BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 67

Chapter: 67

………Da ƙyar ya iya lallaɓata tasha fruit salad ɗin, dan da gaske barcine a idonta sosai. Ganin tanata faman lumshe idanu dole ya barta. Itama sai ta miƙe tana ɗaga masa hannu. “Yaya good night”.

  Kafin ya samu damar cemata komai tabar falon da hanzarinta dan bata buƙatar yace zai dakatar da ita. Shima baiyi yunƙurin dakatar da itan ba. ya dai bita da kallo. 

    Kamar yanda ya saba bayan gama duk wata al’adar rayuwarsa yay shirin barci. Yaso yin kwanciyarsa anan amma zuciyarsa taƙi aminta da hakan. Ya fito a nutse yana kulle ƙofar. Sashen Fadwa ya fara nufa dan bazaiƙi sauke nauyin da ALLAH ya ɗaura masa ba komi sukai masa na laifi. Yayi mamakin samunta a falo bata kwanta ba. Sai dai hankalinta gaba ɗaya yana akan waya ne. Ta mugun shagala a yin editing video da zatai posting, wanda ɗauka ce mara daɗi, dan kuwa faɗa suke da wata mai suna Teema. Faɗan kuma ya samo asaline akan ita Teema ɗin ta ɗaura hoton Shareff a shafinta tana bin waƙar soyayya. Sai wasu a cikin followers ɗinta suka ɗakko videon suka dinga tagging Fadwa da gaba ɗaya a yau bata buɗe data ba sai da yammar nan, dan tashin hankalin Anaam ya saka a kwana biyun nan ta rage yin posting akai akai kamar da da arana takan ɗora videos sama da uku. Sima itace ta fara kiran Fadwa ta sanar mata lokacin fitowarta a sashen Shareff kenan. To shine fa tun ɗazu ɗin ake tafka rigima tsakanin Fadwa da mabiya bayanta su Sima. Itama Teema da nata magoya bayan sunama Fadwa izgilin Teema zata shigo itama ata uku kafin shekara ta ƙare. (????gsky naso ace kuje tiktok kuga rigimar nan guys????????).

   Tsaiwarta a kusa da ita ta sakata wani mugun zabura, daka ganta kasan ta firgita. Ta kife wayar akan kujera a daburce take masa sannu. Idanu ya tsira mata cike da mamaki matuƙa, dan baiga abin zabura ɗin ba anan. Ya maida dubansa ga wayar da take faman ja tana turawa ƙasan throw pillow, zuciyarsa ta ɗarsu a karo na biyu game da ganinta da ɗaukar hankalinta da waya keyi, sai dai na yau yafi ƙarfi dan ƙarara alamun rashin gaskiya sun bayyana akan fuskarta. Komai baice mata ba ya juya ya fice.

  Ta bisa da kallo zuciyarta na luguden daka, dan ta tabbata shirunsa wani abu ne mai zaman kansa. Gaba ɗaya sai hankalinta ya rabu biyu, matsawa tai jikin window, sai ta hangosa zai shige sashen Anaam. Jikin windown ta bari, ta ɗauka wayarta da sauri ta nufi bedroom harda murzama ƙofar key.

    A falo ya samesu Anaam najan hanun Aysha akan sai taje su kwanta a ɗaki ɗaya. Ita kuma Aysha ta dake cewar ita bazata ba a ɗakin baƙi dake kusa da dining zata kwana. Shigowarsa ta sakasu dakatawa daga jayayyar tasu, Aysha kuma ta samu damar zare hanunta ana Anaam tana mata gwalo. 

   Filon dake saman kujera tai saurin ɗauka ta jefama Ayshan, da gudu Aysha ta ƙarasa shigewa ɗakin tana cigaba da dariyarta. “Zan kamaki ne ai yarinya”. Ta faɗa tana kallon Shareff dake kallonta.

    “Barcin kenan?”.

  Kanta ta langaɓe masa gefe fuska a narke sai dai batace komai ba. Cigaba da takowa yay har zuwa gabanta, ya kamo hanunta yana faɗin, “Muje”. Kafaɗa ta noƙe masa. Dan haka ya tsaya yana kallonta. “Miyasa?”. Ƙara narke masa tai murya a karye. “Sai dai ka goya ni”. Ya waro idanunsa sosai a kanta, fuskarsa na sassauta tsukewar da take. “Da ɗinkin zan goyaki?”. 

  “To bakai kaja akayi ba”.

Karon farko ya saki murmushi har haƙoransa na bayyana. Jikinsa ya rungumota da ɗaura kansa saman kafaɗarta. “Muka dai ja akayi”.

  “Dawa?”.

Ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin jan jikinta daga garesa. Ƙaramar dariya ya saki dan yanda tai ɗin kamar wadda aka kirama mutuwa. “Da ke mana, harfa wani kanannaɗeni kike. Ko muje a ƙara yanzu ma? Na san dai ya daina zafin ai”.

