AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

“Greet her for meâ€.
(Ka gaishe min da ita)

“Za ta ji insha Allahâ€.
“As for Mummy (Game da Mummy, ofishin su sun kirata jiya, kyale ta kada ka kirata don ka rarrasheta, da kanta zaka ga ta dawo. Ka yi kokari ka gina kyakkyawar mu’amala a tsakaninta da yarinyar kafin ka koma makaranta. Ka nunawa yarinyar yadda zata yi hakuri da ita.Sukuma ka rabu da su za su shirya kansu a junansuâ€. (Yana nufin ita da Daddy)
Da haka suka yi sallama.


ABOULKHAIR DA WAYAR AALIMAH!
Sai da ya gama komai da ya saba yi kafin ya kwanta, kama daga wanka, brush, shan black tea, ya daura pajamas sannan ya shige cikin quiltdinsa da wayar Aalimah a hannunsa. ‘Yar kankanuwar waya Daddy ya saya mata kirar Iphone. Contact list shi ne abin da ya fara shiga, contacts din ba su da yawa, ba su fi ashirin ba. Ya ci gaba da scrolling contactsdin, akwai mamere, watau Mamanta kenan, mon pere (Babanta), sai Bhaiyya, wato Yayanta Aboubacar da harshen India. Sai ta Daddy, ta Basma, ta Khaleesat, Malam Raazii, Kawu Oussama, Kawu Edrissa, Balkissa Eedrissa, Grandma Kasisi, Grandma Bintou. Sai lambobin maza guda biyar wadanda ya ga ba zai jurewa zamansu ba.
Alex ya fara gogewa, ya goge Harrison, ya goge Mr. Edward Proffessor. Bai san cewa course tutor dinsu ne ba ma. Harrison kuma course mate dinta ne. Lambar da ta rage guda daya ce ta tsaya masa a makoshi, kuma ya kasa goge ta. Akwai bukatar ya dauke ta a tasa wayar, sannan ya goge. ‘MAHMOUD’. Ba don komai ba sai don ya kawo karshen alakarsu ko ma wane ne. Har wani heart ta makala masa bayan ta rubuta sunansa. Bai yi mamaki ba, don yarinya kamar Aalimah ba yadda za a yi a ce ba ta da mashinshini har zuwa wannan lokacin. But he’s jealous, in ya ce jealous to guda daya kenan. He is very-very jealous! Don ya lura ko ma wane ne wannan Mahmoud din ba yau ya fara son Aalimah ba, kuma bai fara don watarana ya daina ba.
Zuciyarsa ba ta gama tsinkewa ba sai da ya shiga message inbox. Sakonnin Mahmoud din ne rututu masu barazanar tarwatsa kwanyarsa. Bai iya ci gaba da karantawa ba ya hada su duka ya goge su daga doron kasa. Abu daya ya dan kwantar da hankalinsa, ba reply mai zafi daga Aalimah, ga dukkan alamu ba ta damu da yin rubutu cikin waya ba, babu wani social media da ta bude, she only text Mahmoud twice, saying that she saw his messages, she’s doing morethan fine. She will call him when she is opportune, he know how tedious her studies is. (Sau biyu ta yi ma Mahmoud sako, inda tace ta ga sakonsa, tana nan lafiya, zata kira shi in ta samu dama, ya san yadda karatunta yake da tsauri). Wannan ne kadai ya dan sanyaya ransa. Amma ya rantse gobe sai ya raba Aalimah da Mahmoud yadda zuciyarsa za ta buga ya mutu ya huta.
Ya dauki lambar Daddynta, mamanta da ta Yaya Aboubacar. Lambobinsa ya zuba cikin wayar tata, ya yi saving da Mon Amour (MY LOVE da harshen faransa), sannan ya yi mata downloading din whatsapp application. Da niyyar cewa shi kadai zai dinga mata magana ta cikinsa, not even Daddy karshenta kenan. Sannan ya koma cikin gallery na wayar, duka yawanci selfie ne ita da Basma a makaranta, wani a mota, he can guess that she adores Basma a lot (tasu ta fi zuwa daya).
Murmushi ya yi da ya tuna Khaleesat ko Daddy bai cika shiri da ita ba sabida I don’t care attitude dinta. Tafi shiri da Mummy. Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskar da ta zame masa madubin zuciya daga jiya zuwa yau. Ta rusa duk wasu plans da ya yi wa rayuwarsa, ta kuma zamo babban kalubalensa na rayuwa a yanzu. Mallakarta is the greatest challenge of his life now. Ban da barci ya fi kowa iya sata da Aboulkhair yau ma bai runtsa ba kamar yadda ya ga dare da rana jiya.
