AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Jirgin Ethiopian Air ya sauke iyalin Ishaq Raazee a filin jiragen saman Diori Hamani International Airport da misalin karfe goma na safiyar lahadi agogonsu na can. Sun samu Hamoud babban dan Uncle Oussama yana jiran saukarsu, shi da Balkisa ‘yar Uncle Edrissa babbar kawa ga Aalimah kenan kaf dangi. Iyalin Ishaq sun zamo kamar wasu taurari sha kallo a cikin gidan Malam Ibrahim Raazee a yau saboda murjewa da kyan fatarsu, duk da cewa kowa a gidan fari ne kal! Amma nasu ya sha bamban da na kowa. Kan ka ce meye wannan? Gida da makwabta ya kacame da murnar zuwansu, aka shiga aiko da akussan abinci daga kowanne bangare. Inna Kasisi kam ko a launin fuska babu wani alamu da zai nuna maka ta yi farin ciki da zuwan nasu, sabgogin gabanta kawai ta ke na dora sanwar abincin rana na gidan bakidaya, kasancewar abincin gandu ake yi a gidan.
Inna Bintou ce ke ta hidima da su tun shigowarsu da ‘yammatan gidan (jikoki) sa’anninsu. Daddy Ishaq kasa yi wa Inna Bintou alkunya ya yi irin wadda ya saba, wato fara shiga sassanta, dakin mahaifiyarsa ya shiga kansa a duke yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ta kara tsufa mai nuna alamun girma a tare da ita tsayin shekaru shidda da ya kwashe bai sako kafarsa a gidan iyayensa ba. Zama ya yi a kan kilishi ya tankwashe kafafunsa, zuciyarsa ta yi nauyi mai cakude da matsananciyar nadama. Sam ta ki yarda ta zauna a dakin, sai dai ta shigo ta dauki abu ta fita ba tare da ta dubi bigiren da yake ba.
Ko da ta gama girkinta ba ta zubo masa ba, amma ta zuba wa su Aalimah. Shinkafa fara tas! Da miyar dage-dage wadda ta ji fala-falan ganyen kabeji da naman rakumi zuku-zuku. Abincin ya yi masa kyau a ido, ya kuma ba shi sha’awa. Ya shiga tunano yadda suke santin abincin Innar shi da yayyensa Oussama, Edrissa da kaninsa Mansour da sauran kannensu ‘ya’yan Inna Bintou. Da yake a faranti guda ake zuba musu, in an cinye a yi kari, kafin a zo karshe a yi wawa a rikice da kokawa. Kwalla ta ciko idanunsa, amma bai bari ta gangaro ba.
Reaction din Inna ya nuna masa Inna tana fushi da shi, duka tsayin wannan lokacin tana kullace da shi a kan banzatar da ita din da ya yi, ya shiga tambayar kansa me ya shiga kansa? All these while da ya manta da iyayensa, ya manta da girman hakkinsu a kanshi da kulawar da Allah ya ce ya ba su.
A lokacin ne Malam ya dawo daga rangadin da ya tafi wajen rakumansa a can wani kebantaccen muhalli. Tsufa ya bayyana sosai a tare da shi. Inna Bintou ce ta je ta sanar da shi zuwansu. Ko abinci kasa ci ya yi sai da aka kira mishi jikokin nashi, tare suka ci abinci a kwano guda yana tambayar Aalimah yanayin karatunta. Ta gaya masa komai lafiya, sannan ya ce da Basma, “Ina Mu’azzam? Ina kuma Abulkhair?†Cikin harshen buzanci.
Daddy yana yi musu sosai don haka suna ji sama-sama, sai ta juya nata harshen ta soma ba shi amsa cikin yaren Faransa.
“Monsiuer Abulkhair ya koma makaranta, bai ma san za mu zo nan ba, na tabbatar maka da sai ya ajiye jarrabawar da yake yi ya zo. Mu’az kuma yana nan yadda yake, annoying kamar koyaushe. Ya fi son rayuwa a LAS VEGAS fiye da ko’ina a duniya. Ba ya zuwa gidanmu don wai muna yi masa hayaniya. Mum and Dad, su suke zuwa wajen Mu’azzam. Grand-pere (kakanmu) Mu’az ba ya son mu ko kadan, Monsiuer Abulkhair kadai yake so a cikinmu. Ba dama mu yi magana in yana zaune he will throw a tantrum (zai yi masifa). He is the most annoying person in the world (ya fi kowa ban haushi a duniya), watakila shi ya sa ya kasa samun mataâ€. Ta karasa cikin dariya.
