AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Washegari Mummy ta koma aiki, tsakaninta da Aalimah kadaran-kadahan, babu tsana babu hantara, amma babu soyayyah. Duk hidimominta da ‘ya’yanta ta ke yi ba ta sanya ta. Ba ta sanya ta a shirginta balle ta dame ta, sabgogin gabanta kawai ta ke yi. Aalimah, ba ta sanya hakan a ranta ba balle ya dame ta, sai ma wani ladabi na musamman da ta ke yi wa Mummyn kamar uwar da ta haife ta, ko da Mummyn ba za ta nuna appreciation ba.
Ta dora wa kanta gyaran komai na Mummyn wanda Easther ke yi kamar gyaran kayan sanyawarta, shirya mata takardun office in ta hargitse, rike mata jaka zuwa mota, gaisuwa da tsugunno har kasa. Taya ta hidimar gida, da kula da Yesmin saboda ita kanta Easther ayyukan gidan wani lokacin suna fin karfinta kasancewar ita kadai ta ke komai da komai, Mummy ba ta son yawan ‘yan aiki kada su cika mata gida, don haka Aalimah ta karbi rabin hidimar gidan in dai tana gida ko ba ta da lacca ko a karshen sati dan abin da su Basma ke yi a gidan bai taka kara ba balle ya karya. A ganin Aalimah, a yanzu kam she can do anything for Mummy in dai za ta barta ta rayu da danta. Wanda ranshi ne kawai ba ya cirowa ya bata saboda so da kauna.
Ya ci gaba da kai su makaranta da dauko su da komawa wajen Aalimah su sha hirar soyayyarsu a dukkan intervals dinta, in dare ya yi kuwa lokacin bude ofishin soyayyarsu kenan a waya, yadda suke son junansu ba sa son karatun da suke yi. Tun Basma ba ta ba su hankalinta don ta dauka haduwar jini ce, har ta soma disa wa alakarsu dindimemiyar ayar tambaya.
Mummy kam ba ta fahimci komai ba, har gobe. Don hasashenta da hankalinta bai taba hasaso mata hakan za ta iya kasancewa ba. Khaleesat kam babu harkar kowa a gabanta balle ta damu da sanin me wani nata yake ciki. She’s always busy with her text books and islamic lesson. Basma ta sha kama Aalimah na yin night call a toilet, sai dai ba ta san da wa ta ke yi ba, ta ma fi zaton wannan nataccen saurayin nata na Nigeria ne. Abin da ya fara cika mata idanu shi ne kusan kullum, Monsieur Abulkhair dinsu na makarantarsu, kuma duk sanda ta zo neman Aalimah za ta gansu tare. Mafiyawan lokuta karatu suke yi yana koyar da Aalimah lissafi da sauran abin da ya shige mata duhu, sai dai idanunsu kadai za ka kalla ka hango wani kwantaccen al’amari da suke dauke da shi ga junansu. Kasa boye tambayoyinta ta yi rannan ta tambayi Aalimah a kan hanyarsu ta isa ga inda Abulkhair ya yi parking domin su tafi gida.
“Is Monsieur Abulkhair in love with you?†Ta yi tambayar ne don shakuwar da ta ke gani a tsakaninsu ta wuce hankalinta, amma ba wai don akwai wani abu a ranta game da hakan ba, so ta ke ta tabbatar da abin da zuciyarta ke gaya mata.
Hararar da Aalimah ke jifanta da shi, ta kuma ki ba ta amsa ya tabbatar mata da zarginta. Dariya ta yi, sannan ta kai wa Aalimah dundu a baya.
“Ke da shi din kun dace, saboda dukkaninku halinku daya, charming, cheerfuland compossionate personality. Sai dai zan so in tuna miki rules din Daddy kafin shigowarmu makaranta, duk wadda ta sake ta yi saurayi, AURE!â€.
A yadda Aalimah ke jin Abulkhair a ranta, she can give him the life itself(zata iya bashi rayuwarta dungurungum) idan za ta iya, ba karatu kadai ba. Abulkhair, ba ya son tunowa cewa hutunsa ya zo karshe, zai koma Baton Rouge (Louisiana) kwanaki biyu masu zuwa.
Sosai Aalimah ke rokon Basma kada ta gaya wa Mummy komai a kansu. Da Basma ta tambayi dalili, sai ta ce, “Mummy ta fara sona Basma, mun fara samun fahimtar juna, I don’t want to lose this love from her, (bana son rasa wannan soyayyar daga gareta) tunda ban san yadda za ta karbi al’amarin baâ€.
Basma ta yarda da uzurinta, amma zuwa can sai ta ce, “But she must know (dole ta sani) tunda karewa ma jikoki za ki kawo mata!â€.
“Sai ki bari in jikokin sun zo sai su fada mata da kansuâ€.
