yace “Then zan iya ajiyeki anan na tafi.”
Kallansa tai da sauri sannan ta kalli waje tace “anan?”
Kai ya daga mata alamar eh sannan yace “kina tantama?”
Tace “shikenan, ka barni anan din.”
Daurewa yai ya juyo ya kalleta duk fuskarta ta kumbura, idanunta sunyi jaa samansu sun kumbura yace “Am sorry na san ba hurumina bane sai dai yau ma zan sake ciga hurumin da ba nawa ba, wannan zabin kina gani shine ya dace?”
Dagowa tai daga jinginar datai tace “me kake nufi? Ba dai kana so kacemin na cigaba da zama da mijin da na kamashi da mace a cikin gidana ba?”
Gabansa ne ya fadi, abinda ya faru kenan? Yanayin fuskarsa ne ya canza dan ya tausaya mata, kauda kanta tai ganin kallan tausayin da yake mata tace “meye laifina? Kula dashi danai ko kuwa kula da mahaifiyarsa? Meye laifina dan na kula da mijina? A tunanina inayin daidai gwargwadon abinda zan iya bansan menene laifina ba……..”
Hawayen da taji suna neman zubo mata ne yasa ta kasa cigaba da maganar, Khalid ne ya kalleta duk da tausayinsa daya kamashi bai hana cemata “kina tunanin duk abinda ya faru baki da laifi kenan?”
Kallansa tai bayan ta dake tace “fadamin menene laifina?”
“Wani irin rashin kula da rayuwar da bataki ba da kikeyi da har za’ace bakisan kanwar mijinki ba? Wannan wace irin rashin kula da gidanki ne?”
Shiru tai tana tunani, tabbas duk matsalar daga nan ta fara, datasanta da duk…..
Dakewa tai tace “Naji wannan ne laifina bayan shi kuma fa?”
Shiru yai yana kallanta kafin yace “komai daya faru rabi naki ne, sannan bakya tunanin gidanku ya kamata kije?”
Fuska ta hade sosai tana kallansa kafin tace ” tafi ka barni anan.
Bai kulata ba yaja motar suka cigaba da tafiya itama haushi baisa tace komai ba.
Wayarta ta daga ta kira Bala.
Bala na tsaye a na canza key din gidan wayarta ta shigo, ya gaisheta.
Tace “sun tafi?”
Yace “a’a.”
Takardar fa?
Bai nan komai ba.
Shikenan tace ta kashe wayar.
A bakin kofar gidansu yai parking, sannan ya kalleta yace ” ki kwana anan gobe na maidake gidanki.”
Kin kulashi tai bata kalleshi ba, fita yai daga motar shima ba tare da yace komai ba ya dau jakar ta a booth ya shiga ciki.
Da wani kallo ta bishi tana mamakin hali irin nasa, ko kadan baya burgeta namiji sai tsinanen zafin rai? Ita sam ta tsani namiji mai gadara da neman isa.
Khalid ne ya shiga ciki.
Yana shiga tsakargida yaga Asiya a tsaye tana kiran su Amie su fito su wuce islamiya, kallanta yai tana ganinsa ta matso tana yaya an dawo?
Eh Asiya in zaki wace kiyima bakuwa magana a cikin mota kice ta shigo.
Bakuwa? Mota? Kallanta yai bai amsa ba ya wuce ciki.
Su Amir na ganinsa suka gaisheshi suka fito da gudu suna sa takalmi.
Umma data idar da sallah ne a daki ta fito tace “Khalid? Kaine da ranan nan?”
Zama yai kusa da Abba yana cewa eh wlh.
Kallan Abba yai sannan ya kalli Umma dake kikarin zama, Abba yace “ya akai?”
Dan hannunsa yasa ya shafi keyarsa yace “matar danake ma aiki ne muka taho tare.”
A tare sukace “ina?”
Khalid yace “ta samu matsala da mijinta ne shine na kawota nan kafin komai ya warware.”
Fuskar Abba dauke da mamaki yace “iyayenta fa?”
Khalid yai dan shiru kafin yace “ba’a kusa suke ba, da alama kuma batada kowa a kusa.”
Umma tai shiru kafin tace “kace ta shigo ne?”
Na fadawa Asiya, shiru sukai suna tunannin wannan abu.
