AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@
Al’amari in dai tsakanin Zulaiha da Ishaq Raazee ne, to dan Adam ka koma gefe kawai ka yi kallo. Ba karamar soyayya ce a tsakaninsu ba, wadda aka gina tun tali-talin kuruciya.
Kwanan Daddy biyu a gidan Mu’az asabar da lahadi ya ya aka yi, ya ya aka yi? Ko su Abulkhair ba su sani ba, sai ga su sun dawo tare su ukun. Shi dai Abulkhair dan kallo ya zama in ya tuna duk irin lallashin duniya da suka kwana uku suna yi wa Mummyn shi da Yayansa Mu’azzam, kan ta yi hakuri ta koma dakinta, ta kau da ido daga auren Daddy. Amma ta ki sauraronsu ta bude wa Mu’azzam wuta ya nema mata visa zuwa kasar da Ishaq ba zai kara sanin tana (existing) ba. Dalilin Abulkhair na kiran Daddyn kenan, wanda da farko ya yi niyyar ba ta sarari har sai ta gaji da zaman gidan Mu’azzam din ta dawo don kanta.
Amma darajar ‘ya’yanta da tunanin da ya yi, kada su ga ya wulakanta musu uwa don ya yi aure ya sa ya sauya niyya ya je din. Shi kadai ya san irin lallashin da ya yi mata har ta sauko. Abin har dariya yake bai wa Abulkhair, yana tuki yana jinsu suna ta muhawara kan ita ba ta yarda Gumsu ta zauna mata a gida ba, shi kuma yana nuna mata tarin alfanun da zaman nata tare da su ke da shi, in kuma ba ta amince ba, to ta ba ta yaran bakidaya tunda ita da ma ba wani zaman gidan ta ke yi ba. Nan ma ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta yarda ba. Gumsu ta koma Nijar kawai ta yarda duk shekara ya je. Shi kuma ya ce, wannan rashin adalci ne.
Ya gaji da lallashinta, zai yi abin da ya ga dama. Zai kama wa Gumsu gida kusa da su, amma zai raba yaran biyu ya ba ta rabi, tunda ita ba ta san abin da zai taimake ta ba sabida kishin banza.
Ba tarbiyya ba ce iyaye na magana ‘ya’ya su sa musu baki ba tare da sun yi umarni a gare su da hakan ba, amma da ya ba wa Mummynsu shawarar ta kyale Gumsu ta zauna tare da su, amfani ne mai yawa a gare ta.
Sanda suka iso, yaran ba su dawo daga makaranta ba. Sai Gumsu kadai a kitchen gida ya turnike, ya hautsine da kamshin girkin abzinawa, ga shi ta bi ko’ina na gidan ta turare da turaren wuta mai dadin kamshi a burner. Ta yi musu sannu da zuwa, ta gaida Mummy, amma ko kallonta ba ta yi ba ta haye sama. Abulkhair sai ya ji ba dadi, yanzu ne ya kalli matar sosai, mace mai tarin nutsuwa da kamala. Kyau kuwa ba a magana, ga ta nan irin Aalimahrsa, in Aalimah ta yi shekarunta she will look exactly like her. Ya tambayi kansa kenan duka matan kasar su Daddy za su kasance ababen so? Wani murmushi ya subuce masa, ya ce,
“Aunty Gumsu, I’m Abulkhair. Your second son. Wannan girkin naki mai kamshi za ki zubo min yanzu. I’m very-very hungryâ€.
Dariya ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, haka kawai ta ji saurayin ya shiga ranta. He is very smart and jovial. Ta ce, “Mon pils (Dana) ba za ka jira in shirya tebur mu ci bakidayanmu ba? Kannenka na hanyar dawowa yanzuâ€.
Ya girgiza kai, “Minti biyar nan gaba in na kara girkin nan naki bai shiga bakina ba, ulcer za ta kama niâ€.
