AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Wannan saurayi shi ne Abulkhair Ishaq Raazi, dalibin medicine a jami’ar Louisiana. Da na biyu ga Ishaq Raazi. Sanye yake da farar T.shirt samfurin Balenciaga da dogon wando monclear. Ya tara suma mai yawa a kansa. Aalimah, ta samu kanta da kasa dauke ido daga Abulkhair, sosai ta ke kallonsa wani abu na dan sukarta a kirji. Kallo ta ke yi masa wanda ba ta taba yi wa kowanne Da namiji ba.
Ya gama yi wa gidan da falon kallon kurillar da yake masa, ya juyo sai karaf! Suka hada ido da Aalimah, ya kamata tana yi masa kallon kurillah, kallon da ya wuce kima.
Da sauri ta sunkuyar da kanta. Dariya ya yiya matso gabanta ya tsaya. Tana iya jiyo tashin sassanyan kamshinturarensa, wanda ya danne duk wata ni’ima na dukka turaren da ta fesa. Ya sanya hannu ya dago habarta, ga mamakinta ta kasa hanawa. Karewa ma lumshe idanunta ta yi tana karbar wani bakon yanayi a zuciya da gangar jikinta. Muryarsa (kamar ta rowa).
“Ba kya shan hannu da maza, amma kin fi kowa iya kare musu kallo ko?â€
“By the way, you are beautiful my sister. One of the prettiest creatures I came across. Enjoy your stay in Bostonâ€.
Daga haka ya cika ta, ya yi mata wink, sannan ya nufi daya daga cikin dakunan da ke falon kasa, wanda tunda ta zo ta ke ganinsu a rufe. Ya bude ya shige ya rufe, ya barta nan tsaye kamar mutum-mutuma. Yo mutum-mutuma mana? Tunda mutum ce amma bata motsi?Ta tabbata da za a tsaga jikinta a daidai wannan lokacin za’a tarar gudun jini, ya katse a cikin dukkan jijiyoyinta, na adadin wasu mintuna da bata kididdige ba. Zata iya rantsuwa bata taba katari da namijin da ya dau hankalinta irin shi ba. Da ta tuna ya ce ita kyakkyawa ce, daya daga cikin kyawawan halittun da ya taba cin karo da su a rayuwarsa, sai ta ji kamar zaginta ya yi. However, statement din ya yi mata dadi. Ya sanya ta murmushi.
Ba shi ne mutum na farko da ya fara gaya mata tana da kyau ba,Mahmoud ya fada a baya. Sai dai shi ne wanda ya fada ta ji kalmar ta tsirga har cikin bargo da ruhinta. Duk da ta tabbata ba gaskiya ba ne abinda ya fada din. Ya fada ne don ta ji dadi, ko don wani dalili nasa na daban. Amma how could a hunk like him could notice the beauty of another person? (Ta yaya kyakkyawa kamarsa zai iya gane kyan wani dan adam? A nata ganin nasa kyawun ya isa ya disashe duk wani kyawu da zai gani. Wannan tunaninta ne amma.
Ta daga kafa da niyyar komawa sama ta ji dirin motar Daddy. Da sauri ta bude kofar suka soma shigowa daya bayan daya. Duk wadda ta shigo sai ta ba ta runguma da sumba sannan ta wuce. Daddy ne karshen shigowa, abin da ya fara tambayarta shi ne,
“Dan uwanki ya iso?â€
“Yes, he’s here atleast ten minutes ago Daddyâ€. ( Eh, yana nan, akalla mintuna goma da suka wuce Daddy).
Karasa shigowa ya yi yana mai dafa kafadunta da murmushi a kan fuskarsa.
“Hope you study your pharmaceutical books very-very much?†(Dafatan kin karanta littattafan harhada magunguna ki sosai sosai?â€
Dariya ta yi,
“I do Daddy, and also, your pouded yam and egusi soup is ready on the tableâ€. (Na yi Daddy, kuma sakwararka da miyar agushi sun kammala akan tebir).
Murmushi ya yi,
“Wato ‘yar tana son Babanta irin sosai-sosai ko?â€
Murmushi tayi. Kafin tace.
“Yes, she do Daddy,sosai-sosai take matukar son saâ€.
Yadda suke maganar tactically with nodding head sai da suka baiwa su Basma dariya. Ya barsu a nan ya wuce upstairs yana dariya shima yana cewa,
“Let me bath and pray. I will then hurriedly come and eat my sakwara. God bless you my child with amazing husband. Basma tell Abulkhair that we are having dinner together by 8pm.(Bari in yi wanka inyi sallah, sannan inyi sauri inzo in ci sakwara ta, Allah ya albarkaceki ‘ya ta da miji na ban mamaki. Basma gayawa Abulkhair zamu ci abincin dare gabadayanmu karfe takwas na dare)â€.
Shi ne farkon halartar table din. Ya yi wanka ya sake kayan jikinsa, gashin nan ya sha gyara ya kwanta luf sai sheki yake yi na abzinawan usli. Daddy shi ne na biyun saukowa shi ma ya cire kayan office ya yi wanka ya sanya na zaman gida. Suna daki suna sallah kafin su fito kusan a tare.
