GURBIN IDO

GURBIN IDO 31-35

31

Ya samu nasarar dasa tsoronsa sosai cikin zuciyar maimunatu har ma fiye da yadda yakeso,washegari da suka fito tafiya kasa hada idanu tayi da anty maama,wani irin kunya da nauyinta ta dinga ji,cikin motar kuwa tana cure waje daya,kamar xaka ce ket! Ta zura da gudu,wannan karon a bayan ya zauna,ya kame owners corner abinsa,duk wani motsinsa tana ankare dashi,saidai da kunnuwanta don tuni ta saye idanuwanta cikin mayafi.

Duk tsahon awannin da suka diba suna tafiya aiki yake da na’ura,daga system zuwa wayar hannunsa,tsahon wadan nan awannin ko daya baiji tayi wani qwaqqwaran motsi ba,abinda ya sanyashi daga kai suna dab da shiga garin gombe ya dubeta.

Ko ta cikin yalwatacce mayafin data lulluba har saman kanta yana iya hangen zallar quruciua da kuma qanqantar data yi masa,wani takaici na sake kamashi kan anni,sam ita babu ruwanta da duba da cancanta ne ko kuma dacewa?,gwara unaisa ta cika shekarun da zai kirata da mace,saidai ko ita din ma bata burgeshi ba ballantana wannan rabin macen,ta yaya ma idanuwansa zasuji wata diya mace ta burgeshi?,baya zaton zuwan wannan ranar,wannan duka shaheeda ta tafi dashi,tabar masa fankon zuciyar,ta yaya fankon zuciya kuwa zata san dai dai daba dai dai ba?,sai yaja dan qaramin tsaki acan ciki,yana maida dubansa ga allon computer,yana karanta saqon rubutun da ya mamayr fuskarta.

Katafaren wuni ake cikin gidan dr marwan,don sanda duka isa gidan a cike yake maqil,abinda ya sanya ammi ta bada maqullin wani kebantaccen waje dake gidan aka sauki maimunatu da danginta,aka kuma cikasu da cimaka kala kala,kafin yammaci inda suka hau shirya maimunatun bisa jagorancin anty maama,don Allah ya sanya mata matuqar qaunar maimunatu,tana burgeta ainun.

Sanda suka kammala sunso su kaita cikin gidan wajensu anni da amma,amma sai annin tace a wuce da ita gidanta kawai,maimunatu tasu ce,babu wani abu sabo da zasu gaya mata,don haka direct aka fito da ita zuwa jerin gwanon motocin da aka aje domin miqata gidan captain ja’afar marwan khalid akko.

Duk abin nan da ake tana jin komai ne tamkar a mafarki,wasu hawaye masu dumi suka zubo mata sanda taji.motocin sun fara motsawa zasu bar gidan dr marwan,babu abinda ya fado mata a sannan sai

“Allah ya nunan ranar aurenki,ya baki miji na gari” sai gata yau a bigiren zuwa gidan mijin da batasan yadda zasu rayu dashi ba,a lokacin da qasa ta jima da rufe idanun mahaifiyar tata

“Allah ya jiqanki daada”ta fada cikin ranta,wannan din addu’a ce da kullum rana batasan sau nawa take yinta a ranta da kuma sarari ba.

   Tana jin sanda 'yan uwanta da sauran 'yan rakiya ke yaba kyau da kuma tsarin gidan,kowanne bakinsa na furta addu'o'i a kanta,abinda ita ta rasa gane kansa har yanxu,Allah ya zaunar da ita yakuma dawwamar da ita a gidan mutumin nan?.

   A hankali yake takawa zuwa sassan ammansa,sanye da wani irin sassalkan yadi ruwan hanta,wani irin dinki aka masa me kyau wanda yake nuni da zallar zamani da kuma wayewa,takalmin fata ne a qafarsa budadde wanda ya dace da kayan jikinsa,kamar yadda saman kansa yake sanye da hular da itama ta dace da kalar takalmin qafarsa.

   Wata irin tafiya yake,sam jikinsa babu kuzari hakanan Babu karsashi a tattare dashi,ya tura qofar falon amman,akwai sauran baqi da suka rage cikin gidan,umma ce qanwa ga ammansa ita da wasu mutum uku,su suka gaya masa amman tana bedroom dinta,sai ya wuce kansa tsaye.

