AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Shi ya dawo ya dauke su. A kofar gida bayan su Basma sun fito daga mota ya dakatar da ita. Tsare gida ya yi sosai, sannan ya jefo mata tambaya.
“Will you call him (Za ki kira shi)?â€
Da lumsassun idanunta masu gazar-gazar eye-lashes ta dago ta dube shi. Ita ma ta jefa masa tambayar, “Who?â€
Don ita shaf! Ta manta sun yi zancen Mahmoud dazu.
Runtse idanunsa ya yi ya kasa budewa, shi kadai ya san kishin Mahmoud da ke cinsa a zuci. Bai sani ba ko bayan lambarsa da ya goge daga cikin wayarta ko ta haddace lambar a cikin kanta. He don’t know how intimate they are. Daga yadda Mahmoud ke magana da kuma sakonninsa da ya karanta ya fahimci sun jima tare, kuma ta saba kiransa. Wannan tunanin ya tsaye masa a zuciya ya hana shi sukuni. Wani zazzafan so yake wa Aalimah, wanda shi kanshi yake ba shi tsoro.
Sai da fuskarsa ta yi jajawur sannan ya ce da ita,
“Saurayinki!â€
Murmushi ta yi ta dauke idonta a kansa, sannan ta ce, “Ba zan iya sanin cewa zan kira shi ko ba zan kira shi ba, sai ka gaya min sunan budurwarkaâ€.
Bata fuska ya yi ya yamutse ta abin dariya kamar wanda aka nunawa kashi.
“But, I don’t have, I have only friendsâ€.
Murguda masa baki ta yi ta fice daga motar, sai kuma ta dawo ta zura kanta ta tagar murfin motar a hankali ta ce,
“Ni ma Mahmoud abokina ne!â€.
Da gudu-gudu ta bi bayan su Basma ganin yadda yanayin fuskarsa ya canza bakidaya. Tana tsoron ya kife ta da mari, duk da ta san ba zai yi hakan ba.
Ficewa ya yi da motar ya fasa shiga gidan. Yana fitowa mota kirar Rolls Royce ta sanyo hancinta harabar gidan, wadda ke cike da korran shuke-shuken grass carpet. Tun daga nesa ya gane ko motar waye, “Mummyâ€. Fasa zuwa inda ya yi niyya ya yi, ya yi reverseya dawo da baya. A tare suka yi parking a harabar adana motocinsu, suka kuma fito a tare. Da sassarfa ya karasa gare ta ita ma ta taho suka hade, ta rungume shi. Sun dade ba su ga juna ba, kewar mai yawa ce. Duk da yana kallon mahaifiyarsa matsayin mai laifi ga rayuwar mahaifinsu, hakan ba ya nufin matsayinta ya canza a zuciyarsa ko wani abu makamancin hakan. A mother is always a mother!
Tana rike da hannunsa suka shiga gidan, su dai su Basma, Aalimah, Khaleesat da Yesmin sai ganin Mummynsu suka yi a tsakiyar falonsu. Wani ihun murna da kowaccensu ta saka ta yo kan Mummyn ta rungume ta, ba ka jin komai sai kalaman kewar juna da soyayyar junansu.
Aalimah ta koma gefe tana kallon soyayyar UWA da ‘ya’yanta, wata irin kewar iyayenta ta kama ta. Ta koma gefe ta rakube kamar marainiya.
Sam ba ta ga tahowar Abulkhair gare ta ba. Hannunta ya kamo ya soma janyo ta har gaban Mummy. Ta gintse farin cikin da ke kan fuskarta lokaci guda. Duk wata fara’a da ke kan fuskarta sai ta dauke. Girgiza mata kai Abulkhair ya shiga yi, sannan cikin nutsuwa ya soma magana.
“Mummy, Aalimah is saying welcome back to youâ€.
Aalimah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na son zubowa. Kamar Anty Zulaiha ba za ta yi magana ba, sai kuma kwarjinin dan nata da ya kafe ta da kyawawan idanunshi ya cika mata ido.
Ta sassauta grinning din fuskarta, ta ce, “Ita ba ta da baki? Ko kai ne bakinta?â€
Aalimah ta zube a kan gwiwoyinta a gaban Mummy Zulaiha cikin sanyin murya ta ce, “Welcome Mummy. And I’m sorry if I hurt you. I’m very sorry!â€.
Aunty Zulaiha ta dan rufe idanunta, sannan ta bude ta dubi yarinyar. She’s innocent, tana da innocence looks. She’s looking just like her husband kamar shi ya haife ta. Yanayin su na sanyin hali iri daya ne. Wannan ya sa ta ke kama da su Basma. Tunda ta zo ba za ta ce ga wani abu da ta yi da ya bata mata rai ba. Tana shaping tarbiyyar su Basma ne kawai, ba lalata su ta ke yi ba. Sunkuyar da kanta ta yi kasa.
Basma ta ce, “PleaseMum talk to Aal, she’s our sisterâ€.
