NOVELSUncategorized
A GIDANA 34
Knocking din motar ya fara cikin tashin hankali, Zainab tana zaune ta zubawa takardar ido, bata taba tunanin wannan lamarin ba, lalai Adam, kallansa tai
yanata jijiga kofar motar, zuge glass din tai ta kalleshi, da sauri yace “Honey ki taimaka ki ban takardar dan Allah ki yafemin na tuba wlh, Honey ki
taimaki rayuwata dan Allah.”
Kallansa kawai takeyi, Honey dan Allah ki yafemin, wlh wlh bansan meya shiga kaina ba.
Daurewa tai tace “ka biyoni inda ka ajiye motarka ka dauka”
Da sauri yace “Honey ki bari mu tafi tare, dan Allah ki tsaya ki………”
Jan motar datai ne tai gaba ya sashi zubewa a kasa wani zazzafan hawaye ne ya zubomai.
Zainab tana zuwa kofar gidan ta ajiye motar a inda ya ajiye, tunanin wanda zataba key dinshi tai sannan tai hanyar ciki, tai sa’a sai ga Amir nan.
Yana ganinta ya karaso da gudu yana cewa “Aunty Umma nata nemanki.”
Kallansa tai sannan ta mikamai key tace “Amir ka tsaya a jikin motarnan zakaga wani yazo yana neman key ka bashi wannan.”
Amsa yai sannan tai ciki, tana shiga taga Umma a tsaye tana zagaye, Umma!
A hankali ta kirata tana kallanta, da sauri Umma ta taho, itama Zainab ta nufo ta, sai da suka matso kusa da juna sannan Umma tace “Alhamdulila dan na
tsorata da akace bakya nan a waje ina tsoron kar wani abu ne ya faru kikai wani gun.”
Tsayawa tai tana kallan Umma, ashe haka uwa ke da dadi?
Murmushi ta mata sannan ta nuna mata takardar tace “ya sakeni Umma.”
Da sauri Umma ta amsa, da yake ba boko tai ba sai dan wanda Khalid ya nuna mata a gida ta dai dan fahimta gane cikin kokonto da sauri ta kalleta tace “Har
Uku?”
Murmushi Zainab ta sakeyi tace “Eh Umma.”
Shiru Umma tai tana kallanta, kafin tace “ki shiga ciki ki sanar da mahaifinki.”
Kai ta daga sannan tai ciki, Umma ta bita da kallan tausayi sosai dan har sai dataji idanunta sun dan ciko.
Gun Abba ta nufa ta sanar dashi yanda akai, hankalinsa shima ya tashi yace “wannan wani sakaram miji ta samu dahar zaiyi saki uku lokaci daya?”
********
Adam kam yaci uban tafiya yana tafe kamar mara lafiya, dakyar ya iso ga uban yunwa dake damunshi, yana zuwa Amir ya bashi key ya tafi ball dinsa, shiru Adam
yai yana kallan gidan data fito dazu, gaba daya ya rasa abinda xaiyi sai dai yasan duk abinda zaice yanzu a banza yake gwara yaje gun Goggo su samo shawara.
Jan motar yai ya fito, a hanya ya tsaya yasai biscuit da juice ya cucusa sannan ya karasa gida.
Bala na tsaye yana kallan Adam dake ta danna mai horn, Bala na kallansa bai ko binta kansa ba yana jin radio dinsa, haushi ne ya kama Adam ya fito a zuciye
ya nufi Bala yace “kai Bala ka bude min gate ko sai na ci mutuncin ka?”
Bala cikin maganarsa ta hausar yan niger yace ” Hajiya ta kira yanzu tace ku bar mata gida dan haka bazan bude ba.”
Adam cikin kofula ya nufoshi, Bala ya kalleshi yace “ka tabbatar zaka iya dukana?”
Kallansa yai kamar zai karasa gunsa sai naga ya bude gate ya shiga, Bala yace “awa biyu na baku ku fito daga gidan nan, dan Hajiya tace inbaku fito ba na
dau hukunci da kaina, sannan kunsan mu buzaye ba hakuri, nan da awa biyu yan sanda zasuzo inkunga dama karku fito.”
Adam ya wuce ciki, haryaje zai shiga ya dawo da gudu ya zare key din motarsa dan dama ya saba wannan shirman balle in a gidane sau dayawa ma baya rufe
motar.
