AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Abulkhair na da kyakkyawan ji at times, sosai ya ji abin da suka ce. Ya dafe sitiyarinsa ya ci gaba da sarrafa shi cikin gwaninta yana murmushi. Can kasan zuciyarshi kuma ya ji ba dadi for calling Mu’azzam da ANNOYING da suke yi tunda suka fara wayo. Wane bayani zai yi musu su fahimci. Yayansu is not annoying, but rather; he’s fighting with his destiny?(Yayan su ba mai ban haushi bane, a’ah, yana gwagwarmaya ne da kaddarorinsa). Shekarunsu da iliminsu sun yi kadan su san mece ce matsalar Yayan nasu?
Ya fara sauke Yesmin da Khaleesat, sannan ya kawo Basma da Aalimah har gaban block din da za su shiga lacca, ya sauke Basma, ya kara gaba kadan zai sauke Aalimah ba tare da ya ce da su komai ba. Da ta zo fita kasa jurewa ta yi sai da ta saci kallonsa, shi ma satar kallon nata yake yi ta gefen idanunsa, har ta fice rungume da folder dinta a kirjinta. Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa babu waiwaye. Wani numfashi ya ja ya kuma sauke shi sharply, sannan ya ja motar.
Daga university of Boston kai tsaye ma’aikatar su Daddy ya nufa. Akwai abubuwa da yawa da yake so su tattauna, wadanda suke bukatar nutsuwa, kuma wadannan yaran da hayaniyarsu ba za su barsu su tattauna su a gida ba, sannan ba zai iya komawa gida ya yi ta jira har sai Daddyn ya dawo ba, hypertension sai ya kama shi in tunanin Aalimah bai zauta shi ba.
Yana nukatar karin bayani akan ta daga bakin Babansa. Yana kuma son jin me ya hada iyayensa fada duk da ba yau suka soma ba, kuma kullum Mummy ce da laifi sabida anti-social nature dinta. Ya kira ta jiya ya gaya mata ya zo gida zai yi four weeks winter holiday dinsa bai ganta ba, ya kuma tambayi Daddy tana ina? Ya ce masa tana Las Vegas, ba tareda wani karin bayani ba, ya tambaye ta yaushe za ta dawo?
Ce masa ta yi Daddyn ya kore ta, kuma ita ba za ta dawo ba sai Aalimah ta koma Nigeria. Ya tambaye ta abin da ya faru ta ce ya tambayi wanda ya kore ta. Ko kadan bai sa damuwar komai a ransa ba ya ci gaba da sabgoginsa don ya riga ya fahimci abin da ya faru. Mummy and her anti-social nature and the existence of stranger. Maybe this time around Daddyya motsa kwanjinsa, ita kuma tunda tun farko ba haka ya sabar mata ba ta kasa dauka.
Haka ya yi ta kiyasce-kiyasce har ya iso ofishin Daddy.
Sai da sakatariyar Daddy ta yi masa iso, ya kuma bi layin mutum uku da ke kan layin ganin Daddyn, daga bisani ya samu ya shiga. Fridge ya fara budewa ya sha ruwa sosai. Kansa ya dau zafi da yawa, Daddyn na kallonsa yana ci gaba da aiki cikin na’ura mai kwakwalwa. Sannan ya zo ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar makeken tebirin Ishaq Raazee. Dan Nijar din da ya rikide ya zama gawurtaccen Ba’amurke cikin shekaru ashirin da bakwai tsayin zamansa a Amurka. Ishaq Raazee ya raini ‘ya’yansa da rainon Bature ta hanyar maida su manyan abokansa, daga matan har mazan. Ba sa iya boye masa komai na rayuwarsu. Shi ya sansu fiye da sanin da mahaifiyarsu ta yi musu. Shi tashi soyayyar ba ta hana shi ba su tarbiyyah ba, amma ita ba ta san komai ba sai son ‘ya’ya da kokarin ganin sun fi ‘ya’yan kowa gata da jin dadi.
Duk amincin Abulkhair da Babansa yau ya samu kansa da kasa bude mishi cikinsa da amayar masa da damuwarsa. Sabon al’amarin da ya hana shi bacci daren jiya bakidayansa, ya hana shi nutsuwa tun wayewar gari.
Ya zo gaban mahaifinsa don ya gaya masa ko ya samu sassauci, amma ga shi ya kasa. Kallonsa Daddy ya ci gaba da yi yana murmushi, bai ce komai ba shi kadai ya san me ya fahimta tun jiya a tare da Dan nasa. Amma tunda bai furta ba bari ya bi shi da yadda ya zo masa.
“Mummy, na yi magana da ita ta ce kai ne ka kore taâ€.
Aboulkhair ya katse shirun nasu ganin Daddy bai da niyyar tankawa.
“Ni ban kore ta ba, zabi na bataâ€.
