NOVELSUncategorized

A GIDANA 32

{32}
**********

Goggo na zaune tana ta cusa abinci kana ganin kasan cin dole da cin yunwa take ma abinci, Adam na zaune a gefe cikin takaici yace “yanzu Goggo har kinsamu damar dafa indomie kina ci? Muda rayuwarmu take neman shiga garari?”


“Kana sane ko jiya tsinaniyar yarinyar nan bata banni naci abinci ba so kake na muti kafin ma samu ba Zainab hakuri.”

 Kallanta yai gaba daya duk ya canza, kana ganinsa kasan a birkice yake, yace “Goggo koza’a mutu Zainab bazata taba komawa dani ba, kema kinsani, yanzu akam takardarta wlh sai ta kaimu kotu.”

 Goggo ta tsame hannunta daga plate din ta kalleshi tace “duk ba kai kaja mana wannan masifar ba.”

 Da sauri yace “wai kin dane zancen ni naja mana ki nemo mana mafita ko kuwa? Abinda ya faru ya faru amma Sai kara tusawa kikeyi, dana sani ke kanki kinsan nayi, haryanzu bansan uban me ya shiga kaina ba.”

 Goggo ta kalleshi bayan tasha ruwa tace “nidai mafita daya ce yasin bazan koma kauyeba, kasani tunda kai aure matarka ta dakoni ko da wasa ban sake zuwa can ba, kanina inya ishen da zancen Sadiya nasan abin makaranta kana kallo Zainab ke taimakawa mu tura, mo hanyar ban komaba kuma wlh yanzu bazan koma ba.”

 Cikin masifa yace “nima cewa nai mu koma? Tambayarki nake yanda zamuyi.”

 Itama cikin masifa tace “kaina zaka huce? Uban wa yasa ka ja mana?”

 Haushi ne ya kamasu duka kowa yai shiru.

 Adam ta kalla sannan tace “wai kai da uban me kake da kudin da take baka duk wata?”

 Haushi ne ya kamashi bai tanka mata ba.

 Goggo ta sake cewa “ko kuma me kale gani idan ka bata takadar sai dai kace mata bazaka bata takardar saki ba harsai ta barma gidan nan.”

 Kallanta yai da sauri yace “mene?”

 Goggo tace “kana gani dai korarmu za’ai nan da awa anjima kaga dai key ake canzawa, kuma wlh tunda ta furta ko za’a mutu sai ka bata takardarta, gwara muma mu cafki gidan, ai harga Allah kaima cutarka kuliyarcan tai.”


Shiru yai yana kallanta kafin yace “kina tunanin Zainab zata yadda?”

 Tace “karma ta yadda, in bata yadda ba kace mata kuje kuton ai ita idan gari ce aikin gidan tv take mutane dayawa sun santa bazata taba bari sirrinta ya fito duniya ba, kasan yanda take san aikin nan nata.”


 Kai ya jinjina cikin gamsuwa sannan yace “Goggo Allah banasan rabuwa da Honey.”

Yai maganar kamar mai shirin kuka.

 Tace “inka kara cemin Honey sai na wankeka da mari shasha shan banza, kai dai wlh banga amfanin ka ba, sam ni na rasa banzan hali da sokon tunaninka.”

 Adam yai shiru gaba daya hankalinsa ya kasa nutsuwa, wani bangare na zuciyarsa na kwadaitamai abinda Goggo tace.

Goggo ta kalleshi tace “tu ra mata sako a waya, ka fada mata in tanasan takardarta sai ta baka gidan nan.”

 Da sauri yace “yanzu?”

Tace “da sai yaushe?”

 Nan ya dako waya yana kallanta.

••••••••••

Rasy dake kwance Bash na gefenta yana neman kai hannu cikin rigarta ne ta buge hannun sannan ta kalli wayarta dake kara, dagawa tai tace hello.

 Khalid yace “Raziyya kinga dama kin daga?”