Amma yau ya yi barci yadda ya kamata da wata irin nutsuwa da ya dade bai samu ba a rayuwarsa.
Washegari, Aboulkhair ya yi wanka ya shirya cikin shirt da wando ‘yan gidan Nordstrom, rigar orange ce da ratsin baki, wandon fari tas. Sumar nan ta sha taza ta kwanta luf a kansa. Samun kansa ya yi da zakulo turaren da ya fi kowanne kamshi mai sanyi cikin tarin turarukansa masu ban sha’awa, sannan ya fesa. Ya fi son shi fiye da dukkan turarukansa, saboda Mu’az ke ba shi (SAUVAGE Dior). Duk wani abu kuma da ya fito hannun Mu’azzam is preciousa gun Aboulkhair. Ya san dai ba yau ya fara fesa turare ba, amma shi kansa ya san wanda ya fesa yau bai fesa shi don radin kansa ba.Is meant for AALIMAH ta ji yana kamshi.
Wani murmushi yake saki shi kadai yana yi wa kansa dariya. Sanda ya fito su ma duk sun yi shirin makaranta suna dining suna karyawa har Daddy, sai Aalimah da ke ta shige da fice daga kitchen zuwa dinning area din tana miqo musu abubuwan da suke bukata.
Sosai ya ji haushi, amma bai ce komai ba har ya zauna. Shi ma ita ta yi serving dinshi ba tare da ta yarda sun hada ido ba.
Ya dubi Basma, “Ina mai aikin Mummy?â€
“Aal, ta hana ta zuwa by 6am ta ce ita za ta dinga yin breakfast, Easther ta yi lunch and dinnerâ€.
Ya dubi Daddy ko zai ce wani abu? Ya ga bai ce komai ba, sai shi ma ya yi shiru. After all ita mace ce kuma rainon Nigeria, she might be willing to do so. Shi kansa ya fi son cin nata abincin a kan na Easther, tunda ya ci pounded yam sau daya. Amma anya hakan ba zai zamo takura a gare ta ba?
Muryar Daddy ya ji yana yi wa su Basma fada kan su dinga shiga kitchen din da safe tare da ita za su fi sauri, kuma su ma su koya. Ajiyar zuciya ya yi cikin jin dadi.
Fara cin abincin ya yi, su kuma suka koma sama don dauko jakunkunansu da mayafansu. Khaleesat da Yesmin da ma uniform ne a jikinsu. Daddy ya riga su ficewa, su ma mota suka wuce don su jira shi, bai dade ba ya gama ya fito. Kofar direba ya shiga ya rufe, sannan ya mika hannu ya bude kujerar gefensa. Basma za ta shiga, ya ce, “No, koma baya, daga yau seat dinta neâ€.
Ta ce, “Who?â€
Harara ya galla mata ba shiri ta shige bayan don ta lura daga zuwansa zuwa yau he’s a changed person. Aalimah ba da son ranta ba ta zauna a gaban, ba ta so ko kadan su Basma su fahimci tsakaninta da Yayansu akwai wani abu, kunya ta ke ji sosai balle ta san Basma da digimi da maida allura garma. Sai da suka hau titi sosai ya dan juyo ya dube ta. Ta yi masa kyau sosai cikin doguwar riga ruwan kasa da veil dinta sakar kasar Kuwait. Takardun hannunta ta ke dubawa tana da gwaji yau (test). A duk lokacin da ya dube ta his feelings for her heightened bai san dalili ba. Cikin tattausar murya ya ce, “Babu gaisuwa Aalimah?â€
Ko su Basma da ke baya ba su ji abin da ya ce ba, sabida raunin muryarsa. Ba tare da ta dago ba ta ce,
“Bonjour?â€
Ya amsa, sannan ya ce, “What time is your interval (lokaci na hutu tsakanin wata lakcar da wata). Ta gaya masa.
Daidai lokacin da suka shigo Boston campus ya ajiye su ya juya. Ko da ya koma gida kasa hassala komai ya yi, sai tunanin Aalimah. Tashi zaune ya yi daga kan resting chair ta falon da yake kwance a kai, ya hau saman gidansu. Akwai wani balcony da galiban daddy ke zama da yamma ya yi karatun jarida a weekends can ya je ya zauna. Wayarsa ya lalubo ya nemo lambobin da ya yi saving jiya daga wayar Aalimah ya kira ‘UNCLE MONSOUR’. Gara ya fara yi wa kansa yakin neman auren Aalimah kafin Daddy ya gama yangarsa ya fara nasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button