AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Dr. Monsour Raazee, na zaune cikin ofishinsa da ke cikin sabuwar jami’ar Bayero yana marking takardun dalibai ya ga shigowar kiran mai dauke da lambobin kasar Amurka cikin wayarsa. Amma kuma ba Aalimah ba ce ba, kuma ba yayansa Ishaq ba, sannan it is not his darling son MU’AZZAM ISHAQ RAAZII, wanda sati ba ya shigowa ya shude ba tare da ya kira shi ya gaishe shi ba, musamman a ranakun karshen mako. To ko Aalimah ce ta canza layi? Haka ya mika hannu ya sanya ta a handsfree yana ci gaba da marking din da yake yi saboda tsabar kwarewa da aikinsa.
“Assalamu alaikum Uncleâ€. Ya jiyo muryar saurayin mai wani irin accent shi ba bature ba, shi ba balarabe ba, ba ma kuma za ka sanya accent dinsa a jerin na Hausawa ba duk da uwarsa cikakkiyar bakanuwa ce.
“Ameenwa’alaikumus-salam warahmatullah, da wa nake magana?â€
Kunya da jin nauyi da nadama baki daya sukayi rubdugu a kan Aboulkhair, a girmansa ba zai iya tuna rana ta karshe da ya kira wani cikin dangin mahaifinsa ya gaishe shi ba, tun suna yara Mummy ke gaya musu they don’t love them, they are always saying ‘baku da tarbiyyah’ don kawai ba sa sona!’
Ya runtse idonsa yana jin wata irin nadama tana ratsa shi. A shekarun girmansa kuma he is very busy with schools musamman da ya fara karatun jami’a ya bar iyayensa ma bakidaya ya tare a jami’a, sannan ga yanayin karatunsa, he hardly find time for himself ma balle ya tuna mutanen da suka shafe shi. Ko askin kansa ba ya samun damar yi sai gashin na neman rufe masa ido. Ko kadan bai dauko Mummy ba, sai idanunta da duhun fatarta, he is a perfect photocopy of his father. Mu’azzam ne mai kama da ita, sai dai shi kuma ya yi hasken fatar Daddy, bai yo yawan sumar kai ba, sannan he shaves regularly (yana yawan yin aski).
Ya yi nisa a tunani, wanda ya mantar da shi cewa ya kira waya har kawun ya amsa. Muryar Kawun nasa ya ji yana tambaya cikin sanyin murya,
“Ko ABOULKHAIR ne?â€
Ya cije labbansa cikin mamaki mai cakude da jin kunya da jin dadi duk a lokaci daya, ya ce,
“Ni ne Uncleâ€.
“I guessedâ€. Inji Dr. Mansour, “Ya ya ku ke, ya Babanka da ‘yan uwanka da mahaifiyarku?â€
“Suna lafiya Uncle, I’m sorry for not calling you. Nayi nadama uncle.Uncle na ji kunyarka, amma ka yarda da niban taba mantawa da ku ba. Bana tare da iyaye na, ina karatu a Louisiana shekaru hudu kenan. Yanzu ma hutu na zo, kuma nanda sati hudu zan koma.I need your blessing!â€.
Hausa yake iyakar iyawarsa tana subuce masa yana cakudo ta da turanci.
Dr. Monsour ya yi murmushi kamar yaron na kallonsa. Hamdala yake yi cikin zuciyarsa, addu’ar mahaifinsu da kalaman mahaifiyarsu ba su fadi a banza ba. Inna Kasisi ta sha cewa kowa ya daina damuwa da rayuwar Ishaq da ‘ya’yansa, idan ‘ya’yan na halal ne da kansu za su neme su. Malam kuwa ya sha cewa, “Da izinin Allah kan ‘ya’yansa da jikokinsa ba zai rabu ba ko bayan ransa. Ishaq da ‘ya’yansa da suka zama saniyar ware, yana rokon Allah ya karkato da hankalinsu gida, su rungumi ‘yan uwansu da iyayensu.
Kiran sunan yaron ya yi wanda ya fada cikin damuwa da shirun Kawun nasa.
Ya ce, “Aboulkhair, Aboulkhair! Kana jina?â€
“Eh Uncle, I’m still onlineâ€.