Tunda ta fara kakan yake sauraronta, yana duba maganganunta filla-filla. Shi kuma a wurinsa Mu’azzam is a nice person fiye da dukkan jikokinsa. Duk sanda ya tambaye shi me ya hana shi aure, sai dukkan walwalar fuskarsa ta canza, idan ya takura da tambayar sai ya ce,
“Idan ba ka daina yi min zancen aure ba Mallam zan daina kiranka a waya, ba kun yi min auren ba? Me na tsinta a cikinsa?â€
“Mu’azzam, ba mu muka yi maka aure ba, Babarka ce ta yi maka, babu saninmu, babu hannunmu. Babanka ya zo bagatatan ya ce za a daura maka aure don a ceci rayuwarka ba ka da lafiya, shi ya sa na amince wa Oussama ya je aka daura, amma ba mu san komai a kai baâ€.
Dattijo Ibrahim Raazee ya yi ajiyar zuciya. Ya dubi jikokinsa biyar da ke zaune a wajen ciki har da Aalimah. Sannan ya kai dubansa ga Basma wadda ta fi kowa kaifin baki cikin jikokinsa. Ya ce da ita cikin auzinanci,
“He is not annoying, he is compassionateâ€.
Ta daga manyan idanunta irin nasa da suka gado, ta dube shi, “Non Grand pere (a’ah Kaka), he’s annoying, and he don’t like usâ€.
Sai ya yi murmushi ya kyale ta suka shiga wata hirar. Ya fahimci babu wanda zai kankare wannan belief din daga zuciyar Basma, na cewa, Yayanta mutum ne mai ban haushi, mara dadin mu’amala, sannan ba ya sonsu.
A can dakin Inna kasisi ta gama duk sabgoginta ba abin da ya rage mata a tsakar gidan, dole ta koma dakinta ta yi alwala ta tada sallah. Duk Daddyn Basma yana zaune sunkuye da kai ya kasa cin nau’ikan abincin da aka tara masa a gaba. Sai da ta idar ta yi addu’a ta shafa, sai ta ci gaba da zama a kan sallayarta. Ya ga cewa wannan ita ce damarsa ta karshe, kada ta sake ficewa a dakin.
Ya shiga rarrafawa a kan gwiwoyinsa har ya tadda ita. Hannayenta biyu ya kama ya rike cikin nashi, sai kuma ya kwantar da kai a cinyoyinta ya fashe da kuka.
Cikin kukan yake rokonta ta yafe masa, ya gane dukkan kurakuran da ya tafka da kansa, ya yi nadama ya dauki niyyar gyarawa, in ma cewa ta yi ya baro kasar Amurka ya dawo gida zai yi mata wannan biyayyar. Tun zuciyarta na tururi har ta soma karyewa. Shi din ba karamin yaro ba ne ya ba wa hamsin baya, har da furfurarsa. Amma ga shi yana kuka cikin tsananin nadama, ta gode wa Allah da hakan ta faru da sauran numfashinta. Ta san kaidi irin Jai mazajensu jahannama a dalilin fushin iyaye.
Lokaci ya yi da ita ma za ta nuna wa Zulaiha matsayinta na UWA mai cikakken iko a kan danta, ba ita da ba ta da ikon komai a kansa ba, shi ne ma yake da shi a kanta.
“Mon pilsâ€. Ya ji ta ambata ayayin da ta kai hannunta cikin tarin sumar kansa. Mon pils na nufin DANA.
“Na yafe maka duniya da lahira. Ka je wajen mahaifinka ya dawo tun dazunâ€.
Dagowa ya yi idanunsa sharkaf da hawaye yana yi mata godiya. A yadda ya san taurin rai irin na Innarsa bai zaci wannan yafiyar ta gaggawa ba. Allah kadai ya san shekarun da ta kwashe tana kwankwadar damuwa da bacin rai a kansa.
Dakin Malam ya nufa, nan ya tadda su Aalimah suna ta shan hira da kakansu. Kana jin tashin muryar kowaccensu tun daga bakin kofa ana ta auzinanci mai cakude da faransanci, amma ban da ta Aalimah. Da ya yi sallama ya shigo duk suka yo kansa da magana, Aalimah tana daga gefen daman kakan tana danna wayar hannunta, nutsuwar yarinyar da rashin hayaniyarta na burge shi. Sai ta tuna masa da dansa Mu’azzam, haka yake shi ma, in za ka ji muryar mutum goma a wuri ba za ka ji tashi ba. Wani tsananin tausayin Mu’azzam ya kara lullube shi.
