AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aalimah ta dauko daya daga cikin text books dinta na makaranta ‘Basic and clinical pharmacology’ ta soma budewa wai don ya kawar mata da nacin tunanin Abulkhair da ya daura aure da zuciyarta cikin dan lokaci kalilan. Amma kowanne shafin littafin wanda (Bartram G. Katzung) ya rubuta, fuskar ABOULKHAIR ke appearing maimakon rubutun littafin. Babu shiri ta rufe ta soma kuka. Kuka sosai na tunanin wata cutar kwakwalwar ta same ta. Yo in ba hallucination ba wanda ta san ana ganin mutane a cikinsa mene ne wannan? Hayaniyar su Basma ta ji suna hawowa benen. Da gudu ta yi toilet ta shige ta rufe kanta.
Tsaida kukan ta yi, ta wanke fuskarta da sabulu, sannan ta fito. Canza kaya suke zuwa na barci, sai ita ma ta bi layinsu. Suna ta karadinsu irin wanda suka saba kafin su kwanta barci. Babu wadda hankalinta ya kai ga idanunta balle su yi noticing canjin yanayi a tare da ita. Kuma dama sun sani; ba ta cika surutu ba, sannan ba duka hirarrakinsu ta ke ganewa ba.
Wani sabon dare ga Aalimah Mansour Raazee, mai cike da rudani, wanda ya kawo sauyi cikin kyakkyawar rayuwarta. She fall madly in LOVE ba tare da saninta ba, kuma ba tare da ta shirya wa hakan ba. Barcin daren yau ya zamo ragagge a gare ta. Ga shi ita kanta ba ta san hakikanin abin da ya faru da itan ba. Abin da ta sani kawai shi ne, zuwan Abulkhair ya yi affecting kwakwalwarta da jin dadinta da walwalar ta.
Tana hasashen yadda za ta iya ci gaba da rayuwa a haka, cikin gidan Ishaq Raazi, muddin dansa Abulkhair na cikinsa. Sai asuba wani wahalallen bacci ya sure ta, wanda a cikinsa ta ga mutum biyu; Mahmoud da Abulkhair cikin yanayi mabanbanci.
Aboulkhair cikin farin ciki, Mahmoud cikin tsaka mai wuya, kuma wai duk a kanta. Sai da ta makara sallar asuba. Ita da ta ke tashin su Basma sallah, yau su suka tashe ta. Idonta ya yi jajawur ya yi luhu-luhu da kyar ta ke iya bude shi. Khaleesat ce ta fara lura da idanunta.
“Aal, kin tashi da ciwon ido?â€
Basma ta juyo, “Ai kuwa. In mun shiga makaranta sai mu je hospital a sa miki maganiâ€.
Duk damuwa ta bayyana a fuskokinsu. Murmushin kwantar da hankali ta yi musu.
“Ba fa ciwo yake yi ba, laifina ne, ni ce ban yi barci yadda ya kamata baâ€.
“But why?†Har suna hada baki wurin tambaya.
Sai ta rasa abin da za ta ce musu. Su kuma sun ki dauke idonsu a kanta har da kama kugu suna kalonta cikin tuhuma kamar su din ta yi wa laifin rashin barcin. Kafadunsu ta dafa duk su biyu a tsanake, ta ce, “calculus! I’m finding it difficult to understandâ€.
Kuma da gaske din ne, darasin yana ba ta matukar wahala wajen fahimta duk da kwarewarta a fannin lissafi. Basma ta yi dariya kafin ta yi dan juyi a tsakiyar dakin, ta ce, “Hey! Daina damuwa Aal, we have a calculus-gem in this house. Just tell him your problem and consider it solved! Na rantse sai kin ci abin da ya fi ‘A’ a calculusâ€.
Har ta je kitchen ta hada breakfast ta dawo ta fara shiryawa surutun da suke yi kenan. Na irin kwarewar Yayan nasu a fannonin lissafi da dama.
“Yo Allah na tuba ‘calculus’ ai shan ruwa ya fi shi sauki a wajen Monsieur Abulkhair, da har wani cikin gidan nan zai hana kansa barci a kansa. Sannan he is doing his teaching patiently. Unlike this ANNOYING son of Mum…!†(yana yin koyarwar sa a tsanake, ba kamar wannan dan Mummyn mai ban haushi ba).
