AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

45

#

Mummy ta manta ba ita za ta kai Daddy aljannah ba, wannan buzuwar dai da ta raina wadda ba ta je makarantar boko ba, ko Abuja ba ta taba takawa ba, bayan danta ya share sama da shekaru ashirin da bakwai a kasar Amurka. Daidai da rana daya kuma hakan bai taba damunta ba, ba ta taba daga ido ta dubi wani abu da Ishaq ya mallaka ba. Wadanda ba su yi karatun bokon ba, Eedrissa da Oussama sun share mata hawaye, sun gama mata komai. Dole Kasisi ta ce me ake da boko?
Ita dai kam bai amfana ta da komai ba daga nata ‘ya’yan. Daya ya tsallake ‘boarder’ ya je ya kafa iyali a inda ba shi da kowa, saboda ya auri ‘yar Nigeria, sai shekara-shekara ta ke ganinsa. A hakan ma nashi da kyau shi, tunda mace ba ta hana shi kyautata ma iyayensa ba. Sannan yana matukar kokari wajen lika ‘ya’yansa jikin iyayensa da ‘yan uwansu. Dayan kuma tun da ya tsallake kasar da sunan aiki ya fidda kansa daga sahun ‘ya’yan da ta haifa, ya koma dan Zulaiha mijin Zulaiha. Kowa banza ne tunda bai yi rayuwa a America ba, har wadanda suka samar da kwan haihuwarsa a duniya.
Kuka Aboulkhair ya soma yi a hankali yana fidda shessheka, kukan tausayin mahaifinsa da yin Allah wadai da wannan hali da mahaifiyarsa ta rika a matsayin dabi’a. Wutar Allah yake hango masa karara. Yana kyautata zaton ko a waya Daddy ba ya kiran Inna Kasisi ya gaishe ta yadda ya kamata, kullum he is busy bautar iyalinsa da nemo musu kudi. Sau da yawa yana ganin mahaifinsa (Malam Raazee) yakira shi in ya ji shirunsa ya yi yawa, in suka gaisa sai ya ce,
“Na yi mafarkinka ne kai da takwara da Aboulkhairi, to nesa ba ta maganin kusa balle in ganku. Ina fatan dai lafiya ku ke?â€
Wadannan sune kalaman Kakansu duk sanda ya kira wayar Daddy, har ya haddace su. Sai ya kira shi sau goma bai kira shi sau uku ba. In ya ba su wayar kullum nasiha yake musu kan su ji tsoron Allah a duk inda suka samu kansu, su tsaida sallah, su bi iyayensu, su rike ZUMUNCI, in sun yi hakan za su shiga aljannah. Shi ma ya san halin ko’inkulan na Daddy ga iyaye da danginsa ya shafe shi, Mu’az ne kawai mai kula da lamarinsu duk da halin rashin lafiyar da yake ciki he’s doing well with Daddy’s parents and family. Rabin albashin Mu’az ya san inda yake kai su duk da Mu’az din bai so ya sani ba.
Kwantar da kai ya yi a kan cinyar Daddy ya yi ta kuka, gwiwoyinsa suna durkushe a kan carpet kansa a kan kafafun Daddy. Gani yake yanzu in ya zo neman auren Aalimah babu mai ba shi, tunda daga shi har Daddy halinsu daya. Shi ma Daddyn could not help yin kuka, kukan yake amma na hawaye ba mai sauti ba. Ya sanya hannunsa cikin sumar Abulkhair yana shafawa a hankali, yana mai tuno dukkan kura-kuransa yana yarda da su, tare da yin nadamarsu daya bayan daya.
Ko da halin Zulaiha a kan tabarbarewar zumuncinsa da kowa nasa da kokarin fin karfinsa da ta ke yi, most at times shi ma da sakacinsa. Ya yi mata riko irin na mijin bature da macen baturiya; wadanda ba su san kowa ba a rayuwa sai kansu da ‘ya’yansu.
“It’s ok Aboulkhair, stop crying like that, Allah zai gyara mana komai. Sannan yanzu na sa damba a rikon Aalimah sai inda karfina ya kare. Wannan sakona ne ga mahaifiyar ku ku gaya mata. Zan ci gaba da dakon igiyoyin aurenta saboda ta bani the most expensive gift of life. Wannan kuma ba komai ba ne sai ku din nan ku biyar. Duk abin da nake nema a ‘ya’ya na same shi daga gare ku. Kun zame min abokai a lokacin da ta raba ni da su. Kun zame min DANGI a lokacin da ta raba ni da su. You brought all the happiness that children brings to the parents. (Kun bani duk wani farin ciki da ‘ya’ya ke baiwa iyaye).
