AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Kama hannunta Basma ta yi suka hau sama, Khaleesat da Yesmin suka biyo bayansu. Ba wadda ta iya ce da ‘yar uwarta komai. Alwallah suka yi kowacce ta tada sallah. Ko da suka idar, Basma ta lura Aalimah ta kasa barin kan sallayarta kamar yadda ta kasa tsaida hawayen idanunta.

Ta raba aure! Ta raba ‘ya’ya da uwarsu!! Shi ne damuwarta!!!.

Kunna fitilar dakin Basma ta yi ta dubi Aalimah, “Malama, ba za ki zo ki kwanta ba? It’s past tenfa!â€
Kuka na sosai Aalimah ta fashe da shi.
“Ku yi hakuri Basma, gobe zan koma hostel, I’m not here to bring ‘anarchy’ between your parents. I’m sorry, very sorry…†Kukanta ya kara karfi sosai.
Basma ta sauko daga gadon ta zo ta zauna a gabanta. Kama ta ta yi ta rungume a jikinta, ta ce, “Aal, stop crying, kwantar da hankalinki. Ba nisa ta yi ba, za ta dawo. Kada ki damu kanki. Ba nisa zata yi ba. Our Mum will not go out of America because of you, she don’t even have friends. She’s going to that ANNOYING son of her’s. She mightbe in LAS VEGAS!â€.
(Maman mu bazata bar kasar Amurka saboda ke ba, ko kawaye bata da su, ta tafi wajen wannan Dan nata mai ban haushi. Yanzu haka tana birnin LAS VEGAS!â€
Aalimah ta maimaita kalmar LAS VEGAS!Akan halshenta har sau uku. Ta kuma karanta kalmar a zuciyarta sau ba adadi a wannan ‘yan dakikan da basu gaza biyar ba. She has been hearing things about Las vegas… Nan da can, daga bakin su Basma, and her fellow Boston students. Haka kawai sunan garin ke mata dadi da kwarjini a zuciyarta. Yake sanya mata wata irin nutsuwa, a duk lokacin da taji an ambace shi. Jikinta da zuciyarta kuma ke yawan bata wani irin feeling; there’s something STRANGE associated with her life and this city……..Wato haka kawai jikinta da zuciyarta ke ba ta akwai wani BAKON al’amari mai karfi dake da alaqa da rayuwarta da wannan birni,wanda a wannan lokacin ba za ta iya cewa mene ne shi ba.

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM – Buhainat: Aalimah
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870

