AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

A can kasar America kuma Abulkhair ya kira wayar Aalimah a karshen satin kamar yadda ya saba, inda gidan wayar Verizon wareless suka tabbatar masa ba’a amfani da layin, ya kira na Basma shi ma haka, sannan na Khaleesat, shi din ma dai babu. Tsoro da fargaba har ma da mamaki suka kama shi, musamman da ya gwada na Daddy shi ma haka. Wuninsa guda yana abu daya, amma ya kasa samun kowannensu. A karshe ya gwada na Mummy. Cikin sa’a sai ya same ta. Ya tambaye ta ko me ya samu wayoyin Daddy da na su Basma ya kasa samunsu? Nan take gaya masa ai suna Nijar yau satinsu daya. Ya ce ta ba sh lambar da ta ke magana da su.
Tsaki ta yi, ta ce, ita tunda suka tafi ba su yi waya ba, ba ta da lokacinsu. Ya san halin Mamanshi sarai in ya ci gaba da damunta, za su yi ta ba dadi, dole ya hakura, a kalla hankalinsa ya kwanta tunda lafiyarsu kalau. Ya ci gaba da rubuta jarrabawarsa cikin nutsuwa. Sai dai fa Aalimah na ciki kowanne bugun numfashinsa, tafiyar tasu ta tabbatar masa Daddy (takes the first step) ga gyaran rayuwarsa da iyaye da ‘yan uwansa.
Ana saura kwana uku su tafi Inna Kasisi ta kira manyan ‘ya’yanta da na Bintou maza, da shi Daddyn a babban falon Malam Raazee, shi ma Malam din yana zaune. Cewa ta yi Malam ya bude taron da addu’a, akwai damuwa a fuskar Daddy Ishaq don har zuwa lokacin Innar ba ta gama sake masa sosai ba. Kuka Inna Kasisi ta saka wani abu da ta dade ba ta yi shi ba, mace ce mai taurin zuciya kwarai da nuna ba ta da damuwa a kan komai, ko da tana da damuwar. Hankalin manyan ‘ya’yanta ciki har da Daddy ya yi matukar tashi. Lallashinta suka shiga yi suna rokon ta fada musu damuwarta, sun yi alkawarin magance mata ita muddin ba ta fi karfinsu ba. Sai da ta yi mai isarta, sannan ta ce, ba ta yarda Ishaq ya koma Amurka ba, ko dai ya kara aure ya bar matar a nan tare da su, shi ya koma din inyaso ya dinga zuwa in ya samu sarari, ko ya baro Amurka bakidaya ya zo ya zauna cikin ‘yan uwansa tare da iyalinsa.
Zufa ce kawai ta lullube Daddy, saboda cikin zabin nata duka babu mai sauki. He has a life where he live, a career, a family and everything. Ko zai baro Amurka ba lokaci daya ba. Zabinta na biyu kuma karin aure wani karin nauyi ne a gare shi da bai san yadda zai yi ya dinga sauke shi ba.
Bai ma taba hasaso wa kanshi irin wannan rayuwar ba (polygamy), duk da ita ya taso ya tarar a gidansu. Shirunsa ya sanya kowa da ke dakin ma ya yi shiru, ita kuma Inna ta ci gaba da sharbe. Malam ya yi gyaran murya don katse shirun, ya ce,
“To Ishaqu ka ji bukatar mahaifiyarka a kanka, wannan karon ina bayanta, kullum na kasance cikin bin ra’ayinku in dai bai saba wa addini ba, ina hana ta nata hakkin na uwa. Ka kara aure matar ta zauna da mu, ko ka dawo gidaâ€.
Da kyar Daddy ya iya hadiyar miyau, sannan ya muskuta, “Malam da Inna na ji batunku. Da man kowanne bakon haure a kasashen ketare dole watarana zai dawo gida. Ina da wannan niyyar ko Inna ba ta furta ba, amma ba zai yiwu a lokaci daya ba. Duka yaran karatu suke yi ba su gama ba, Mu’azzam ne kadai ya tsaya da kafafunsa.
