AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

FREE PAGES 1

Jirgin ‘American Airways’ ya sauke AALIMAH MANSOUR a birnin Massachusetts na kasar Amurka a ranar ashirin da biyar ga watan Mayu, na shekara ta dubu biyu da goma sha shidda(2016). A sannu ta bi jerin gwanon masu saukowa daga jirgin rataye da matsakaiciyar jakar hannu ta mata. Sanye ta ke da doguwar riga da veil dinta kirarTahran (maroon colour) ta zagaye fuskarta da veil din rigar. Takalmin kafarta baki ne mahadin jakar hannunta marar tsayin dunduniya. Taku ta ke cikin nutsuwa har ta taka kwaltar filin jirgin (Boston Logan International Airport) ta shiga van din da sauran fasinjoji ke shigawadda za ta karasa da su zuwa ainahin ginin cikin filin jirgin, inda aka yi mata duk wasu immigration checks, daga karshe ta dauko jakar kayanta ta fito.
Hasken sassanyar ranar da ya soma ketowa ya dallare mata ido, ta sanya tafin hannunta ta kare saman idanunta daidai lokacin da masu taxi suka soma isowa gare ta.
Tambayarta suke inda za a kai ta. Ta diregajiyayyun dara-daran idanunta a kansu kamar mai kiyasi, kamar kuma mai tantance wanda ya kamata ta zaba,da ganinta ka ga bakoa kasar da bai taba zuwa ba, kafin ta tsaida idonta a kan wani dan tsamurmurin bature ta nuna mishi adireshin inda zai kai ta, wanda ke rubuce cikin jotter dinta, wadda ta fiddo daga jakar hannunta. Daukar jakar tata ya yi ya sanya a bayan motarsa ya bude mata kofar baya, ta shiga ta zauna. Ya zagaya ya shiga mazauninsa, ya tada motar.
Tafiya suke sannu kan hankali a kan kwaltar manyan titunan birnin Massachusetts tana karewa kyawawan titunan kallo.
Birnin Massachusetts na daya daga cikin manyan biranen da kasar Amurka ke tinkaho da su. Ya kuma kunshi al’ummatai daban-daban, daga yarekala-kala na duniya. An kiyasta population din birnin Massachusetts a shekarar (2017) da adadin (685, 094 population).

Yana kusa da Cambridge daga gabas, tana iyaka da Hampshire da Vermot daga Arewa, daga yamma zagaye yake da babban birniNew York, daga Kudu da birnin Connecticut da Rhode Island. Daga gabas kuma zagaye ta ke da Atlantic Ocean. Birni ne daga Arewa maso gabashin USA.

Mai taxi ya tsayar da motar a cikin estate din (Martha’s Vineyard) a kofar wani kyakkywan lodge cikin birnin BOSTON (Capital of Massachusetts).