To shi Mu’az haka zai karasa rayuwarshi babu farin ciki babu future kawai don Allah ya dora masa lalura? Hawaye ya ji sun ciko idonsa, ya yi sauri ya dauke su da yatsun hannunshi, duk a kan idon mahaifinsa. Duban yaran ya yi, ya ce duk su je su yi sallar la’asar lokaci ya yi. Ya rage daga shi sai Babansa.
Sun gaisa sosai, da tambayar iyali da hidimomin rayuwa. Ya ba wa Malam hakurin tsawon lokacin da ya dauka bai zo gida ba. Ya roke shi ya taya shi kara bai wa Inna hakuri. Ya yi alkawarin canza tsarin rayuwarsa. Ya gane mutum komin matsayinsa a duniya shi ba komai ba ne in babu albarkar iyaye a tare da shi. Duk tsayin shekarun nan ba wai dadi ne ya boye shi ba, ko kwanciyar hankali. Sam ma zai iya cewa tun shekarunsa biyu a American rabonsa da kwanciyar hankali, wato tun haihuwar Abulkhair. Matsalar rashin lafiyar Mu’azzam bai taba barinsa cikin kwanciyar hankali ba, bai barshi ya tara komai ba, kawai dai ya fi karfin abin da iyalinsa za su ci da bukatocinsu, sai gidan da ya mallaka da abin hawa. Shi ma wani babban mai mulki a siyasar kasar da yake aiki a karkashinsa ne ya mallaka masa su.
Komai na rayuwarsa a American da iyalinsa ya fede wa mahaifinsa, amma ya zaftare duk wani abu da ya shafi rayuwar Mu’azzam, saboda shi kansa ba ya son tunawa, kuma ba zai iya tattauna wannan al’amarin da kowa ba ban da Abulkhair, Zulaiha kuwa ba don rashin yafiyarsa gare ta da yin Allah ya isa gare ta a kansa zai kare ba, da sai ya yi mata.
Hira ce aka yi tsakanin uba da Da irin wacce ba a taba yi ba. Malam ya fahimci rayuwar dan nasa sosai, ba wai daular duniya ta boye shi ba, shi ma a can inda yaken matsaloli ne dankare tare da shi. Ba za a sanya Ishaq Raazee matsayin attajirai a Amurka ba, amma yana da rufin asirinsa irin na diaspora.
Kyakkyawan lodge da rantsattsun motocin hawa guda uku. Ga parmanent aikinsa a hannu. Sannan matarsa da ke aiki da babban bankin kasar Amurka ta fi shi tara abin duniya. Aikin Mu’azzam da kamfanin man fetur na CHEVRON CORPORATION ya kara taimakawa wajen rufuwar asirinsu. Kasancewar Mu’az din wani mutum da bai san dadin abun hannunsa ba, saboda ba shi da buri, ba shi da future planning a kan komai. Aikin ma yana yinsa ne don kar ya zauna ba ya komai, yana kuma biyan kudin hayar mansion din da yake ciki.
Shi yake biyan kudin makarantar Abulkhair baki daya, duk da cewa abin da yake biya din babu yawa kasancewar Abulkhair dan kasa ne, a can aka haife shi, duk cikinsu shi kadai ne mai nationality din Nijar, ba zai iya manta wahalar da Daddy ya ci a kan nasa karatun ba lokacin yana consulate officer karkashin ofishin jakadanci na kasar Nijar a kasar Amurka, lokacin Daddyn ba shi da hanyar samu mai yawa. Don haka zai iya cewa yana da buri a kan DADDY, ya kasance cikin wadata shi da wadanda suka shafe shi da kannenshi. Bayan wannan ba shi da wani solemn buri a rayuwarsa. Daga sanda ya fara aiki da Chevronya dauke wa Daddy hidimar lafiyarsa.
Sai da suka gama hirar suka soma labarin ‘yan uwa na nan kasar da Mansour da ke Nigeria. Mahaifin nasu ya tambaye shi ko shi ne ya sanya Mansour ya ba shi rikon Aalimah? Nan ya yi masa bayanin yadda komai ya kasance. Cewa, Mansour din a kan-kansa shi da maidakinsa suna da burin Aalimah ta yi karatun a Boston jami’ar da mahaifin maidakinsa ya yi ce. Ya gaya masa tun kafin hakan ya sha rokon Mansour ya ba shi yaran guda biyu (Aalimah da Aboubacar), amma ya ki. Sai kuma ga shi shi da kansa ya neme shi ya gaya masa ya samo mata scholarship a garin da yake. Malam ya jinjina son boko irin na Mansour a wasu lokutan har ya fi Ishaq muhimmanta ilimin boko. Kamar daga sama mahaifin nasa ya jefo masa tambayar da ta birkita shi.