Amma yanzu ina ji a jikina akwai wani babban gibi da na rasa, duk wannan rayuwar farin cikin da nake tsammanin ina ciki, my life is incomplete. Ina jin wani wawakeken rami a wani gefen na zuciyata Abulkhairi. Bayan kowacce soyayyah dan Adam yana bukatarta fiye da soyayyar kowa. Wannan ba wata soyayya ba ce face ta UWA! I missed MOTHER’S LOVE which is like no other. I’m lucky she is alive (nayi kewar soyayyar Uwa, wadda babu kamarta, nayi sa’a tana raye) yau da ban san inda zan sanya kaina baâ€.
Aboulkhair ya share hawayensa, sannan ya kara dukar da kansa cikin cinyoyin Daddy, as if kansa zai kutsa cikin rigarsa ya shige cikinsa, shi kuma ya sake haifo shi.
“Daddy, ku ba ni auren Aalimah, I mean Aal… Daddy zai dinke komai. Zai faranta ran Inna Kasisi. Above all, I LOVE HER SO MUCH DADDY, I mean it, from the bottom of my heart…!â€.
Dariya Daddy ya kama yi, kafin ya ce,
“I knowâ€.
Da sauri ya dago ido yana yi wa Daddyn kallon mamaki, ya san dazu a office bai furta masa ba, sabida kunya yake ji, kuma ya san Daddy sai ya yi masa dariya, saboda ya sha cewa sai Mu’az ya haifi ‘ya’ya biyu zai yi aure. Sai ya zama cikakken medical doctor. He is now in year 4. Akwai kwararan shekaru biyu a gabansa kafin ya gama MBBS, sannan ya zo ya yi Specializing. Wannan na nufin; sai ya kwashe shekaru kusan hudu zuwa biyar kwarara nan gaba kafin ya mallaki Aalimah???
Ina ruwansa da auren Mu’az?Mutumin da aure baya cikin vocabulary dinsa. He can’t even develop emotion!Duk da lalurar da Allah ya jarrabce shi da ita, ya gwammace ya yi ta daureb kansa da kwayoyi, shi zai zauna ya yi ta jira ya yi aure ya haihu? Tunanin da yake ta yi kenan idonsa a kan mahaifinsa, wanda ke ta binsa da murmushin kauna kamar ya hadiye shi, saboda farin cikin da kalamansa suka jefa shi. Sun wanke duk wasu damuwoyi da suka lullube shi a ranar.
Wannan ne babban abin da zai yi ya gyara komai din, har Khaleesat da Basma ya yi musu nasu tanadin wanda ya san hakan ne kadai zai wanke dattinsa daga idanun ‘yan uwa da iyayensa, wanda ya yi shekaru ashirin da bakwai yana barbada musu a idanunsu.
“Kana mamakin ya aka yi na sani? Na sani tun daga lokacin da ka tasa ta a gaba sai ta cinye sakwara, bayan kai ne ka sa ta kasa ciâ€.
Zuru ya yi yana kallon Daddy, wato iyaye sun fi kowa karantar ‘ya’yansu.
“Amma Aboulkhairi…†Daddy ya ci gaba da magana, sannan ya dakata. Tattaro dukkan attention dinsa ya yi ya mika wa Daddyn, burinsa ya ce gobe zai nema masa auren AALIMAH.
Daddy ya ci gaba da magana, “Cire gaggawa daga cikin lamarin nan, domin ita gaggawa daga shaidan ta ke. A yanzu haka in na nema maka auren Aalimah da kyar za su ba ni. Musamman Yaya Oussama wanda shi ke ba da aure a family dinmu. I have wronged them so much. I’ve to cover my mistakes first, make-up my short comings, eradicate the inconveniences.(Na bata musu da yawa, dole in fara wanke kurakurai na tukunna, in wanke laifi na). Idan na je musu da nadama ta da kuma nema maka auren Aalimah concurrently (a lokaci guda) cewa za su yi abin da ya kawo ni kenan.
Don haka mu bi abin a hankali, mu fara gyara girgidadden zumuncin. Ina ji a jikina komai zai zama daidai ba da jimawa ba. But I want you to exercise patience, concentrate on your studies, make me proud with flying colours kamar dan uwanka. Shi ne babban abin da zai ba ni karfin gwiwar nema maka auren Aalimah. Amma yanzu ba ni da guts na yin hakan tunda baka da halin rike iyaliâ€.
Da sauri Aboulkhair ya dubi Babansa, damuwa kwance baro-baro a kan kyakkyawar fuskarsa, “Daddy, allowee dina ya ishe mu, ko aikin karfi zan hada da shi in ciyar da ita. Daddy don Allah…!â€
6/28/21, 7:32 AM – Buhainat: 07030137870

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button