Ya fada ba tare da ya dauke kai daga aikin da yake yi cikin na’ura mai kwakwalwa ba. Abulkhair ya yi dan jim! Kafin ya ce,
“Is that related to Aal… I mean Aalimah?â€. Ya fada kansa a kasa, muryarsa na sarkewa da ya zo furta sunan. Tun jiya in zai furta sunan sai harshensa ya sarke ya rasa dalili.
Murmushi Daddy ya yi, ya kashe system din gabadaya ya juya kujerarsa mai tayoyi baya ya fuskance shi da murmushi bisa lebbansa, “Pronounce the name properly (furta sunan yadda yake daidai)â€.
Kunya ta rufe Abulkhair, ya kasa dago ido ya kalli Babansa.
Ji yake yana dagowa Daddy zai karance abin da ke cikin idanunsa tsaf! Tunda ga shi yana kokarin karanto rudanin da ke tattare da muryarsa akan furta sunanta. Shi kuma ba zai so hakan ba, saboda shi kansa bai yarda da kansa ba. Bai yarda da feelings dinsa are morethan emotion ba. Bai yarda zuciyarsa ta kamu da son Aalimah ba, don a ganinsa babu dalilin hakan.
Abin da ya yarda da shi shine there are certain characteristics about her da za su rikita kowanne Da namiji mai cikakken hankali ba shi kadai ba. Her well-structured body, her pointed nose… these thick eye-lashes… this red soft lips are all breadth taking! (Wannan ginannen jikin nata, wannan tsayayyen hancin nata, wadannan jajayen tausasan lebban, wannan cikakken gashin idon da gashin girar, duka masudauke numfashin mutum ne!) Kowanne namiji zai yi mafarkin samunta matsayin matar aurensa!!!
Shirun Abulkhair ya yi yawa, sannan ya ki dago kansa. Daddy ya ba shi mintoci masu kyau don ya gama duk tunanin da zai yi, amma ganin ba shi da niyyar magana kuma ya kasa dubansa, sannan yana cinye masa lokaci, sai ya kira sunansa cikin nutsuar murya. For all he know, Abulkhair dinsa ba miskili ba ne, Allah ya sa kada Aalimah ta sauya shi. In hakan ta faru ya ya zai yi da miskilai biyu? A Aboulkhair yake samun duk abin da yake so daga aboki, he is cheerful as well as passionate. Dayan, da shi da babu, duk daya. Ba rashin lafiya kadai ke aiki a jikinsa ba, har da hali. Tunda yana samun sound-medical treatment.
A wannan din yake jin dadi, yake samun duk abin da yake so daga aboki, ba zai so abin da zai yi spoiling farin cikin Aboulkhair ba, zai yi duk wani kokari ya samar da shi gare shi, ko da hakan na nufin… hadiye sauran tunanin ya yi, don yana ganin nan din ba filin yinsa ba ne ba.
Dago kansa ya yi ya dubi mahaifinsabut he is still lowering his gaze (har yanzu yana yin kasa da ganinsa) duk a kokarinsa na kada mahaifin nasa ya karanto idanunsa.
“Wouldn’t you speak out abin da ya kawo ka? Kana ganin ayyukan da ke gabana, sannan dube ka ko wanka ba ka yi ba, dubi kayan jikinka, dubi gashin kanka. Dubi idanunka, bana jin duk son ka da barci yau ka yi shi yadda ya kamata, ka koma gida za mu yi maganar Mummyn in na dawo, amma nan office neâ€.
Yana so ya gaya masa ba maganar Mummy ce kadai ta kawo shi ba, in da sabo ai sun saba da cases din Mummy da yin yajinta zuwa wajen Danta. Gara ya yi ta zama a gaban Daddyn har ya gama aikin su koma gidan tare, a kan ya koma ya zauna shi kadai a gidan. Bai san me zai faru da shi ba, he’s afraid of going back to Boston University.
Tunda can din ma in ya je bai san me zai aikata ba. Gara nan din sau dubu a kan ya koma gida.
“Zan jira ka Daddy har ka gama, sai mu koma tareâ€.
Ya samu kansa da furta kalaman daki-daki ko Daddyn ya fi fahimtarsa. Amma Daddyn ya nuna shi bai fahimci komai ba.
“Ni kuma bazan iya ci gaba da aiki na kazo ka sani a gaba ba sai ka ce wani uwata. In dai uwarka ce na ce ban kore ta ba zabi na bata. In za ta iya sona da duk wanda ya shafe ni ta zauna, in ba za ta iya ba she could go to someone who has no relatives, but Ishaq Raazee is a family Man. Wannan shi ne kawai sakona gare ta. Abin da ta zaba determines ci gaba da zamanta gaban ‘ya’yanta or notâ€.
Sosai ya fahimci Daddyn, amma har yanzu bai yi magana a kan gabar da yake son ji ba. Kuma da alama ba shi da niyya. Ya ci gaba da zama, ya ci gaba da yin shirun.
