AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870
“…You goddam talkatives!Kuna duba agogo kuwa? Har downstairs nake jiyo karadinku tun asuba. Kun hana ni barci, kun hana kunnena zaman lafiya. Kun san cewa doguwar tafiya na yi, ina bukatar hutu, kuma ba abin da na tsana irin a hana ni barci da safe… za ku wuce ku karya ku tafi, ko shi ma Daddyn sai kun makarar da shi ya hana ni barci saboda ku?â€
Turanci yake zubawa kamar Charles Dickens ya sauka a Massachusetts. Tuni jikin Aalimah ya hau bari an fara abin da ta ki jini, wato (fada). Sum-sum-sum suka shiga wucewa, Allah ya so duk sun gama shiryawa. Basma har da zumburo baki, Aalimah ce karshen wucewa ta gabansa duk ta gigice. Babban abin da ke maida ita upset shi ne hargagi. Ai kuwa ta ci uban tuntube da kafarsa ta dama, ta tafi za ta ci da baka. Da wani irin zafin nama ya taro ta da dukkan hannayensa. Ido ya bude yana kallon cikin idanunta sosai da dukkan nasa idanun, kamar mai son karanto al’amarin da ke cikinsu. Ba ya so ya yarda da abin da kyawawan idanun ke gaya masa, cewa al’amarin da ke cikinsu, daya yake da wanda ya hana shi runtsawa a tsayin daren bakidayansa.
Yadda nasa idon ya tasa ya yi jajawur yayi luhu – luhu haka idanun nan da ke kallonsa suke. Sai dai kuma a nassi mai kyau na zuciyarsa na gaya masa, kada ya bari ta gane, dukkaninsu are too young da soyayya! Yanzu ne suke kokarin gina future dinsu. Kafin haka, soyayya da duk abin da ya shafe ta ba nasa ba ne. Infact, it’s out of his vocab bank (vocabulary bank).
Zuciya ce dai da ba ka da iko da linzaminta. He has a mission that he want to fulfill(yanada uzrin da yake son gabatarwa) kafin soyayyah. Yanzu ne yake shekara ta uku a jami’a, sannan yana da mashahuriyar damuwa da ke danne duk wani situation da ka iya samun zuciyarsa, na farin ciki ko na bakin ciki.
He will help his sister to concentrate on what she’s here for (zai taimakawa ‘yar uwarsa ta maida hankali kan abindaya kawota) ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi.
A hankali ya lumshe idonsa na tsawon lokaci ba tareda ya san lokacin da yayi hakan ba, sannan ya bude su a kan Aalimah, wadda ta yi suman wucin-gadi a hannunsa. Dago ta ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya sake ta, amma bai iya ci gaba da fadan ba, kamar wanda aka daurewa bakin. Ita ce karshen fita, da sassarfa ya biyo stairs ya sauko daga benen. Bai kalle su a dining ba ya wuce dakinsa.
Cikin quilt dinsa ya shige da sauri ya dukunkune kansa, zuciyarsa na racing wajen bugawa. Numfashin da yake shaka ya ji yana sauyawa da wani irin mayataccen kamshi, kuma kamshin (is feminine) wato na mace ne mai tada hankalin duk wani lafiyayyen Da namiji. Ya fahimci ma kamshin daga jikinsa yake, in fact shi yake kamshin sexy perfume din (‘Nude’ by Rihanna) wanda babu tantama a jikin Aalimah ya kwaso. Abulkhair ya ji komai nasa yana canzawa har numfashinsa. Wani situation ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Ya dauki lokaci cikin yanayin da yake ciki din yana kuma neman hanyar samun sauki. First, he have to get rid out of these clothes.(Gara ya cire kayan nan). Mikewa ya yi zaune ya soma zare su daya bayan daya, sannan ya shige toilet ya sakar wa kanshi shower.
Saukar ruwan a tsakar kansa zuwa jikinsa na tafiya tare da kawo sassauci a bugun zuciyarsa. Duka wannan ya faru cikin mintunan da ba su wuce goma sha biyar ba. Al’amarin ya zamo tamkar wani majigi da ya gifta a idanunsa. Har mamakin kansa yake yi, tunda dai ba yau ya fara ganin mata da yin alaqa da su ba. Matan ma ajin farko da suka amsa sunan mata a duk inda ya yi rayuwarsa cikin kasar America, daga sakandire har jami’a.
Sunyi dukkan rayuwarsu a Washington D.C ainahinaikin da ya yi sanadin kawo mahaifinsu kasar Amurka(consulate officer ne a baya). A Washington din duk suka yi sakandire shi da Yayansa MU’AZZAM, shi Aboulkhair bai ma karasa a can din ba.Abubuwa da yawa suka raba Daddynsu da Niger consulate America.Amma ba don dukkaninsu suna so ba.
Na farko rashin lafiyar Mu’azzam, wanda likitoci suka bada shawarar inda hali a sauya masa inda yake rayuwa zai fi jin dadin canza rayuwarsa, kuma a barshi a inda ya fi so. Sannan kuma Daddyn ya samu hanyoyin budi daban-daban wadanda samunsu ya fi na consulatedin kasarshi nesa ba kusa ba. Sannan lafiyar Mu’az tafi musu komai. Wannan ne mafarin komawarsu Massachusetts ba don suna son garin ba.
Kamar wanda ya saba zama a Abuja ne a ce ya koma Adamawa ko Yobe. Sai dai Alhamdu lillahi lafiyar Mu’az ta inganta.
