AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM – Buhainat: 🌹 Aalimah 🌹

SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

LAST FREE PAGE

Kai ta daga, cike da tausayinsa. Babban mutum kamarshi haka, mai manyan ‘ya’ya da furfurarsa da komai yana ta kwantar da murya, yana lallashinta kan dan abin da bai kai ya kawo ba. Ko bai roke ta ba, ba ta yi niyyar gaya wa Daddynta komai ba balle Mama, da ba’a gaya mata abin da zai daga mata hankali.
Ta ce, “Daddy na yi maka alkawarin zancen nan ya wuce. Amma ina rokonka ni ma don Allah kada ka yi wa Mummy fada. It’s human nature (halittar dan adam ne).
Ko ka yi fadan ba abin da zai canza ta. Akwai mutane irinta da yawa da ba sa son kowa ya rabe su, they will act absent mindedly, su rasa tsinkayensu da tunaninsu.
Yanzu kamar Mummy she’s very well educated, amma ka ga ta kasa hangen cewa, abinda take shukawa a kaina ba inda zai je musamman a kasar nan, you’ll soon come to know it.
A lokacin da za ta aikata ba ta yi tunanin hakan ba. Abinda take so kawai shine in matsa in bata gidan ta. Don haka ko me za ka zo mata da shi yanzu ta riga ta shirya maka. Daddy act smart, sai a zauna lafiya. Ni kuma ba zan sake cewa zan koma hostel ba har sai na gama karatuna, zan zauna da Mummy yadda ta ke Daddy, it’s a promiseâ€.
Hannayensa biyu ya ware mata,
“Give me a hug my daughterâ€.
Kunya ta ji sosai ta soma dariya, kafin ta karasa ya rungume ta. Sannan ya sake ta ya dan bubbuga kafadunta.
“What do you like to eat?â€
Ta ce, “Na yi girki Daddy, mu je gida mu jira su Basma su dawo mu ci abinci tare yadda muka sabaâ€.
Ya ce, “No, it will take time, mu je in sama miki abin da za ki ci, ki ci a gabana ki koshi, sannan mu je mu dauko su Basman mu koma gidaâ€.
Wani gidan cin abinci ya kai ta, ya tula mata kayan dadi a gabanta, irin wanda ba ta taba ci ba. A gefe ga Pizza, Shawarma da kazar Kentucky fried chicken. Ta ci iya cinta, ta kora da sassanyan Pepsi, ta yi gyatsa, ta yi hamdala. Ya yi wa su Khaleesat guzurin nasu suka tafi, Khaleesat aka fara dauka a makarantarsu ta islamiyya da yake in ta tashi daga boko islamiyya ta ke shiga wadda ta ke daura da makarantar bokon nasu, ita da Yesmin, ta wasu larabawan Libya. Sannan suka dau hanyar Boston University bayan Daddy ya kira Basma yace kada ta biyo Vangasu nan zuwa daukarta. Khaleesat cike da murna da ganin yau Aalimah ta fito, wannan ya tabbatar mata Daddy came to know Mummy’s mischiviousness (Daddy ya ganeketar Mami).
A kalla dai ba su sabawa uwarsu ba tunda ba su suka gaya masa ba. Abin da ya sa Basma ma ba ta damu sosai ba kenan a kai, ta san jami’ar Boston wil not take that any longer they will trace for Aalimah (bazasu dau wannan ba, zasu bi bayan Aalimah). Ta yi mamaki ma da aka dauki tsawon wannan lokacin. Tana ganin Aalimah a motar sai Ehoo! Ta rungume ta tana ta faman sambatu.
“Aal, are you alright? We are sorry Aal, we can’t do anything for youâ€.
Harararta Daddy ya yi sosai, mai dauke da maganar da ba sai ya furta ba.
Da sauri ta ce, “I’m sorry Dad, she’ll throw a tantrum (zata yi balbalin bala’i) (tana nufin Mamanta)â€. Ya girgiza kai kafin ya ce.
“Wannan na nufin kun fi jin tsoron Mamanku a kainaâ€.
“Of course, Dadâ€. In ji su duka su biyun har suna hada baki.
Dariya ya yi, a ransa yana fadin, ni kaina wani lokacin tsoron nata nake ji, amma this time around za ta gane kurenta. Yesmin ba ta san bikin da ake ba, tana ta kokawa da robar ice-cream dinta. Aalimah ta baiwa kowacce ledar takeaway dinta. A cikin motar suka hau ci don duka yunwa suke ji.
“Kada ki so ki tona yadda nayi kewarki a makarantar nan Aalimahâ€. In ji Basma.
“I can estimate (zan iya kintatawa)â€. In ji Aalimah ba tareda ta dago ba tana kokarin hudawa Yesmin lemo.
Daddy yana jinsu yana jin dadi a ransa, zumuncin Basma da Aalimah yana yi masa dadi, ‘yarsa Basma haka ta ke, zuciyarta a bude ta ke, kuma ba ta boye duk abin da ke zuciyarta,whilstKhaleesa ‘yarI don’t carece, though she’s nice too (yayin da Khaleesat mai halin ko’in kula ce, duk da haka tana da kirki).
“Bazan ba ki hakuri kan abinda ba ni da laifinsa ba Aal, Mummy tana da kirki, amma wani lokacin ba ka gane kanta. Na tabbata za ta zo ta so ki idan ta gane kyawawan dabi’unki. Ban taba ce miki komai ba, tunda Mummy ta fara abinnan, ina jira ne sai Daddy ya sani. I’m sorry Aalâ€.
“Zan iya rokon alfarmar ki bar maganar nan haka Basma?Mum is my mother, meye a ciki don uwa ta yi wa danta wani abu da bai ji dadin sa ba?â€