Ni kuma sai ya kasance ina da abin yi a nan din kafin in dawo, don ba zai yiwu in zo in zame muku lalura ba. Magana ce ta WATARANA da babu wanda ya san wace rana ce. Maganar karin aure kuma Inna ni yanzu tsofai-tsofai da ni wane aure zan kara?
Gidana babu ko dakin ajiye mace, in kuma na ce a nan zan ajiye ta yanayin aikina ba zai bari in dinga zuwa akai-akai ba, zai zama akwai zalunci a ciki ta fannin matar. Inna ko za ki fadi wata alfarmar in yi miki bayan wannan?†Ya fada cikin taushin murya mai cike da ladabi da kwantar da kai, hadi da lallashi.
Amma budar bakin Inna kasisi sai cewa ta yi, ita ta riga ta gama magana, har ta tanadar masa matar, ta ji ta yarda ba zai iya dawowa Niamey yanzu ba, amma dole ya auri GUMSU!
Wata sabuwa inji ‘yan caca, shuka tsakiyar rani!
6/28/21, 7:33 AM – Buhainat: &&&&&&&&&&
17
Gumsu kanwa ce ga Inna Bintou, ba’abziniyar Arlit ce, mijinta sojan sama ne, ya rasu a wani hadarin jirgin sama da ya faru a kasar Kenya a shekarar da ta gabata. Ya barta da yara biyu. A hannunshi ta samu ta yi karatun boko mai zurfi a France inda aka tura shi yin wani course na tsawon shekaru uku, inda ta samu ta hada digiri na farko a fannin pastry art. Sun yi aure da uban ‘ya’yanta bayan kammala sakandirenta. Zamansu a birnin Paris ya sanya mata sha’awar shiga makaranta. Ashe da rabon zai amfane ta a gaba. (Aah toh zama da Mummy ai sai wanda ya je makaranta)
Cikin ‘yan uwansa kaf! Wadanda ya girma da wadanda suka girme shi babu wanda ya goyi bayansa kan kin bin umarnin Inna, ashe cikinsu babu wanda ba shi da cikin Zulaiha kan yadda ta raba su da dan uwansu. Ganin ba shi da zabi in dai yana so ya yi rabuwar lafiya da Inna ban da amince wa bukatarta ya ce ya amince da maganar auren, amma zai je ya shirya sai ya dawo a yi maganar auren. Inna ta yi tsalle gefe ta ce sam! Ba ta amince ba. Kafin ya tsallake boarder din Nijar zuwa wata, za a yi auren nan.
Daddy ba shi da zabi ban da amincewa don son gamawa da iyaye lafiya. Amma fa yana hango kanshi da mata biyu, ko ya ya zai yi da su? Ya tuno kishi irin na Mummy Zulaiha da ko kyakkyawar gaisuwa ba ta bari yayi da mata, yau ita za a yi wa kishiya? Sai kuma yaji wani murmushi ya subuce mishi. Watakila sanadiyyar hakan ya yi silar daidaituwar halayenta masu ci masa tuwo a kwarya, musamman aikin bankinta wanda ya sanya kwata-kwata ba ta da lokacinshi balle na ‘ya’yanta, sai ko a karshen mako kadai.
Sai da ya daga booking dinsu zuwa wani satin, saboda maganar auren.
Inna ta so ya fara zuwa su daidaita da juna kafin daurin auren, ya ce shi ba shi da bukatar hakan, ba sai ya ganta ba, in dai ta yi mata (Innar) ta kuma yarda da tarbiyyarta, to a yi. Murmushi Inna ta yi tana fadi cikin ranta, za ka zo da bayani yaro. Matan abzinawa ka ke jin labari.
Su Uncle Oussama sun tafi har Arlit sun karba wa dan uwansu Ishaq auren Gumsu. Da sadakin manyan rakuma goma, sun kuma dauko ta sun taho da ita Niamey.
Duk abin nan da ake, Aalimah da su Basma ba su san wainar da ake toyawa ba. Sai zuwan amarya Gumsu dakin Inna Kasisi tare da matan Uncle Edrissa, Fatsume da Fattu. Gidan ya soma cika da matan ‘ya’yan gidan sun zo karbar amarya. Abinci na musamman Inna Bintou da Inna Kasisi suka shirya wa amarya da ‘yan uwanta da suka rako ta, kodayake abin nasu duk na gida ne, dangin Inna Bintou ne wadanda duk familyn an sansu.
