AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Ya aka yi-ya-aka-yi? Cikin hira Aboubacar ya gaya wa Mahmoud zuwan Aalimah. Kwanansu bakwai sai ga shi a Kano. Gidansu na New site ya fara zuwa, inda aka gaya masa sun tashi. Ya kira Aboubacar a waya, shi ya kwatanta masa sabon gidansu da ke Sultan Road.
‘Yammatan biyu na zaune a falo sun dau wanka, kowacce da abin da ta ke yi. Basma tashar Arewa 24 ta ke kallo ana diramar Dadin Kowa, sosai abin ya dauki hankalinta yadda ake nuna typical Nigerian life da ba ta sani ba. Aalimah chatting suke yi da Abulkhair, wani abu da ya zame musu jiki tun zuwanta saboda ta roke shi kada ya kira ta ko sau daya, ba ta so Mama ta san akwai wani abu a tsakaninsu, za ta shiga damuwa a kan karatunta. Za ta yi tunanin ko ma ba karatu ta ke ba, tunda a gidansu ta ke.
Abulkhair ya fahimce ta, kuma shi ma yanzu ta kansa yake yi, ya shiga shekara ta biyun karshe a karatunsa, ko lokacin da yake chatting din da ita ma squeezing dinsa yake yi, saboda yana so ko me ta ke ciki ya sani, kada nisa ya nesanta shi da ita.
Aboubacar ya shigo, Mahmoud a bayansa, bayan sun yi sallama. Aalimah ta amsa ba tare da ta dago ba, komin canjin da rayuwa za ta kawo Mahmoud ba zai kasa gane Aalimah ba. Jikinta ne ya ba ta ana kallonta, kuma kamar yaya Aboubacar ba shi kadai ba ne ya shigo. Da sauri ta cira kai, suka yi ido hudu da Mahmoud. Sai da gabanta ya fadi, yana nan a yadda ta sanshi sai dan gogewa da ya yi. Yana sanye da shudiyar shadda kansa babu hula. Ajiyar zuciya ta yi ta janyo mayafinta a gefe ta lulluba, ya samu waje kusa da Aboubacar ya zauna, jikinsa a sanyaye. Yanzu ya kara tabbatarwa ya rasa Aalimah a bisa dalilai da dama.
Aboubacar da Basma sai kallon-kallo, kwana uku kenan bai shigo gidan ba sai yau a dalilin abokinsa ta ganshi. Aalimah ta rusuna ta gaida Mahmoud cike da jin wani irin nauyi domin har gobe Mahmoud mai kima ne a idanunta. Ba ta ji dadin abin da Abulkhair ya yi masa ba, wanda shine ya raba tsakaninsu, sannan bayan ya goge lambarsa daga wayarta ya yi masa kashedin sake kiranta ita din ba ta kara bi ta kansa ba, ko wajen Yaya Aboubacar ba ta karbi lambarsa ba. Idanunta sun rufe sun makance da soyayyar dan uwanta, wanda ya shigo cikin rayuwarta da wani irin karfin mulki, ya hana ta mallakar kowanne tunani sai nasa.
Hawaye ne suka ciko idanunta, “Ni mai laifi ce Mahmoud, ka yi hakuriâ€. Abin da ta iya furtawa gare shi kenan.
Murmushi Mahmoud ya yi, “I understand. Na dade da sanin haka za ta faru Aalimah. Shi ya sa na ce miki I’m scared da tafiyarki America. Da ni da ke duka babu mai iko da kansa ko zuciyarsa, sannan shi mijin aure rubutacce ne ga mace tun halittarta. Da ma ba ki yi min alkawarin ba za ki so kowa ba. Cewa ki ka yi you are hoping that destiny tied us together… to fatan bai karbu a wajen Ubangiji ba. Dan uwanki ya kira ni daga baya…â€
Da sauri Aalimah ta dago ta dube shi. Abulkhair wane irin mutum ne? Tsoronta Allah, tsoronta kada ya kasance zaginsa ya yi.