“Ai haka ta ke da mita kaman tsohuwaâ€. In ji Khaleesat.
Dariya suka yi ita da Khaleesat, Basma ta harare ta. Daddy uffan bai ce musu ba, shi kadai yake sakawa yana warwarewa a ransa na matakin da zai dauka a kan Mummy, yana kuma tunanin maganganun da suka yi shi da Aalimah. yarinya karama na koyar da shi ‘psychology’. Na yadda zai tafiyar da matarsa mai baudadden hali. Ya san duk maganganun da Basma ke yi wa Aalimah borin kunya ne na halin uwarsu. Ya jinjina wa Mansour da Aseeya na irin tarbiyyar da suka bai wa Aalimah.
Daya bayan daya suke shigowa gidan, Aalimah, ita ce karshen shigowa. Tsoron Mummy ta ke ji, tsoro mai yawa. Sanda suka shigo ita kadai suka hango zaune a dining tana shan wani damammen abu cikin kofi kaman oat, Yesmin ta yi wajenta tana kai mata ledar takeaway da suka taho mata da shi. Ido ta daga tana kallonsu one-by-one bayan ta hambare Yesmin ita da ledar tata.
Ta kan Basma ta fara don me ta kashe wayarta tana so ta tambaye ta karfe nawa za ta gama lectures ta dauko ta, shi ne ta sa ta yi wahalar banza? Sai ta koma kan Khaleesat, uban wa ya ce su taho ba su jira ta ba bayan sun san za ta zo daukansu kamar kullum? Sannan ta dawo kan Aalimah, har huci ta ke yi.
“Wato don ba ni na haife ki ba ban isa in sa ki aiki ba, tunda mai aikina ba ta nan aiki ya yi min yawa, shi ne ki ka kira ubanki? To don Allah in kin isa ki sa ya yi min duka ko ya sake ni, in bar miki kasar ki yi abin da za ki yi a cikintaâ€.
Ko tari babu wadda ta yi a cikinsu, ‘ya’yanta sun zuba mata ido, Aalimah ta sunkuyar da kai kasa sai hawaye ta ke yi. Ba ta saba da fada ba, ko Mamansu duk zafinta hadawa ta ke da nasiha. Mummy fada ta ke kamar ta ari baki ba wanda ta bari a cikinsu. She’s doing it fiercely kamar babu mijinta uban ‘ya’yanta a tsaye a cikinsu.
Wata tsawa da Ishaq Razee ya daka mata sai da ta sa Aalimah karasa fashewa da kuka, Yesmin kuma ta yi tsalle a sittin ta kankame Basma. Shi ma ya bude nasa famfon yi yake kamar zai doke ta. Duk yadda suka yi da Aalimah na cewa, he will act smart ya kasa. Da ma an ce mai hakuri bai iya fushi ba.
Bai zo da wannan niyyar ba ya zo ne da intention na hukuntata cikin ruwan sanyi. Amma ya lura zuwa wannan lokacin Zulaiha ta dade tana amfani da sanyinsa tana yin yadda ta ga dama da rayuwarsu. Ta yi masa laifi, sannan ta nuna ta fi kowa daukar zafi. Har da yi wa Aalimah kazafi wai ta kira shi. Ya tabbata Tabarmar kunya ta ke nannadewa da hauka. Gaskiya ne da ake cewa, mace komai shekarunta wani lokacin ba ka raba ta da dabba. Yanzu kamar Zulaiha mai manyan samari da ‘yammata ta tsaya tana wannan haukan just because ya kawo ‘yar dan uwansa gidansa?
Tun yana yi da turanci har ya saki ya koma da buzanci, ya koma harshensa Temachek, ya saki ya koma Francaise. A karshe ya ce,
“Please kindly get out of my mansion, go to the one who has no relatives, but I belong to IBRAHEEM RAAZI’S. I couldn’t scratch them from me for your selfish interest and your personal satisfaction. Is that clear? (Don Allah ki bar min gidana, ki tafi ga wanda bashi da dangi, amma ni jinin Razee ne, bazan iya ciresu daga jikina ba sabida son kai irin naki da biyan bukatar ranki)Ko sai na sake maimaitawa?â€
A kidime ta dago ta dube shi, he’s no longer her silent Ishaq. Wannan sassanyan mutumin mai kama da ko cokali aka sa masa a baka bazai ciza ba.Gabadaya ya hautsine mata ya koma cikakken buzunsa. Abin takaicin a gaban ‘ya’yanta, a kan wata ba’abziniyar ‘yarsa mai kama da danyen nama. Kafa ta sa ta hambare tebirin cin abincin tangarayen dakekai suka rikito suka kwankwatse nan take. Ba ta bi ta kansu ba ta wuce da gudu ta yi sama. Shi kuma Daddy juyawa ya yi ya fita daga gidan.
Kafin a jima Mummy ta sauko jaye da trolley. Dogon bakin wando na mata ne a jikinta da farar shirt an yi rubutu da bakin fenti ‘calvin klien, ta nade kanta da veil wanda ya sauka kan kirjinta, ta kuma ratayo jakar hannu mai dan girma Gucci. Ta rufe kwayar idanunta da black shades mai fadi don kada a gane halin da kwayar idanunta ke ciki. Suna tsaye cirko-cirko ta wuce su fuuu! Kamar guguwa ta fice. Sai karar reverseda mota da ficewarta gidan aguje suka ji. Yesmin ta sa kuka tana kiran, “Mummy…!â€
Za ta fice Aalimah ta kamo ta. Ta fi kowa shiga tashin hankali, kuka ta ke tun daga karkashin zuciyarta. She must leave this family for them to live in peace… ko Daddy na so ko ba ya so za ta koma hostel ko ta koma Nigeria.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button