NOVELSUncategorized

A GIDANA 30

#OneLove❣

{20}

 Asiya na zaune tana ta mulmula iloka, daga gefenta kuma Abba ne zaune yana jin radio a gefensa, hannunsa rike yake da mafici da alama kuda yake dan kora in suka zo inda yake.

 Kallan Asiya yai yace “Kannen naki na gun ball ko?”

 Tace “dazu Umma tace na korosu amma Allah Abba suna dawowa da sukaga Yaya bayanan ni bansan ma sanda suka sake fita ba.”

“Oh ni yaran nan bansan jaynarsu da kwallo ba, bare yau sun samu dama kuna hutun tsakiyar term.”


 Dariya tai tace “in lokacin islamiya yai sa dawo ai dole.”

 Umma ce ta bude labulen dakin tana sallama, Abba ya kalleta ya amsa.
Mayafinta ta cire ta zauna gefensa sai data kalli Asiya dake ta neman kudinta sannan ta kalli Abba tace “yau bakaji dadin da nake ki ba a rayuwar nan.”

 Abba yai dariya yace “kamar irin kin gama biyan bashin dake kanki duka din nan.”

 Dariya tai tace “wlh bakaga dana kai musu dubu biyar din nan a dunkule yanda naji wani dadi ba, ai insha Allahu tunda aka fara biyansu yanzun nan zamu gama.”

 Abba yai dariya yace “ai sai hamdalla.”

Umma ta kalleshi tace “ni tun jiya nake san tambaya, dama aikin driver yana kaiwa dubu ashirin?”

 Abba yace “eh dama yawanci sha biyar ne, in ka hadu da na gari ya baka ashirin.”

 Umma cikin jin dadi tace “kai Allah yama matar nan albarka, ina san sake mata waina amma banasan ta kara sa kudi a kwanan, kuma bazan iya sa mata a leda ba.”

 Abba yace “haka ne kam.
Asiya ya kalla yace “taimaka ki dan ban ruwan can.”
Mikewa tai ta mikomai.

*********

Agoggon hannunsa ya kalla, sama da awa daya kenan suna tsaye a gun nan, ta glass ya kalleta, ganin alamar ta dan rage karfin kukan yasa ya bude kofar da take.

 Kallansa tai ba tare da tace komai ba, kallanta yai sannan ya bude gun zamansa ya bude jakarsa ya dako ruwa, mika mata yai, kamar bazata amsa ba ganin ruwan dan duri ne bawai na cikin gorar bane.

 Kafafunta ta zuro waje sannan ta mika mai hannu, robar ya mika mata ta sake mikamai ta mai alama daya zuba mata, nan ya bude ruwan ya zuba mata a hannu ta wanke fuskarta.

 Sai data wanke fuskarta sannan ta kalli jikinta, hankalinta a tashe tai maza ta koma ciki sannan ta bude glass tace “dan bude boot din motar, bansan ko na cire wata yar karamar jaka ba, in tana nan ka bani mayafi a ciki.”

 Baice komai ba ya bude yai sa’a jakar nanan, da alama wata yar karamar tafiya akai da ita, dakko mata yai sannan ya dawo ya bude mota ya mika mata sannan ya zauna.

 Shiru sukai a cikin motar, dan kallanta yai yace “Do you feel better? Mu wuce?”

Kallansa tai itama idanunta sun yi wani irin jaaa wanda ya sashi sauke idanunsa gefe, tace “Do you think i’m pitiful?”

 Idanunsa ya dago yace “are you not?”

 Kanta ta kawar gefe tace “kaini mu wuce police station.”

 Da sauri ya juyo ya kalleta yace “muyi me?”

 Tace “ko me zanyi meye naka a ciki? Kaini.”

 Shiru yai kafin yace “bakya tunanin kome ya faru gwara kiji ta bakinsa tukun na? Sannan yarinyar nan fa bakisan dame tazo ba.”