Yau asabar, ta kama da yammacin yau din Abulkhair zai bi jirgin kasa zuwa inda ya fito. Tun safe yake dacin rai, Aalimah ta shirya masa breakfast amma yana fitowa daga wanka da ya zo ya gani sai ya hau fada, wai shi bai ce mata chips zai ci ba, ta kwashe ta maida kitchen tun bai kifar ba. Gefe ta koma ta langabe kai abin tausayi, sai dai fa duk fadan nan da yake yi ya ki yarda ya kalli kwayar idanunta.
Mummy da ke kan dining din tana cin nata ta dube shi cikin jin haushi, “Amma me ye laifinta, ta bata lokacinta ta shirya maka ba tare da kowa ya sanya ta ba? Besides, the cooking is good, as far as I know, you love chips so muchâ€.
“To yau na daina sonshi. Ni ban ce muku ma zan ci abinci ba, I’m not hungryâ€.
Aalimah na gefe tana kallon sakarci, uwar ta bi duk ta damu, sai lallaba shi ta ke kan ya ci, yana dada botsarewa.
Daddy ya shigo falon daga jogging din da ya je waje, ya tadda su a haka. Yana shigowa Mummy cikin damuwa ta soma gaya masa yadda aka yi.
“Idan aka kyale shi haka zai kama hanya ya tafi ciki ba komaiâ€.
Ya ce, “Wa ya yi girkin?â€
Ta ce, “Aalimah ceâ€.
“Kuma ya ce ba zai ci ba?â€
Abulkhair ya sunkuyar da kai sai cika yake shi kadai. Daddy kwafa ya yi ya iso har gabansa ya ce, “Gara ma ka ci, ka ci na bankwana sai bayan wata ukku. Idan kuma ka sake ka kara ko kwana daya kan hutun nan I know how to deal with you. I will cancel even the phone callsâ€.
Da sauri ya dago ya dubi mahaifinsa, with shock in his eyes.
Ya ce, “Yes, I mean itâ€.
Aalimah ta sunkuyar da kai kamar ta ce, kasar ta tsage ta shige. Wato maganar da ya taba gaya mata na cewa, Daddy ya san da zancensu da gaske yake yi? Yau ina za ta sa kanta da kunyar kawunta? Mummy ta ce,
“Wane phone-call za a yi cancelling?â€
Daddy bai ba ta amsa ba ya yi wucewarsa.
Basma ta shiga boye bakinta tana dariya, ganin yadda Monsieur ya kwalalo ido an ce za a hana shi waya da Aalimahrsa. Mummy dai ta kasa gane me suke ciki, ta tashi ta bar wajen.
Aalimah ta daga kafa za ta bi bayanta, ya sha gabanta. Ta dago idanunta da suka yi rauni ta dube shi, ta fi shi shiga damuwa a kan tafiyarsa. Ta fi shi shiga taraddadin yadda za ta iya ci gaba da rayuwa cikin Massachusetts babu shi, kanta ya bude da calculus da sauran danginsa, yanzun ba ta shayinsu. He made all her courses very clear and simple to her ta yadda ba ta bukatar taimakon kowanne namiji a Boston yanzu. Ya taka rawar mutane guda hudu a dan zaman da suka yi tare; dan uwa, aboki, malami kuma masoyi. Ya koyar da ita karatu ya koyar da ita yadda za ta so shi. Ba ta son ta soma tunanin ta yadda za ta fara kewarsa…!!!
“Is that the kind of adios we are going to do? (wannan ce irin sallamar da za mu yi?)†Cikin zuciyarta ta ce, “Kai zan tambaya. Ka zo kana ta dagawa iyayenka hankali for no reason (babu dalili) don kawai sun ce ka koma makarantaâ€.
Zancen zuci ta ke, ba ta san cewa a fili ta ke yi ba.
Yatsun hannunsa ya tura cikin tarin sumar kansa, yanayin fuskarsa kadai ya nuna tsantsar damuwar da yake ciki. “na rasa hanyar da zan nuna musu bana son komawashi ya sa na ce bari in ki cin abinci, watakila su gane zuciya ta, ba ta da lafiya su barni in zauna, amma ki ji abin da ya ce he will cancel even the phone callâ€.
Ya fada yana bata fuska kamar mai fadar wani mummunan abu.
Dariya Aalimah ta yi, ya bata rai sosai, “Au dariya ma ki ke mini? Ba komai, it’s all a matter of time. I will wait, as he insist, I know it is not easy to possessed a diamond, but when one have it, he will do what he wants with it (Zan jira, kamar yada ya dage sai na jira. Nasan ba abu ne mai sauki ba mallakar lu’u’lu’u(dutsen yakutu), amma idan mutum ya mallake shi zai yi abinda ya ga dama da shiâ€.