Aalimah da Basma na dakin ‘yammatan gidan, Rumana kanwar Balkisa na yi musu kalba kanana ta tafiya, ba su san an daga tafiyar ba sam. Balkissa ta shigo da gudu kamar an jefo ta, tana fadin, ‘Amaryar Oncle Ishaq ta zoâ€. Cikin harshen Faransa.
“Amarya?†Su duka biyun suka tambaya a tare with astonishing tone. Balkissa da Rumana ma har suna hada baki wajen ba su amsa, “Au? Ba ku san Baban Basma ya yi amarya ba? Gumsu kanwar Inna Bintou?â€
A tare Basma da Aalimah suka mike tsaye, Basma cike da tsoro, mamaki da firgita amma ita Aalimah ba ta san a wane yanayi ta karbi labarin ba. Khaleesat ta fado dakin daga yawon da ta tafi tana fadin,
“Gidan nan yau a cike yake da mata kamar gidan bikiâ€.
“Bikin Babanki akeâ€. In ji Rumana.
“Wanne Baban nawa? Kin san Babannin gidan nan yawa gare suâ€.
“Wanda ya haife kiâ€. In ji Balkissa.
Khaleesat ta zame ta zauna a kan kafafunta bakinta na marmar yana fadin,
“In wasa ki ke ina rokonki ki bariâ€.
Rantsuwa Balkissa ta hau yi tana gaya musu, ai an kwana biyu da yin maganar, ta ji Babanta yana gaya wa Mamanta ta dauka ma sun sani.
Kwasa suka yi dukkansu da gudu suka yi sassan matan gidan don ganewa idanunsu. Ya kuma tabbata gare su; Daddy ya kara aure, sun kuma yi nasarar ganin fuskar amaryar, wata tsaleliyar sambaleliyar ba’abziniya, gashinta har duwawunta. Ya sha ado ko ta ina. Tana nannade cikin laffaya.
Jikin Basma ya yi sanyi, ta rasa me ta ke ji a ranta game da al’amarin. Tausayin Mummynta ko taya Daddynta murnar samun wannan hadaddiyar mace? Khaleesat muraran ta nuna kishi tun daga kwayar idanunta har furucinta,
“Da ma Daddy ya kawo mu gidansu ne don mu halacci bikin aurensa shi ya sa bai damu ba da Mummy ta ce ba za ta zo ba?â€
Dakin da Daddy Ishaq ya sauka a cikin gidan wanda ciki da falo ne, an yi shi ne don saukar baki, can aka kai amarya Gumsu, bayan ta huta ta yi sallah ta ci abinci.
Khaleesat kayanta ta hau kwasa babu ko ninki tana dannawa a jaka, ita gobe za ta koma America ba zuwa ta yi ta taya Daddy honey moon ba. Basma ta fidda hannu ta kwashe ta da mari, sannan ta ce, “Ki san irin kalaman da za ki dinga furtawa a gare shi, ba sa’anki ba ne, ba abokin wasanki ba ne. Ubanki ne! Yana da damar auren mata uku bayan Mummy, Ubangiji ya lamunce masaâ€.
Sosai Khaleesat ta saki kuka ta fada jikin Aalimah, yayin da Aalimahn ta rungume ta tana lallashinta. Ita ma nasiha ta shiga yi mata kan ta fidda kanta daga cikin al’amarin kada ta bi bayan kowannensu. Tare ta taso ta gansu, kuma kowannensu yana da hakki a kanta, ta yi masa adalci.
Daddy Ishaq ya shiga dakin amaryarsa Gumsu (Moiram) ya karbi kyakkyawar kyautar da ta yo mishi guzurinta, irin wadda bai taba zaton akwai a diya mace ba. Wayewar garin kuma ya sha albarka daga iyayensa.
Sai da suka kara sati daya a kan sati biyunsu, kwananshi uku tare da amarya, ko sallar jam’i da kyar ka ke ganinshi, ta asubah kuwa bai kara samun ko daya ba, a daki yake yinta tare da matarsa.