Aalimah ta maimaita kalmar LAS VEGAS!Akan halshenta har sau uku. Ta kuma karanta kalmar a zuciyarta sau ba adadi a wannan ‘yan dakikan da basu gaza biyar ba. She has been hearing things about Las vegas… Nan da can, daga bakin su Basma, and her fellow Boston students. Haka kawai sunan garin ke mata dadi da kwarjini a zuciyarta. Yake sanya mata wata irin nutsuwa, a duk lokacin da taji an ambace shi. Jikinta da zuciyarta kuma ke yawan bata wani irin feeling; there’s something STRANGE associated with her life and this city, which so far… she don’t know.Wato haka kawai jikinta da zuciyarta ke ba ta akwai wani sabon al’amari mai karfi dake da alaqa da rayuwarta da wannan birni,wanda a wannan lokacin ba za ta iya cewa mene ne shi ba. In aka ce strange ana nufin bakon abu. A kalla hankalinta ya dan kwanta da kalaman Basma. Tunda ta tabbatar mata Mamansu bazata bar su saboda ita ba. Khaleesat is busy with her I don’t care attitude, ta dade tana sharbar barcinta, Yesmin ce dai sai da dabara suka samu ta yi barci, don sun ce mata gobe za su kai ta wajen Mummy.
Duk da ba ta kwanta da wuri ba, hakan bai sa ta makara sallar asubah ba. Ta yi sallah ta tashe su dukkaninsu suka yi, har Yesmin. Barci suka koma, ita kuma kitchen ta nufa ta soma kici-kicin hada musu breakfast. Simple breakfast ta yi musu don zuciyarta ba dadi, plaintain (Agada), chips, da liver souce ta hada, sai ruwan shayi da ya ji kaninfari da cinnamon, wato (kirfa). Ta shirya komai a dining sannan ta koma sama. Tashinsu ta yi duka kowacce ta soma shirin wanka, daga nan sai shirin tafiya makaranta. Aalimah ji ta yi wani farin ciki ya zagaye ta, yau za ta je makaranta bayan zaman ukuba na sati hudu.
Suna karyawa Daddy ya aje fork din hannunsa ya dube su duka, “Daga yau Basma da Khaleesat ku dinga shiga kitchen tare da Aalimah, ku dinga koyon girki you are no more a kids now, ba wadda ba ta isa aure ba da a Nijar ko Nigeria ku ke, kuna jina?â€
Dariya suka hau yi kasa-kasa, wai aure.
Basma is 16+, Khaleesat is fourteen, amma Daddy na kira musu aure. Su a gurinsu they are babies, nono ne kawai ba sa sha.
Khaleesat ta ce, “Yaushe za ka bi bayan Mummy?â€
Hade rai ya yi sosai, ya ce, “She’s in Las Vegas. He called me yesterdayâ€.
Daga haka ya mike, ya ce su wuce kada su makara.
Har department dinsu Aalimah ya kai ta, ya ga malaman tsangayar da level-coordinator dinsu. Shi kadai ya san uzurin da ya ba su suka yarda za su yi mata covering abinda ya wuce ta. Allah ya so ta ba a fara jarrabawar karshen zango ba, amma ana gab da farawa, don haka a karshe sun gargade ta da ta maida hankali sosai ta kamo darussan da suka wuce ta.A yau har aboki ta yi wai shi Alex, baturen Poland don ta lura kwakwalwarsa is sharpduk a kokarin ta na cimma ‘yan ajinsu abinda ya wuce ta, kuma a yinin ranar kadai data zauna da Alex ta amince mutum ba zai iya rayuwa mai kyau shi kadai ba. Yana bukatar tarayya da mutum dan uwansa cikin kowanne al’amari na rayuwa, ba kamar yadda ta dauka a baya ba.
Yau kwanan Mummy uku da tafiya, kuma karatun Aalimah ya farfado. Don Daddy ya dawo da Easther babu nauyin komai a kanta, sai na karatun. Kusan kullum tana waya da Daddy da Mama, Yaya Aboubacar, Mahmoud, kannenta da mutanen Nijar. Ba kudi kadan Daddy ya loda mata a wayar ba. Haka Daddy ya takura kansa yake squeezing time dinsa wajen kai su da dauko su. Amma ya ce yana cigiyar direba.
Yau Aunty Zulaiha ta cika sati daya da barin garin. Gidan ba kowa daga ita sai Easther, yau din da ta kama juma’ah ba ta da lecture. Daddy ya ce ta maida hankali ta yi bitar littattafanta, kuma ta yi masa pounded yam and egusi soup yana so ya ci in ya dawo. Ba abin da ba su da shi a store da freezers don Mummy Zulaiha ba daga nan ba wajen iya cefane, ba ta wasa da cikin iyalinta.
A satin kadai saboda nutsuwar da ta samu ta yi fresh da ita, fatarta har wani sulbi da sheki ta ke yi sabida kyawun muhalli da weather din Massachusetts da ya karbe ta. Karfi da yaji jikinta da fatarta so suke su zama irin na su Basma.
Ta wuni tana karatu, sannan ta je ta yi wa Daddy girkin da ya sanya ta, daga bisani ta yi freshen up ta sanya daga cikin kayan da suka sayo a Zainab Sumu Primitive Modern. Bubu ne na swiss lacedark green mai stones. Ta kame gashin kanta a tsakiyar kanta, ta fesa turarenta (Nude by Rihanna). Ta sauko falo ta zauna da tintimemen text book dinta (Concepts in Pharmacogenomics) tana ci gaba da nazari. Easther ta fito ta yi mata sallama ta tafi gida.
Mintuna kadan da fitar Easther aka shiga danna bell ta ajiye littafin a zatonta su Basma ne suka dawo. Ta bude da sauri, amma maimakon su Basma wani handsomesaurayi ta gani a tsaye goye da jakar baya.Bazata iya kintata shekarunsa ba. Wani kyakkyawan murmushi ya sakar mata, tutsiysr karen fararen hakoransa ta fito, ya ce,

“Hi Pretty, I’m ABOULKHAIR!â€

Murmushin sanayya itama ta mayar masa, duk da bata san shin ba, amma jini ya bayyana kansa.
“….And I’m Aalimahâ€.
Hannu ya miko mata da nufin su yi musabaha. Maida hannayenta biyu bayanta ta yi ta sarke su.Sannan ta ba shi hanya tare da janyo trolley dinsa ciki. Ya karasa shigowa ciki yana kare wa gidan kallo, sannan ya dawo da kallonsa ga Aalimah wadda ta ja gefe tana ta kallonsa. He’s very handsome, elegant and energetic.
“Aalimah, ‘yar Kawu Mansour, kanwar Aboubacar na Kano Nigeria, right?â€
Daga masa kanta ta yi, har yanzu murmushin ta ke yi. Farat daya ta ji ya zauna mata a zuciya, irin mutanen nan ne da psychologist ke kira cheerful and passionate,masu shiga ran mutum ba tare da ya shirya ba, ko kuma zuciyarsa ta tsaya yin shawara da shi kafin ta karbe su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button