AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Wannan ita ce sallamar Aalimah da Abulkhair. Da yamma ya bi motar haya zuwa birnin Baton Rouge daga Boston inda Louisiana State University ta ke. Tafiya ce ta one hour kacal a tsakaninsu.
Yana zaune a seat dinsa yana ta juya wayar hannunsa. Daddy ya ce bai yarda ya kira Aalimah ba ko ya yi mata sako, sai a karshen mako kadai. Idan kuma ya ketare zai zare hannunsa ya barshi da dabararsa. Hukuncin is so painful so much unbearable… To amma ya zai yi? Yana son mallakar Aalimah kuma Daddy ya yi na’am, alfarma daya yake so ya yi masa kada ya hana ta karatu da soyayyah, don ya fita kunyar iyayenta. Shi kuma zai yi duk iya kokarinsa na samar da ita gare shi. Ya san jiran zai zamanto kamar jiran zuwan ranar tashin kiyama (seem like endless), amma ya amince with time and Allah’s will da kuma tsawon numfashi komai mai tabbatuwane. .
Da tunani ya cika masa kwanya sai ya kira Yayansa Mu’az, shi kadai ne zai iya mantar da shi duk wani hali da yake ciki da salon tashi kaunar ta dan uwa which is exceptional. Mu’az na dagawa abin da ya fara cewa shi ne.
“Something or someone snatched away my brother from me. What is it? Or who is she?(Wani abu ko wani mutum ya janye min dan uwana daga gareni, menene wannan abun ko wacece ita?)â€
Ajiyar zuciya Aboulkhair ya yi, wasu lokutan Mu’azzam kamar yana karantar shafukan zuciyarsa. Duk abin da yake ciki kafin ya gaya masa yake ganewa. Shi ne dai har gobe ya kasa gama sanin Mu’azzam. He is like a magician when it comes to reading minds (kamar wani mai sihiri yake in aka zo batun karantar zuciyar mutane, musamman shi Abulkhair). He care for him too much fiye da sauran kannensa. Tare suka yi duk wata dabdala ta kuruciya a birnin Washington kafin kaddara ta dawo da su zama a Boston (Massachusetts). Haka duk kaddarorin rayuwar Mu’az sun faru ne a kan idonsa. Wani abu da ya dasa wata irin kauna da jin kai a zuciyarsa. Ba don Mu’az ya fi son rayuwa shi kadai a inda yake ba, da zai iya hakura da karatu a Baton Rouge ya zauna tare da shi, ya ba shi dukkanin farin cikin da dan uwa zai iya bai wa dan uwansa duk da ya san hakan ba zai fidda shi daga halin da yake ciki ba.
‘Kwalla’ abu ce mai sauki daga idanun Abulkhair when it comes to MU’AZZAM. A yanzun ma kwallar ce ta cicciko idanunsa. Ya canza position din rikon wayar daga kunnen dama zuwa na hagu, amma bai yi magana ba. Mu’az a tausashe ya ce, “Na ce mene ne ya dauke hankalinka daga gare ni, ko WACE CE?â€
With a very low tone ya ce, “AALIMAHâ€.
Dariya Mu’azzam ya yi irin dariyarshi mai tafe da gentleness tune.Wai yau Abulkhair ne da soyayyah! Abulkhair din da ya sha cewa, tunda ba zai yi aure ba, shi ma ba zai yi ba, yau shi ne da dakon soyayyah tun kan a kai ga zama Doctor din kula da shi da aka ci wa alwashi. Lallai ko wace ce wannan Aalimah ta ciri tuta, kuma zai so ya ganta. Dariyar Mu’az ta sanya Abulkhair rufe fuskarsa da tafin hannunsa, kamar Mu’az din na ganinsa. Wai shi ya ji kunya.
Mu’az ya ce,
“Then where will I find my psychiatric Doctor?â€
Cikin tsokana ya yi maganar, kamar yana magana da karamin yaro.
Dariyar da Abulkhair yake yi ta mantar da shi duk wasu damuwoyinsa,
“The boy will keep striving to be what he promised to be. This is a promise!â€.
(Yaron zai cigaba da kokari har sai ya zama abinda yayi alkawarin zama. Wannan alkawari ne)â€.
Da wannan suka yi sallama.
Wani dare mai wuyar barci ga Aalimah. Ji ta ke kamar wani sashe na jikinta ba ya tare da ita. Abulkhair ya shigo rayuwarta da karfi, ya zauna da muhimmanci. Ta kasa barci sai juyi a kan gadonsu. Duk kuma juyin da ta yi sai ta ji amsa kuwwar dadadan kalamansa cikin kunnuwanta. Sai ta ga gilmawar kyakkyawar fuskarsa a idanunta. Idan wannan ita ce soyayyah, to ba ta yi mata kamun sauki ba, sannan aba ce mai wahala cikin zuciya da kwakwalwar dan Adam.
Da safe ta sha tsokana a wajen Basma, ganin yadda ta yi cooling ta rasa duk wani karsashinta, Basma ta ce, “Ko Baton Rouge za mu koma da karatu ne?â€
Harararta ta yi ta sauka kasa, don taimaka wa Mummy a kitchen kafin zuwan Easther.
