GURBIN IDO

GURBIN IDO 31-35

       A hankali ya daga kansa zai kalleta,sai ya samu itama shi take kallo,ba tun yau ba,yasan anni sarai,yasan kuma tunda ta tada zancan nan akwai abinda ta taaka,kamar zaice wani abu sai kuma yace

“Ba damuwa” a taqaice,yadda yayi saurin amsawar ya bawa anni mamaki,ya kuma tabbatar mata akwai wata a qasa,kuma ruwa baya tsami banza,amma kuma zata zanya idanu taga me zai aikata

“Idan ka tashi ka hada mata da waya,don ya kamata ace tana waya da ‘yan uwanta,bawai don ta taho ta taho kenan ba”

“To” ya sake cewa da ita

“Kiyi picking ledojin chocolates din ki biyoni mota zaki rakani unguwa” yace da amna bayan ya sauketa daga kan cinyarsa ya kuma miqe,ta sauka kuwa da sauri tana murna,ta hau tsincewar tana ta yiwa anni da ta bishi da kallo surutu,hankalinta bai kwanta ba,tasan halin ja’afar itama,wannan saurin amsawar da yayi ba’a banza ba,amma koma meye ya shirya yi,indai cutuwa ne ga maimunatun ba zata bari ba.

    Shegen miskilanci gami da zurfin cikinsa yana nan har yanzu,yana da wannan nuna shakulaton bangaron kan abubuwan da yana sane dasu sarai,suna kuma cikin ruhi da zuciyarsa,amma sai yayi kamar bai damu ba,kamar baya ankare da abun,kuma kamar baya gani,saidai duk randa ya magantu ko ya dauki wani action akai kowa zaiyi mamakin hakan,wannan ya sanya anni ta sake sanyama ranta zata kula da komai da irin abinda zai biyo baya,ta sauke ajiyar zuciya tana hade hannayenta waje daya,fuskantar ja'afar ko yin gaba da gaba wajen saukeshi daga ra'ayinsa ya zuwa wani babban aiki ne da ba kowa zai iya shi ba,fatanta ubangiji ya dubesu,rayuwarsa ta sai saita,ya kuma riqe amanar yaran mutane kada suji kunya.

*Kwanaki anni tayita qirgawa tana jiran taji yace wani abu,ko kuma ya tanka game da maganar da sukayi da ita,saida har ta gama irga kwanaki bakwai baice komai akan maganar ba.

     A daren ranar ya koma gida da wuri kai tsaye daga wani gidan saukar baqi,inda suka tattauna da wani babban mutum da ya bawa company dinsa kwangilar ginin wata university da zai bude.

         A gajiye ya shigo gidan,ya wuce sassansa kai tsaye ya fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa,duk da gajiyar da yayi amma yanason yaje gida wajen anni,don haka  sai ya shirya cikin wani irin straight leg jeans da shirt masu azaban kyau,ya kuma sakaya qafarsa cikin wani rufaffen sneakers daya dace da kayan jikinsa,ya sake gyara sumarsa tsaf,kai bakace dare bane,ya dauki maqullansa da wayarsa guda daya a gurguje ya sauko,yana so yaje yayi ya gama ya dawo ya kwanta,don gobe yake sanya ran zai wuce lagos.

    A nutse yake tuqinsa,yana kuma amsa wayar da suke da jabir ta speaker din motar har ya isa gidan,sai daya tura hancin motar zuwa farfajiyar gidan sannan sukayi sallama dashi,ya dai daita tsaiwar motar a parking lot na gidan yana duban inda masu gidan ke ajiye motocinsu,akwai kotar hisham data abbi duka a wajen,da alama suna gida,sai ya balle murfin motar ya fito zuwa cikin gidan,cikin takun nan nasa dake nuni da qasaitarsa da kuma aji da yake dashi cikin jininsa,duk inda ya gifta sai ya bada ajiyar qamshinsa a wajen,wani qamshi na musamman da zaiyi wahala ka jishi jikin wani,turare na musamman yake amfani dashi,na jiki kuma ya banbamta dana kaya,hakanan na gashin kansa daban da wanda yake shafawa qirjinsa,dama can haka yake,dan gayu ne daya zarta kowa cikin gidan dama familyn khalid akko.

   Jifa jifa ma'aikatan gidan ke kawo masa gaisuwa har ya dangana da sassan ammansa,wanda kusan ko da yaushe yazo gidan wajenta yake fara zuwa,ya sameta zaune a falon gidan,sanye da hijab,yatsarta kuma sarqafe da da tasbah counter,idanuwanta na kan tv.

