NOVELSUncategorized

A GIDANA 35

#OneLove❣

{35}

Umma ta zuba mata ido tasan ita kadai tasan me takeji da har komaima fada takeyi, ganin yanda Umma ke kallanta ne yasa tai kasa da ido, a hankali Umma ta sa hannun kan goshinta, zafin dataji ne yasa ta kalleta da sauri, Zainab ta kalleta cikin mamaki sannan tasa hannu a wuyanta, itakam bataji komai ba.

 Umma fitowa tai ta wuce gun Abba da sauri, Abba ne ya kalleta yace “Ina yar……”

“Abban Khalid yarinyar nan fa batada lafiya, tsabar zafin abinda ta gani da alama yasa batasan ma meke faruwa da ita ba.”

 Cikin mamaki yace “meta gani?”

 Shiru tai batace komai ba, murmushi yai yace “nayi shiru tunda sirrinku ne yanzu ya za’ai? Asibiti za’a kaita?”

 Khalid ne bansan inda yake ba, nakira wayarshi bata shiga ba, gaba daya hankalin Umma a tashe yake, Abba ne ya miko matw paracetamol a cikin magungunansa 

yace “ki bata wannan tasha ta kwanta in akai sa’a kiga komai yazo da sauki.”

 Amsa tai ta fito da sauri dakin ta shiga Zainab na zaune ta kurawa kasa kallo, jin motsin Umma ne yasa ta kalleta da sauri, Umma ta mika mata magani, amsa 

tai tasha batare da ta tambayi dalili ba, Umma ta zauna kusa da ita tace “kin fadawa baban naki?”
 Kai ta daga ahankali, Umma tai shiru tana kallanta cikin tausayawa.

 Juyowa Zainab tai sannan tai murmushin yake tace “Umma abinda na fada miki…….”
Bazan fadawa kowa ba, kai ta girgiza da sauri tace “bashi ba, ko an sani ma magana ta wuce ai, kawai bansan Dady yasan meya faru ne, sannan kiyi hakuri dan 

yace zaizo.”

 Kai Umma ta jinjina tace “dole yazo ai saboda halin da kike ciki, amma meyasa bazaki fadamai ba?”

 Idanunta ne suka fara canzawa tace “taya zan fadamai abinda nasan zaizamarmai tabo?”

 Umma tai shiru tana kallanta, bata tambayeta dalili ba ita kuma Zainab batace komai ba sai dai a ranta tace tasan tabbas Dady ya sani bazai yafewa kansa ba 

zaiyi tunanin duk abinda ya faru ne yajawo haka.


********

 Taku biyu tai zuwa gaban Khalid, batare da ta juyo ba tace “Adam da Ya Fiddausi ni kaina bansan ya akai suka hadu ba, sai dai tun sanda na dawo daga 

makarantar kwana take bani labarin saurayin datai, wani irin so suke ma junansu, wanda gaba daya iyayenmu suka maidashi dan gida, a lokacin ina makaranta.
 A gidan mu yawanci yake cin abinci saboda karatun da yake a BUK, Yaya na tsananin sansa, dadin dadawa daya ce mata shi AA ne yasa ta kwallafa rai dashi, 

tanada yawan ciwoka wannan kam kowa yasan saboda ciwonta ne, ga wahalalen ciwon baya da take dashi, akoda yaushe Adam ne ke kula da magungunanta, dan ko 

yana makaranta in lokacim shan maganinta yai yana kiranta, wani irin soyayya sukema juna wanda ni har mamaki nake in na dawo ta dinga min zancen, sau biyu 

ina ganinsa sai dai yanda yake nunawa Yaya tsantsar so da kauna yasa ma gaba daya nima na aminta da shi, iyayenmu sun sadaukar da duk wani kauna akanshi, 

dan akwai sanda yazo gunta cikin tashin hankali saboda bashida kudin biyan kudin makaranta, haka ta sanarwa Baba ba tare da wani kokonto ba suka saida keken 

dinki Mamanmu aka bashi ya biya.

 Sam yanda suka daukeshi kai kace sirikinsu ne, dan shi im ta tashine da an daura musu aure kafin ya gama karatun, Baba ne ya hana a cewarsa hankalinsa zai 

rabu biyu, gashi yace bayasan tai karatu saboda yanayin lafiyarta, gwara ta xauna shi ya musu, Baba baiso ba sai dai ita Yaya ta nuna hakan takeso dan duk 

abinda ya fada shi take so.