Aalimah Mansour, ta yi ajiyar zuciya, ta lalubo adadin kudin da ya bukata ta ba shi, ya ba ta canjinta, ya kuma fitar mata da jakarta daga bayan motarsa. Sannu a hankali ta karasa kofar gidan tana nazarin kayatacciyar unguwar. Tana daga cikin manyan estate (kebantattun unguwanni) a birnin Boston. A saman kofar gidan an rubuta lambar gidan da kuma sunan mamallakin sa ‘ISHAQ RAAZEE’.
Kararrarwar kofar gidan ta shiga dannawa, sai da ta danna sau uku kafin ta jiyo muryar mace na fadin tana zuwa cikin harshen Nasara. Gabanta ya ci gaba da lugude kamar zuciyarta za ta fado daga cikin kirjinta. Ba ta da idea na irin karbar da za ta samu daga Kawun nata, haka ba ta da sanin irin karbar da za ta samu daga matarsa Mummy Zulaiha da ‘ya’yanta, matar da kowa a family dinsu ya kwana da sanin ba ta son kowa ya rabe ta, daga mijintasai ‘ya’yanta. Kada a rabi inuwar arzikin da suke ciki. Balle kuma su, da nata mahaifin duk cikin zuri’arsu shi ne mai karamin karfi. Banda Mamada ta dage ba za ta yi zaman hostel ba, alhalin ga Kawunta da iyalinsa a kasar da ba abin da zai kawo ta gidan Kawun nata.
Ta tabbata sai ta fi samun nutsuwa a zaman hostel din, amma ya ya za ta yi da umarnin iyayenta? Ta riga ta dora zuciyarta a kan son karatun nan, kamar yadda ta ke son rayuwarta. Sannan ba ta san kowa ba a kasar bayan su. Asstrict as her Mum is, (sabida tsantseni irin na mahaifiyarta) a kan tarbiyyah, ta tabbatar mata ko dai ta zauna gidan Kawunta ta yi karatun a gabansa, ta fuskanci kowannne irin kalubale na matarsa da ‘ya’yansa, ko ta hakura ta yi aure. Hankalinta zai fi kwantawa ita ta hakura da nata burin akan karatun nata.
Mahmoud, saurayi daya data ke da shi a rayuwarta, ko ta ce wanda ya taba cewa yana son ta da kalmar aure, dalibi ne shibai shirya ba, yanzu ne yake shekarar karshe a jami’a, sun kulla soyayyarsu ita da Mahmud Kaita ba tare da sanin iyayenta ba, karewa ma boye tarayyarta da Mahmud ta ke don muddin Mama ta san tana da tsayayye, duk sonta da karatun ga ‘yar tata, za ta hakura ne ta yi mata aure. Banda babban Yayanta Aboubacar (Abubakar)babu wanda ya san da maganagr Mahmud a gidansu, shi ma ya sani ne a dalilin Mahmud din abokinsa ne, kuma ta dalilinsa suka san juna.
Duk wannan tunanin Aalimah na yin shi ne a tsaye a kofar gidan Kawunta kafin a zo a bude mata kofar, cikin mintunan da ba su gaza biyar ba. A daidai lokacin ne kuma Easther (‘yar aikin) Mummy Zulaiha ta bude mata kofa. Kallon juna suka tsaya yi na rashin sani ita da Easther din na ‘yan sakanni, kafin ta ba ta hanya tare da yi mata alamun ta wuce ciki ba tareda ta tambayeta wanda ta zo nema ba. Ba kuma komai ya sanya Easther bai wa Aaalimah hanya babu tambaya ba, sai kamanninta da ta gani mai dimbin yawa da yaran gidan, musamman matan.
Aalimah ta wuce ciki tana jan jakarta cikin nutsuwa. Easther ta mayar da kofar ta rufe. Daidai lokacin da Mummy Zulaiha ta bullo daga upstairs a shirye tsaf, tana taku kwaf-kwaf akan tsanin takalmin ta irinna matan da duniya ke yi da su, suka kuma sameta dai-dai da ra’ayinsu, makale da jakar hannu da mukullin mota alamar fita za ta yi.
Sakin baki ta yi cikin madaukakin mamaki tana kallon ba’abziniyar budurwar da ke shigowa. Doguwa, sambaleliya, fara tas! Mai dogon hanci da manyan fararen idanu, labbanta sirara jazur da su, ma’abociyar yalwar sumar kai, wadda ta fallasa kasantuwarta daga ruwa biyu, wato kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba cikakkiyar bahaushiya ba ce, jinin su maigidanta Ishaq Razee ce. Yarinya ta karshe da ta yi tsammanin gani a kasar America, kuma cikin gidanta, a dai cikin family din maigidanta.

Aalimah ta saki murmushin yake, wani lallausan murmushi mai ban sha’awa na nuna ladabi, ta russuna tana gaida matar Kawunta, wadda mamaki ya hana ta ce mata kanzil. Sai da ta gaishe ta har sau biyu, Zulaiha ba ta farfado daga suman mamakin wucin-gadin da ta yi ba, har sai da karamar ‘yarta Yasmin ta taba ta, tana fadin,
“Mummy ana gaishe kiâ€.
Firgigit ta yi, ta dubi Aalimah tana ayyana abubuwa da yawa a cikin ranta, me ya kawota? Wato Ishaq wuyansa ya yi kaurin da zai soma kwaso abzinawan danginsa yana kawo mata gida ba tare da shawara da ita ba? Abin da ba za ta taba dauka ba kenan. Amsa gaisuwar ta yi kadaran-kadahankafin cikin shaqaqqiyar murya ta ce,
“Ke da wa ku ka zo?â€
Aalimah ta sunkuyar da kai cikin muryarta mai sanyi, ta ce,
“Ni kadai ce Auntyâ€.
“Ke kadai tun daga Nigeria?â€
Ta daga mata kai alamar “Ehâ€.
Kamar za ta ce wani abu, sai kuma ta fasa ta ci gaba da saukowa daga stairs din. Ta dubi Easther cikin rashin walwala ta ce,
“Ki ba ta abinci ki nuna mata dakin kwana, ni fita zan yiâ€.
Easther ta amsa, “Yes, Ma!â€
Ta dubi Aalimah cikin hadiye fushi ta ce, “Ki wuce ku je. Sai na dawo. Zan kai Yasmin makaranta ne, daga can zan koma officeâ€.
Cike da ladabi Aalimah ta amsa, ta bi bayan Easther, Mummy Zulaiha da ‘yarta Yasmin suka fita.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button