Ta yi dariya ta wuce kitchen tana fadin, “Ina kuwa zan so ulcer ta kama min Da? Bani minti biyu Mon pilsâ€.
Kan ya shiga dakinsa ya fito ta shirya masa abincin a tebir. Ya zauna ya nada yana ta santi. A haka su Aalimah suka shigo suka same shi bai kai ga tashi daga tebir din ba.
“Welcome Monsieur Abulkhairâ€.
Basma da Khaleesa suka hada baki wajen fadi cikin bayyanannen farin ciki.
Yesmin na mai rugawa gare shi, Basma kansa ta tsaya, Khaleesat na gabanshi, Aalimah kuma sai ta shige dakin Gumsu da sauri tun kafin su yi ido biyu.
“Ina ka tafi ne daga dawowarmu Miami muka neme ka muka rasa?â€
A gurguje ya yi musu bayanin tafiyarsa Las Vegas, kuma Mummy ta dawo tana sama. Ai ba su gama ji ba suka runtuma saman benen har ana hankade Yesmin a kafar bene. Da ma haka yake so ya mike ya bi bayan Aunty Gumsu a kitchen.
“Aunty, don Allah zan iya shiga dakinki?†Ya fada yana sosa sumar kansa nannadaddiya irin ta Babanshi.
Moiram cikin son fahimtar me zai yi a dakin nata ta ke dubansa, sannan ta ce,
“Mu je in raka ka. Kai da dakin uwarka?†Ta wuce gaba yana binta a baya.
Tana shiga Aalimah na fitowa daga bayi, ta dauro alwalar sallar magriba, kanta babu kallabi ba ta lura da wanda ke bayanta ba ta shiga yi mata magana.
“Aunty Gumsu kin sa min wayar a caji?â€
Kalaman bakinta suka makale yayin da ta yi ido biyu da Abulkhair. Wani kallo ya yi mata wanda ya sanya ta komawa bayin. Ta rufo kofa.
Gumsu ta ce, “A’ah? Ya ki ka koma?â€
Ta juyo ga Abulkhair, sai ta ga shi ma ya juya zai fita. Ya shigo ne kawai da ma don ya ganta ko ya samu nutsuwa daga kewar ganinta na kwanaki hudun, kuma ya ganta;kanwa ta kar tsami, kwannafi ya kwanta.
“Kai ma ka koma?â€
Cikinsu ba wanda ya ba ta amsa ta dai neme su ta rasa. A shekarunta da zurfin iliminta nan da nan ta yi murmushi, ta kuma gano su. Ta kama kugu ta ce, “Inye? To tsakanin ita ko shi wane ne ba dan cikin Daddyn ba? Don in dai don ta kamanni ne dukkaninsu suna kama da junaâ€.
Ba ta da wanda za ta yi wa wannan tambayar sai Daddyn nasu. Kunyarta da suka ji ya ba ta dariya. Ta tura kofar bandakin tana ce da Aalimah, “To fito ya tafiâ€.
Hannayenta duka biyu ta sa ta rufe fuskarta. Ba ta so Aunty Moiram ta dago al’amarin nan ba,. Ta so ya yi ta zama lullubabbe kamar yadda yake a idon mafi yawan al’ummar gidan. Ga Moiram da tsokana, tun daga ranar kuwa ta sa su gaba, ba dama su kalli juna sai ta yi musu gyaran murya, don Daddy ya tabbatar mata Aalimah ‘yar dan uwansa ce. Babban burinsa a nan gaba shi ne, hada wannan aure.
Haka a daddafe Abulkhair ya karasa hutunsa ya koma Baton Rouge, babu wani sakewa da ya samu da Aalimah, kullum tana makaranta, kuma Daddy ya hana shi binta makaranta. Duk ya bi ya tsani karatun nasa da nata. Amma kullum Mu’azzam karfafa shi yake yana cewa, ya yi for his sake, ya yi don ya samu abin da zai rike Aalimah, shi ba zai ciyar masa da mata ba.
