AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Inna Bintou da Inna Kasisi, sune matan Malam Raazee. Ishaq da Mansour ‘ya’yan Kasisi ne, wato uwargida. Haihuwa suke kusan duk shekara, don haka ‘ya’yan Malam Ibrahim ashirin da biyar a duniya kafin haihuwar ta tsaya wa matan nasa. Ishaq ba shi ne babba ba a ‘ya’yan Kasisi, yana da yayye har biyu, sannan shi, sai Mansour.
Ba duka ‘ya’yan Malam Razee ke son karatun boko ba, hasalima mazan duka ba sa so, sun fi son sana’ar mahaifinsu in ka cire Ishaq da Mansour, matan kuwa suna gama sakandire yake yi musu aure. Dalili kenan da sanda Ishaq ya zo masa da maganar ya samu matar aure a Nigeria yana so ya yi aure bai ja zancen da nisa ba, shi ya ma fi son hakan. Sai ya tuntubi Mansour ko shi ma yana da wadda yake so a hada? Ya ce shi kam ba yanzu ba, sai ya gama karatu.
Ishaq da Zulaiha sun hadu a jami’ar Ahmad Bello, kanwar wani course mate dinsa ce Ahmad Madobi, ‘yan asalin jihar Kano ne. Lokacin yana aji biyu a jami’,Zulaiha da ‘yan gidansu suka zo wajen Yayanta Ahmad, a lokacin yana tare da Ishaq Ba’abzine (kamar yadda suke kiransa). Abin nan da Turawa ke kira ‘love at first sight shi ya afku tsakanin Ishaq da Zulaiha.
Zulaiha baka ce (black beauty), yarinya danya sharaf ‘yar saandire. Iyayenta ba ‘yan boko ba ne, ‘yan kasuwa ne. Har Kano Ishaq ke zuwa daga Zaria wajen Zulaiha. Wata irin zazzafar soyayya ce ta shiga tsakaninsu, wadda ta sa iyayenta gwammacewa su cire ta daga makaranta su yi mata auren, don kuwa ta yi watsi da karatun ta kama Ishaq. Sai aka yi sa’a shi ma nashi iyayen ba masu tsattsauran ra’ayi ba ne a kan karatun, suka yi musu aure.

Hankalin iyayeyn Zulaiha bai tashi tashi ba sai da iyayen Ishaq suka ce Nijar za su tafi da ita can main house din su. Sun dauka tunda yana Nigeria bbai gama karatun ba haya zai kama su zauna. Daga karshe ba su da yadda za su yi, sun aminceAURE ba inda ba ya kai ‘ya mace, suka amince Ishaq ya tafi da matarsa kasarsa ta haihuwa, ya baro ta tare da iyayensa ya dawo makaranta ya ci gaba da karatunsa cikin kwanciyar hankali, tunda ya mallaki abin da zuciyarsa ke so.
A irin zaman amincin da ake yi tsakanin Inna Kasisi da Inna Bintou, ‘ya’yan wannan sune na waccan, sai ya zama cewa, Zulaiha surukar Bintou ce ba surukar Kasisi ba. Ita ke kula da al’amarinta tunda mijinta ba ya nan. Malam Razee bai ragi Zulaiha da komai ba ta fannin bukatunta tamkar mijinta na kusa da ita, makarantar da ta ke yi ma ta kudi ce, wadda shi ya sanya ta a can Yamai, har ta gama sakandire.
Sai dai sam Inna Bintou ba ta jin dadin surukuta da Zulaiha, sabida baudaddun halayenta;Yarinya ce mara godiyar Allah da fadin rai. Duk abin da suke mata a raine ta ke kallonsa ba ta godewa, ba ta jan jikokinsu a jiki, ba yaron da ya isa ya shigar mata daki. Ba ta taimaka musu da komai na hidimomin gida, ga ta da girman kai da raini ga kowa. Inna Kasisi kawai ta ke shakka a gidan, don ita kam ko kusa ba ta daukar raini, tana da zafi. Hatta ga ‘ya’yanta, mijinta ma lallaba ta yakeyi. Ita da kanta ta fahimci wasu daga halayen Zulaiha ba tare da Inna Bintou ta ankarar da ita ba. Don haka ta kara jan girmanta ta rike tamau a idanun Zulaiha. Ba ta shiga duk wata sabgarta, in taro suke yi a gidan na abin da ya shafi ‘ya’ya da jikokinsu, Zulaiha ba ta shiga sam, kullum tana killace kanta tana yi wa kowa kallon bai isa ba.
Malam Ibrahim bai san ko daya daga halayen Zulaiha ba, sosai yake kyautata mata iyakar iyawarsa, tunda yana ganin an rabo ta da iyayenta da kowa nata. Matan kuma babu wadda ta taba dosarsa da irin wannan zancen, don bai raine su da tsegumi da gutsiri tsoma ba.