 Nan ta fahimci waye tace “Drivern mota kiran wayar na menene? Na tabbatar banci bashinka ba.”

 Murmushi yai yace “kin bayyana kanki ko sai naje gidanku na fadawa iyayenki abinda kikeyi?”

 Da sauri ta mike tsaye tace “gidan mu?”

Yace “eh kokin dauka bawanda zai san inda gidanku yake?”

 Kumbura fuska tai cikin bacin rai, Khalid yace “mu hadu dake gobe a kano, zan kiraki inji inda kike, kada ki kuskura kik’i daga wayarki inba haka ba zan wuce Naibawa yar lemo na fadawa iyayenki abinda kikeyi, Ahhhhhh bansan ya zasuji ba insuka ji, bayan yayarki ta rasu, ina tsoron halin da zasu shiga.”


 Yana kaiwa nan ya kashe wayar.

 Cikin takaici da bacin rai tabi wayar da kallo, a Zuciye ta cillar da wayar kan gado sannan tai wata kara mai karfi tace “Kyankyasan nan…….”
Bash ne yasa hannu zai riketa kafa ta sa ta haureshi a matse matsin kafarsa, wani irin kara yasa shima tare da durkushewa a gun.


*********

Umma zama tai a gabanta Zainab Taci abinci sannan ta fito daga dakin bayan taga ta zauna tana hutawa, Zainab tabi bayanta da kallo cikin wani yanayi.

 Abba dake falo ne ya kalleta yace “Uwar ‘ya an fito?”

 Zama tai kusa dashi cikin tausayi tace “da alama batada wanda zata dogara dashi taji dadi.”

 Kallanta yai yace “kamar ya?”

 Kai ta girgiza alamar rashin sani tace “haka kawai nakeji kamar ta dade cikin kewa tana neman wanda zai dubeta.”

 Shiru Abba yai cikin tausayinta shima.

 Zainab ta kalli hoton Ummy a wayarta tai murmushi tare da kwantar da kanta akan dan karamin gadan Asiya, Ummy na!

 Ta fada tana shafar hoton, sako ne ya shigo wayarta, kallan sakon tai cikin mamaki ta kara karantashi.

 Gaba daya mamaki ne ya kamata, duk da tasan karshen zamanta da Adam yazo amma bata taba tunanin zai nemi bata takardarta bugu daya ba, sannan abinda ya kara bata mamaki wai ta bar mai gidanta?

 Wata dariyar bakinciki ta saki tace “Ummy wace rayuwa nai duk tsawon shekaru na???? Me yasa nake gani kamar duk wahalar danasha bata biya min komai ba??”

Umma ce ta turo kofar dakin, Zainab ta kalleta tare da gyara zama, Umma ta ajiye mata ledar juice din tace ” badai tunanin kike ba?”

 Kallanta tai tana san fada mata abinda ke ranta amma gani take daga ganinta sainta zake???

Kai ta girgiza tace “a’a.”

Umma tace “ko nazo mu zauna tare? Dama na fita ne na dauka kina san hutawa.”

Zainab tai murmushi tace “zan kwanta ki huta kema.”

 Nan Umma ta juya tana murmushi.


****

Tana fita Dady ya kirata a waya, kallan wayar tai kafin ta daga.

 Daga can yace “Zainab ashe kin kira?”

 Murmushi tai tace “eh na kira dazu.”

Yahkuri bangani ba sai yanzu dana dau waya zanyi waya ma ga kiranki.

Shiru tai kenan Basma batace mai komai ba ko me?

 Tace “dama kira nai mu gaisa ta daga tace kana toilet.”

Oh Basma ta daga? Ai bansani ba saboda ina fitowa na taho kila shiyasa bata samu damar fadamin ba.”

Zainab tace “bakomai.”

Ina aiki ne in na tashi ma kira, kafin ta kara magana
ya kashe wayar da alama aiki yake sosai, sai dai ba karamin sanyi jikin ta yak ba ta kwanta kawai ta rufe idanunta.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button