 Kallanshi tai zuciyarta na sake kuna.

 Juyawa yai ya zauna, hawayen da suka zubo mata ta share tace “Kaini gida.”

Okay kawai yace ya ja sukai gaba.

 Suna isa ta bude motar ta fito, kallansa tai tace “ka tsaya.”

 Ta wuce ciki.

 A falo ta tadda Goggo da Adam sunyi jugum jugum.

 Ko kallansu batai ba ta wuce dakin Sadiya direct, sai dai ba kowa a ciki, ba ko kayanta a ciki, Adam wanda Goggo ta sashi ya tsuguna, shine ya kneel down.
 Rufo kofar dakin tai sannan ta wuce dakinta ko kallansu  batai ba, takadda ta dauko da biro sannan ta fito falo.

 Kallan Adam tai sannan ta ajiye mai takaddar tace “rubuta ka fita!”

 Kallanta yai da sauri yace “na rubuta me Honey?”

 Hannunta kawai ta dunkule wanda take jin kamar ta wanka mai mari, dan gaba daya kallan Fuskarsa ba karamin daga mata hankali yake ba.

 Kallan Goggo tai tace “kice ya rubutan takardata sati uku duka sannan ku hada kayanku ku bar gidan nan cikin awa daya, in ba haka ba kuma wlh yan sanda zan kira, dukanku kunsan halina kunfi kowa sanin abinda zan aikata.”

Goggo ta kwalalo ido hankali a tashe tace “Zainab me kike nufi?”

 Zainab wacce ta dake tana kokarin hana wani hawayen zubowa gabansu tace “Daga sanda ya kawo karuwarsa cikin gidan nan na tabbatar ya riga ya ajiye igiyar aurena dake hannunsa, yafi kowa sanin bazan kara zama dashi ba, daga sanda kika mara mai baya gun zaman karuwarsa a cikin gidan nan na tabbatar kinsan karshen zamanki a gidan nan yayi.”

Adam wanda ya kamo kafafunta ya rike ta kalla tace “rubuta ka fitar min daga gida, in kuma yan sanda kake jira suzo su fitar dakai to.

 Ta hankadeshi ta wuce dakinta tasa key.

 Adam hankali a tashe yaje bakin kofar da rarrafe, yana kuka “Honey ki taimaki rayuwata kunfi kowa sanin bazan iya rayuwa ba ke ba, Honey!”

 Zainab dake zaune a kasa a dakinta, idanunta na zubar da kwalla, mikewa tai tunawa datai ko asuba batai ba gashi azahar har ta nufo, sallah tai ta zauna kawai akan sallayar tana kuka rike da wayarta.

 Sunan Dady kawai take kallo a jiki, sannan ta dana kiran wayar Nabila wacce ta san a kashe take amma haka kawai taji tana sannta kira.


*****

Goggo cikin takaici ta matso gaban Adam kamar zata rufeshi da duka sai ta fasa tasa hannu ta dagoshi tace “zonan.”

 Adam ya kalleta yana kuka kai baka ce namiji bane, Goggo tace “yanzu Adam abinda zakajamin kenan? Banyi sa’ar jin dadi a gareka ba ina farin cikin ina jin dadi ta hanyar matarka yanzu itanma ka ja mana shiga garari?”

 Adam yace “Goggo Allah banyi komai da ita ba, nasan nayi laifi daga kawota zuwa sha’awarta amma Allah Goggo abinda kuke tunanin ya faro bai karasa faruwa ba.”

Hannu biyu Goggo ta dumamai a baya tace “dan ubanka yanzu da abu ya faru da karya faru meye amfaninsa? Ka manta ayanda muka ganka? Sannan dan dakikanta mai makon ma kana ganinta ka rufe jikinka sai ka tsaya galala, da uban wa yace ka kawo mana tsiya har cikin gidan mu?”