   Sai da yayi knocking ta bashi izini sannan ya tura ya shiga bakinsa dauke da sallama,luf luf dakin yake a tsaftace gana fidda wani irin qamshi me dadi,kai baka ce ba biki akeyi cikin gidan ba,tana saman gado tana gyarawa amna kwanciya,sai ya matsa ya rusuna gabanta yana gaidata,ta amsa kana shuru na sakanni ya biyo baya,ta gama gyarawa amnan ta saka mata pillow sannan ta waiwayo ga ja'afar

“Zaku wuce kenan?” Kai ya jinjina mata,yana zare hular dake kansa,can qasan zuciyarsa kuwa wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke,yana jin komai har yanzu kamar a mafarki

“Ma sha Allah,Allah ya tsare,ubangiji yasa a shiga a sa’a,Allah ya kauda dukkana abunqi,ya albarkaci tarayyarku,kayi qoqari ka riqe amanar yaran mutane,ka kuma ji tsoron Allah a zamantakewarku,ka sauke nauyin da duka Allah ya dora a kanka,na horeka ka zama adali,ka kiyaye haqqin kowacce akan ‘yar uwarta,karka yi zalunci,kada kuma ka bari a zalunci kowa,Allah ya shige muku gaba”

“Ameen ya rahman,na gode amma” ya fadi yana jin jikinsa yana yin sanyi,wannan daren yana tuna masa da daren aurensa na fari ne da shaheeda,wanda akwai tarin bambance bambance masu yawa.

  Matsawa yayi gaban gadon ya dora hannunsa saman kan amna ya shafa,sannan ya duqa yayi kissing kuncinta,ya maida mata abun rufar ya miqe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihunsa

“Sai da safe” yace da amma yana takawa zai fice

“Allah ya bamu alkhairi” ta fada tana bin.bayansa da kallo,duk yadda yake qoqarin boye damuwar dake saman fuskarsa ita ta karanci hakan,saita rakashi da addu’a

“Wannan hadin ubangiji kasa ya zama silar waraka a rayuwarka”.

   Motarsa ya wuce kai tsaye kamar yadda ya zaba tafiya shi kadai babu dan rakiya ko daya,don zuwa yanzun ma yasan abokansu sun tsufa gidan jabir koma suna shirin juyowa,yace baya buqata,shi din ai ba auren fari xaiyi ba.

  Yana shirin bude motar yaji sallamar khadim a bayansa,sai ya waiwaya yana amsawa,cikin girmamawa ya miqa masa wasu ledoji dake hannunsa

“Gashi inji ammi” jim yayi na sakanni yana bin ledar da kallo,sai kuma ya bude masa back seat bau tare da yace komai ba,khadim din ya fahimta abinda yake nufi,don haka ya qarasa ya saka musu su a baya,har ya juya zai tafi yace masa

“Kace mata na gode” yayi maganar ne sanda yake shigewa cikin motar,ya maida.murfin ya rufe ba tare daya jira cewar khadim ba.

   A hankali yake tuqin kamar wanda baison isa gidan,tafiyar data daukeshi mintuna masu tsaho fiye da mintunan da zasu isheshi a al'adance,horn daya mai gadin gidan ga dage masa gate din,sai a sannan yadan ja motar da gudu ya shige da ita farfajiyar gidan,sannan ya faka ta a parking lot idanunsa na sauka kan wata qaramar sabuwar mota ruwan zuma,ya dauke kansa yana kashe tasa motar.

  Har ya fito ya tuna da ledojin da ya bari cikin motar,sai ya koma ya debosu,tun kafin ya bude ma ya fuskanci meye a ciki,sai ya riqesu a hanauyensa,dai dai sanda me gadin gidan ya iso cikin rusunawa ya fara gaidashi,amsa masa yayi cikin kulawa,saboda yana daga cikin dabi'arsa girmama duk wanda yake aiki a qasansa,barshi dai da zafinsa miskilanci rashin daukan raini da rashin son wasa da aiki,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya fiddo 'yan dari biyar biyar sababbi guda shida ya miqa masa,hannu biyu ya sanya ya karba yana ta zabga godiya,yayin da shi kuma yayi gaba abinsa ba tare da yace tak ba.