Mummy Zulaiha ta yi duk iyaka tunaninta, hange iya hange ta rasa yadda za ta yi da auren mijinta da Gumsu. In ma wani tarko ne Kasisi ta dana don maida Danta jikinta, to hakika ya yi babban kamu. Rana dai-daya ne da ba za ta ji Daddy na waya da mahaifansa da ‘yan uwansa ba. Sannan a duk yadda ta dauki Gumsun ta wuce nan, ta dauka irin illiteratematan kasarsu ne ta taka ta yadda ta ga dama, sai ta samu Moiram beyond her imagination. Cikin dan lokaci ta siye zuciyar mijin da ‘ya’yansa da kyawawan dabi’unta da cikin cin abincinsu. Hatta Yesmin yanzu tsakaninsu sai oyoyo in ta dawo daga ofis daga nan za ta sauka kasa wajen Gumsu, ba ta kara ganinta sai ta neme ta.
Ta duba ta ga cewa in ta raba Gumsu da gidan, mijin mada kyar za ta dinga ganinshi kullum, sannan yaran ba za su fasa binta inda ta ke ba, tunda idata hana su Basma ba za ta iya hana shi bata Aalimah ba. Basma kuwa ba mai iya raba ta da Aalimah a halin yanzu sai aure, sai mutuwa.
Don haka dole ta zubar da makaman yakinta na hana Gumsu zaman gidan, ta ce da Daddy ya saki gidan da ya kama za ta zauna da ita. Shi kuma da ma ya fi son hakan. Ta shiga daki ta rufe kanta kamar ta yi hauka. Ta yi kuka, ta yi kuka a karshe ta dangana, ta sallama, ta yi saranda cewa Ishaq ba nata ba ne ita kadai yanzu. Sun mallake shi ne su biyu, ba ta da dukkan karfin iko a kansa. Uwarsa ta murza kambun nata ikon, wanda ta dade tana danne mata. Da ma wai Hausawa suka ce, rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya. Ya kamata ta canza hali tun wankin hula bai kai ta dare ba. Tunda tarin ‘ya’yan da ta haifa da tsayin girman kafadunsu bai hana iyayensa yi mata kishiya ba, babu abin da ba zai iya hanawa a gaba ba. Wani abu na karshe da ta tabbatar zuciyarta da rayuwarta ba za su iya dauka ba (rabuwa da Ishaq Raazee).
To amma ta wacce hanya? Ta wacce hanya za ta bi ta gyara halin nata wanda ita a kan karan-kanta ta san ba mai kyau ba ne? Halin dan Adam yana iya canzawa ne? An halicce mu ne da halinmu; the good, the bad and the ugly. Ita ta san nata halin is not good, neither bad, but ugly mace mai raba mutum da iyayensa da ‘yan uwansa wadanda aljannarsa ke karkashin duga-dugansu ya ya sunanta? Ta kasance mai son kanta da yawa. Ta rayu tana gaya wa ‘ya’yanta dangin ubansu ba sa sonta, idan har za ta yi adalci me suka yi mata na rashin so? Ta zauna da su na lokaci mai tsawo ba su taba yi mata wani abu na nuna kiyayya ba, ita ce ma ta ke musu mugun hali.
Sosai Mummy Zulaiha ta soma kuka mai cakude da nadama da ta tuna tsayin zamanta a America ba ta taba kiran Inna Kasisi ta gaishe ta ba, ko da a waya, matsayinta na wadda ta haifa mata mijin da ta ke tinkaho da shi. Ta shiga lalube cikin zuciyarta, iyayen Ishaq da ‘yan uwansa ne suke kinta, ko dai ita ke kinsu?
Kukanta ya tsananta ne da ta tuna cewa ba ta da wata hanya da za ta gyara wannan gingimemen kuskuren nata a yanzu ba tare da an fassara shi da auren Gumsu ba, ba tare da an yi tunanin wata makarkashiya ce a zuciyarta ba sabida Gumsu-Moiram.