Ana i-gobe za su tafi ya tadda Malam da Inna a gefensa a turakarsa suna cin abincin dare ya zauna ya dukar da kai. Malam ya yi ta tsokanarsa, wai sai kyallin goshi yake yi, ga kamshin jikinsa ya karu. Shi dai murmushi yake yi, sannan ya fadi abin da ya kawo shi. Yana so zai tafi da Gumsu tunda ba a kammala gyaran sashin da za ta zauna ba. In ya samu hutun wata shekarar zai dawo da ita, ko ya hado ta ita da Aalimah don ya yi mata alkawarin zuwa Nigeria in ta gama shekararta ta farko.
Hamdala Inna ta rinka yi a zuciyarta, ko banza ta samu ta dinga ganin danta akai-akai, ko wani bangare da ya shafe shi. Ya gaya musu ya yi processing din visa dinta, yana jira ta fito, don haka zai sanya yaran a jirgi su tafi gobe saboda makarantunsu, shi kuma zai jira visar Gumsu su koma tare. Inna ta kara jin dadi a cikin ranta.
Washegari shi da Hamoud suka kai yaran filin jirgin saman Diori Hamani. A kujerar gaba yake Hamoud na tuki. Yana lura da yadda yanayin kowaccensu yake, Khaleesat fuska ba rahma sai cin fushi ta ke. Basma ta zama mara karsashi, wannan surutu da karadin duk babu shi. Yesmin nata fama da choculates da biscuits dinta. Aalimah, tana cikin yanayin da ba za a iya fassarawa ba, sai dai ga duk wanda ya santa da yaran zai fahimci canzawar walwalar yaran ne ya yi affecting mood dinta. Gyaran murya ya yi lokacin da suka shiga receptionna filin jirginsuka zazzauna a kan kujerun jiran saukar jirgi, ya dube su dukkaninsu.
A nitse ya kira sunayensu, kowacce ta amsa. Sannan ya ce Yesmin ta je wajen Hamoud. Ya dawo da hankalinsa gare su, ya soma magana irin ta uba mai cikakken iko a kan ‘ya’yansa.
“Iyayena sun min aure saboda su tabbatar da suna da amfani cikin rayuwata, kuma suna da iko a kaina, kamar yadda na san ina da iko a kanku. Aure sunna ce ta ma’aikin Allah sallallahu alaihi wasallam. Abu ne da ake yinshi ba don son zuciya ba. Na karbi auren da iyayena suka umarce ni da shi da hannu bibbiyu don bin umarnin Allah da ya yi umarni da a yi musu biyayya don samun rabauta duniya da lahira ba don bana son Babarku ba, ko don in tozartata. Don haka bana fatan hakan ya kawo sauyi cikin mu’amalata da ku, har ma da mahaifiyarku. Ruwanku ne ku je ku gaya mata kafin zuwana in yi mata bayani yadda za ta fahimta. Ruwanku ne kuma ku fidda kanku daga ciki tunda da ni da ita kowanne mai hakki ne a kanku. Ruwanku ne ku sauya akalar rayuwarmu zuwa mai kyau ko mara kyau sabida na yi aure don cika sunnar Ma’aiki da son gamawa da iyaye lafiya. Ku tashi ku shiga jirgi, Allah ya yi muku albarkaâ€.
A salube kowacce ta mike ta dau jakarta, don fasinjoji na ta wuce su tun dazu suna shiga jirgi. Aalimah ta kamo Yesmin suka yi sallama da Hamoud. Daddy na tsaye a inda yake hannayenshi zube cikin aljihu, idonsa kyar a kansu. Har sun bi sahun masu shiga jirgin, Basma ta juyo suka hada ido. Murmushi ya yi mata, sai ta saki trolley dinta ta dawo da gudu ta rungume shi, ta sumbaci goshinsa. Ganin haka Khaleesat ma ta dawo ta rungume shi tana hawaye. Tausayinsa ta ji sosai da nadamar abin da ta ke yi da farko. Ta kuma yardar wa zuciyarta Daddy bai zo Niamey don ya yi aure ba, Allah ya rubuto masa auren ne cikin kaddararsa. Babu kuma wanda ya isa ya tsallake kaddararsa, amma ba don ya daina son mahaifiyarsu ba.