  Sai da yayi addu'ar shiga gida sannan ya kutsa kai cikin babban falo,shuru yake babu alamun motsin me rai cikin gidan,cikin nutsuwa ya fara takawa zuwa stairs,sai kuma ya tsaya cak saboda maganar da abbi da kuma amma suka gaya masa a daren jiya da yau,ledojin hannunsa ya kalla,a hankali sai yayo baya,ya kuma nufi qofar dake hannun dama na falon.

   A hankali ya tura qofar,falo ya bayyana,wanda aka qawata da kalolin kujeru da curtains masu azabar kyau,royal blue da golden,komai na falon,a tsaftace yake cikin qamshi da sanyi daya gauraye da sabunta,ci gaba yayi da tafiya har ya isa qofar bedroom din,itama ya turata ya shige.

   Dai dai lokacin da take zaune saman abun sallah,saboda ganin yadda lokaci yaketa tafiya,an doshi sha biyu na dare,kuma ana binta sallar isha'i da kuma shafa'i da wuturin da batayi ba.

  Can qasan maqoshinsa yayi sallama idanuwansa suna sauka a kanta,gabanta ya buga fat,don bata tsammaci shogowarsa din ba,saboda dukkan wata magana daya gaya mata a jalingo ta haddacesu tsaf a kanta, janye kansa daga wajen da take yayi,ya isa gaban madubi ya ajjiye ledar a kai,sai ya tsaya yana goye da hannayensa a qirjinsa.

   Raka'ar qarshe take amma kawai sai ta miqe taci gaba da kawo wasu raka'o'in,abinda ya sanyashi sakin hannayensa kenan,ya kuma juya a hankali ya fice a dakin bayan yaja qofar kamar yadda ya ganta.

  Sallamewar sallarta ta fito ne hade da ajiyar zuciya,ta danyi shuru tana karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,tana kuma jin yadda zuciyarta take bugawa,lumshe idanunta ta sakeyi,ba shakka tana tsananin tsoronsa,tana tsoronsa bilhaqqi da gaske,hoton sanda ya zuba mata lafiyayyen marin nan ya gilma a idanunta,sai kuma sanda yake zuqar hayaqin taba yana bulbular da ita daga bakinsa zuwa hancinsa,sai ta girgiza kai,tana jin wani bala'in haushinsa yana ratsata.

  Yaya akayi ya kasance mashayin taba?,bayan shi din ya fito ne daga gidan tarbiyya kamar haka?,mutane masu karamci dattako da sanin darajar dan adam?,bata tunanin akwai wanda yasan yana sha din cikin gidan,don ko da wasa bata tabs jin anyi magana makamanciyar wannan ba.

   Tunanin ta ture gefe,ta fara karanto azkar dinta da bata samu tayi ba a yau din,gefe na zuciyarta kuma cike taf da kewar amna,tana jin cewa zaiyi wuya bata nemi su anni su bata yarinyar ba,don ko a yau ma sai da akayi wayon janyeta sannan suka tahi,wanda ita bata kawo hakan ba,ta tsammaci zasu taho ne da ita,amma sai taga akasin hakan,to me zata zauna ne tayi a gidan?,gwara gwara ma ace da amnan,zata taimaka mata wajen debe kewa.

    Kamar yadda ya shiga sasssan maimunatu haka ya shiga na unaisa,saidai ita ya sameta tsaye ne a gaban mudubi tana kallon kanta bayan ta gama sake feshe jikinta da turare tana gyara zaman rigar jikinta.

    Sallamarsa hade da turo qofar ya sanyata saurin maida mayafinta saman kanta, ta rufe ruf,saidai tana iya hangensa ta cikin mudubin,wani sassanyan abu ya ratsa zuciyarta ya kuma haifar mata da yalwataccen murmushi akan fuskarta,a fakaice taci gaba da binsa da kallo,tana jin wani farinciki yana ratsata,burinta ne na tsahon wasu shekaru Allah ya cika mata shi,duk da cewa ranta ya baci a dazun da ganin irin gidan daya zaba a jjiyeta kuma tare da wata,saidai anty talatu ta kwantar mata da hankali

“Kinsan baso yake ba,ta yiwu yayi hakanne don ya baki haushin dama harkiyi wani abu da zai janyo a fasa gaba daya,dole fa saikin anjiye rashin haqurin nan,kin janyo hankalinsa a hankali a hankali,sanda zai canza miki gida ko ya rabaki da qasar ma gaba daya bai sani ba” qwarai ta gamsu da maganganunta,don haka ta ajjiye komai gefe a ranta.