Haka ya cigaba da karatunsa, duk sanda Baba ya samu kudi burinsa yamai dinki ko ya bashi ya kashe, ni da nake boarding sai nai zuwa nawa amma dakyar Baba ke 

bani dubu daya da dari biyar a gabana kuma zai ba Yaya dubu hudu-biyar yace taba Adam.

Haka suka share shekara 3 suna cin soyayya mai tsafta dan yasha faduwa jarabawa in bai samu damar biya ba haka Baba zaici bashi a biya mai, hartakai an samu 

ya kammala karatunsa.

 Wata biyar da kammala karatunsa komai ya fara canzawa, dan ko Yaya ta kirashi baya dauka, hankalinta ya tashi, har garinsu ta nike gari taje sai dai randa 

taje mahaifiyarsa ke fada mata an tafi sa ranar Adam sannan tace ta rufa mata asiri kafin ma wani yaji ta kwashi kafarta ta tafi dan da wacce xai aura.

 Dakyar Yaya ta kawo kanta gida, tundaga ranar ciwo ya rufketa, banda kiran wayarsa da kuka ba abinda takeyi, abinci wannan sai ana dura mata takeci.
 Baba dakanshi yaje garin sai dai wulakancin da mahaifiyarsa ta masa akan yana musu bakin ciki dan zai auri mai kudi da kuma wanda Adam ya masa akan shi aba 

Fiddausi hakuri shiyanzu saura wata uku bikinsa gini ma sukeyi na inda zasu zauna.

 Haka Baba ya dawo cikin tashin hankali da bakin ciki, Yaya ta shiga tashin hankali ta rame duk ta kanjame ga azababbem ciwom baya da takeyi, a haka ne na 

kammala karatu na dawo gida.

 Ranar daurin auransa……..

 Hawayenta ta share sannan ta cigaba, ranar da komai na rayuwarmu ya ruguje, Yaya ciwonta ya tashi ga ciwon yunwa da damuwa, munje asibiti akace jininta ya 

hau sosai sannan zuciyarta ta fara kumbura, haka aka bamu gado aka yanke mana uban kudi zumzurutu da zamu biya, saboda munje asibitin gomnati abu yaki 

yiwuwa dole muka dawo na kudi.

  A ranar auransa ciwonta ya tashi a asibiti gashi sunce bazasu mana komai ba harsai mun bada rabin kudi tunda haryanzu basuga komai ba.

 Haka Baba ya fito ya saida mashin dinshi wanda ba wani kudi ya hada ba, ya daga gidan mu sai dai ba mai siya, Mama tai kuka da kanta ta nufi kauyensu akan 

yazo saboda sunansa kawai take kira, Mama ta nemi yazo ko na awa daya ne in ta ganshi sai ya koma, sai dai mutumin nan da aka tambayeshi wacece ma sai cewa 

yai bai taba ganinta ba da alama neman taimako tazo.

 Haka Mama ta dawo tana kuka, ga Yaya numfashinta ma ya daina fita daidai, hankalina a tashe na shiga gun likitan na sa gwiwowina a kasa ina neman ya 

taimaka wa Yaya.

 Juyowa tai tana kallansa tace “kasan meyace?”

Bata jira amsarsa ba tace “cewa yai sai na bashi kaina zai taimaketa.”

 Haka na fito ina kuka sai dai ganin yanda yaya take ga Mama na kuka a gefenta, ga Baba ya dawo jiki a sanyaye yasa na koma dakin nan.

 Hawayenta ta share ta cigaba haka na ba likitan dako sunanshi bansani ba kaina, sai daya biya bukatarsa sannan yazo aka bata gado, sai dai duk sanda zai 

dubata sai ya kusanceni, haka duk dare banda kuka ba abinda nakeyi, a rana ta uku da kaita asibiti, ciwonta ya tashi sosai, gun likita na nufa yana biya 

bukatar sa Allah yai ajalin Yaya.

 Tana kaiwa nan ta hadiye wani abu daya tsaya mata, Mama tana ganin yaya ta tasu ta fadi a kasa ciwom barin jiki ya kamata, har yau tana nan komai yi mata 

akeyi.

 Takowa tai zuwa inda Khalid yai mutuwar tsaye tai, tace “kanada magana akan abinda na aikata?”

 Kallan idanunta dake nuna mikin da aka bude take sannan ta share hawayenta tace “tundaga nan nike ciyar da gidan mu, saboda Baba na gida yana kula da Mama, 

tun kuma daga sanda na taso da kudirin halaka rayuwarsa dan da wannan kadarin kadai na taso zuwa yanzu” 
Tadan ja numfashi sannan tace “in ka gama jin abinda kake san ji ni zan shiga ciki.”