    Fuskarta fadade da fara'a ta gyara zamanta tana masa maraba

“Kaine a daren nan?” Ta fada tana ajjiye masa ruwan data dauko masa da kanta,sai yasa hannu ya karba,duk da baya jin qishi amma kuma bazai iya wucewa tayinta ba,saboda kima da martabar da take dashi a wajensa,ya gaidata cikin girmamawa

“Lafiya qalau,yasu maimunatu?” Sunan yajishi tamkar baqo a wajensa,don bai gama tantance wacece maimunatun ba,wadda ya lura duk zuwa shine suna na farko da take fara tambayarsa

“Lafiya qalau” ya amsa mata,yana zarcewa da shan ruwan daya tsiyaya din,sai daya ajjiye cup din sannan ya dubi amma

“Amna fa?”

“Ina zaton tana wajen ammi,suna can sassan babanku da ita,yau rigima takeji tun yamma,wai sai an kaita gurin adda maimunatu” bai fahimci gundarin abinda maganar ta amma ke nufi ba,yadai dauka key dinsa ya maqala a yatsan hannunsa yana shirin tashi,dai dai lokacin da salma ta fito daga dakinsu,ta kuma ratso cikin falon cikin kwalliya,tana baza qamshin turare.

        Kafin ta qaraso ta ankara dashi,sai duka karsashinta ya zagwanye,ta sake saita kanta da kyau don kada tayi wani laifin,ta qaraso ta rusuna tana cewa

“Barka da dare yaaya”

“Yauwa barkanki dai” sum sum tafara takawa zuwa gaba,sai a sannan ya waiwaya zuwa inda take

“Ke!” Ya kirata da nannauyan muryan nan tasa da take sanyasu cikin rudani da tsoro

“Na’am yaaya”

“Zo nan” ya fada yana mata sign da hannu ba tare daya sake dubanta ba,gabanta nata dukan uku uku ta dawo,ta sulale saman carpet din ta zauna tana dubansa yana danna wayarsa,sannan ya karata a kunne,second uku kacal yace

“Ka bude ka shigarmin dasu sassan anni” iya abinda ya fada kenan ya katse wayar,sannan ya maida dubansa ga salma,sai tayi qas da kanta,yana da wani irin kwarjini wanda ba kowa ke iya sanya idanunsa cikin nasa ba

“Ina zakije?” Dan muskutawa kadan tayi,duk sanda ya sanyata gaba da wata tambayar komai qwace mata yakeyi,kamar ba ita salman ba,’ya gayu me aji,wadda take kadawa maza ganye,’yar jami’ar dake gab da kammala degree dinta

“Yaa….. Ahmad ne yaxo” wani kallo ya watsa mata,wanda yasa tayi dana sanin bashi wannan amsar

“Koma ciki ki saka hijab dinki” iya abinda yace da ita a taqaice kenan,ya maida dubansa ga wayarsa,bata da iko ko qwarin gwiwar musu dashi,don dole ta miqe ranta a bace kan yadda zai bata maka kwalliya ta koma dakinsu,ahmad din nan ba baqo bane,koshi kansa yasan da zamansa,tunda sai da iyayensa sukazo nema masa izinin fara zuwa wajenta,amma shi da yake wani irin mutum ne mai shegen tsari da qa’ida,ji yadda yayi kamar bai ganeshi ba.

      Da sallama ya shiga sassan annin,tana zaune a qasa,ta dora qafafunta saman tuntum,daya daga cikin masu aikinta na mata yankan farce,fa'iza khadija da laila na zaune daga gefe suna kallo duka harda annin.

     Sallamarsa tasa dukkansu suka gyara zamansu,hadi da hada baki wajen amsa sallamar tasa,anni ta waiwaya ta zuba musu harara

“Ya’yan nema marasa kunyar Allah,ni da yake marainiyar wayonku ce magana nayi muku har babu adadi amma ba wadda na samu ta tankani,amma da yake dodon naku ke magana har hada baki kuke wajen amsa sallama kamar na Allah…..” Laila daketa motsi tana yiwa anni sign na tayi shuru don Allah amma tayi kamar bata gani ba takasa shuru

“Amma anni don Allah ba cewa nayi bari mu qarasa ganin wannan ba?” Da yatsa annin ta nunata

“Ke arcan,kiyi ta kanki yarinya,ni zaki yiwa sanabe?”