   Cikin salo ta amsa sallamar tasa cikakkiyar amsawa,bai sake cewa komai ba itama ya ajjiye mata ledar,ga zatonta zai qaraso koda gefanta ne yace wani abu da ita,saidai gani tayi yana shirin ficewa,muryarsa can qasa ya furta

“Gudnyt” ya tursasa zuciyarsa ta fada,duk don son ganin yayi abinda ya dace bakin gwargwado.

  Gabanta ne ya fadi sanda yake gab da fita,ta daga kai tana dubansa ta madubin,zuciyarta tana bata shawarar tsaidashi,yayin da wata zuciyar ke hanata,tana gaya mata girman wannan rana a wajenta,ita yafi kamata ace an tsaida,an kuma nema kasancewarta cikin dakin,tana wannan shawarar da tattaunawar da zuciyarta har ya fice.

   Kasa zaune tayi,ranta ya baci sosai,ta dinga kai kawo tana tunani a ranta,shin sassansa ya tafi ko kuwa na maimunatu?,sai taji zuciyarta taqi aminta da hasashen daketa mata yawo,don bai kamata ace sassan maimunatun ya fara sauka ba,tunda a qa'ida itace babba,ta girmewa maimunatu,ita ya kamata ta fara karbar baquncinsa,tafi maimunatu sanin rayuwa dama komai da komai da za'a tarairayi mutumin da ya jima babu mata a gefansa kamarsa,don haka ta gyara rufin mayafinta,ta kuma bude qofar ta fito.

   Bata ma isa sassan maimunatun ba taji motsinsa daga sama,don haka taja birki,ta kuma koma nata sassan,girman kai yana sauko mata,tana jin ba zata iya nemansa a yau ba itama.

   Yana shiga dakin ya sauke ajiyr zuciya mai qarfi kamar zai tofar harda qirjinsa,ya soma bin dakin da kallo,an qawata masa shi yadda yakeso ya kasance,idanunsa daya bayan daya suna sauka kan hotunan shaheeda da amna da amra wanda aka musu tare yasa aka gyarasu aka shiryasu a falon gwanin burgewa,kai kace idan ka kirayesu zasu amsa,zakayi tsammanin har yanzu sune ke rayuwa cikin gidan,addu'ar da baya gajiya dayi musu yayi wani abu na motsa ransa,ya wuce zuwa bedroom dinsa.

   Sai daya gama duba komai daya ce a sanya masa a dakin,wanda yake buqatar ya canza masa waje ya canza masan ya ajjiyeshi inda yakeso,sannan ya fidda kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,sai ya wuce toilet kai tsaye,ya daura alwala sannan ya fito ya kuma bude walking wardrobe dake manne da bedroom dinsa ya shiga ya duba wasu navy silk pyjamas Natalya's company,ya shirya kansa wadata jikinsa da turaren da yake amfani dashi duk dare,sannan ya feshe kansa da BB hair spray.

   Abun sallarsa ya shimfida sannan ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarsa ga alqibla.

  Unaisa kuwa kusan raba dare sukayi suna waya da anty talatu qanwa ga mahaifiyarta haj Aayah,tana gaya mata abinda yafaru,ita kuma tana shirya mata yadda zata aiwatar da komai,sun jima sosai suna tattaunawa kafin suyi sallama

“Amma dai lafiya ko?” Haj Aayah da suke kwance daki daya da qanwarta wadda bata kai ga komawa gida ba ta tambayeta

“Eh to,lafiya amma ba lau ba” abinda ya farun ta gaya mata,sai ta sauke ajiyar zuciya

“Yaron nan fa ba lafiyar kwanya ya cika ba,idan anyi magana sai kuce depression ne ya kamashi bawai ciwon hauka ba,ni tsorona ma kada ya kama min diya ya jibga,don banjin zanyi kawaici,babu yadda banyi da unaisa ta haqura dashi ba amma ta kasa haqura” murmushi talatu tayi

“Banda abinki yaaya,ta yaya yana da ciwon hauka zan goya ma unaisa baya ta aureshi,an gaya miki ciwon damuwa ne,kuma a yanzunma komai yana wucewa tunda gashi ya amshi mata har biyu,mudai burinmu kawai diyarmu tayi zarra ta zama star dinsa,don kishi da bafulatana sai an kula,shegen surkulle garesu” haka suka yita tattauna maganar a tsakaninsu a daren.