Asiya data fito ne ganin mota a kofar gidansu yasa ta nufeta, Amir yace “Ya Asiya motar yaya ce?”
Bata kula su ba ta nufi motar.
Zainab dake ciki ta bude kofar tana kallanta, Asiya ta gaisheta cikin nutsuwa sannan su Amir ma suka gaisheta.
Kanwar sa?
Asiya ta daga kai tace “eh, ya Khalid yace ki shigo.”
To, islamiya zaku?
Tace “eh Aunty.”
Zainab tana tsaye tana kallansu gar suka wuce tai murmushi tace da alama age mate din su Nabila ce sai dai ta fisu nutsuwa, tunowa tai da fadan da sukeci haka kawai ta samu kanta da murmushi.
Kallan gidan tai bayan tazo jikin kofa ta tsaya, itadai ta kasa shiga ciki.
Abba ne ya kalli Khalid yace “ka shigo da ita bakowa ne zai iya shigowa gidan mutane kai tsaye ba.”
Nan Khalid ya mike ya fito.
A waje ya ganta tana ganinshi ta hade rai, shima fuskarsa a hade take yace “ki shiga.”
Wucewa gaba tai kai kace gidansu ne, tun daga tsakar gidan take mamakin gidan, gidane dan karami, soro inda dakin Khalid yake sai kofa ta ciki, kana shiga dan madaidaicin tsakargida ne wanda aka sumumteshi tsaf, daga gefe akwai rijiya, sannan bandaki a ta gaban rijiyar.
Daga can kusa da asalin cikin gidan kuma kitchen me a gun, gefen kitchen din kuma inda suke sa murhu ko gawayi.
Sai dai kidan a share yake tsaf, hatta gun wanke wanke an wanke gun tas, duk da ta raina gidan amma ta aminta da tsaftar gidan a haka suka shiga, Umma na tsaye a kan barandar tana ganinta ta fara lale lale da babbar bakuwa.
Zainab ta shigo cikin kunya.
Umma ta nemi data shiga cikin falan, Zainab ta shiga, Abba ne a zaune ta gani kafarsa daya babu yana jingine da bango duk da haka yana ganinta yace “barka da isowa.”
Zainab ta zauna ta gaisheshi sannan ta gaida Umma, Khalid dake tsaye ya juya ya bar falan.
Tana ganin yabar falan kunya ta kara kamata, Abba ya kalleta bayan ya amsa gaisuwar yace “ashe abu kuma baiyi dadi ba?”
Kasa tai dakai batace komai ba, yace “bakomai ki zauna anan sai ki kira mahaifinki asan abin yi.”
Gudum yin musu yasa kawai tace to.
Umma ce ta nuna mata dakin Asiya nan ta mike ta shiga, gaba daya itakam kunya ma takeyi, ya akai bata tafi hotel ba?
Umma ta shiga ajiye kawo mata abinci, kunya ta kara kama Zainab dole ta mike ta tayata ajiyewa.
Umma ta zauna kusa da ita tace “karki sa komai a ranki kiyi sallah kici abinci ki huta, Allah zai kawo mafita kinji.”
Kallan Umma tai haka kawai tunanin Ummy ce a kusa da ita yazo mata, idanuntane suka ciciko a hankali hawaye ya zubo mata.
Umma ta kalli yanda duk idanunta ya kumbura, tausayinta ya kamata tace “yahkuri kinji.”
Zainab ta share hawayenta sai dai ta kasa cewa komai, kawai jitai ta nasan Umma ta rungumeta ta rasa me yasa take ganin kamar Ummy ce a gun.
Umma ganin yanda take kallanta yasa ta fahimceta, rungumeta tai tana cewa “bakomai kinji, insha Allahu Allah zai kawo miki mafita duk da bansan me ya faru ba amma nasan ke mace ce ta gari.”
Kamar ta tabo Zainab kawai Zainab tasa kuka, wannan kukan jitake kamar a jikin Ummy take yinshi.
Khalid wanda ya fita siyo juice a shagon kusa dasu me ya dawo rike da leda, yana shigowa yani yanda Zainab ke kuka, kusa da Abba kawai ya ajiye ya fita zuciyarsa na tausaya mata.
Wayar Abba ya dauka ya fita Yana fita ya daga waya ya kara kiran Razy.