AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

103
#
Wani matsanancin tausayi irin na iyaye ga ‘ya’yansu ya kama Ishaq Razee. Ya san Aboulkhair fiye da kowa cikin ‘ya’yansa. Ya amince yana nufin kalamansa. Karatun likita kuma ba wasa ba, kada hidimar iyali ta dauke masa hankali, ya hana shi kuma rashin nutsuwa da soy ayyah su hana shi karatun. Gara ya kasa karatun a kan ya zama Mu’azzam, shi ga karatun, ga kwalayen masu karshen kima da daraja, ga kuma career mai matukar daraja, amma ba ya zancen auren. Nan da shekaru goma a gaba ma ba shi da niyya, shi kuma ba zai taba takura masa ya yi ba, uzurinsa ya kai uzuri, kwanciyar hankalinsa a hakan da yake rayuwa ya fi musu komai.
Idanunsa suka cicciko da kwalla, gab yake da ya zubar da hawaye sabida tausayin dan sa Mu’azzam.
Ga wannan mai lafiyar shi ma yana kokarin zame masa wani abin tausayin. Hannu biyu ya sa ya dago shi daga durkuson da ya yi a gabansa kamar mai neman gafara, nan kuwa Aalimah yake nema.
Zaunar da shi ya yi a barin jikinsa ya rike hannayensa, “Aboulkhairi, ni ta bangarena ba ni da matsala da zarar na dinke barakar da ke tsakanina da ‘yan uwana zan iya yi maka aure daga yanzu zuwa kowanne lokaci, in ciyar da kai, in ciyar da matarka, in suturta ku, in ba ku muhalli ku haifa min jikoki su ma in ciyar da su. In dauki nauyin kula da lafiyarku da karatunku har zuwa sanda za ku iya rike kanku. Matsalar daga iyayen Aalimah ne.
Sun dauki duk wani buri da suke da shi a kan babban dan su Aboubacar sun dora a kanta, they wanted her to be very well educated, kamar kakanta na wajen uwa Prof. Kashim.Mutuwarsa ta taba mahaifiyarta tun daga zuciya har kwakwalwa, she dropped her career and became a mental patient too, ta tsaya da burin danta Aboubacar ya zame mata magaji ga mahaifinta. Su biyu rak! Ya haifa,dan uwan nata Suraj yayi mata nisa.
Aboubacar ya ki yarda ya karanta pharmaceutical science, ainahin kwas din marigayi Prof. Kashim, sai mijinta ya shwarce ta da ta ba wa Aalimah damar da ta ke son bai wa Aboubacar. Yana so kada ta zama discouraged don ta haifi ‘ya’ya mata da yawa fiye da maza, yana so ta yarda mata ma ‘ya’ya ne kuma ta yi farin ciki da haihuwarsu.
Alhamdu lillah Aalimah ta fara kokari sosai a karatunta. Ka ga ya kamata yanzu in ce su cire ta daga makaranta su aura wa Dana? Shi kadai ya san yadda ya yi fafutukar da ya yi ya samo mata scholarship din nan babu ko sisina, ko kudin jirgi uwarta ta biya mata ba su karbi nawa ba. Hakan ya kamata Aboulkhair?â€
Da matukar sanyin jikin Aboulkhair ya girgiza kai, da zai iya, da zai so ya ce da Daddy “aurena ba zai hana burin iyayenta cika a kanta ba, zai zamo ne a step toward her achievements… zan zamo tsanin cikar burinta… zan taimaka mata ta duk hanyar da zan iya……â€. Maganar zuci yake bai san a fili yake yi ba. Saboda ya zama very infatuatedakanAalimah, ya kasa controlling emotions dinsa da damuwar zuciyarsa.
“Be strong my son, ina tabbatar maka za ka iya JIRA, musamman idan ba ka ganinta. I’m not against early marriage(bana kin auren wuri)sabida ni ma sanda mahaifina ya yi min na ji dadi, na tabbata ni dan gata ne, kuma iyaye irinshi kadan ne. Da kuma za’a samu yawaitar irinsa a duniya, da zina ta ragu a cikin al’ummah.
Mahaifiyarku ajinta biyar a sakandire na aure ta, yau ga ta da degree har da masters . So ni ta fannina na yarda aure da hidimar iyali ba sa hana goal attainment. Daga iyayenta ne, and their convenience. Ni ko gobe Mansour ya ba ka Aalimah zan biya sadaki. Amma na rokeka ka daga min kafa in gyara nawa ruguzajjen ginin tukunna. Kada ka dagula min al’amura. In kuma za ka yi min abin da na fi so shi neWAIT FOR HER!(Ka jira ta). Jikina yana ba ni matarka ce, kuma uwar ‘ya’yankaâ€.