Ya ce, “Ka daina damuwa, I’m your father, an halicci iyaye da dabi’ar zama masu karbar uzurin ‘ya’yansu. Na ji uzurinka, kuma in gaya maka ban taba damuwa da hakan ba, tunda na san lafiya ku ke. Amma ka dinga koyi da dan uwanka wajen kula da zumunci. Ya fi ka yawan hidimomi tunda shi babban ma’aikaci ne, still ya rike danginsa kam-kam. He is not with us, but we are feeling him beside us. (Baya tareda mu, amma jinsa muke kamar a gefen mu). Sallar bara da ta wuce tare da shi muka yi sallar idi a Nijar, ya je Zinder (garin su Inna Kasisi), ya je Tessaoua (garin su Malam Ibrahim Razee), har Arlit (garin su Inna Bintou) ba inda bai je ya ga dangi su ma sun ganshi ba. Ga albarkar kakanninsa da iyayensa yana sha ta ko’ina, ba ka yi wa kanka kwadayin hakan?â€
Ya ci gaba da kawo masa ayoyi da hadisai da Allah ya yi umarni da zumunci, da kyautata shi, musamman ga maza kuma manyan jikoki a family. A karshe ya saka masa albarka, shi kuma ya yi alkawarin zai ci gaba da kiran kowa. Ya ce yana son kiran Maman Aalimah da yaya Aboubacar, amma bai sani ba ko sun manta shi?
Dr. Mansur ya ce, “You are welcome to call everybody within your family, babu wanda ya manta da ku ko don Mu’azzam. Allah ya yi muku albarka bakidayaâ€.
Bayan sun gama waya da Daddyn Aalimah ya dade a wurin, ya jingina da karfen balcony din zuciyarsa ta yi masa dadi. Sai kuma ya fada wani tunanin. Wato duk yadda yake da tabbacin ya fi kowa sanin Yayansa Mu’az har gobe bai zo rabi a sanin nasa ba! Abubuwan mamakinsa yawa gare su, kuma ba wanda ya isa ya san cikinsa hatta da iyayensu idan aka zo maganar abin alkhairin da yake yi a rayuwa. Sai dai ya tsinta nan da can kuma bai isa ya yi masa zancen ba, yanzu zai ce bai san maganar ba, ko ya ce ya kyale shi da unnecessary magana, ba ya son yin magana mai tsawo.
Ajiye tunanin Mu’azzam ya yi a gefe, don abubuwan mamakinsa ba masu karewa ba ne. He is just far beyond everyone’s assumption (ya wuce da sanin kowa). He is a patient, amma abubuwan da yake yi da yadda yake gudanar da rayuwarsa masu lafiya dari bisa dari ba za su iya ba.
Maman Aalimah Hajiya Aseeyaita ce mutum ta biyu da ya kira. Ita kam ba ta gane shi ba, sai da ya kara da bayanin kansa sannan ta gane. Sosai ta shiga janshi da hira, tana tambayar kannensa da mamanshi. Abin da ya ba shi mamaki, ba ta tambayi Aalimah ba, sai su Basma. Abin ya burge shi kwarai da gaske. Kawaici wani abu ne mai kyau cikin al’adun malam bahaushe, wanda Mamansa ba ta sanshi ba. A gaban kowa, kiri-kiri ta ke nuna son ‘ya’yanta da nuna babu ya su a duniya. Su ne kadai ‘ya’ya. Sannan ya kira Yaya Aboubacar.
Aboubacar sa’an Aboulkhair ne, bai fi watanni biyu Aboulkhair ya ba shi ba. Don haka hira sosai suka yi, irin ta ‘yan uwa. Ya ce ya gaida Aalimah duk da ba a fi kwana biyu ba sun yi magana shi da ita.
Yau dai Aboulkhair ya yi wa kamfanin wayarsa na VERIZON ciniki mai dumbin yawa, don bayan gama wayarshi da ‘yan gidan su Aalimah ‘yan Nijar ya hau kira, duk wasu manya a dangin ba wanda bai kira ya wanke kansa ba.
Inna Kasisi na yi masa tirjiya da hutsancinta, haka ya yi ta lallashinta har ta ware suka yi hira. Ya yi mata alkawarin he will keep calling kuma zai zo Nijar next hutunsa. Albarka kuma ya sha ta wajen malam da manyan Uncles dinsa. Ba su da riko ko kadan sai kaunar junansu. Ya kuma yi mamakin matsayin da Mu’azzam ke da shi a family dinsu. Ya raina kansa, don ba wanda zai yi magana da shi har ya kare bai tambayi Mu’az ba, bai fada mishi alherin da yake masa ba. A karshe da ya gama wayar Mu’azzam din ya kira. Yana dagawa cikin sauri ya ce da shi,
“At office, call laterâ€.