   Itako maimunatu wani nutsuwa ta sauko mata bayan ta gama dukka addu'o'inta ta isa ga gadonta ta kwanta,gadon data dinga ji kamar ba nata ba,dakinma kansa jinsa take kamar an bata aronsa ne,kewa da kadaici suka dinga damunta,sosai ta dinga ji cikin ranta inama ace an bata amna,sannu a hankali idanuwanta suka dinga nauyi,bacci kuma me qarfi ya fusgeta.

Follow my arewabooks account for more latest pages

Arewabooks:HUGUMA


YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?

GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

zaki saka kudin ta wannan account number din

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

Saiku tura shaidar biya zuwa ga
07040727902

IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR
09134848107

THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE????????????????????????????????
[11/24, 10:10 PM] S

   Rigarsa da hularsa ya dauka ya bude murfin motar ya fice ya koma zuwa seat din gaba,sannan ya bashi umarnin ci gaba da tafiya bayan ya gyara zaman kujerar yadda zaiji dadin jingina ya zama comfortable sosai.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 32

WASHEGARI

  Tun sanda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba kamar yadda ta saba,tana ta azkar dinta,yayin da rabi da rabi na hankalinta ke kan tunanin yadda rayuwa zata kaya mata cikin gidan.

   A hankali taji idanunta suna mata nauyi,gajiyar zaman mota daga gembu zuwa gombe ya sanya bata kai ga qarasawa ba bacci yayi awon gaba da ita,ba kuma ta farka ba sai wajen qarfe tara saura na safe.

   "Hasbunallahu wani'imal wakil" fa fada s sauri hamma na qwace mata,ta miqe tana linke abun sallar data tashi akai,daga nan kuma fa zarce sa bubbuge bubbugen qura duk da dakin babu abinda yayi,ta kauda abinda yake zaune ba'a kan tsari ba,daga nan ta wuce toilet kai tsaye,ta hada ruwa tayi wanka.

  Sanda ta fito hudubar anty maama da yadikko matar kawu sulaiman akan tsafta da kula da kanta,duk da cewa kwatakwata qazanta ba dabi'ar ta bace.

   Cikin mayukan dake jere saman madubinta ta bude wasu ta shafa,sannan ta duba makekiyar wardrobe dinta ta jikin bango.

   Tsaiwa kawai tayi tana kallon tarin uban suturun da a yanzu suke mallakinta,sai takejin kamar ta zurawa rayuwa jikinta da yawa,banda haka ina ita ina wadan nan kayan da batasan ranar da zata gama sanyasu ba?,haka ta dinga dubawa har zuwa lokacin da hannunta yakai kan wata atamfa,kalarta ce ta dauki idanun maimunatu,data gwada sanyawa kuwa saita amsheta,tayi mata kyau matuqa da gaske,batayi amfani da dankwalinta ba,a maimakon hakan sai ta nema qaramin hijab ta maqala a kanta.

   Bakin gado ta koma ta zauna,ta rasa abinda zatayi,sai kuma ta fada tunane tunane,abubuwan da suka faru a rayuwarta,suke ma kan faruwar,tsakiyar haka taji kamar qararrawar falon nata neman dauki,hade da knocking,tayi kamar kada ta fita,amma jin baa fasa knocking din ba ya sanyata miqewa.

   Cikin nutsuwa ta fita,qafafunta suna nutsewa cikin lallausan carpet dake malale a wajen har ta iso falon ta doshi qofa,dai dai sanda yake saukowa daga samansa,sanye da wata jallabiya saqar qasar morocco,ruwan a qasa da aka yiwa ado da wani zare mai dan kauri ruwan madara,yankakken hannu gareta,don haka dukka singalalinsa dake lullube da gargasa waje yake,sumarsa tadan hargitse kadan,haka nan fuskarsa na nuna alamu na jin bacci.