Wani numfashi Aboulkhair ya zuka ya kuma dawo da shi da sauri. Dariya ta kama Daddy, amma ya gintse. Yana mamakin wane irin so ne haka ya kama Aboulkhairinsa cikin kwana daya rak? Tarihi ne ke maimaita kansa. Ya sani duk ‘ya’yansa maza shi suke gadowa a halayya dabi’a. Shi ma haka ce ta faru da shi a kan mahaifiyarsu the very first time he saw her, bai kuma nutsu ba sai da ya aure ta. Baya fatan hakan ta faru da Aboulkhair, tunda ba shi da ikon ba shi Aalimah a yanzu, rashin nutsuwarsa kuma daidai yake da tabarbarewar karatunsa, wanda ba ya fata…
“Would you keep encouraging me to wait? (zaka cigaba da karfafa min gwiwa wajen jiran?â€) Ya tambayi baban kamar zai yi kuka. Abin nasa har da shagwaba-shagwaba.
Gyada kai Daddy ya yi yana masa murmushin bada karfin gwiwa da son karfafa gwiwa.
“Yes, I will keep encouragingâ€.
“Would it take long?â€
Aboulkhair ya kara tambaya.
“No, five years is like a blink of an eye (kamar kiftawar ido shekaru hudun suke). Especially when a person makes himself busy with studies. Make frequent phone calls when he is far, but he should make sure the phone calls doesn’t distract or affect his study times, once in a day or twice in a week. And it shouldn’t contain deep emotional talks that would inturn arouse his fantasies. It ought to stick on “how are you†and “how is studies?â€
Dariya Aboulkhair ya shiga kyalkyalawa kamar babu gobe. Shi kansa Daddyn dariya yake yi, zukatansu suka yi dadi tamkar babu sauran damuwa a cikinsu.
Yana komawa dakinsa ya rufe kofa ya dauki wayarsa da niyyar ya kira Yayansa, amma sai ya duba lokaci, lokacin shan magungunan Mu’az ne yanzu, yana sha kuma zai yi bacci. Kamar ya kyale shi, amma sai ya ga ba zai iya ba, ya kamata yasan komai da ke faruwa tsakanin Mummy da Daddy daga bangaren kowannensu don yayi sulhu. Ya manta da situation din Mu’az da tunanin zai shiga lokacin barcin sa ya danna masa kira. Sai da ta kusa katsewa kafin ya daga.
“I’ve been expecting your call since yesterday, where have you been?†(nayi ta tsammanin kiranka tun jiya, ina ka shiga?â€
A cikin muryar akwai maturity, akwai nutsuwa da haiba, akwai gentleness, akwai kwarjini da kamala, akwai wani abu wai shi ‘class’ da sanin ciwon kai. Sannan it is so caring as well as affectionate ga wanda ake magana da shi. Shi ma wanda ya yi kiran respect ne da affection zallah a tashi muryar. Ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya daidaita tone din muryarsa yadda ba zai zama boring ga mai saurare ba, sannan ya zauna a gefen gadonsa ya yi wa wayar rikon aminci, yadda ba za ta zame ba.
“Is Mummy beside you? Mummy na kusa da kai?â€
“No, ta shiga barci tun dazu. Ni ma I’m about to take medicines(gab nake da shan maganina) in kwanta, wani aiki ne ya dan tsare ni da ba za ka same ni ido biyu baâ€.
“Kayi hakuri da rashin kiranka tunda na iso, bana cikin nutsuwa, I metatedious threshold inthe house…†Ya warware masa komai; tun daga farko har karshe da nasa observation din na halin Momy tun suna kanana. Da irin kukan da suka yi dazu shi da mahaifinsu. Amma bai gaya masa he is in love da Aalimah ba, komai da lokacinsa.
Shiru Mu’azzam din ya yi, kamar ruwa ya cinye shi. He didn’t cry. Ba abu kankani ke sa Mu’azzam kuka ba, sannan ba ya jan magana da nisa, his words are specified, he is very selective and picky before he utter a word. Amma duk sanda ya furta magana zata kasance ta kunshi ma’anoni masu yawa a dunkule. Aboulkhair ya yi zaton sam ba zai yi magana ba har sai shi din ya gaji ya ajiye wayar, bai damu ba, sabida ya san dan uwansa fiyeda kowa a duniya. Ya san bynowzuwa yanzu ya gama tunanin yadda zai shawo kan matsalar iyayen nasu gaba daya cikin dan wannan lokacin da ya dauka shiru.
Daga baya Mu’azzam din ya kira shi.
“This is totally opposite with what she told me…â€. (Abinda ka fadamin kwatakwata bai yi dai-dai da wanda ta fada min ba). Mu’azzam ya fada cike da tausayin mahaifinsa.
Suka yi maganganu na maza masu hankali na dan gajeran lokaci, kafin Mu’azzam ya ce,
“Is the girl still in the house? (Har yanzu yarinyar na gidan?)â€
“Yes, she is, the nicest sister I ever met (eh tana nan, ‘yar uwa mafi dadin mu’amala dana taba haduwa da ita a rayuwaâ€.