Idanun Aboulkhair kur! A kan steps din benen cikin falon, wanda yake fuskanta. Hira Daddy yake masa, amma da alama ba ya fahimtarsa, kunnuwa kam ya zuba yana sauraronsa. Abinda ya sani bayan wannan shine, zuciyarsa na neman yin tsalle ta fito daga allon kirjinsa. A lokacin da ta ke saukowa daga matattakalar benen rike da hannun Yesmin. Bai san ya kafa idanunsa a wurin ba sai da ya daina ganin reflection dinta a kan benen.
Kusa da Daddy Basma ta zauna, Khaleesat a gefenta. Kujerar Yesmin a dining din da ma karama ce, sai kujerar Mummy wadda ba wanda yake zama a kai ko da ba ta nan, sannan wata kujera guda daya a kusa da ta Abulkhair wadda Aalimah bata taba ganin wani cikinsu ya zauna a kai ba.It’s a seven-chaired dining table. Don haka empty kujerar da ke kusa da Abulkhair ta nufa ta zauna. Murmushi ta sakar masa kusa da fuskarsa tana kokarin zama.
“Ina fatan ban takura ka ba?â€
“Ta ina zan takura don kin zauna a kujerar Mu’azzam? Daddy, another one chair is needed on this table (ana bukatar karin kujera a tebirin nan) for Aal…alimahâ€. Ya fada muryarsa na sarkewa da ya zo fadar sunan.
Daidai lokacin da Khaleesat ta soma serving kowa curin pounded yam a kan platedinsa. Tana diban hadaddiyar miyar da ta ji ganyen alayyahu da na ugu da zallar tsokar kaza tana zuba wa kowa. Ba tare da Daddy ya dago ba yana kokarin kai lomar farko bakinsaya ce.
“She replaces him in us, he don’t want to stay in his family, So no need of another chair. (Ta maye mana gurbinsa, ba ya son zama cikin iyalinsa, abin da ya sani, yake so kadai shi ne sana’arsa. Saboda haka babu bukatar karin kujera)â€.
Ya yi murmushi bai amsawa Baban nasa ba, ba’a fadin laifin Mu’azzam akan idonsa, Yayan da baya taba yin laifi ne,kuma dan uwanda babu kamarsa. Ya soma cin abincin, “Tastes goodâ€. Inji Aboulkhair yana duban tsakiyar idanun Aalimah. Wadda tayi murmushi ta sunkuyar da kanta.
Daga haka bai kara magana ba. Sai dai lokaci zuwa lokaci idonsa na satar kallon Aalimah. Ita ma duk dagowar da za ta yi sai ta tsinci idanuwan Abulkhair cikin nata. Gabanta ya ci gaba da tsananta faduwa. Wani al’amari da bai taba faruwa da ita ba a kan Da namiji shi ke faruwa da ita akan Aboulkhair. Gabanta bai taba faduwa ba da kasantuwar Mahmoud a wuri, kallon idanunsa ko wani abu makamancin hakan.
Can tsakar kanta ta tsinkayi muryar Abulkhair yana tambayar Babansa ina Mummy? Ba ta ji amsar da ya ba shi ba, saboda ta yi nisa cikin wata duniya mai hasaso mata abubuwa kala-kala masu tsauri a kan Abulkhair. Wadanda ita kanta ta kasa sanin abin da ya janyo su ko dalilin afkowarsu cikin tunaninta. Shi ne Da namiji na farko da ya fara kai hannunshi jikin ta a shekarun balagarta.Habarta kawai ya taba, ba da wata manufa ba, amma ta samu zuciyarta cikin wani sabon yanayi. And she don’t want the feeling to grow higher! Runtse idanunta ta yi da karfi tana kiran sunan Allah. Cikin zuciyarta ta ke rokonSa Ya kawar mata da wannan bakon yanayin da ta samu kanta a ciki akan dan uwanta.
A haka aka gama cin abincin ba tare da ta ci wani abin kirki ba. Plate dinta fal sakwara ta barshi ta mike ta soma tattare plates din. Abulkhair ya dago idonsa daga kan Yesmin da yake yi wa fadan yadda ta bata jikinta da miya. Kallonta ya yi ido cikin ido, sannan ya ce,
“Give it a good six mosels, (kiyi ma sakwarar nan kyawawan loma guda shidda) sannan ki bar wurin nanâ€.
Da sauri ta dube shi, jin yadda ya yi maganar authoritatively, irin yadda ta ke yi wa nata kannen. Sannan fuskarshi babu wasa. Sosai ta nutsu, ta saita kanta a gabansa. Abin da bai sani ba, kasancewarsa a wurin ne yasa ta kasa cin abincin. Gabadaya a takure take, wani yanayi ne da bata taba samun kanta a ciki ba.
Marairaice fuska ta yi kamar za ta yi kuka, kuma da gaske gab ta ke da ta yi kukan…
“Wallahi na koshi…†ta furta da iyakar gaskiyarta.
Inda Allah ya ceceta kafin ya ce komai Daddy ya yi kiransa. Ya mike ya bar dining area din, ita kuma ta karasa tattare kayan da suka ci abincin, ta yi kicin da su. Ta dawo ta gyara komai, ba ta zauna a cikinsu ba ta ce musu da abin da za ta yi, ta haye sama.