AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Gidan Ishaq Raazee karamin ‘American lodge’ ne, ginin sama da kasa. A saman, dakin maigidan da na matar gidan har ma da na yaransu mata guda uku yake. A kasa kicin ne da babban English parlour wanda a cikinsa dakin manyan ‘ya’yansu maza yake. Mai aikin gidan, wato Easther ba ta kwana, zuwa ta ke da safe ta tafi da yamma in ta kare girkin dare. Don haka Easther ta rasa dakin da za ta kai bakuwa Aalimah, gidan ba a gina shi da niyyar karbar baki ba, tana ganin bai kamata ta kai ta sama ba, tunda maigidan a sama yake, bai kuma kamata ta ajiye ta a kasa ba babu kowa sai ita kadai. A falon kasan, akwai wani daki bayan na Yayansu dake makaranta, amma a rufe yake ba ta taba ganin an bude shi ba, balle tayi tunanin ajiye ta anan, don haka sai ta kai ta dakin su Yasmin kawai, wanda ke daura da na mahaifiyarsu. Cike da zullumin ko ta yi ba daidai ba. Ta koma kicin ta hado mata abinci a kan ‘tray’ ta ajiye mata a gefen gado. Ta yi mata sallama ta koma bakin aikinta.
Kafin Aalimah ta yi komai, wanka ta shiga don ji ta ke jikinta har wani danko-danko yake mata. Ga ta da son wanka dama kamar agwagwa komai sanyi, balle kuma a lokacin zafi. Hatta gashin kanta ji ta yi yana mata kaikayi – kaikayi, duk da yau kwananta uku da wanke shi. Ta sunce ta dauko kayan wankanta daga jakarta ta shiga toilet din da ke cikin dakin.
Ta tsaya na dan lokaci tana nazarin bandakin. Ba ta taba zuwa kasar waje ba, amma kuma hakan bai maida ita bakauyiya ba. Nazarin bandakin ta shiga yi wanda ke dauke da bathtube na jacuzzi, kalarsa light blue komai da ke cikin bandakin kalarsa kenan. Ta mika hannu ta zare ribbon din da ta daure tulin gashinta ya wargaje a kafadunta, baki sidik mai tsayi da salki, na abzinawan usli.
A cikin toilet din har da hand dryer makale a gefe. Ba karamin jin dadin hakan ta yi ba. Ga shampoos nan kala-kala masu tsada a jere, wannan na da nasaba da kasancewar su ma yaran gidan mata guda uku, gashin gare su kamar ita. A lokacin ta manta da komai ta tara ruwan dumi cikin jacuzzi ta shiga ta soma abin da ta fi so a rayuwarta, wato ‘wanka’. Ta jima tana kalkale sassalkar fatar jikinta kafin ta soma wanke sumar kanta tana cudawa da kumfar(head& shoulder). Ta gama ta busar da shi da hand dryer, ta dauro alwala ta fito. Doguwar rigar atamfa (fitted-gown) ta sanya ta dauko hijabin sallarta ta tada sallah.
Sai da ta rama sallolin da ake binta sannan ta samu nutsuwa tazauna ta soma cin abincin.
Faten dankalin Turawa ne da aka yi da Mushroom da zallar tsokar naman kaza. A gefe kuma gasasshiyar hanta ce a cikin bowl na tangaran ta sanya fork tana cin hantar a hankali bayan ta gama da faten dankalin. Da ta gama, ta kora da lemun kwali na Apple mai sanyi, sannan ta kishingida a sofa tana hutawa.
Mamanta, Daddynsu, kannenta da masoyinta Mahmud suka fado mata a rai. Ta san suna can suna sauraron kiran wayarta. Da sauri ta sauko daga gadon ta lalubo wayar a jakarta. Tana kunnawa ta tuno ba ta da internet connection, kuma ba ta da credit na kasar. A rashin saninta da cewa gidan (WiFi) suke amfani dashi. Ta maida wayar gefe ta ajiye ta dauki kayan da ta ci abinci da su ta sauko kasa.
Kofofin falon ta shiga nazari tana son gano wacce ce ta kicin?Sai ta jiyo karar kwanuka kamar ana wanke-wanke da karar zubar ruwa daga famfo. Nan ta gane kofar da ke can karshe ita ce kicin. Ta karasa ta tadda Easther suka yi wa juna murmushi na rashin sabo, Easther ta karbi ‘tray’ din ta hada da wadanda take wankewa, sai ta kasa komawa daki ta jingina da cabinet din kicin suka soma hira.
Aalimah ta ce tana so ta taimaka mata su ci gaba da aikin tare. Easther ta ce ta rufa mata asiri ta koma daki kada ta yi laifi wajen uwar dakinta, tunda ba ta ce ta sa ta aiki ba. Amma ta kasa komawar, sai ta samu daya daga kujerun karamin dining da ke cikin kicin din ta zauna, Easther na aikin suna hira jefi-jefi da turancinta mai rauni.