“Me ke damun takwarana Mu’azzamu? Kun dade kuna ce da ni ba shi da lafiya, amma daidai da rana daya daga kai har shi ba wanda ya taba bude baki ya gaya min hakikanin me ke damunsa. Ban taba ganinsa da wasu kamanni ko alamomi na mara lafiya ba. Karewa ma duk ya fi ku kyakkyawan tunani da tsinkaye. Ya fi ku son zumunci da muhimmanta shi. Rashin lafiyar me ku ke cewa yana yi da har ya sanya ku yi masa wani irin aure da har gobe ba mu ji karshensa ba? Sannan me ya hana shi yin aure a halin yanzu a wannan gabar ta rayuwarsa?â€
Gumi (zufa) Daddy Ishaq ya shiga tsattsafarwa daga kowanne sashe na jikinsa, ya kuma kasa amsa tambayoyin mahaifinsa. Malam din ya tsura masa ido, ya kuma fahimci halin rudanin da maganganunsa suka jefa dan nasa. Take wasu tunaninnika marasa dadi suka shiga darsuwa a ransa. Ya kaurara murya ya ce, “ISHAQA!â€
Ya dago a hankali ya dubi mahaifinsa.
“Mu’azzamu kanjamau gare shi ko (yana nufin acquired immune deficiency syndrom)?â€
A firgice Ishaq Raazee ya ce,
“A’ah, non, quite non, pereâ€.
Yana ganin yadda mahaifin nasa ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya, ya lumshe idonsa irin na samun kubuta daga tunanin da ya dade yana wahalar da mutum. Sannan ya ce,
“Gaya min gaskiya, shi ba namiji ba ne to?â€
Cikin yamutsa fuska da rashin fahimtar hausar ya ce, “Malam, kamar ya ya shi ba namiji ba ne?â€
Sai Malam din ya sauya harshe, ya yi masa bayani yadda zai gane da abzinanci. Yana nufin wanda ba zai iya biyan bukatar auratayya ba. Ya fada masa gaskiya, in wannan ce matsalar Mu’azzam ba wani abu ba ne, babu irin maganin da bai sani ba a rayuwarsa, in ma shi bai sani ba, to ya san inda zai kai shi a yi masa maganin lalurar a Tessoua. Daddy ya rasa yadda zai yi. Bai san wane bayani zai masa ya fahimta ba. Lalura ce irin wadda bai taba sani ba a duniyarsa, kuma za ta yi masa wuyar fahimta. Nan dai ya tabbatar masa wannan ba ita ce matsalar Mu’azzam ba, sannan ya yi ta kame-kame. A karshe ya ce, likitoci suna kan bincike da sun fadi sakamako zai gaya amsa. Amma ya tabbatar masa ya kwantar da hankalinsa, Mu’azzam ba ya tare da ko daya daga cututtukan da ya ambata a sama.
Suna haka sauran ‘ya’yan Malam suka soma shigowa shigifar daya-bayan-daya daga gidajensu, daga unguwanni daban-daban da suke zaune a nan Niamey (Yamai). Daga ‘yan cikin Innarshi zuwa na Inna Bintou abokiyar zamanta. Kai ka ce Larabawan Kuwait ke shigowa suna zazzaunawa. Musabiha ce ta rika gudana tsakanin Ishaq da ‘yan uwansa, sai tambaye-tambayen lafiya da iyalin juna. Su goma sha tara cif! Sauran shidan mata ne a gidajen aurensu. Mansour da ke Nigeria ne kawai babu a cikinsu yau.
Cikin su mutum biyu ne suka girmi Ishaq, Uncle Edrissa da Uncle Oussama, wadanda suka kasance sun fito ne daga ciki daya, ragowar duka kannensu ne. a mazan akwai wadanda ba su kai ga yin auren fari ba suna karatu, sun biyo Ishaq da Mansour. Amma a nan jami’ar Abdou-moumoun babbar jami’ar kasar Nijar.
Ranar ta zamo wata ranar reunion ta iyalin RAAZEE. Matan ma da ke gidan aure duk sun zo wajen Yayan nasu da suka dade ba su gani ba, da kyawawan ‘ya’yansa wadanda suka dauko gida a kamanninsa.
Da daddare bayan kowa ya koma gidansa dakin Inna Kasisi ya koma. Ya ce, shi ba abincin wanda zai ci sai nata. Murmushi ta yi da ta tuna wani abu, ya fi kowa son girkinta. Har satar dumame yake mata tana barci, in kuma Mansour ya cinye masa abinci kafin ya dawo yana cin uban duka. Bai sani ba tun tafiyarsa dakin Malam ta shiga kicin ta shirya masa lafiyayyen abincin abzinawa na asali. Ya ci ya yi hani’an kamar mai yin cin biyan bashi.
