Labarai

A Karshe dai Za’a Sulhunta Rikicin Dake Tsakanin Mawaƙi Rarara Da Mustapha Nabraska

A Karshe dai Za’a Sulhunta Rikicin Dake Tsakanin Mawaƙi Rarara Da Mustapha Nabraska

Fitaccen Dan jaridan nan dake Abuja Alhaji Sani Musa Mairiga, ya ce insha Allah zai shiga tsakani domin kawo zaman lafiya tsakanin Shaharanran mawakin siyasar nan Alhaji Daudu Kahutu Rarara da kuma Dan wasan Kannywood Mustapha Badamasi Naburaska wanda shine mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje akan farfaganda.

Tun bayan zaben fitar da gwani na Jami,iyar APC a Jihar Kano ne Wanda Mataimakin Gwanan jihar Nasira Gawuna ya lashe kuma ya zama dan takarar gwana a karkshin jam’iyar APC, aka fara takun saka da kuma nunawa juna yatsa tsakanin Rarara da kuma Naburaska, saboda mawakin yace bazai goyi bayan Gawuna ba,har ma ya rerawa Dan takarar jami’yyar ADC waka.

Alhaji Sani Musa Mairiga ya ce ya fara wani yunkurin shiga tsakani domin kawo karshen wannan matsala, inda ya ce nan bada jimawa ba komi zai daidaita.

“Insha Allah a matsayin mu na musulmai bai kamata mu zura Ido Muna kallon yadda suke yamutsa gashin Baki da kuma tayar da jijiyoyin waya ba.”

Sani Mairiga yace ya fara tuntuɓar Rarara domin wannan zaman wanda za su yi, walau a Kano ko a Abuja.

Ya kuma bukaci musulmai da su cigaba da son juna domin akwai mutuwa akwai kuma hisabi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button