“Barka da dare” mai rahila me aikin ta gaidashi kanta a sunkuye

“Kina lafiya” ya maida mata yana daga tsaye

“Alhmdlh yallabai”

“Ajjiye ki tafi” ya fada mata kansa tsaye,da hanzarinta ta miqe bayan ta ajjiyr nail cutter din,sai data bace a falon sannan ya waiwaya ya dubesu duka su ukun,ya sauke kallonsa ga fa’iza babbar cikinsu

“Xoki dauka ki qarasa mata” cikin sauri ta taso ta zauna inda rahila ta tashi

“Nidai ki bini a hankali,kada garin rawar jiki ki yankemin jiki ina lallaba rayuwata”.

    "Tashi kije ka karbomin abinci wajen amma,idan kinso ki xauna ko kiyi mistake" ya fada cikin gatse,yana zama a qasan carpet daura da anni tare da duba agogon hannunsa,saura minti daya a fara haska wasan tseren dokuna, favourite thing nasa kenan,ya yiwa khadija umarni da ta bashi remote,tana miqa masa ta samu ta sulale daga falon,ya canza tashar yana jin anni na mitar me zasu kalla a nan?,shi dai baice da ita komai ba ya maida kansa ga kallonsa,har zuwa sanda laila ta dawo da wani qaramin kwando kamar na kaba,saidai an saqa wannan ne da wata irin roba me kyau,ta ajjiye masa a gabansa,sannan ta duqa ta fara shirin serving dinsa.

“Stop” ya fada da sauri,a dan tsorace ta daga kanta,sai ya sauke dubansa ga yatsunta ba tare da yace komai ba.

     A tsorace ya dunqulesu cikin tafin hannunta,sai a sannan ta tuna,babu abinda yafi tsana irin tara farce

“Na baki minti biyar ki tabbatar sun koma kamar na hannun kowa” abinda yace da ita kenan,ta gyada kanta tana miqewa,bataso ya gani ba,saboda bikin rumaisa za’ayi,cousin dinsu,diyar uncle umar,mai bin dr marwan.

Ku bibiyi shafina na arewabooks don samun sabbin shafuka

Safiyyatulkiram: 35

INA MASOYA KUMA MA’ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE..

TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE

A YERWA INCENSE AND MORE ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI KHUMRAHS MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA

SANNAN SU NA DA TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA. BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI KULACCAM MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA

AKWAI TURAREN AL’AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH DIN SA

SANNAN SU NA DA TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA

BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI

AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL

AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA

SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI.

KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI

NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215

INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more

YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE


 Ficewarsu sai falon ya zamana daga shi sai annin,yaja kwanukan yayi serving kansa da kansa,ya dauki plate din ya dora saman qafafunsa ya fara ci.

      Duka anni na karantarsa ba tare da tace komai ba,yadda yake cin abincin nasa ya sake tuna mata da ja'afar din,har yanxu qasaitarsa da jan girman nan nasa yana nan,rashin daukan wasa qarancin magana da rashin walwala,saidai kuma baya wasa da cikinsa,har yanzunma haka abun yake,yadda taga yana cin abincin ya tabbatar mata babu komai a cikinsa

“Ni na rasa wanne irin wayo da dabara ne wannan,ka baro abincin mata har biyu a gidanka kazo kana cinyewa bayin Allah abinci?” Idanunsa ya sauke ka fuskar anni,da gangan take musu gorin abinci,duk sanda kaji tana gorin abinci to ‘yan rigimar nata ne a kusa,batasan cewa shima yau da tasa rigimar yaxo ba,don haka baice mata ta tafas ba,sai daya gama yana goge hannunsa da tissue,duk da ba da hannun yaci ba,ya janyo takardun da yasa a shigo masa dasu ya ajjiye a gabanta.

     Kallon takardun tayi sannan ta maida dubanta gareshi tana bata fuska

“Meye wannan din?,kasan dai ba wani bokonku nayi ba da zaka turon takardu gaba ko kana wani cushe fuska kamar tsohon kashi” can qasan ransa ya murmusa,amma ko days ba alamun murmushin a saman fuskarsa,yasan zata fadi sama da haka ma idan tana jin rigimarta

“Takardun makaranta ne da kika nema a samar mata” fuska ta yatsine

“A samarma wa?” Ta fada tana jifansa da kallo

“Kin manta maganar da mukayi kenan?”

“Na manta,saika tunamin” hannu ya miqa ziwa gabanta zai janye takardun nasa yana fadin

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button