     Kukan ƙarya ta sakar masa wai ya mata sharri sai sunje shari’a gaban su Abba. 

  Cikin ɗage gira da ƙoƙarin damƙota ya ce, “Oh really? To kafin muje bara na idasa abinda na fara shari’ar tafi armashi”. 

  Saurin goce masa tai tabar wajen da gudu. Binta yay da sassarfa, cikin saurin ya riƙe ƙofar da take neman rufewa ya shige shima. Sosai ta marairaice fuska, dan da gaske ta ɗauka yin zaiyi. “Please Yaya MM wlhy ni bana so, kawai kaje wajen matarka ka kwanama na yafe”.

     Damƙota yay tare da ɗagata cak ya dire saman gado, watsal-watsal ta shigayi da turasa, hakan yasa suka shiga ƴar kokawa wadda ya ƙyaletane kawai. Ya fara kai mata cakulkule tana dariya da turesa. Shima dariyar yakeyi da ƙoƙarin kaima wuyanta zuwa kirjinta kiss. Da haka yaci nasarar haɗe lips ɗinsu waje guda. Tun tana son kauda kanta har yaci galabar shagaltar da ita ta fara bashi haɗin kai. Romancing juna sukeyi cike da sauka a layin manta matsayin junansu. Da sauri ta damƙe masa hanunsa dake ƙoƙarin zame rigar barcinta da tuni ya sauketa akan ciki dama. Jin yana ƙara ƙasa da ita ta dawo hayyacinta. Dakatawa yay tare da buɗe shanyayyun idanunsa dake cike da fitina yana kallonta, dai dai itama ta buɗe natan dake da raunin gani dan tuni ya zare gilashinta dama. Ƙoƙarin janyewa tai ya sarƙesu cikin nasa. 

   “Why?”.

 Ya faɗa da ƙyar muryarsa a matuƙar ɗashe tamkar mai mura.

     “Akwai ciwo”.

   Ta bashi amsa cikin raɗa itama dan muryar tata ko fita batayi rawa take ma kamar mai shirin sakin kuka. Kansa ya girgiza mata alamar kar tayi, amma kamar ya zugata sai gasu suna zirarowa da gudu. Rungumeta yay tsam a ƙirjinsa tamkar mai tsoron a ƙwace masa ita. 

  “Zubar hawayenki dai-dai suke da ƙuna mai raɗaɗi a zuciya. Ni mai raunine akan ki Juwairiyya. Da ke kaɗai aka raini wannan zuciyar tun daga ƙuruciya har girma. Nakanfi buƙatar nisantarki a zahiri, amma a baɗini ke ce sirrin ƙwarin gwiwar dukkan wani nasarorina. Nakanji himma da ƙawa zucin jajircewa a karan kaina domin ke kaɗai ƙwalli. Idan na danganta matsayinki a zuciyata da kalmar SO kawai nakanji tayi ƙanƙanta da rage miki kimar zamowa ke wacece ɗin. Da ace so kwalba ne da tuni ƙarfin ikonki ya tarwatsashi daga zuciya saboda GIRMAN KI. K ɗaya tilo, k ɗaya ƙwalli a tarihin da UBANGIJI ne sarki mai ikon sarrafa zukata kawai ya lulluɓe saboda hikimarsa. Ki rayu dani duk tsanani koda ace baƙya buƙatata a irin matsayin da ke kike da shi a wajena. Na miki alƙawarin nawa ya wadatar damu da har ƴaƴan da zamu haifa.”

   Maganar yake da harshe, amma ita zuciyarta ce ke neman ɓarkewa gida biyu domin yana karantasune a gareta tamkar maimaici akan abinda ta gani a ɗazun. Taigar jikinta gaba ɗaya ta gama miƙewa, da ace ba rungume take a jikinsa ba babu abinda zai hana ya ga yanda take tsuma. Ya ɗago kanta a hankali tare da daidaita fuskokinsu. Da sauri ta maida fuskarta ta sinne a ƙirjinsa, yay ƙoƙarin sake ɗagowa amma ta hana hakan.

     “Please Babie say something”.

   Kuka kawai ta sakar masa dan zuciyarta mai rauni ce, a yanzu kuma ta ƙara raunana ne fiye da raunin daya kasance halittarta, jiyay gaba ɗaya ma ya rikice, ya tashi zaune da ita a jiki, buƙatarsa kawai ta kallesa, sai dai taƙi yarda tai hakan sam. Dole ya barta, ta sake zamewa ta kwanta tare da jan bargo ta ƙudundune jikinta har kanta. Shiru yay yana kallonta ƙirjinsa na harbawa da ƙarfi. Ya jima tsahon lokaci a haka, kafin ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauri alwala……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button