Bala ya bishi da kallan takaici yana tuno abinda suka mai jiya, har fara yake su wuce awa biyun nan dan wlh sai ya rama wulakancinsa.
Adam ne ya shiga falo, Goggo na zaune ta soya dankali da kwai tana ci tana kallan tv, daga bakin kofa ya tsaya ya zuba mata ido, gefe ta hada tea dinta mai
kauri.
Kallansa tai tace “Adam ka dawo?”
Kasa mata magana yai sai kallanta kawai da yake, kallansa tai tace “matsalarka kenan sai kai abu kazo kana nadama, kai dai dakai sa’a matarka nasan aikinta
in ba haka ba uban wa zai bar ma gida?”
Haryanzu kallanta kawai yake tana cin abincinta tana magana, ganin yaki shigowa ne yasa tace “karka damu duk wanda yai saki da wanda aka saka sai yaji haka
nadan wani lokaci amma komai zai warware a hankali, kazo kaci abinci naka na kitchen.”
Ganin takaici yaki karewa ne yasa ya matso ya kashe tv din sannan ya kalleta rai a bace.
Kallansa tai tana kurbar tea tana harararsa kafin tace “uban wa yasa ka aikata? Da zaka nemi hucewa akaina?”
Huci ya fara yi yana kallanta, bata tankashi ba dan gani take duk saboda ya saki matarsa ne, abincinta ta cigaba daci, kawai jitai yasa kuka.
Kallansa tai tace “tashi kaje daki kayi abinka ni karka sani a gaba kamar ni na kashe ma aure.”
Cikin masifa yace “bake kika kashemin ba amma kinada babban hannu a ciki.”
Kallansa tai tace “a ina kenan?”
A zuciye yace “ta kwaci sakinta bata kuma bamu gidan ba, yanzu Bala yace mu fita nan da awa biyu.”
Cup din tea din dake hannunta ta yar bata sani ba, tea din ya zube dan har kan cinyarta, ko zafin bataji ba dan ma ba tafashashe bane, Adam ne ya matso
yana kuka yace “Goggo ya zamuyi?”
Kallansa kawai take kafin tace “Sakin ka bata kafin ta baka takardun gidan?”
Yace “cewa tai in na bata zata bani.”
Baki kawai ta bude tana kallansa, yacigaba to na bata kuma ta koren dan da kafa ma na nufi gidan.
Nawa ka mata?
A hankali yace uku……..
Wani wankenken mari yaji ta zabgamai, da sauri ya kalleta, rufeshi tai da duka ta ko ina da hannu biyu, tana dukanshi tana wannan wannan nikam bakin cikinka
ne zai kasheni ban taba ganin mutum wanda gaba daya baida lissafi da tunani ba irinka, ka kwashe komai na gadon mu ka cinye a tsinanen karatun da ba abinda
ya tsinana mana, kayi aure mun taho nan tunda aka bikinka ko kauye bamu kara zuwa ba sannan yanzu kazo kana cemin ka bada saki uku ba tare da ko daki biyu
mun samu inda zamu zauna ba?
Adam kuka kawai yake yana cewa “na dauka zata bani wlh.”
Daina dukanshi tai kawai ta fashe da kuka wiwi, Shikenan rayuwarmu ta kare munga ta kanmu.”
Adam yana kuka yace “Goggo nanda awa biyu yan sanda zasuzo su koremu.”
Kallansa tai kamar ta kara jibgarsa sai dai a wannan lokacin mafita take nema, wayarta ta dauko ta hau kiran Zainab, ta roketa ko dakin waje ne ta taimaka
ta barsu su zauna, duk yanda ta kira Zainab bata dauka ba, daga baya ma ce mata akai wayar a kashe take.
Hankalin Goggo ya sake tashi matuka.
Kallan Adam tai da sauri tace “tashi mu hada kaya, duk wani abu mu tattare mu debi rabanmu.”
In muka kwashi kayan ina zamu?
Tace “kai ka tafi wani gidan ka kwana ni zani gidan Hajiya bilki na dan kwana biyu sai musan abin yi.”
Kallanta yai yace “ni banida inda zani, Ziyad bayanan sannan ko yana nan ma a gidan iyayensa yake kwana anan, Goggo ki taimaka ki tafi dani”‘
Wayarta ta dauka ta kira Hajiya bilki sai dai tai rashin sa’a domin bata kasar sunje sari dubai.