Zubewa tai ta zauna a kasan da yake tace “yau mun shiga uku wannan da zai kasheni da raina.”

******

Kallan kan gadansu tai, da sauri ta rufe ido, jitai komai na cikin dakin batasan ganinsa, hatta sallayar datai sallah da sauri ta mike daga kanta daga ta rufe idanta Adam take ganowa da yarinyar daya kira da kanwarsa.

Dakyar ta canza kaya a dakin ko wanka kasa yi tai dan Alwalar ma dakyar tai in ta tuna Adam na shiga toilet din.

 Jakarta ta jawo tasa kaya kala biyu ta dauko kayan aikinta ta banko kofa ta fito.

 Adam da Goggo na zaune a bakin kofar, suna ganinta suka matso, Adam yace “Honey ki taimaka min wlh wlh ba abinda…….”

Yanda ta watsa mai wani kallo ne yasa ya sha jinin jikinsa yai gum.

 Goggo ce tai saurin cewa tace “Zainab nasan nina haifi Adam amma yadda na daukeki a raina yafi yanda na dauki Adam, ke kanki kinsan yanda nake sanki.”

 Zainab ta kalleta tace “ya rubuta?”

 Goggo tace “dan Allah Zainab kiyi hakuri.”

 Zainab wacce ta kalli falan tana tuno yanda Sadiya da Adam da Goggo suka maidata mahaukaciya a gidanta, ta daure tace ” zan turo yan sanda ina fita daga gidan nan, in kunso ku rubuta min takardata ku ajiyemin in kuma ba haka ba mu hadu a police station daga nan mu wuce kuto.

Sannan gidan nan yanzu zan sashi a kasuwa ruwanku ne ku zauna ruwanku ne ku fita, motar dana baka na barmaka dan dama kai na saiwa ku kashe kayanku a ciki ku fice min daga gidana, wannan shine uzuri na karshe da zan muku.


Goggo ce ta riko ta da sauri tace “Zainab ki taimaka kiyi hakuri wlh muma cutar mu tai tsinaniyar yarinyar nan.”

Adam yana kuka yace “Honey kiyi hakuri dan Allah.”

Cikin tsananin masifa ta juyo, kamar zata rufesu da duka  tace “inyi hakuri? Duk wani abu da ya kamata ina maka shi inama, nice shanka, nice tufafinka, kula da mahaifiyarka, komai na rayuwa na dauke maka shi amma ka rasa abinda zaka saka min dashi sai wanan? A gidana? Ka kawota kacemin kanwarka? Na bata gurin zama,  na dauketa kamar yadda na dauki kanwata, ashe karya kake min dakai da mahaifiyarka? Bazan taba yafemuku ba wallahi.
Idan har kunasan zaman lafiyanku ku ficemin daga gida na fada muku.”

Ta juya rai a bace ta bar gidan, tana fitowa ta kalli Khalid dake jingine da mota yana nazarin abubuwan dake faruwa, me Adam yama kanwarta haka?
Wayarta yake ta kira anki dauka.


Bala ta kalla ta mai alama yazo, yana zuwa ta kalleshi tace “mutanen ciki zasu fita anjima, yanzu ka kira key walder ya canza min key din kofar nan yanzun nan, sannan kafin dare su barmin gidana, su baka takarda ka ajiyemin, in basu fita ba zuwa dare ka kirani a waya zan turo wadanda zasu fitar dasu.

 Ta bude mota ta shiga, kallanta yai, hade rai tai ta shiga ta zauna.

 Baice komai ba ya shiga ya zauna shima tace ” mu bar gidan.”

 Yace “okay!”

 Yana san tambayarta yarinyar amma baisan shiga abinda ba’a sashi a ciki ba.

 Yana tada mota Adam da Goggo na fitowa da sauri, ya dan kalleta ta glass.

Muje!

Shiru yai yana kallan Ada da Goggo, kallanta ya sakeyi.

