MADADI Page 91 to 100

Hajia ganin lokaci yana ja mahaifar taqi ta fad’o sai kawai ta yanke shawara akan su tafi asibiti zaifi kwanciyar hankali………
Hankali a tashe Ramlatu ta bude wardrobe cikin sauri ta dauko riga da zani na atampa, hajian ta kar’ba tana kokarin sanya mata Allah sarki Naja’atu Idan kuka ga Naja’atu a lokacin sai kun tausaya mata dan tayi masifar galabaita kokarin kwanciya ma takeyi hajia na hana ta………Hajia Rabi ce ta shigo d’akin da sauri ta kalli Ramlatu da fadin ” Taimaka mu kamata yanzu nasa ‘Dan Azimi ya fito da mota.” Sai suka fara kokarin miqar da ita, tana lanjarewa kuka take da fad’in su yafe mata mutuwa za tayi, lokacin da take wannan maganar gabad’ayansu jikinsu mutuwa yay Hajia kuwa da yake mai saurin kuka ce tuni hawaye sun ‘balle mata.
Ya Ramlatu tace”Ba zaki mutu ba Naja’atu insha Allah zakiyi dogon zango a duniya kiyi hakuri kinji ko ita haihuwa haka take da sammatsi muna zuwa asibiti zasu taimaka miki.”
Girgiza kanta kawai take tana karanto sunayen Allah dari ba d’aya a zuciyarta.
Hajia tace”Yana da kyau aje a sanar da iyayenta halin da ake ciki.” Ya Ramlatu tace”Hakane bari nasa Dan Azimi ya buga musu kofa.”
Naja’atu riqe hannunta tayi tana girgiza mata kai magana takeso tayi amma bakinta yayi nauyi wani irin ciwo mararta yake mata, Hajia Rabi ta riqeta a jikinta tana tofa mata Addua duk sun rasa yanda zasuyi ita ba miji ba ballantana a kirasa yazo ya dauketa yasa a mota……..Cigaba sukayi dayi mata taimako irin na gida, cikin ikon Allah ta dinga wani irin yunkuri kamar wacce zata sake sabuwar haihuwa mahaifar ce ta fad’o kafin wani uban jini ya biyo bayanta.
Gabad’ayansu suka shiga godewa Allah dan ganin yanda ya gajarta musu wahala basu sha wahalar zuwa asibiti ba amma a zahirin gaskiya haihuwar tazo da tangard’a! amma dai tunda Allah ya raba lafiya sai su gode masa……..Kafin gari ya waye komai yayi tsaf! Hajia Rabi da Yaya Ramlatu sun gyara maijego da babynta mai kama da ubansa, dakin yayi tsaf dashi sai qamshin turaran wuta yakeyi…..Da Asubah Hajia ta sanar da Alhaji haihuwar ya dinga murna da farin ciki yana Allah Allah a idar da Sallar ya sanar da Mahaifin yarinyar, to shima Malam yayi farin ciki dajin cewa yarinyar shi ta haihu cikin koshin lafiya, cike da farin ciki ya shiga gida domin ya sanarwa da matarsa halin da ake ciki.
Yaya Ramlatu itake tsaye a kan Naja’atu da yaronta dan da gari ya waye ma itace tayi wa yaron wanka ta shiryashi cikin kayan sanyi sannan ta kai Naja’atu toilet ta gasa mata jikinta sosai tasa ta ta zauna a cikin ruwan d’umi! Naja’atu ta dinga mamakin irin dawainiyar da Ramlatu keyi mata ko a mafarki bata ta’ba tunanin hakan na iya faruwa ba.
Kafin takwas na safe Naja’atu tasha gayu tayi kyau tamkar ba ita ba, Ya ramlatu ta taimaka mata ta shirya jikinta cikin wani Swiss les mai kyau! Hajia kuwa da kanta ta shiga kicin tayi mata abun kari na mussaman sannan ta zauna a kusa da ita sai data tabbatar da taci ta koshi tukkuna ta fita daga dakin……Bayan kowa ya gama shige da ficensa a dakin, Naja’atu a hankali ta kai hannu inda yaron yake ta daukoshi ta riqe a hannunta, tsira masa ido tayi kawai tana kallonsa, yaron kamar sa daya da ubansa tamkar Bash yayi kaki! ya tofar, wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga zobo mata, wai yau itace ke dauke da d’an Bash a hannunta, ashe dai sai ta fara haifawa Bash d’a kafin ta haifawa Abbah Abbas, gabanta ne ya fad’i Data tuna irin kauce kaucen da Abbah Abbas din ke mata, to yanzu dai gashi ta haihu lafiya kome zai biyo baya oho! itakam idan Abbah bai mai da ita gidansa ba to tana jin ita da aure har abadah!