Hankali a tashe ta kalli Adam, nan ta sake kiran wata kawarta, ita kuma jin zatazo kwana yasa tace tanada baki, Goggo hankalinta ya tashi nan fa ta shiga
kiran duk nambobin kawayenta dana kusa da wadanda ba wani ma shiri suke ba, sai dai duk wanda yaji kwana zatazo sai ya fara kame kame da alama dukansu bamai
san tazo kwana.
Hankalinta a tashe tace kafin yan sanda su wulakantamu a unguwar nan ka tashi mu kwashe kaya tunda kunada yar motar nan masan yanda zamuyi.
Haka suka kwashe kaya, Goggo sai data kwashe duk wani fruit da juice na gidan, taso kwasan su dankali Adam yace a ina zaki dafa inkin dauka? Haka ta ajiye
amma sai data kinkimi indomie da taliya.
Haka su fito sukai ta lafta kaya a boat din mota a waye, Bala na ganinsu ya fara waya wai da yan sanda yana cewa kuna hanya? To sai kun iso.
Goggo naji suka sake rudewa, haka suka fito Adam najan Goggo tana makalewa dan itakam wannan gida bata san barinsa, suna zuwa gate ta koma ciki da gudu
tana kuka.
Falo ta koma ta zauna akan kujera, Bala da Adam ne suka biyota, Bala yace “Goggo kin fito ko sai na radeki?”
Kallansa tai tace “ka radeni amma bazan bar gidan nan ba.”
Dariya yai yace “to ki zauna bari su karaso.”
Adam ya kalleta yace “Goggo?”
Wani mugun kallo tamai tace “nikam ka ciceni wlh, kai dayin tsiya ni da shiga tashin hankali?”
Adam zaiyi magana sukaji ana bubuga kofa, kallanta yai da sauri yace “gasunan ki fito kafin a toxartamu.”
Mikewa tak ya jawota tana tafe tana tirjewa kai kace karamar yarinya ce, a haka suka isa gate, Lokacin Bala ya bude musu.
Kallansu sukai sannan suka kali Bala ogan yace “wad’an nan Hajiyar take nufi?”
Bala yace eh
Kallansu yai yace “kum wuce ko kuwa?”
Haka Adam yaja Goggo ya cusata a mota suka tafi.”
Bala ya bisu da harara badan Hajiya tace duk abinda suka dauka karya hana ba ai da sai ya kwashe kayan da suka kwaso.
Suna tafe a hanya goggo na hawaye, daga ta tuno sai ta make Adam.
*******
Khalid kam wanda baisan abinda ake ba daga gun aikinsu da Salmanu ya wuce tasha ya hau kota zuwa kano, yana isa ya kira Razy wacce gaba daya tun jiya take
cikin tashin hankali, haka ta daga cikin takaici, Khalid yace kina ina? Ko kina gidanku?
Da sauri tace “ina Tarauni, nan ta sanar dashi inda take.”
Haka ya hau adaidaita ya karasa gidan data kwatantamai sannan ya kirata.
Fitowa tai dan tun jiya ta kori Bash ita kadai ce a gidan, a kofa ta ganshi a tsaye, baki tadan tabe ganin ko mota bashi da ita.
Kallansa tai tace “anan zamuyi maganar?”
Yace “eh”
Kallansa tai tace “ko ka shigo ciki?”
Kallanta yai yace “bana shiga gidan karuwai.”
Labanta ta ciza cikin takaici tace “to anan zamuyi maganar?”
eh.
Haushi ne ya kara kamata ta kalleshi rai a bace, jingina yai da bango, tace “ka shigo jikin gate din to banasan sirrina ya fita ne.”
Yanzu kam ya dan kalleta sannan ya dan shiga ya tsaya daga jikin gate din.
Kusa dashi taje ta tsaya, kallanta yai yace “Me nene tsakaninki da Adam da har kika lalatamai rayuwa?”
Hannunta ya kalla wanda ke kokarin taba kirjinsa, kallanta yai sannan yai wani murmushi yace “me? Nima seducing dina zakiyi?”
Cikin kallan jan hankali tace “kai ba namiji bane.”
Biro ya ciro ya ture hannunta dashi sannan ya kalleta yace “you can’t seduce me ko kayanki kika cire a gabana.”