Yau ta yi nadamar rashin amini, kin mutanenta bai tsaya a kan iyayen Ishaq kawai ba har nata dangin babu wanda ta ja a jiki. Ba ta da kawa ko aminiya tunda mahaifiyarta ta rasu a shekarar baya.
Shi ne kadai amini, abokin shawara, mai ba ta kyakkyawar shawara duk da yana da masaniyar ba za ta dauka ba, abin da ranta ya kwanta da shi, to shi ta ke yi. Amma har kwanan gobe bai bar gaya mata gaskiya a kan yadda ta ke mu’amala da kowa ba, musamman dangin mahaifinsa. Ya taba gaya mata, Inna Kasisi ta taba ce da shi; Ban san me na yi uwarka ta ke gaba da niba. “Mummy why?â€
Wayarta ta janyo hannunta na rawa ta kira shi. Shigarsa ofishinsa kenan da sanyin safiyar litinin. Kiran nasa a daidai wannan lokaci ba daidai bane. Don haka ya rufe kansa a tankareren ofishin sa wanda ke cikin kamfanin man fetur na ChevronCorporationreshen jihar Las Vegas ya amsa kiran mahaifiyarsa with utmost respect.
“Mu’az, ina cikin wani hali. Ta kare min. Komai ya kare mini, ga kishiya ga mugun hali. Ka yi hakuri na san ba ka da lafiya, amma kullum cikin kara maka damuwa nake da matsalolina wadanda kullum ni nake janyo wa kaina su…â€. Ta saka kuka.
Zama ya yi a lallausar kujerarsa baka wuluk! Ya yi loosing tie din wuyansa. Fahimta yake tattarowa ya sanya wa kalaman Mummy, don ya gane inda matsalar yau kuma ta sa gaba,she is always in trouble with her husband, kuma in ya ba ta shawarar ba ta dauka. Wannan baya hana gobe ta sake neman ya bata shawarar. Wannan ba ya hanawa gobe ta kwaso sabuwar matsalarta ta kawo masa. Yana jin dadin yadda ta maida shi aminin ba ta kama gurbatattun kawayen zamani ba.
Duk da in an dubi amintar tasu ta tsakanin Da da mahaifi ce, tana gaya masa ne don ta ji saukin damuwarta ba don ta yi amfani da abin da zai shawarce ta ba. Amma yau ji ta ke ko me Mu’azzam ya ce ta yi, za ta yi ko ba ta so, don ta zauna lafiya ta dawo da martabarta a idanun mijinta.
“Mummy me ya faru?â€
Ya tambaya da kwantacciyar murya cikin tattausan turanci, wanda ya kama harshensa fiye da kowanne yare, sabida rashin abokin yin wani yaren bayan shi. In ka ji yana Hausa ko French, to ya je Nijar ne, ko yana magana da Monsour Razee, kanin mahaifinsa mai matsayin uba da aboki.
Ta sassauta kukanta, ta gaya masa duk halin da ta ke ciki bayan sun dawo. Halayen Gumsu da yadda Daddy yake martaba ta. Ta ce, ba wai ya sauya mata ba ne, amma ta lura ba ta da martaba da tasiri mai sosai a zuciyarsa, yanzu ya fi muhimmanta ‘ya’yansa da Gumsu. Ta gaya masa ta gane dukkan halayenta ba masu kyau ba ne a al’adar Malam Bahaushe.
Tana so ta gyara ta rasa hanya. Ba ta so a alakanta canzawarta da wanzuwar Gumsu. Tana so ta gyara tsakaninta da Inna Kasisi da Malam Raazee. Tana matukar nadamar watsar da su din da ta yi da rashin daukarsu da daraja. Ko ba a fada mata ba ta san halinta ne ya sanya Inna Kasisi tursasa wa Daddy yin aure. Ya ya za ta yi ta dawo da kyakkyawar alaka ta mutuntawa da girmamawa a tsakaninsu???â€