ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad
_____
[9/17, 12:49 PM] 80k: ππππππ
πΊ DA ‘IMANπΊ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ written by safiyya Abdullahi musa huguma
πππππππ
πΊπΊ
πΊ
β―1β£
A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al’ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah
sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da ‘yar jakar swagger dake maqale a kafadarta
babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi’a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi
ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadinββbarka da dawowa antyn muββ
ββyauwa sannunkuββta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan
hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki
”gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba”
”yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa”
cike da masifa hauwa ta qwalalo ido
”iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai daukaοΌ”
ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto”haba kulu na,wata kai yake a gurina ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke baοΌ”
duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da tadinsu
sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya cikin farar leda tana lodawa a botiki
bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana’ar tasu wato yada habaici da baqaqen maganganu
”hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin uwa kayi zamanka”
”kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da itaοΌba ana fasa musu kai da cewar kyakkya wa,bace ‘yarsuοΌ,ai dole su maisheta jari”
”hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za’a dire abun kunya cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa”
duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu
isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace”haba isyaku me yasa baku iya tafiya ne a hankaliοΌ”
baki ya murguda ya galla mata harara
”eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin gida”
ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya gaga tana fadin
”ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai kanshi to zamu kwashi ‘yan kallo dake wallahi”
bata saurari kurarinta ba ta yarfawa isyaku mari domin dama ko da,safe kafin ta fita sai da ya mata wata tijarar kuma tana kallo bata ce uffan ba sai dariya ma data sheqe da ita ,ai kuwa kanta tayo yana fadin
”kutumar uba,wallahi yau sai kin gane shayi ruwa ne”
gadan gadan ta nufota wand hakan yayi daidai da shigowar malam mamuda cikin gidan
”kai kai lafiyaοΌ”
”yauwa malam gwara da Allah ya kawoka,wallahi mun gaji da zaman wannan balagaggiyar tsakaninmu,ita ba aure ba ita ba karuwanci ba,ta ishemu ta ishi yarranmuοΌ”ya katseta da fadin
”to yanzu me kuma ya faruοΌ”
”wai wannan dan talilin yaro ta daddage ta zabgawa mari don kawai ya zuba mata kunu bai sanig bau,to wallahi ba zan yarda ba,ko ya rama ko ni na rama masa da kaina”
”kai isyaku me yasa haka”
”baba ban sani bane ba fa,kuma ni wallahi sai na rama”
”ke maryam bashi haquri”
babu yadda ta iya haka tace kayi haquri
shi kuma ya tubure ramawa zaiyi,da qyar uwar tasa ta lallabashi ya haqura
hawaye na bin kuncinta ta shige dakin nasu,maman na zaune bisa daddumar yadda ta barta ko motsawa bata yi ba bare tasa baki a cecekucen da akeyi,bata ce da maryam din uffan ba kamar yadda itama batace din ba,ta dauki dadduma guda daya daga inda suke ajjiyewa ta tayar da sallah
ta dade akai tana miqawa Allah kukanta kafin ta sallame,tana ninke sallayar ne taji maman tace
”na sha gaya miki maryam dole kici gaba da haquri matuqar dai kina zaune ne cikin gidan nan”wasu sabbabbin hawayen ne suka zubo mata,ta koma gefan daya daga cikin kujerun falon ta zauna tana fadin
”mama,ke kanki shaida ce akaina,amma duk yadda kakai ga haqiri wataran mutanen gidan nan sai sun saka kayi misbehavingοΌyanzu mama kamar isyaku fa qanin bayana mamaοΌ”
”ya isa kada ki saka abun cikin ranki,Allah yana tare dake ba wai ya manta da ke bane”
cikin sanyi wanda ya zamto halittarta ta goge fuskar tata cike da tawakkali da miqa lamuranta ga Allah
”to mama”shine abunda ta fada a sanyaye
mrs muhammad ce
ππππβπ»βπ»βπ»
[9/17, 12:49 PM] 80k: πππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
π ABADANπ
πΊππΊππΊ
WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
πΊππΊππΊππΊ
πΊππΊππΊ
πΊππΊ
πΊπ
πΊ
assalamu alaikum masoya,xaku ga nun canzs sunan littafin mu zuwa ABADAN,haka ya faru ne sakamakon yin wani littafi a baya mai wannan sunan,ina muku fatan alkhairi
βΆ2β£
Hundatu ce tayi sallama ta shigo rumfar sanye da unifoam ruwan tsamigaye riga da zani sai farin hijabinta kafadarta rataye da jakar makaranta fara,tana cire takalminta hade da socks tace
”anty maryam ya na ganki yau a gida da wuriοΌ”
dan dafe kanta tayi kadan tace”yau da wuri na kammala aikin ne shi yasa,kuma dama bana jin dadi sosai”
cikin nuna damuwa ta zauna saman kujera
”sannu antin mu,ko na karbo miki maganiοΌ”
murmushi tayi har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana
”idan banda abun hindu wanne me chamist za’a samu da uwar ranar nanοΌ”
ta dage gira”haka ne fa anty”
”ki duba locker kusa da gadona akwai paracetamol ki dauko ki sha,tuntuni da kika shigo baki gayamin ba har kika tsaya fada da mutane koοΌ”
Ad
_____