Khaleesat ta ce, “She is nice Mummy, she cooks for us, she’s taking care of us very well in your absence (ki yi mata magana Mummy ‘yar uwarmu ce)â€. In ji Basma (tana da kirki Mummy, tana dafa mana abinci, tana kula da mu da ba kya nan sosai)â€. In ji Khaleesat.
“And she bought for me sweets alsoâ€. In ji Yesmin.
Duk sun daure ta da jijiyoyinta. Ko ita ce tafi kowa rashin adalci a duniya. Sai ta mika hannu ta kama hannun Aalimah. A hankali ta ce,
“Thank youâ€.
Dadi ya kama sudukkansu, kar dai Abulkhair ya ji labari. A haka Daddy ya shigo ya cimmasu. Tsaye ya yi a tsakiyar falon ya kama kugu yana kare mata kallo. Ga hannunta cikin na Aalimah shi ne abin da ya dan sanyaya zuciyarsa. Sama ya wuce rike da suitcase dinsa ba tare da ya ce da kowa komai ba.
Mikewa Mummy ta yi ta bi bayanshi, yaran kuma kowacce ta kama sabgar gabanta cike da farin ciki. Aalimah ta mike za ta shiga kitchen suka hada ido da Abulkhair da ke zaune a kan daya daga cikin kujerun dining table ya zuba mata ido. Wani irin sonshi da kaunarshi ya kara mamaye ta.
Murmushi ta hau yi masa ba ta san tana yi ba, ya wani dauke kai ya juya mata baya. Sai a lokacin ta tuna ashe fa fushi yake yi da ita ta yi masa laifi. Karasawa ta yi kicin don yin abin da ta nufa, amma sai ta ji duk ta damu, zuciyarta ta yi mata babu dadi da fushin nasa.
Da ta fito daga kicin din kuma ba ta same shi a falon ba ya fice ya bar gidan. Tana jiyo hucin motarsa don ba za ta ce kara ba. Motocin Daddy are not making sounds wato (ba sa kara).
A can dakin iyayen suna can suna tafka ta a tsakaninsu, Daddy ya ce, don me ta dawo masa gida bai neme ta ba? Ta ce, saboda gidan mijina ne, gidan ‘ya’yana, kuma mijina ba sakina ya yi ba. Nan kuma ta kwantar da kai ta shiga ba shi haquri har da kukanta.
Mikewa ya yi zai bar mata dakin ta kamo shi ta kankame, ta shiga rantsuwa tana daukar masa alkawarin wannan karon ta dau laifinta, za ta canza ya ba ta dama, she has no business ( ba ruwanta) da kowa nasa da duk wanda zai kawo gidansa. Cewa ya yi I’m tired(na gaji) da tuban muzurinki.You will never change Zulaihatu, (bazaki taba canzawa ba) mai hali ba ya fasa halinsa, I’m tired of all these, ya kamata mu bai wa juna sarari, har kowannenmu ya je ya yi kwas a kan halin dan uwansa. Na kasa saninki fully har gobe, in na ci gaba da biye miki halaka ni za ki yi…!â€
Yadda ta rungume shi cikin jikinta da runguma mai tsananin karfi, jikinta yana rawa da karkarwa da jin kalamansa, shi ya hana shi karasa magana. They missed each other to such an extent… don haka duk wani mai korafi ma a tsakaninsu ya adana korafin nasa a gefe zuwa gaba. Amma ko daga yanayin Zulaiha a yau da yanayin bugun numfashinta ya san ta yi nadama wannan karon, wadda yake fatan Allah ya sa ta dore. In kuma hakan bai yiwu ba, duk son da yake mata wannan karon zai ba ta mamaki ta inda ba ta zata ba. Al’amarin mace da miji sai Allah, cikin daren suka shirya kansu.
A can dakin su Aalimah kuma, kowa ya yi barci ya barta. Wayarta ce a hannunta tana jira ko Abulkhair zai kirata? Ta kasa barci ko kankani. Ganin har karfe sha daya na dare bai kiratan ba bai kuma yi mata sako ba ya tabbatar mata fushin nasa na gaske ne. Ji ta yi duk ta tsani kanta, don me zata batawa mutum mai kyakkyawar zuciya irin Abulkhair? Mai sonka shi yake KISHIN KA, shi ya damu da al’amarinka. To amma don me zai damu kansa da zancen Mahmoud? Ya sa pressure sosai a kan zancensa. Ita ba ta dauki al’amarin Mahmoud da zafi ba, ba ta yi masa alkawarin za ta aure shi ba amma yafi karfin wulakanci a idanunta.
Abin da ta san ta ce da shi shi ne, “We can not runaway from our destinies but she is hoping that destiny tied them together (ba za mu iya gujewa kaddarorinmu ba, amma tana fatan kaddarar ta barsu tare). To kuma ga kaddarar ta yi gardama. Kamata yayi Aboulkhair ya dubi present dinta ba past dinta ba. Damuwa ta yi damuwa a zuciyar Aalimah, ta jefa zuciyarta cikin wani yanayi mara dadi. Ba ta san ta kamu da son Abulkhair har haka ba sai yanzu da ta ke ganin yana kokarin barinta kan abin da bai kai ya kawo ba a ganinta.