Hawayen take sharewa wasu na sake kwararowa, cikin wannan halin ya shiga dakin ya sameta.
Bata san ma ya shigo ba sai qamshin turaransa ne ya sanar mata shigowar tasa, da sauri ta dago kanta tana kallonsa suka tsirawa juna ido………Dauke kansa yayi daga kallonta cikin nutsuwa ya zauna gefanta tare dasa hannunsa ya kar’bi yaron yana dubashi.
Tausayinsa da tsantsar kaunarsa suka sake karya mata zuciya sai kawai ta dukufar da kanta ta cigaba da rera kuka wanda na rasa ko na menene!
Abbah bakinsa yasa kunnan yaron dama da hagu yayi masa kiransa sallah sau uku sannan yasa masa kalmar shahada duk dai a kunnuwan nasa ya d’ago kanshi cikin nutsuwa ya tsirawa fuskar yaron ido……….Hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska ni kaina a lokacin dana kalli fuskarsa sai dana tausayawa masa, dan kallon fuskar yaron tasa yasa ya tuno da abubuwan da suka shud’e yana tunanin da Naja’atu na gidansa da tuni wannan yaron dake riqe a hannunsa nasa ne, kallon fuskar yaron tasa ya tuno da fuskar ubansa duk da sau daya ya ta’ba ganin Bash amma baya ta’ba tunanin zai mance kammaninsa,
Tamaza! yayi yayi saurin aro dauriya da jarumta ya kalleta tare da fad’in “Sannu ina fatan babu abunda ke damunki.”! shuru tayi masa ta kasa magana saboda kukan da yaci karfinta
Gyaran murya yayi a nutse ya kira sunanta.” Naja’atu.” Dago kanta tayi tana kallonsa hawaye na sake zubowa, “Kukan me kikeyi bayan Allah ya sauke ki lafiya ai sai ki gode masa.”
Murya na rawa tace”Abbah tausayin ka nake ji wallahi dan Allah ka gafarta min abunda nayi maka wallahi ban zubar maka da ciki ba.” Kawai sai ya tsaya yana kallonta, Kafin yayi murmushi ya dan sunkuyar da kansa yana nazarin maganarta, wai tausayi shi maganar ma dariya ta bashi
Yace.”Cikina daya zube a jikinki dama haka Allah ya hukunta, maganar tausayi kuma ki daina nima na kusa samun k’aruwa ko baki da labarin amaryata nada ciki.” Yafad’a yana kallonta ido da ido
Sai taga maganar tasa kamar akwai cin fuska a ciki, a sanyaye tace”Na sani Allah ya rabasu lafiya.” Ya amsa da ”ameen ya Allah Wane suna kike so a sakawa yaron ki.”Da sauri ta kalleshi, yace.”Eh inaso nayi masa hud’uba ne kafin na tashi.
Tace”Ko wane suna asa masa.
“A’a kina da ikon ki za’bi sunan da kike so a saka masa dan haka ki duba dai.
Kai tsaye tace” Kasa masa sunanka tunda a yanzu kai ka zame masa uba.”
Girgiza kansa yayi yace.”Kece ‘Yata shi wannan sai dai a kirasa da jika na, dan haka ba sunana ya kamata a saka masa ba na Malam za’asa masa ko kuma a saka masa sunan babansa Bashir.”
Da sauri tace”Abbah dan Allah kada kasa masa sunan wannan mugun mutumin azzalimi wanda ya kwashe kayansa daga gaban ma’aiki, ni sunanka nakeso kawai kasa masa.
Yace.”Ki daina tsine masa kina kwashe masa albarka yana a matsayin uban danki sannan ita shiriya ta Allah ce watakila Allah ya shiryeshi ya dawo ku daidaita kanku……..Fad’ar wannan magana da yayi sai ta sake tunzura ta dinga zazzagin Bash din tana tsine masa albarka da fadin Sai dai ta mutu babu aure akan ta koma gidan Bash har da cewa insha Allahu ba zaiga annabi ba.