 Da sauri ta wuce kafin tajira mai zaice, tana shiga tasa kuka.

 Gaba daya Khalid ya kasa ko motsi, saboda abinda yaji bai taba tunanin abin yakai haka ba.
ne ya kamata, sannan ya juya dakyar ya fita daga gidan.


*******

 Kanasan cemin tsinaniya dubu ashirin kadai gareka a banki?

 Kallanta yai yace “to me nakeyi dazan samu kudi?”

 Ranta a bace tace “duk ina uban kudin da matarka take baka? Duk wata dubu saba’in take baka ko ka dauka bansani ba? Kudin da take baka ko ita bata cin 

rabinsu.”

 Kallanta yai yace “ina suke kuwa? Duk na cinye.”

 Haushi ya kamata tace “amma wannan wannan ni dai banji dadin haihuwa ba, to yanzu gidan ubanwa kake so mu kwana?”

Inafa na sani mu koma kawai can gidansu kawo shehu.

Kaci gidanku mu koma mu musu uban me bayan kasan yanda muka rabu?

 Haushi ya kamashi yace “to sai dai kuwa mu kwana a mota.”

 Kallan motar tai sannan tace “in muna bukatar bayan gida fa? Dan ni yanzu ma ji nake.”

 Sai kije na kan hanya.

Kwade kansa tai tace “cemaka akai banda mafadi, nidai wlh Adam ka cuceni wannan abu dakai wlh ni ka cuta.” Ta karasa tana murza ido.

 Ya kalleta a kufule yace “sai dukana kike kina cewa nina ja miki, amma kinsan hadda ke ko? Dakin tubure sanda zan kawota ai da duk ba haka ba.”

 Baki ta saki tana kallanshi tace “kenan laifi nane?”

 Bawai naki kadai ba namu ne duka.

 Haushi taji tundaga nan bata sake mai magana ba, haka suka sai naman tsire da lemo sukai parking suna ci kowa rai a bace, suna gamawa ta kalli gari tace 

“yanzu haka zamu kare a titi?”
Kallanta yai yace “ko mu roki babanta? Ko dan daki daya ya sai mana.”

Wani banzan kallo tamai kafin tace kai Addu’a ma karyasa a daureka.

 Da sauri ya shafi hannunsa sannan yai shiru, haka suka zauna a mota suna kallan juna kafin Goggo baccinya dauketa yo bata saba zama gum ba badan kallo ko 

taune taune.


******

Yana tafe gaba daya zuciyarsa ba dadi.

 Yana shiga kan layinsu yaga motar datai parking mutumin dake jikinta yana tambaya, Khalid yaje wucewa yaji ance Khalid!

 Yana juyowa yaga Dady, mutumin yace “yauwa ga Khalid din ma.”

 Da sauri Khalid ya karasa ya gaisheshi.

 Dady ya sallami mai motar sannan ya kalleshi ya amsa gaisuwar yana cewa “Allah yayi a hanya zamu dinga haduwa.”

 Murmushi Khalid yai, tafiya suka fara Dady yace “Ashe abokinka sakinta yai.”
 Da sauri Khalid ya kalleshi, Dady yace “baka sani ba? Saki uku ya mata.”

Idanunsa ya dan runtse cikin takaici wannan haukar na Adam, Dady ya murmusa yace “mungode sosai da taimakom da ka mana, dama tunda na ganka hankalina ya 

kwanta dakai, ashe raban zaka cecemu ne.”

 Da sauri Khalid yce “ba wani abu danai”

Dady ya kalli gidan da Khalid ya tsaya sannan yace “nan ne?”

 Khalid yace “eh”

 Nan ya shiga yabar dady a waje yana kara kallan gidan.

 Umma na tatar koko ya shigo, tana ganinshi ta hade fuska, murmushi yai yace “tuba nake Ummana duk dabansan laifina ba.”

 Tace “inata kiranka wayarka a kashe.”

 Yace “Yahkuri Ummana, munyi bako.”

 Bako? Ya iso kenan?”
Yace “eh ashe kunsan da zuwan.”

 Ajiye abin tatar tai ta matsar dashi ta shiga ciki tace “shigo dashi.”

 Haka Dady ya shigo ya shiga falo.

 Abba dake zaune yana jin radio ya kalla bayan ya zauna, gaisawa sukai cikin girmama juna, Khalid ya ajiye musu ruwa sannan ya dan matsa gefe.