Suka kyalkyale da dariya har da tafawa. Bude kofar aka yi ba zatonsu ba tsammani, wanda suke zunden nasa ne ya shigo. Kayan barci ne a jikinsa wadanda suka nuna manyan damatsansa (muscles) da halittar kasaitaccen kirjinsa wanda ke lullube cikin shara-sharan pajamas ruwan madara ‘yan gidan Ralph Lauren. Wannan kwantaccen gashin na jiya it’s no more like it was before. Ya cukurkude ya hargitse. Yana shigowa fada ya rufe su da shi.
6/28/21, 7:32 AM – Buhainat: Aalimah
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870
“…You goddam talkatives!Kuna duba agogo kuwa? Har downstairs nake jiyo karadinku tun asuba. Kun hana ni barci, kun hana kunnena zaman lafiya. Kun san cewa doguwar tafiya na yi, ina bukatar hutu, kuma ba abin da na tsana irin a hana ni barci da safe… za ku wuce ku karya ku tafi, ko shi ma Daddyn sai kun makarar da shi ya hana ni barci saboda ku?â€
Turanci yake zubawa kamar Charles Dickens ya sauka a Massachusetts. Tuni jikin Aalimah ya hau bari an fara abin da ta ki jini, wato (fada). Sum-sum-sum suka shiga wucewa, Allah ya so duk sun gama shiryawa. Basma har da zumburo baki, Aalimah ce karshen wucewa ta gabansa duk ta gigice. Babban abin da ke maida ita upset shi ne hargagi. Ai kuwa ta ci uban tuntube da kafarsa ta dama, ta tafi za ta ci da baka. Da wani irin zafin nama ya taro ta da dukkan hannayensa. Ido ya bude yana kallon cikin idanunta sosai da dukkan nasa idanun, kamar mai son karanto al’amarin da ke cikinsu. Ba ya so ya yarda da abin da kyawawan idanun ke gaya masa, cewa al’amarin da ke cikinsu, daya yake da wanda ya hana shi runtsawa a tsayin daren bakidayansa.
Yadda nasa idon ya tasa ya yi jajawur yayi luhu – luhu haka idanun nan da ke kallonsa suke. Sai dai kuma a nassi mai kyau na zuciyarsa na gaya masa, kada ya bari ta gane, dukkaninsu are too young da soyayya! Yanzu ne suke kokarin gina future dinsu. Kafin haka, soyayya da duk abin da ya shafe ta ba nasa ba ne. Infact, it’s out of his vocab bank (vocabulary bank).
Zuciya ce dai da ba ka da iko da linzaminta. He has a mission that he want to fulfill(yanada uzrin da yake son gabatarwa) kafin soyayyah. Yanzu ne yake shekara ta uku a jami’a, sannan yana da mashahuriyar damuwa da ke danne duk wani situation da ka iya samun zuciyarsa, na farin ciki ko na bakin ciki.
He will help his sister to concentrate on what she’s here for (zai taimakawa ‘yar uwarsa ta maida hankali kan abindaya kawota) ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi.
A hankali ya lumshe idonsa na tsawon lokaci ba tareda ya san lokacin da yayi hakan ba, sannan ya bude su a kan Aalimah, wadda ta yi suman wucin-gadi a hannunsa. Dago ta ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya sake ta, amma bai iya ci gaba da fadan ba, kamar wanda aka daurewa bakin. Ita ce karshen fita, da sassarfa ya biyo stairs ya sauko daga benen. Bai kalle su a dining ba ya wuce dakinsa.
Cikin quilt dinsa ya shige da sauri ya dukunkune kansa, zuciyarsa na racing wajen bugawa. Numfashin da yake shaka ya ji yana sauyawa da wani irin mayataccen kamshi, kuma kamshin (is feminine) wato na mace ne mai tada hankalin duk wani lafiyayyen Da namiji. Ya fahimci ma kamshin daga jikinsa yake, in fact shi yake kamshin sexy perfume din (‘Nude’ by Rihanna) wanda babu tantama a jikin Aalimah ya kwaso. Abulkhair ya ji komai nasa yana canzawa har numfashinsa. Wani situation ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Ya dauki lokaci cikin yanayin da yake ciki din yana kuma neman hanyar samun sauki. First, he have to get rid out of these clothes.(Gara ya cire kayan nan). Mikewa ya yi zaune ya soma zare su daya bayan daya, sannan ya shige toilet ya sakar wa kanshi shower.