Da gaske Mahmoud ya fi kama da aboki fiye da saurayi a zuciyarta. Akwai sabo a tsakaninsu, duk da shi ba hakan ba ne a tashi zuciyar. Amma a halin yanzu ji ta ke zata iya komai don ta samu Abulkhair, farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa ya fiye mata komai, hada da wannan karatun da ta ke yi kuwa, za ta iya barinshi in har barin nasa na nufin mallakar Aboulkhair a matsayin miji.
Ba ta da masaniyar cewar Abulkhair ya sanya lambar wayarsa a ciki ya adana, sai ganin wani lafiyayyen french word ta yi yana yawo a fuskar wayarta, mai nuna shigowar kira; Ma cherie, wato My love da harshen faransa. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki ta yunkura ta mike zaune. Sannan ta hau juyawa damanta da hagunta kamar munafuka tana kallon su Basma don tabbatar da barci suke ko idonsu biyu? Ta tabbatar sun yi nisa a barcinsu sai ta lallaba ta shige toilet da wayar a hannunta.
Zuwa lokacin kiran ya katse wani ya kara shigowa. Zama ta yi a gefen bath tube, sannan ta yi sliding wajen amsa kiran.
“Not asleep like me?â€
Ta ji muryarsa cikin damuwa tana tambayarta.
“Ta ya ya zan iya barci kana fushi da ni Yayan Basma?†Muryar da ta yi amfani da ita wajen yin maganar ta nuna zahirin damuwar da ta ke ciki.
Tana jin yadda Abulkhair ya sauke ajiyar zuciya, “Ban san kin damu da ni har haka ba, da ban sa kaina cikin damuwa haka ba. I thought you love him, since you cannot erase him from your memories, you want your relationship to continue…†( na zaci kina sonsa, tunda bazaki iya goge shi daga tunanin ki ba, kina son alaqarku ta cigaba).
Dan runtse ido ta yi, tone din muryarsa na kassara duk wani sauran kwarin gwiwar da ta ke da shi na yi masa bayanin da zai kwantar da hankalinsa. Da kyar ta iya yafito sauti daga makogaronta.
“He is not in my memories, he is where he is (ba ya cikin tunanina, yana dai inda yake). I feel nothing for him†(bana jin komai akansa).
Abulkhair ya kara nitsewa cikin duvet dinsa. Murmushi yake yi wannan karon, duk wata damuwar da ya sanya kansa ya neme ta ya rasa. Murmushin da ake kira daga kunne zuwa kunne don fadinsa.
“Ni kuma fa? A wane bangare aka sanya nawa feeling din? Tunda na shigo gidan nan na rasa kaina, na zama ba ni ba Aal, duk bugun da zuciyata za ta yi ke ce a cikinsa. Aalimah, I want to say it loud I love you… ba zan taba komawa yadda na zo ba sai na samu amsar bakinki. Ki gaya min komai kankantar kalmar da zan amince ba ni kadai nake wahala ba. Amma in kin fi son wancan mutumin don Allah kada ki gaya min, it will go away with my last breath (zai tafi da numfashina na karshe)â€.
Tun da ya fara magana Aalimah ke jin wasu bululluka da suka danne zuciyarta na rugurguzowa suna kara dasa shi a zuciyarta. Zuciyar ta zama ‘yar shafal babu sauran damuwa a cikinta. Lumshe idonta ta yi ita kadai ta ke blushing tana rufe ido tana budewa. Ci gaba ya yi da gaya mata duk abubuwan da yake fama da su cikin zuciyarsa a kanta yana kuma rokon mafi kankantar kalma daga gareta mai nuna kauna ko yaya a gareshi. Kwalla ta ji ta taru a idonta, ta so da kaunar Abulkhair da kuma tausayinsa duka a lokaci daya.
Ta samu kanta a mai tambayar kanta me ta ke da shi da har dan gata irin Abulkhair zai mace a soyayyarta haka? Yaya Aboubacar ya sha cewa she’s the ugliest of their house (itace mafi muni a gidansu). Hancinta kamar an dosana mata shi, idonta kamar kwan zabo, bakinta kamar gidan tsutsa. Ta tuno suffa da kira mai zati irin na Aboulkhair, amma duk bai duba wannan ba a haka yake sonta.
Abulkhair ya fidda ran samun raddi daga Aalimah, yana shirin kashewa ya san yadda zai yi ya yi jinyar zuciyarsa ya jiyo ta tana cewa.
“Ina jin fiyeda abinda kake ji, na fara son ka daga lokacin da na dora idona a kanka. Na kasa barci sabida tunanin kana fushi da ni. Ban taba soyayyya ba sai a kan ka. I love you ABOULKHAIR!â€. .
This is the beginning,kuma farkon kaddarorin rayuwar Aalimah.