FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
.
???? Ni ma dai ban sani ba, amma bari fans su baki amsar ki, don na san su akwai su da tunanin hasasowa. ????
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
TUNATARWA
”’Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, “Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba.” Abin da yasa haka kuwa shi ne rashin nutsuwa cikin sallah.
Allah yasa mu dace.”’
.
EPISODE Forty Two
Kyakykyawar parlor’n tabi da kallo, a ranta tana ayyana tsantsan kyawun sa da tsaruwan sa, duk da ba kaya ne me yawa a ciki ba, saboda kun san yanayin tsarin tura wa, basu cika saka karikitai kamar mu a gida ba, amma haɗuwar sa sai kin yi kamar zaki zubar da yawu tsaban kallo. Hotunan sa ne har guda uku a ƙusurwa-ƙusurwa na ɗakin, babu me cewa shi ne sai idan ka yi masa kallon tsab, sabida mugun haɗuwar da yayi, tamkar dai ɗan ƙasan; ba ɗan Nigeria ba, uwa uba ga shi da skin irin nasu, ga kyawu da ya haɗa, ga kuma kayan da ya saka duk nasu ne.
Ɗahira ta saki baki tana kallon Parlor tamkar wata ƴar ƙauye. Sai jin takun takalman sa tayi daga bayan ta, da sauri ta waiga tana kallon sa
Ba ita yake kallo ba, da alamu ma har ya shiga ɗakin sa, duba da har ya cire rigan saman Jikin sa; yana sanye da Singlet da dogon wandon da ya zo da shi, fuska babu walwala ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin tsararrun kujerun parlor’n
Ɗauke kai tayi tana haɗiyar yawu a hankali sabida jin maƙoshin ta ya bushe, tsayuwan taci gaba da yi a inda take, tunda be ce mata ga inda zata shiga ba, sabida ba wani ɗakuna ne da yawa a gidan ba, daga ɗakin sa sai irin sa na baƙi, sai kuma kichen me haɗe da store har biyu da ƙofa ta baya da zai kai ka Garden ɗin gidan, sai kuma Toilet a parlor’n guda biyu shima.
Tana nan tsaye ya ƙi ya ce mata komi, dole ta ajiye wani ƙyaliya nata ta kalle sa tace, “ina ne ɗakin da zan zauna?”
Uffan be ce mata ba, ya ci gaba da latsa wayan sa, har sai da ta cire rai da zai yi magana, sannan ya ce, “baki da muhallin zama a gidan nan, taimako ɗaya zan miki”. Sai ya ɗago kai yana kallon ta, hakan yasa suka haɗa idanu, kallon kallo kawai suke wa juna, ko wanne na cike da juriyan kallon ɗan uwan sa, domin yanda gaban su ke wani irin bugawa a tare sai ka ɗauka suna jin bugun zuciyar junan su, shi nashi har da wani tsoro ne ya mamaye sa, wanda duk idan dai ya kalli ƙwayan idanun ta masu Colour’n nan, to sai hakan ya ziyarce shi
Wani irin ɗaure fuska ya sake yi, sai tayi saurin sad da kanta ƙasa, domin itama ta kasa ci gaba da kallon sa
“Ga lungu can, nan zaki riƙa kwana”. Ya nuna mata wajen kichen da hannun sa, sannan ya ci gaba da magana, “ko a parlor’n nan ban yarda in ga ƙafafun ki ba”.
Sosai zuciyar Ɗahira ke suya da maganar nan nasa, sai dai ta kasa cewa komi illa sake duƙar da kanta da tayi, take hawaye suka soma sintiri a saman kyakykyawar fuskar ta sabida jin rainin hankalin sa da baza ta iya ɗauka ba, “wai me yake nufi ne? Ni ce zan riƙa kwana a can kamar almajira?”
Shi kuwa tuni ya miƙe ya shige cikin ɗakin sa, ko a jikin sa. Wanka ya shiga yayi ya soma rama sallolin da ake bin sa. Tunda kwana suka yi a hanya.