Ya zabi Jami’ar Louisiana don ya yi nisa da Mu’azzam, saboda wasu dalilai da dama, muhimmi shi ne; ba ya iya jure ganin Mu’azzam cikin halin da ya kan samu kansa.
Bai taba sanya al’amarin mata a gabansa ba balle ya dame shi. Burinsa kadai ya zama ‘psychiatric doctor’ don ya san mene ne matsalar Mu’azzam ciki da bai dinta, ya yi masa maganinta. In haka ne, kenan abin da zuciyarsa ke darsa masa daga jiya zuwa yau akan… Aalimah ba nasa ba ne! He has to be cautious in his relationship with her(dole ya zama mai taka-tsan—tsan a mu’amalar shi da ita). Daga shi har ita, sunadafocus fiye da wannan da zuciyarsu ke son kai su.
Kwankwasa kofar dakinsa ake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi. ‘shower’ din ya kashe ya janyo tawul ya goge kansa da jikinsa a gaggauce. A gurguje ya saka kaya yana jiyo muryar Basma a kofar dakin nasa tana ambaton sunansa a tausashe“Monsieur Aboulkhairâ€. (Kalmar‘Monsieur’ da suke kiran shi da ita is a French-speaking word da ake amfani da ita don nuna girmamawa ga namiji kamar a ce Mr, ko makamancin haka)â€.
Bude kofar ya yi kafin ya ce komai ta mika masa mukullin mota, “Daddy latti, ya ce ka yi ajiye mu, in mun tashi ka dauko mu. Ya fasa neman direban tunda ga kaâ€. Ta fada tana dan ja da baya koda zai kawo mata mari.
Harararta ya yi, sannan ya karbi mukullin. Ya san daddy ya yi haka ne don ya hana shi barcin safensa. Ai shikenan, shi ma dama ya fara tunanin guduwa ya bar musu gidansu zuwa inda zai samu hutun jiki da na zuciya sosai, ya yi huta daga tunanin bakuwar gidan su Aalimah mai kokarin raba shi da numfashinsa da burikansa.
Haka ya sanya su a mota ya kai su makaranta daya bayan daya, Aalimah na jin Khaleesat da Basma suna rada a kunnen junansu,
“What’s wrong with this man ne?†(Me ke damun wannan mutumin ne?) In ji Khaleesat.
“He come with strange behaviours, I’m praying not he becomes ANNOYING like the other person†(ya zo da sababbin dabi’u, ina addu’ar Allah yasa kada ya zamo mai ban haushi kamar daya mutumin)â€. Ta fada cike da damuwa.
Abulkhair na da kyakkyawan ji at times, sosai ya ji abin da suka ce. Ya dafe sitiyarinsa ya ci gaba da sarrafa shi cikin gwaninta yana murmushi. Can kasan zuciyarshi kuma ya ji ba dadi for calling Mu’azzam da ANNOYING da suke yi tunda suka fara wayo. Wane bayani zai yi musu su fahimci. Yayansu is not annoying, but rather; he’s fighting with his destiny?(Yayan su ba mai ban haushi bane, a’ah, yana gwagwarmaya ne da kaddarorinsa). Shekarunsu da iliminsu sun yi kadan su san mece ce matsalar Yayan nasu?
Ya fara sauke Yesmin da Khaleesat, sannan ya kawo Basma da Aalimah har gaban block din da za su shiga lacca, ya sauke Basma, ya kara gaba kadan zai sauke Aalimah ba tare da ya ce da su komai ba. Da ta zo fita kasa jurewa ta yi sai da ta saci kallonsa, shi ma satar kallon nata yake yi ta gefen idanunsa, har ta fice rungume da folder dinta a kirjinta. Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa babu waiwaye. Wani numfashi ya ja ya kuma sauke shi sharply, sannan ya ja motar.
Daga university of Boston kai tsaye ma’aikatar su Daddy ya nufa. Akwai abubuwa da yawa da yake so su tattauna, wadanda suke bukatar nutsuwa, kuma wadannan yaran da hayaniyarsu ba za su barsu su tattauna su a gida ba, sannan ba zai iya komawa gida ya yi ta jira har sai Daddyn ya dawo ba, hypertension sai ya kama shi in tunanin Aalimah bai zauta shi ba.
Yana nukatar karin bayani akan ta daga bakin Babansa. Yana kuma son jin me ya hada iyayensa fada duk da ba yau suka soma ba, kuma kullum Mummy ce da laifi sabida anti-social nature dinta. Ya kira ta jiya ya gaya mata ya zo gida zai yi four weeks winter holiday dinsa bai ganta ba, ya kuma tambayi Daddy tana ina? Ya ce masa tana Las Vegas, ba tareda wani karin bayani ba, ya tambaye ta yaushe za ta dawo?
Ce masa ta yi Daddyn ya kore ta, kuma ita ba za ta dawo ba sai Aalimah ta koma Nigeria. Ya tambaye ta abin da ya faru ta ce ya tambayi wanda ya kore ta. Ko kadan bai sa damuwar komai a ransa ba ya ci gaba da sabgoginsa don ya riga ya fahimci abin da ya faru. Mummy and her anti-social nature and the existence of stranger. Maybe this time around Daddyya motsa kwanjinsa, ita kuma tunda tun farko ba haka ya sabar mata ba ta kasa dauka.
Haka ya yi ta kiyasce-kiyasce har ya iso ofishin Daddy.