Easther ‘yar Africa ce, wato bakar fata wadda aka haifa ta kuma girma a kasar Amurka, wadanda ake kira black- American. Ta ke gaya wa Aalimah su ‘yan asalin kasar Ghana ne daga Kumasi, iyayenta da kakanninta duk a nan aka haife su sun rayu tsayin rayuwarsu suna yi wa Turawa bauta. Ta tambayi Aalimah amma ita ‘yar uwar Daddy ce ko? Don ta ga tana kama da shi da ‘ya’yansa. Aalimah ta gaya mata cewa; “Wan babanta ne Ishaq Razeeâ€.
Daidai lokacin da suka ji shigowar motoci har guda biyu, daya ta maigidan, daya ta Mummy. Yaransu ne suka fara shigowa daya bayan daya suna ta hayaniya, Aalimah ta dawo kofar kicin tana kallonsu. Basma ce a gaba, sai Khalisat sai auta Yasmin. Rabonta da su shekara shidda kenan zuwansu Nigeria na karshe. Lokacin Aunty Zulaiha na da cikin Yasmin. Duk sun yi wani irin girma mai ban mamaki da ban sha’awa, irin girman ‘ya’yan Turawa. Ba mai cewa Basma sa’arta ce domin ta yi biyunta a girman jiki. Mai bi mata Khalisat, Aalimah ta girme ta da shekaru biyu, shekarunta goma sha hudu. Ita da Basma za su yi sha shidda da ‘yan watanni. Bayan haihuwar Khalisat Mummy Zulaiha ta dade ba ta haihu ba,sai da Khalisat ta yi shekaru takwas,sannan ta haifi autarta Yasmin.
Haihuwarta ta farko da ta biyu ‘ya’ya maza ne. Su ma tsakaninsu ratar shekaru biyar ne, haihuwa irin ta turawa Mummy Zulaiha ke yi, haihuwar Khaleesat data yi shekaru biyu bayan ta Basma (unwanted pregnancy) ne wanda ba yadda zata yi da shi.Data haife tan kuma, sai tafi sonta fiye da dukkan ‘ya’yanta mata. Itama Khalisan bata aje Mummy kusa da kowa na gidan ba a kauna da shakuwa. Idan ka dubi Mummy Zulaiha ba za ka ce ta haifi wadannan zaratan ‘ya’yan ba saboda hutu da kula da jiki. Shekarunta sun kusa hamsin, amma tsammani za ka yi talatin da biyar gare ta.
Daga ita har maigidanta Ishaq sun yi auren wuri, aure na soyayya, irin makauniyar soyayyar da iyayenta suka gwammace su cire ta daga makaranta tun tana aji biyar na sakandire su aura wa Ishaq. A lokacin yana shekara ta uku a jami’ar Ahmadu Bello. Ko abin da zai rike ta ba shi da shi, ga hidimar karatu, don haka ya dauke ta ya tafi da ita kasarsu Niger Republic ya ajiye ta a family house dinsu, inda aka ba su daki a babban gidan na zuri’ar Mal. Ibrahim Raazi. Ya maida ita makarantar sakandire a nan garinsu, Yamai, duk da ba ta jin faransanci har a hankali ta koya, in ya samu hutun semester ne yake zuwa gida shi din ma ba kowanne ba.
Tun yana yaro yake son kasar Nigeria da son zama a cikinta, ko da ya gama sakandire ya ce da mahaifinsu Malam Ibrahim Razee shi a Nigeria zai yi jami’a yana sha’awar harshen turanci, bai hana shi ba, amma ya ce ya tafi tare da kaninsa ‘Mansour’ wanda ya samu double promotion sabida hazakarsa suka gama sakandire a shekara guda, shi ma ya yi karatun a can zai fi jinsa kamar a gida in suna tare.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:30 AM – Buhainat: 🌹 *Aalimah🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
FREE PAGES 2
Ba su sha wahalar samun gurbi a jami’ar Ahmadu Bello ba, kasancewar a wancan lokacin neman masu yin karatun gwamnati ke yi ido rufe, ga kuma takardunsu sun yi kyau, wadanda aka yi wa fassarar takardun Nigeria, suka kuma shiga wani tsari na koyon harshen turanci da jami’ar ke yi a wancan lokacin, kasancewar sun yi karatunsu ne da harshen faransa. Komai tare suke yinsa a A.B.U kasantuwar baki da basu da kowa sai junansu, sannan kuma uwarsu daya ubansu daya.
A gida ba sa jituwa kasancewarsu sakonnin juna, kowanne kamar yana ganin hanjin dan uwansa. Amma da suka zo Nigeria ba su da kowa, dole suka rungume junansu. Wannan kuma wata hikima ce irin ta iyaye, mahaifinsu ya yi musu ba tare da saninsu ba.
Daga Mansour har Ishaq dukkansu gifted ne a karatu. Ba fanni daya suke karanta ba, Ishaq na nazarin International Relation, yayin da Mansour ke karantar Mass Communication. A hostel suke rayuwa, duk abin da suke bukata mahaifinsu na aiko musu ta banki.
Mahaifinsu babban malami ne ta daya bangaren kuma babban dan kasuwa a babban birni Yamai, yana sana’ar kasuwancin kayan abinci yana kuma taba kasuwancin rakuma da kiwonsu, wanda ya gada iyaye da kakanni. Matansa na aure guda biyu, wadanda ke haifa masa ‘ya’ya kusan a tare, don in wannan ta haihu yau, bayan sati daya ko wata daya za ka ji dayar ma ta haihu.