Tamkar gunki haka Ɗahira ta ƙafe a inda ya bar ta, ko motsin kirki ta gaza yi, lumshe idanu kawai tayi hawayen ta na ci gaba da zubo mata. Har ya fito tana nan tsaye a wajen bata jirga ba
Kallon ta kawai yayi ya taɓe baki, sai da yaje kichen ya haɗa tea kafin ya dawo cikin parlor’n, zama yayi yana harɗe ƙafafu, sai ya ɗauki wayan sa ya soma latsa wa yana sipping coffee ɗin.
Babu daɗe wa aka yi Nocking a bakin ƙofan, sai ya bayar da iznin shigo wa
Wani matashi ne ya shigo, shi ne me kula masa da gidan, kuma shi ne ya gyara gidan tun da ya kira sa yace “zai zo” har girki shi yake masa
Gaishe sa yayi bayan da ya durƙusa a gaban sa alamun girmamawa
Cikin miskilanci tamkar bazai yi maganar ba ya amsa mishi, kana ya ƙara da cewa, “daga yau ka zauna ka huta, ina da me aiki”. Yayi maganar cikin turanci
“Ok sir thank you”.
“You can go”.
“Ok sir”. Ya sake faɗi yana me miƙe wa tsaye ya fice.
Ɗan ɗago kai yayi ya kalli setting da Ɗahira take, sai ya taɓe fuska yana ci gaba da sipping coffee ɗin sa, kamar shuɗewar mintoci a ƙalla goma, ya ajiye Cup ɗin a saman table, kana yaci gaba da latsa wayan sa. Daga ƙarshe ma kwanciya yayi saman kujeran yaci gaba da abinda yake yi.
Yanda ƙafafun ta ke zugi nan da nan suka soma rawa sabida gajiya, dole ta janye ƙafafun ta ta isa inda ya nuna mata, ajiye Trollyn ta tayi a wajen, sannan ta buɗe ƙofan da take kyautata zaton Toilet ne, ta shige. Zama tayi a ciki tasha kukan ta ma’ishi, kana ta share hawayen ta tare da ɗauro alwala. Tana fitowa babu shi cikin parlor’n, ƙarisa wa tayi wajen Trolly ɗin ta ta zuge ta ciro Hijab, sannan ta zare gyalen da tayi Trollyn dashi ta saka Hijab ɗin, cikin parlour’n ta ƙarisa ta soma sallah saman tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen, rama sallolin da ake bin ta tayi. Har ta idar ta soma kwararo addu’a tana kai wa Allah kukan ta, bayan ta ida sai ta shafa tayi zaman ta a wajen, ta jima tana zaune a wajen ga zafi ya ishe ta, dayake ba’a kunna masa Gen ba, sai ta tashi ta cire Hijab ɗin ta ninke, ta nufi Trolly ɗin ta taja shi zuwa ɗakin kusa da nashi, sai dai a kulle yake, hakan yasa ta tsaya tana tunanin mafita, domin baza ta iya kwana a inda ya nuna mata ba tamkar wata almajira, ko bata da gata sai haka
Juya wa tayi ta mayar da akwatin, sannan ta shige Toilet ɗin, wanka take son Yi Amma babu ruwa me zafi tunda babu wuta, sai ta fito ta nufi kichen inda taga ya bi ɗazu, tana shiga kuwa ta sami komi a dai-dai, ta kunna gas ta matsa ruwa a famfon kichen ɗin; ta ɗaura. Sai da yayi zafi ta sake tare da sirka wa, har ta koma ta shige Toilet bata sake jiyo motsin sa ba, wanka tayi ta fito. Ta duba kayan ta cikin Trollyn ta ta koma Toilet ɗin ta saka, riga da skert ne ƴan kanti, sun yi mata kyau sosai sun lafe a jikin ta, kasancewar bata da jiki
Ta rasa yanda zata yi da kayan da ta cire, sai ta fito dasu ta ninke ta mayar cikin akwatin nata, janyo akwatin tayi ta nufi cikin parlour’n, tayi zaman ta kan kujera, sai dai gaba ɗaya tunani ya addabe ta, ga yunwa da ta soma ji, amma rashin jin daɗin yanayin yasa baza ta iya girki ba.