Haka Inna Bintou ta yi ta hakuri da Zulaiha. A shekarar ne Ishaq da Mansour suka kammala karatunsu suka dawo gida. Kwarai Mansour ya ji dadin zaman Nigeria, ya ji yana son ci gaba da zama a can, musamman da yake ya yi nasa kamun shi ma a Nigeria. Don haka ya yi hidimar kasa a can kafin ya koma Nijar, yana gamawa jami’ar Ahmadu Bello ta dauke shi aiki a tsangayar Mass Communication a matsayin assistant lecturer, sabida kyawun takardunsa. Ishaq shi kadai ya koma Nijar da zama wajen iyaye da iyalinsa.

A ‘ya’yan Inna Bintou mata sun fi yawa, na Kasisi maza sun fi yawa, izuwa wannan lokacin manyan ‘ya’yan Inna Kasisi Edrissa da Oussama sun zama manyan attajirai a Yamai (Niamey) daga sana’ar da suka gada daga wajen mahaifinsu, wato shigo da shinkafa da sauran kayan abinci daga kasar Faransa zuwa Niger. Sun buge gidan mahaifinsu sun gina katon gida na zamani, ginin attajiran Nijar. Gidan ya zama mai sassa daban-daban, sassan iyayensu mata, sassan Malam, sassan matansa, na ‘ya’ya maza da sassan ‘ya’ya mata (jikoki), kasancewar yawancin jikokin gidan a gidan Malam Razee suke rayuwarsu. Gida mai cike da kyawawan ‘yammata da kyawawan samari kamar kana cikin birnin Punjabta kasar Hindu.
Gidan Ibrahimu Sarhamu Razee kenan.
*

ASALIN SU
Asalin kakansu Malam Ibrahim Razee ba dan kasar Nijar ba ne, iyayensa larabawa ne na sahara, wadanda suka fito usul daga saharar TOMBOUCTOU. Ita Tombouctou karkashin kasar Mali ta ke, larabawan ta ma’abota sanin addini ne masu yawo a kan rakumansu cikin kasashen Africa suna neman ilmin addinin musulunci a duk kasar da suka ji labarin ta shahara wajen yada musulunci. Ba su da wata sana’a sama da kiwon dabbobinsu.
A irin yawon neman ilmi da suke yi sun shiga manyan kasashen Africa masu yawa, irin su Mouritania, Sudan, Ethiopia (Habasha), Somalia, Algeria, Libya, Senegal da Malawi. Daga karshe suka shigo Chadi, suka gangaro kasar Niger. A daidai wannan lokacin Niger ta samu ‘yancin kanta daga hannun Faransa a shekara ta (1960). Lokacin da suka samu kansu a Niger sun yada zango a Tessoua inda mahaifin Malam Razee ya tabbatar musu da ya ga gurin zama sabida albarkar wajen da habakar dabbobinsu. A lokacin ita kanta Tessoua kauye ce kayau, ba ta kai ga zama jiha ba.
Mahaifin nasa ya zama babban malami mai bada karatun buzu a Tessoua, a hannunsa duka ‘ya’yansa suka yi karatu, wadanda dukkansu maza ne. Ibrahimu shi ne babban dansa. Yahayya ke binsa, sai Lamin, Hassan da Hussain. Wadanda ya haifa da matarsa daya tilo ‘Zainabou’ wadda ya aura a nan. Buzuwar Tessoua ce ta asali iyaye da kakanninta.

Barkowar ‘yancin kai Nijar, da yaduwar sabbin sana’o’i bayan kiwo a tsakanin matasa cikin manyan biranen Nijar da makobtansu, irin Mali da Chadi, ya sanya wa Ibrahim Sarhamukwadayin barin gida domin neman na kai. Ya kuma roki mahaifinsa da ya ba shi dabbobinsa ya yi jari cikin tarin dabbobinsa, ya ce ba zai taba raba shi da kiwo ba, amma zai ba shi wani abu daga ciki, sannan zai ci gaba da yi masa kiwon rabi kafin ya dawo. Kiwon dabbobi da rakuma shi ne abin da suka gada daga iyaye da kakanninsu, ko bayan ransa bai yarda su watsar ba. Ko ba ya nan kannensa za su yi masa a Tessoua.
Ibrahim Razee ya shiga Yamai (Niamey) da kafar dama. A lokacin da matasa daga kowanne sassa na Africa ke silalowa cikinta, sakamakon (territoire de la capitale) wato capital territory da aka yi mata bayan Faransa ta ba su ‘yancin kai ranar 3 ga watan Agusta 1960.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button