Daddy dai kallonsa yake yana cewa a ransa, ‘I wouldn’t, untill you did (ba zan yi ba har sai ka yi)’.
Mikewa ya yi ya dauki mukullin motar da ya aje a kan tebirin Daddy ya nufi kofa. Sai da ya kai bakin kofa ya kama handle din kofar sannan Daddy ya kira sunansa. Bai amsa ba, kuma bai juyo ba, amma ya dakata.
“Drive with care (ka yi tuki da kula)â€. Abin da ya ce da shi kawai kenan. Ya karasa ficewa daga office din.
Maimakon ya dauki hanyar gida, sai ya samu hannunsa da ke kan sitiyari da juya kan motar ya dauki hanyar Boston University. Jin kansa yake kamar wanda ake directing ya kasacontrolling kansa. A hankali yake tukin motar har ya tsaya a inda aka tanada don adana motoci (parking lot) da ke dab da ‘school of medical sciences’ na jami’ar. Kwantar da kansa ya yi a kan sityari yana tunanin me ya kawo shi? Don me zai zo? Sai ya ji kamar ana yi masa amsa-kuwwa cikin kwanyar kansa da cewa, kada ya koma, atleast ya samu ya ganta.
Bai zo don ya hana ta karatu ba sai don kawai ya ganta. Ganin nata shi ne kadai zai samar masa da nutsuwa ya koma cikin hayyacinsa.
Luckly for him, sai ya hango ta ita da wani saurayi bature zaune kasan wata farar lema da fararen kujeru da tebiri a tsakiyarsu. Daga gani karatu suke yi, amma shi sai idanunsa suka zarce suka soma ba shi delusion na abin da ba haka yake ba. Wani irin bacin rai da bai taba ji a rayuwarsa ba.
Yana can zuciyarsa na neman raba shi da numfashinsa saboda ita, tana nan happily accompanied with someone. Wanin ma wani banzan arne mai kama da skeleton. Tana nufin ta ce; duk wannan azabar shi kadai yake kwankwadarta ko me? Wata zuciyar ta ce, ya ja motar ya yi tafiyarsa ya bar garin ya bi Mamansa, ya ga sanyin idaniyarsa (Mu’azzam) ya manta da Aalimah tunda dama bai bari Daddy ya gane ba. Amma bangare mafi rinjaye ya ce ya dan faffallawa yaron mari ko hudu ne ya huce. Da sauri kuma ya tuna me yin hakan ke nufi a kasar bature. A kan Aalimahr ya kamata ya huce haushinsa, tunda ita har dukan nata zai iya yi ya zauna lafiya.
Aalimah da Alex, sun dukufa karatu, yana koya mata calculus. A wurinta sau dubu gara Alex ya koya mata a kan Monsieur din su Basma. She can’t even look into his eyes balle ya koyar da karatu. Akwai wani abu mai kama da sihiri cikin kwayar idon sa dake fizgarta wanda tun shigowarsa gidansu ya hana zuciya da kwakwalwarta zama lafiya. Sannan shi kansa tunda ya zo bai zauna lafiya ba, daga fada sai masifa wanda hakan ya sanya mata matsanancin tsoronsa bayan unexpressable emotions and feelings din da ta kwana da su a kansa.
A karshe kuma ta yi wa kanta fada, ta gaya wa zuciyarta wannan al’amarin da a yanzu ta gama fahimtar ‘soyayyah’ ne irin wanda ke kasancewa tsakanin mace da namijin da suka kai munzalin balaga comes at a very wrong time for her! ( ya zo a lokacin da bai dace ba). Sannan it could destory her parents dream on her… it can also destroy her future ( zai lalata mafarkin iyayenta akanta, sannan ya rusa future dinta) idan ba ta sanya taka-tsan-tsan ba da jajircewa a cikinsa. Ta sha jin yadda maza suke yaudarar ‘yammata su hana su karatu, su yi musu cikin shege, iyayensu kuma su tsine musu su shiga karuwanci ko su haife shege. Zuciyarta ba ta taba kawo mata tunanin aure nan kusa ba.
Da wannan dalilin dama wasu da dama ya sanya tun safe ta ke yaki da zuciyarta a kan Aboulkhair duk da cewa dan uwanta ne, ta san ba zai cutar da ita ba. Amma ba a shaidar maza a wannan fannin, Mahmoud kadai zata iya shaida a cikin maza. Sannan shi da kansa (Aboulkhair ) ya tilastawa zuciyarta ta ji tsoronsa daga yadda yake behaving ga kannensa tun jiya. Sosai ta himmatu wajen yakice shi daga zuciyarta ta ke ta karatu tun safe. Sun yi lacca biyu suna da hutun awa daya kafin su koma wata, shi ne ta roki Alex ya yi highlighting dinta abin da ya shige mata duhu.
6/28/21, 7:32 AM – Buhainat: Aalimah