Murmushi ya yi yana jin kaunar Yayan nasa na kara ratsa shi.
A fili ya ce,
“Ni ma ba wani abu zan ce maka ba. I just want to hear your voice, (kawai ina son jin muryar ka ne) kuma na jiâ€.
6/28/21, 7:32 AM – Buhainat: 185

Zuwa lokacin azahar ta yi, dakinsa ya koma ya yi sallah, ba ya bukatar abinci don haka ya je ya yi sabgoginsa a cikin gari zuwa lokacin da Aalimah ta gaya masa tana da sarari. Yana yin parking kuwa ya gansu suna fitowa, daga dakin laccar tana rungume da folder.
Tsura mata ido ya yi tana nufo motarshi. A zuciyarsa tambayar kansa yake yi, me ya fi so a Aalimah? A gaggauce amsar ta halarto zuciyarsa… Yana son komai nata… komai ta yi abin burgewa ne a idonsa. He loves her dearly.
Har ta shigo ta zauna a gefensa bai sani ba. Sai da ta hada yatsunta biyu suka yi kas! A kunnensa. Kallonta ya yi, sannan ya dauko wayarta daga inda ya ajiye ta ya lalubo lamba ya danna kira. Ba ta ankara ba ta ji muryar Mahmoud na amsawa da sallamarsa, yana tambayar ina ta shiga kwana biyu? Kafin ta kwace wayar ya bada amsa,
“Ba ita ba ce, mijinta ne, kuma Yayanta, wanda ya bada sadakinta ga iyayenta. This is for your information not to call or text my wife againâ€. Ya datse kiran.
Aalimah ta ji ba dadi har fuskarta ta nuna.Mahmoud yana da mutunci a idonta ko don Yaya Aboubacar. Ko rabuwa za ta yi da shi ba za ta so su yi irin wannan rabuwar ba.
Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta don ganin reaction dinta, amma ya kasa fahimtar komai ban da rashin jin dadin da idanunta suka nuna. Magana ta yi a hankali cikin rarrashi don fahimtar cewa so yake su yi rigima.
“Haba Yayan Basma? Abokin Yaya Aboubacar ne kuma…..†Ta yi shiru ta kasa ci gaba.
“…… Kuma saurayin kiâ€, yayi maza ya karasa mata. “Kawai ki fashe da kuka na raba ki da saurayinki…â€.
Turo baki ta yi cikin shagwaba, “…Ni ba saurayina ba ne, cewa zan yi muna mutunci ni da shi fa… Ni ba ni da saurayi…â€.
Ganin yadda yake kallon bakin nata admiringly ya sanya ta maida bakin nata ta kintse, ta kuma sunkuyar da kanta. Murmushi ta shiga saki kasa-kasa a sanda ya sanyaya murya ya ce da ita,
“Har NI?â€
Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta tana murmushi,
“Kai ma Yayana neâ€.
“Ko?†Ya tambaye ta.
Bai jira amsarta ba ya ci gaba, “Za mu bambance hakan ranar da aka daura mana aureâ€.
Ta kara tusa fuskar tata cikin tafukan nata, cikin matsananciyar jin kunya.
Wayarta ya jefa mata kan cinyarta ya tada motar, “Na bude miki Whatsapp, Daddy ya amince min in dinga magana da ke ta waya, daga yau har zuwa ranar da zai karbi sadakinki. Idan ki ka yi chatting da wannan mutumin Allah ya isaâ€.
Dariya ta soma yi tana fita daga motar. Ganin yadda yake maganar with confidence kamar ta furta masa tana sonshi ita ma. Tana son mutum mai courage, wanda ya iya yarda da kansa.
Ko da ta koma class ta bude littafin da ta ke rubutu, samun hannunta ta yi da rubuta haruffan guda tara, ‘A…B…U…L…K…H…A…I…R, ta zagaye su da zanen zuciya (heart). Kafin ta ankara cewa a cikin littafin daukar laccarta ta ke yi. Hannu ta kai ta dafe goshinta tana ambaton sunan Allah, me ke damuna ni Aalimah? Me ya shiga kaina? Me zuciyata ke nufi da ni a kan Yayan Basma? Ina zan kai Mahmoud wanda ke can wata duniya yana jirana? To amma me? The feelings are entirely not equal! Ko kusa da juna ba su zo ba, infact, abin da ta ke ji a kan Aboulkhair ba ta taba jin irinsa a kan kowa a duniya ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button