   Idanunsa a kanta sanda ta bude qofar yana step na qarshe,ta gane fuskar matashin saurayin dake miqo mata kwanduna dauke da fulasai masu azabar kyau

“Daga gidan dr,amma ce tace a kawo muku” sosai taji dadin karamcin amman har cikin ranta,tasa hannu ta karba tana cewa

“Kayi mata godiya,Allah ya saka da alkhairi” sai ta maida qofar ta tura ta yadda take,ta kuma waiwayo don komawa ciki ta sama musu mazauni.

   Karaf idanunta ya sauka a kansa sanda yake isa gaban babban freezer dake falon tamkar ma bai ganta ba,budeta yayi ya ciro babbar gorar ruwa guda daya,gabanta ke wani irin faduwa,tsoronsa dake shaqe a zuciyarta ya motsa

“Ina kwana” ta fada bakinta yana dan rawa kadan,tana jin kamar zai mata wani mummunan abu ne,banda alamun sauti da taji da sai tace bai amsa gaisuwar tata ba,kunnuwanta na biye da takunsa sanda yake shirin komawa saman,sai tayi ta maza tace

“Ga abinci amma ta aiko dashi” shuru na wasu sakanni suka ratsa yana ci gaba da tafiyarsa,kamar bazai ce komai ba sannan tayi yace

“Madalla,an gode” yaci gaba da hayewa saman,kunnuwanta dai na biye da sautin takunsa,takun da ake yinsa cikin wani irin salo da kuma tafiya wadda jinin sarauta ke yawo a cikinta.

   Sai data daina jin motsinsa sannan ta daga kanta tana duban kwandon hannunta tare dason gane me madalla da yace take nufi?,ita yanzu ya zatayi da wannan abincin?,sai ta maida dubanta ga sassan unaisa dake a rufe,zuwa zatayi ta mata magana ko kuwa ta qyaleta?,kai ta girgixa,zuciyarta tafi karkata da ta qyalesu gaba daya,don haka tayi kitchen da abincin,ta ajjiye acan,bayan ta bude ta diba iya abinda cikinta zai iya dauka,wanda duka duka cikin plate daya ta xuba komai.

    Tunda ta koma daki bata sake jin motsin kowa ba,don ko data gama cin abincin sake kwanciya tayi,ita ba gwanar kallo bace bare ta dawo falonta tayi,sai bayan kusan awa biyu taji tashin mota daga farfajiyar gidan,wadda batasan ta waye ba,saidai tana kyautata zaton tame gidan ce.

    Qarfe daya da ashirin na rana tana fitowa daga alwalar sallar azahar taji knocking da 'yar hayaniya,sake fitowa tayi falon,har yanzun kamar dazun dai babu kowa ba kuma motsin kowa.

   Murmushi ya subuce mata sanda ta bude qofar,laila ce ita dasu hanne da hauwa,sai fa'iza da safina harda khadija,kusan dukkaninsu mutanenta ne,akwai sabo tsakaninsu sosai,abinda yasa ta sake jikinta ta kuma ji dadin zuwan nasu

  "Ina fatan dai yaa ja'afar bai nan?" Fa'iza ta fada tana dan fidda idanu gami da watsa idanunta a babban falon gidan hadi da kallon stairs din,qaramin murmushi maimunatu tayi tana kada kai

“Ya fita” ta amsa musu kai tsaye,don motsin fitar motar dazun ranta yana gaya mata shine

“Na baroshi wajen amma ma fa sanda muke fitowa” safina ta fada tana zare mayafinta daga kanta

“Au to,dama wai don mufi sakewa ne” ta fadi tana dariya,ita dai maimunatu jagora ta musu zuwa sassansu,suna tafe suna gaya mata ba dadewa zasuyi ba,amma tace au dawo da wuri,kuma su hauwa da qyar idan ba anjima zasu wuce ba,zasu biya ta jalingo ne,akwai gaisuwar mutuwa da akayi da zasu fara zuwa sannan su wuce gembu.

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button