Please! Abinda ya fito daga bakinta kenan hawaye na gangarowa.

 Jan motar yai suka bar gidan.

 Tafiya kawai suke batace komai ba shima baice komai ba, ina zani?

Abinda kawai yake zuwa mata kenan, jitai Khalid yace “ina zamu?”

 Kallan window tai tace “ina zani?”

 Cikin sanyin jiki ya dan kalleta.

 Kallansa tai tare da murmushi tace “hotel?”

 Yace “Hotel?”

Tace ” kaini ko ma inane, inda bazan sake ganinsu da abinda ya dangancesu ba.”

 Shiru yai baice komai ba, yana tunanin yanda zaiyi da ita.

Wayarta ta dauka ta kira director tace “zata dau hutun sati daya batajin dadi.”

 Mamaki ya kamashi yace “Zainab sosai ne rashin lafiyar? Kinsan muna bukatarki dayawa.”

Ka taba ji na dau hutu? Ko hutuna ina dauka ne na shekara?”

 Yace “kiyi hakuri, naji abin ne sama ta ka.”

 Zan dawo nextweek.
Bata jira amsarsa ba ta kashe wayar.

Shiru tai.

Khalid yace “ina zamu?”

 Kanta ta kwantar jikin kofa tana tunani, batasan kasancewa ita kadai a wannan lokacin tana ganin in ta zauna ita kadai lalai ciwon zuciya ne zai kasheta, to ina zata? Wa take dashi? Wayyo rayuwata? Allah nasan ni mai laifice ka dubeni.


 Ta karasa tare da rufe idanunta.

 Khalid yai shiru yana tunanin yanda zaiyi da ita.

 Idanunta a rufe tace “muje Danbatta.”

 Bai san sanda yai dan burki kadan ba, ya kalleta tare da yin parking yace “danbatta? Bazaki iya zama a gidan mu ba.”

 Idanunta ta bude sannan ta kalleshi tace “cema nai gidan ku?”

To ina?

 Tace “Gidanku.”

 Yace “mene?”

 Da tana tunanin zuwa gun Dr ne dan tasan yayarsa sosai, ta taba zuwa gidanta a danbatta sau daya, sai dai jin kalaman Khalid yasa ta canza tunani.

 Kallanta ya sakeyi yace “me zakiyi acan?”

In naje ni zanga mai zanyi.

 “Bangane ba, a wani dalilin xaki bar gidanki ki tafi wani gidan?”

 Gidana?

Ta tambaya tana kallansa, idanunta suka sake cicikowa, jin sunan kadai ma tada mata hankali yake.

Tace “ba sai ka wulakantani ba, ajiyeni anan ka tafi, zan je inda nake so da kaina.”

Shiru yai yana tunanin wannan al’amari.

********

“Yau mun shiga uku, yanzu ya zamuyi?”

Wannan da wannan da…..
Ta kalle Adam wanda yake rabe jikin kujera, tace “yanzu da uban me zamu tsira? Duk ka gama cinye dan gadan mahaifin naka agun tsinanen karatun da bansan me ka karanta ba, sannan yanzu gidan matar taka ma gashi ka mana sanadi.”

Adam ya kalleta baice komai ba.

 Haushi ya tuke ta yace ” yanzu ya zamuyi?”

Adam ya kalleta yace “Goggo Zainab ta gama rabuwa dani kenan har abada, yanda ta tsani mahaifinta akan abinda yai, ni na san yanzu ko zata mutu baxata taba kara zama dani ba, na shiga uku na Goggo.”


Goggo a kufule tace “mun shiga uku dai, kasan da aka uban wa ya saka.”

Wayyo yau nikam me zan gani rayuwata ta juya min a lokaci daya.


Can tace “Ina tsinaniyar yarinyar nan taje? Wlh ko zan karar da zanin daurawa ta sai na nemota.”

 Ta karasa da matse kwalla, kanta ke wani irin ciwo.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button