Saukar ruwan a tsakar kansa zuwa jikinsa na tafiya tare da kawo sassauci a bugun zuciyarsa. Duka wannan ya faru cikin mintunan da ba su wuce goma sha biyar ba. Al’amarin ya zamo tamkar wani majigi da ya gifta a idanunsa. Har mamakin kansa yake yi, tunda dai ba yau ya fara ganin mata da yin alaqa da su ba. Matan ma ajin farko da suka amsa sunan mata a duk inda ya yi rayuwarsa cikin kasar America, daga sakandire har jami’a.
Sunyi dukkan rayuwarsu a Washington D.C ainahinaikin da ya yi sanadin kawo mahaifinsu kasar Amurka(consulate officer ne a baya). A Washington din duk suka yi sakandire shi da Yayansa MU’AZZAM, shi Aboulkhair bai ma karasa a can din ba.Abubuwa da yawa suka raba Daddynsu da Niger consulate America.Amma ba don dukkaninsu suna so ba.
Na farko rashin lafiyar Mu’azzam, wanda likitoci suka bada shawarar inda hali a sauya masa inda yake rayuwa zai fi jin dadin canza rayuwarsa, kuma a barshi a inda ya fi so. Sannan kuma Daddyn ya samu hanyoyin budi daban-daban wadanda samunsu ya fi na consulatedin kasarshi nesa ba kusa ba. Sannan lafiyar Mu’az tafi musu komai. Wannan ne mafarin komawarsu Massachusetts ba don suna son garin ba.
Kamar wanda ya saba zama a Abuja ne a ce ya koma Adamawa ko Yobe. Sai dai Alhamdu lillahi lafiyar Mu’az ta inganta.
Ya zabi Jami’ar Louisiana don ya yi nisa da Mu’azzam, saboda wasu dalilai da dama, muhimmi shi ne; ba ya iya jure ganin Mu’azzam cikin halin da ya kan samu kansa.
Bai taba sanya al’amarin mata a gabansa ba balle ya dame shi. Burinsa kadai ya zama ‘psychiatric doctor’ don ya san mene ne matsalar Mu’azzam ciki da bai dinta, ya yi masa maganinta. In haka ne, kenan abin da zuciyarsa ke darsa masa daga jiya zuwa yau akan… Aalimah ba nasa ba ne! He has to be cautious in his relationship with her(dole ya zama mai taka-tsan—tsan a mu’amalar shi da ita). Daga shi har ita, sunadafocus fiye da wannan da zuciyarsu ke son kai su.
Kwankwasa kofar dakinsa ake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi. ‘shower’ din ya kashe ya janyo tawul ya goge kansa da jikinsa a gaggauce. A gurguje ya saka kaya yana jiyo muryar Basma a kofar dakin nasa tana ambaton sunansa a tausashe“Monsieur Aboulkhairâ€. (Kalmar‘Monsieur’ da suke kiran shi da ita is a French-speaking word da ake amfani da ita don nuna girmamawa ga namiji kamar a ce Mr, ko makamancin haka)â€.
Bude kofar ya yi kafin ya ce komai ta mika masa mukullin mota, “Daddy latti, ya ce ka yi ajiye mu, in mun tashi ka dauko mu. Ya fasa neman direban tunda ga kaâ€. Ta fada tana dan ja da baya koda zai kawo mata mari.
Harararta ya yi, sannan ya karbi mukullin. Ya san daddy ya yi haka ne don ya hana shi barcin safensa. Ai shikenan, shi ma dama ya fara tunanin guduwa ya bar musu gidansu zuwa inda zai samu hutun jiki da na zuciya sosai, ya yi huta daga tunanin bakuwar gidan su Aalimah mai kokarin raba shi da numfashinsa da burikansa.
Haka ya sanya su a mota ya kai su makaranta daya bayan daya, Aalimah na jin Khaleesat da Basma suna rada a kunnen junansu,
“What’s wrong with this man ne?†(Me ke damun wannan mutumin ne?) In ji Khaleesat.
“He come with strange behaviours, I’m praying not he becomes ANNOYING like the other person†(ya zo da sababbin dabi’u, ina addu’ar Allah yasa kada ya zamo mai ban haushi kamar daya mutumin)â€. Ta fada cike da damuwa.