6/28/21, 7:32 AM – Buhainat: $$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
64
Daddy shi ya kai su makaranta ranar litinin, kamun Laraba kuma ya samar musu direba. Bakar fata ne dan kasar Cameroon. Sunansa Joseph, suka ci gaba da karatunsu cikin kwanciyar hankali. Tsakaninta da Mummy yana nan yadda yake, babu soyayya, amma babu kiyayyah. Kowa yana zaman kansa, zaman wanda ya ajiye shi. Sai dai ita kanta Mummy tana yabawa da dabi’un Aalimah a zuciyarta, furtawa ne ba za ta yi ba. Tana yabawa da kulawarta a kan yaranta da yadda suke canza dabi’u gradually ta hanyar koyi da ‘yar uwar tasu. Khaleesat har koyon daurin zani ta ke, tana kuma daukan karatun alkur’ani daga Aalimah da sauran al’adunmu na gargajiya, al’adun da ta ke wa kallon kauyanci, amma can a karkashin zuciyarta ta san wannan shi ne daidai, kuma ita ma ba sonta ba ne yaranta su lalace ba, tun a kan Mu’azzam ta yi sanyi da daukan dabi’un Turawa da tsanani, duk da cewa sun yi babban tasiri cikin rayuwarta. Ta manta da yawa daga nata al’adun da hukunce-hukuncen addini.
Zamanta da Aalimah da kasancewarta cikin ‘ya’yanta sai ya zamanto kamar ana tuna mata wasu abubuwa da ta manta. Ta kuma fara sassauta wa kanta kin yarinyar, ta yarda mutum rahma ne, amma jure zama da shi shi ne abin da yake mata wuya. Sai dai in ka yi katari da na kirki irin Aalimah ya fi ruwan sha saukin sha.
Babban abin da ke burge ta da Aalimah rashin kiwa, ba ta da son jikinta ko kankani, ga nutsuwa da rashin rawar kai, ga tsafta da kula da tsaftar jikinta. Ko fensir Yesmin ta yasar Aalimah ba za ta barshi ba sai ta dauke ta adana mata shi cikin jakar makarantarta. Sannan ba ta da rayuwa mai zafi irin ta Basma, ita kam Basma komai nata tana so ya zama na musamman. Kayayyakinta, abubuwan amfaninta sai ta tabbatar fitacce ne (designer) ne ko latest fashion. Zamanta da Basma da shakuwar da ke tsakaninsu bai sa ta yi adopting nata dabi’un ba, ita Basman ce ke tsintar nata tana hadawa da nata.
Abulkhair ya yi kokari sosai wajen maida hankali a kan karatunsa kamar yadda mahaifinsa da Yayansa ke so. Sun yi masa alkawarin tsaya masa a kan komai idan ya jajirce ya fiddo kwalin likitancinsa. Ba Aalimah kadai ba, har da karin guda uku bayan ita in yana so. Dakatar da su yake in sun fadi hakan, “She’s okey for me till eternity (ta ishe ni har abada)â€.
Asabar na zagayowa ba ya iya hakurin yamma ko dare zai fara kiran waya kamar Allah ya aiko shi. Tana zama unease idan kiranshi ya shigo tana tare da kannensa ko iyayensa ba ta iya amsawa. Don haka duk sabar ta ke maida wayarta a vibrating ta soke ta a jikinta, da ta ji shigowar kiran Abulkhair za ta tsallake ko mene ne ta fita compound na lodge dinsu su sha hirarsu kamar sun hadiye juna, duk rabin hirar Abulkhair yana gaya mata yadda yake kewarta ne da yadda zuciyarsa ta makance a kaunarta. Yadda yake managing kafin zagayowar sati ya yi magana da ita. Hakuri ta ke ba shi ta karfafa masa gwiwa kan bin maganar Daddy. Tana tunatar da shi cewa abu mai kyau yake nufinsu da shi (good future). Ya ci gaba da rokon Allah ya barsu da rai da lafiya, shekaru hudu kamar yau ne. Sun fi yin magana a vedio call, yadda za su dinga ganin zahirin abin da ke zuciyar junansu cikin kwayan idanunsu. Ba ya kiranta da daddare, yana barinta ta yi barci isasshe. Wannan ya kara kauda hankalin kowa a kansu cikin gidan, ban da Basma da Daddy ba wanda ya san me suke ciki.
Sun yi jarrabawar karshen zangonsu lafiya, suka samu hutu na sati biyu. Ba da sanin kowannensu ba daddy ya gama yi musu shirin tafiya Nijar. Bai gaya musu ba, sai ana saura kwana biyu tashinsu. Yaran sai murna suke yi, don sun dade ba su je Nijar ba. Sai dai daddy ya ce da Aalimah ta rage murnarta, ba za su karasa Nigeria ba, sai a hutun karshen shekara zai shirya mata zuwan ita kadai. Murmushi kawai ta yi, daga Nijar har Kano duk gida ne a wurinta.
Mummy dai ta bada uzuri da office dinta. Kuma da gaske hakan ne, ba za su barta ba. Sai dai fa gaskiyar magana ko babu office ba za ta yarda ta bi su ba. Ta riga ta sa wa ranta dangin Ishaq ba sa sonta, don haka babu wata alaka tsakaninta da su. Ta yi kokari kwarai wajen dauke hankalinsa daga kansu da nuna wa ‘ya’yanta su manta da wanzuwarsu a doron kasa ba masoyansu ba ne.
Yau rana daya ya zo ya ce zai tafi Nijar da ‘ya’yansa bayan ‘yarsu da ya dauko ya kawo mata, har ya kore ta daga gidan a kanta! Ba ta san me yake ta canza mata Ishaq haka ba, ga shi duk wani karfi da ta ke da shi a idonsa ya yi sanyi, yanzu ba ta isa ya yi abu wanda bai gamshe ta ba ta ce da shi don me? Wani sabon Ishaq ne wannan ba wanda ta sani tun kuruciyarsu ba.