 Zainab kam tundataji Umma ta fada mata zuwansa gabanta ke faduwa haka ta dake ta zura hijab ta fito.

 Tana fitowa Khalid ya mike ya fito.

 Dady ne ya kalleta, Abba yace “Khalid ka bude musu dakinka su shiga ko kuma taimaka min na koma daki na basu guri.”

 Dady yace “bakomai wlh ka zauna magana ce wacce kun sani gwara ayi a gabanka.”

 Abba ya kalli Khalid yace “Khalid karaso.”

 Haka Khalid ya taimaka mai ya shiga daki, Sannan yazo ya fita.

 Dady ne ya kalleta yace “Zainab!”

  Kallansa tai tare dayin murmushi bayan sun gaisa ne ta mikamai takarda.

 Ransa yayi mugun baci dan bacin ransa ya fito karara ya kalleta yace “wannan wani irin butulci ne?”
 Kallansa tai batace komai ba, yacigaba “nasani sarai kin aureshi ne saboda ni, kin samu wanda baya sana’a wanda kuma bashi da burin tabuka komai saboda 

kina tsoron abinda ya faru da mahaifiyarki, yanzu kin fahimci wayanka baya sai ma komai?”

 Idanunta ne sukai jaaa sai dai haryanzu batace komai ba, Dady tausayinta ya kamashi yace “fadamin menene ya jawo sakin nan?”

 Kallansa tai tace “yanda manfadama ra’ayinmu ne ya banbanta da juna.” Yanda tai maganar cikin dakewa tayita sai dai Dady ya fahimci tana cikin tashin 

hankali, hakan yasa yace “tashi mu tafi gida, duk zaman da aka ga kinayi ke kadai ne ma yasa abin yakai haka.”

 Gida?

 Ta fada da sauri tana kallansa, yace “me? Badai kina tunanin na barki anan bane?”

 Kallansa tai tace “Dady kafi kowa sanin yanda nake da matarka wani irin zama zamuyi a gida daya?”

Matata? Matata ba mamanki bace?”

 Shiru Zainab tai kafin tace “kayi hakuri Dady amma bazamu iya zama gida daya ba.”

 Kallanta yai sannan a hankali yace “taya zaki zo gidan mutanen da baki da hadi dasu kice zaki zauna kiyi iddah a gunsh? In ke kin yarda su ce miki akai sun 

yarda ko ni ce mike nai na yadda?”

 Kallansa tai ta matso kusa dashi sannan ta tsuguna a kasa tace “Dady ka taimaka ka barni anan, inasan zama anan, inaji a jikina hankalina zaifi kwanciya 

anan.”

Kallanta yai yace “anan gidan?”

Ta fahimci meyake nufi tace “eh, dan Allah dady kamin alfarmar kabarni, nasan Umma bazata hanani ba.”

 Shiru yai yana kallanta kafin ya ja nunfashi yace “sai na tambayesh.”

 Da sauri tace “na gode Dady ta fada tana share kwallarta.
Dady ya zuba mata ido wai itama tata kaddarar kenen, lalai alhakin Ummy ne ya kamashi, gashinan yarsa na kunsar abinda ya kunsawa yar wani, ita nata ma 

sakin wulakanci har uku.

 Zainab ce takatse tunaninsa tace “Dady ka taimaka ka sanar a gun aikina akan zan dau hutun wata uku, ko kuma kace nayi tafiya gudun kananan maganganu, nima 

zan tura musu email.”

 Kai ya daga alamar fahimta tausayinta na kara kamashi.

Haka ya tambayi Abba da Umma wanda a take suka amince tare da mai alkawarin kula da ita harta gama idarta.

 Haka ya fita gaba daya jikinda yai sanyi, Khalid ya nemi ya maidashi Kano a motar Zainab, nan ya amince sai dai suna fita yace Khalid ya kaishi shago 

zaisai abu, nan fa Dady yahau siyo su Buhun shinkafa, taliya, Marconi, shinkafar turo, indomie, juices ruwa da sauransu, Khalid da sauri yace Dady?

Dady yace “ka taimaka Khalid nima hankalina zaifi kwanciya akalla na taimaka da wani abun, nayi ne dan hankalina ya kwanta, nasan xaka fahimci halin da 

wannan mahaifin ke ciki.”

Haka suka kai kaya yasa dubu ashirin  a cikin katan din juice, Khalid kansa bai sani ba, haka suka ajiye suka nufi kano.

 A hanya sai godiya Dady yakeyi yana jimamin wannan abun…….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button