Washegari ya gaya wa Yayansa Uncle Oussama yana so zai je Tessoua da Zinder son samu har Arlit ya kai yara su ga asalinsa da dangin Inna da ke can, da na Malam. Uncle Oussama ya bada mota Hilux da suke shiga sahara da ita, da kuma dansa Hamoud ya tuka su, ya fi kowa iya tukin mota a gidan, kuma ya saba shiga garuruwa da sahara tare da Malam.
Tun suna tafe kan kwalta har ta soma bacewa ganinsu. Tafiya ce suke ta yi cikin rairayin sahara. Aalimah na kallon yanki da bigire na tsatson mahaifinta tana jin wani shauki a zuciyarta. Tafiya ce mai dadi da ta sanya nishadi a zukatansu. Ga guzurin abinciccika kala-kala a warmers da ababen sha masu sanyi a coolers Inna Kasisi ta yo musu. Duk wanda ya ji yunwa zai bude ya diba ya ci ya sha. Tafiya aka ce yankin azaba, kuma mabudin ilmi. Tsananin ranar kasar Nijar da zafin rairayin sahara ya sanya ita kanta A.C din motar ta daina bada wani sanyi mai karfi. Ba abin da Aalimah ke so a wannan tafiya irin kallon rakuma da makiyayansu, Daddy na ba su labarin kuruciyarsu da yadda suke taya mahaifinsu kiwon nashi rakuman a Tessoua, garin da za su je.
Tafiyar awanni masu yawa ta kawo su birnin Tessoua.Tessoua na daya daga cikin manyan birane goma da kasar Niger ke ji da su. Hamoud ya dauke kan motar ya shiga unguwar da za su, har kofar wani gidan laka mai cike da yawan dabbobi da almajirai fal! A kofar gidan Mazaje ne suna daukar karatu tare da wani dattijo. Wannan shi ne ainahin gidan kakannin su Daddy, wato gidan iyayen Malam Raazee. Dattijon da ke bada karatun shi ke amsa sunan Malam Yahyya, kani yake ga Malam, shi ke zaune a gidan yanzu da iyalansa, sai sauran ‘yan uwan Malam da iyalansu duk a gidan suke kasancewarsa babban gida na gado.
Sun samu kyakkyawar tarba daga jama’ar gidan, abinci kala-kala na abzin, rago guda aka gashe musu don Malam Yahya ya san da zuwansu. Har gonar kiwon kakansu an raka su. Su Basma ‘yan Massachusetts yau an yi kwanan gadon alawayyo. Sauro ya ci rabonsa ya more. Sun ga dangi-dangi sun gansu. Washegari da safe Hamoud ya cika tankin motarsu da mai tatul suka kama hanyar Zinder.
Tafiyar sai ta zame musu tamkar ta yawon bude ido, ga Hamoud da ke yi musu bayanin ko’ina. Basma da Khaleesat, sai suka bude wayoyinsu suka shiga recording abubuwan da suka burge su. Zinder babban gari ne, kuma jiha mai tarin al’umma masu ethnic group daban-daban.
A gidan iyayen Inna Kasisi suka sauka, nan ma an musu tarba ta musamman duk da ba su san da zuwansu ba. Daddy ya bi ‘yan uwa lungu-lungu ya yi musu alheri mai yawa, kamar yadda ya yi a Tessoua. Kwana biyu suka yi harama suka dauki hanyar Arlit. Awanni masu yawa a tsakani suka isa. Arlit nan ne tushen su Inna Bintou kishiyar uwa, wadda ta zame musu babu maraba da uwa mahaifiya. Ta ba su kulawar da ba su samu daga mahaifiyarsu ba, don haka tana da matsayi sosai a wurin ‘ya’yan Inna kasisi. Nan ma Daddy ya yi alheri sosai, don duka dangin nasu tun daga na Tessoua, na Zinder har nan na Arlit suna cikin yanayin rayuwa, abin sai godiyar Allah. Daddy yana shan mamaki in yana jin sunan Mu’azzam a bakin danginshi sosai, ba wanda bai sanshi ba, ba wanda ba ya yi masa addu’ar alheri saboda taimakon da yake musu, wanda Daddyn ba shi da masaniya sam. Jinjina kai yake yana sanya mishi albarka cikin zuciyarsa.
Sun baro garuruwan bayan Hilux dinsu cike da tsarabobi kala-kala na abubuwan amfani, irin nasu. Da suka dawo Niamey ma ba su huta ba, zagaye suke na gidajen ‘yan uwa.