Kallansa tai tace “do you have that confidence?”
Kai yadan karkace ya daga mata kadan sannan yace “you are not that attractive bansan ya akai kika jan ra’ayin maza ba, ahhh na tuna suma tunaninsu ba daya
yake ba.”
Fuskarta ce ta canza, ranta yakai matuka gun baci tace “am not that attractive?”
Yace “badai sun miki karya akan you are ba?”
Yanda take kumbura take hura hanci ne yasa yasan taji haushi sosai kallanta yai yace “fadamin menene tsakaninku?”
“Kai meye tsakaninka da Zainab? Meye naka na shiga abinda bai dameka ba?”
Kallanta yai yace “inje Naibawa?da alama can zan fi jin komai.”
Da sauri tace “zan fadama.”
Kallanta yai yace “meye tsakaninku?”
Bakimta ta ciza idanunta suka ciko tace “kasan bakar rayuwar da muka fuskanta akansa?”
Kallanta yai baice komai ba, hawayen da suka zubo mata ta goge sannan ta kalleshi idanunta na kara cikowa tace “Abinda ya mana ko rabinshi ban mai ba, mu
gaba daya rayuwarmu ya salwantar shifa? Rabashi kawai nai da matarsa.”
Kawai? Ya fada yana kallanta, kome ya muku meyasa baki fadamai ya nemi yafiya ba in har bada saninsa bane?”
Yafiya? Ta maimaita sannan tasa wata dariya tace “gun wa? Gun wacce ta rasu? Ko guna? Ko gun iyayen mu?”
Kallanta yai yace “Raziya!”
Yanda ya kirata ne yasa ta zubamai ido, wannan karan shine lokaci na farko data mai kallan mutunci, murmushi tai na takaici sannan tace “Zan fadama yanzu.”
Kallanta yai sannan ta sake murmushi ta bude baki zata fara magana……….
*********
Hankali a tashe Dady yace “saki?”
Zainab tace “eh dady yanzu na amshi takardar.”
Cikin fada yace “wani irin hauka ne wannan? Taya mutumin da kece wahalarsa zai sakeki ba tare da dogon nazari ba? Me kikai haka?”
Tace “ba abinda namai.”
To fadamin meya faru haka? Yanzu zanyi booking flight zan taho gidan nazo na daukeki.
Da sauri tace “inje ina?”
Ki taho nan mana, ina zaki zauna ke kadai kiyi idda?
Tab ai dataje su zauna gida daya da Basma gwara ta zauna ita kadai, da wace fuska zasu kalli juna a gidan? Gasu Nabila basa nan bare su rage musu matslar
zaman?
Dady ne ya katseta meya hadaku?”
Shiru tai tana tunani, ta ina zata iya cemai ta kamashi da mace a daki?
Daurewa tai tace ya samu canjin ra’ayi na zuciya ne, sannan nima na gaji da zaman,
Canjin ra’ayi? Gajiya da zama?
Kina gidanki? Zanzo anjima.
Da sauri tace “bana gida Dady.”
Cikin mamaki yace “kina ina?”
Ina gidan ina gidan…. can tace “gidansu wannan driver din.”
Mamaki ne ya kamashi yace “turon da Address zanzo.”
Yana kaiwa nan ya kashe, idanunta ta runtse, Umma ce ta kwankwasa kafin ta shigo.
Zainab ta kalla wacce ke rike da waya, abinci ta ajiye mata sannan ta xauna kusa da ita ta kamo hannunta.
Zainab ce ta kalleta cikin jin dadi tace “Umma!”
Murmushi Umma ta mata tace “bakomai, Allah na tare dake.”
Kai ta daga da sauri tace “Umma menene laifina? Dan na kula dasu? Danki yace komai laifinane.”
Ta karasa tana hadiye kukanta.
Umma tai murmushi tace “kyale wannan shi dama haka yake fadar magana dan ran mutum ya baci.”
“Eh mana haka yake duk sanda yazo sai ya konan rai”
Umma tace “kingani ko? Kyaleshi haka wannan halin nasa yake.”
Zainab tace “ga fadar bakar magana ba ruwanshi da yanda mutum zai ji.”
Umma Tace “d’a nane amma akwai wannan” ta fada tana dariya, itama dariya Zainab tai kafin tai shiru tana kallan Umma….