Mahmoud ya yi murmushi ganin yadda ta tsorata. Ya ce, “Abin da ki ke tunani ba shi ne ba. Rokona ya yi in sonki nake na yi masa alfarma na bar masa ke, don ya fi ni sonki. Sannan yana mai tabbatar min babu sauran muhallina a zuciyarkiâ€.
Aalimah ta dafe kai. Mahmoud ya ci gaba, fuskarsa dauke da murmushi.
“The guy is smart! Na kuma yi rantsuwa ni da kaina yana sonki. Na kuma yarda ya fi ni sonki. Na jinjina wa karfin zuciyarsa. Ina son mutum mai nuna kwanjinsa a kan macen da yake so. Ina yi muku fatan alheriâ€.
Aalimah sai ta ji hawaye sun sake ciko idonta. Mahmoud ya sanya hannu cikin aljihunsa ya fiddo abu cikin ambulan ya matsa ya mika wa Aalimah. Ta goge idonta ta karba, ta bude. Da sauri ta dube shi. Murmushi ya yi, “ni ma ‘yar uwata na nema. Na ga abin ya fi danko idan da alakar jini, kada in je wani waje in sake shan kaye a karo na biyuâ€.
Duk halin da ya sanya ta na tsananin tausayinsa, sai da ta yi murmushi. Katin daurin aurensa ne, sati biyu masu zuwa da cousin dinsa.
“Allah ya sanya alkhairi Mahmoud. Na gode, na gode. Ina kuma fatan hakan ba zai shafi tsakaninka da Yaya Aboubacar ba, ni kadai ce mai laifiâ€. Ta fada cikin sanyin murya.
Murmushi ya yi, ya ce, “Aboubacar ai ba ke ki ka hada mu ba, balle ki raba. Ki je ki ji da rigimammen saurayinki. Wannan in ya aure ki ki shirya shan kulle. Yana sonki fiye da kima, yana kishinki fiye da zatonki. Ni ma sakona gare shi ya gaggauta ya killace ki, in ba haka ba shi ma zai sha kaye, zai samu mai sonki fiye da shi. Saboda ke Aalimah daban ki ke. Soyayyarki ba ta yi wa maza sassaukan kamuâ€. Ya mike.
A zuciyar Aalimah ta ce, ‘ba amin ba, Abulkhair kawai nake so, daga nan har gaban abada!
Juyawar nan da za ta yi, Yaya Aboubacar ne da Basma, yana zaune a gabanta a kan kilishi, ita kuma tana kan kujera kamar dalibi gaban malaminsa. Maganganu suke yi kasa-kasa, wadanda daga su sai Ubangijinsu suka san me suke cewa. Mama ba ta gidan da ma, ta je asibitin Malam wanda ta ke zuwa duk karshen wata, su Sultana na makaranta.
“To kai yayan kwabo sai ka zo ka raka ni, zan tafiâ€. Mahmoud ya ce da Aboubacar yana kallon Basma cikin mamaki, sabida yadda idonsa ya rufe da ganin Aalimah bai ma lura da ko wace ce ba. Aalimah na da twin sister ne? Kai! That cannot be possible. Wannan ta fi ta aji, ta fi ta wankakken ido, me yiwuwa ‘yan uwan nasu ne na canâ€. Ya bai wa kansa amsa.
Aboubacar ya mike suka fita yana ce da Basma, “Ba doguwar rakiya zan yi masa ba, tasha zan kai shi ya hau motar Katsinaâ€.
Dariya Aalimah ta yi tana kallon Basma, wadda annuri kadai ke fita a fuskarta, da gani sun daidaita abin da suke ganin matsala ne a gare su. In wani ya gaya mata Aboubacar Mansour ne wannan a gaban mace ba za ta taba yarda ba. Hakika soyayya abu ce mai girma, mai birkita rayuwar ‘ya’ya maza fiye da mata.
Kafin hutunsu ya kare su koma U.S, hatta Daddyn su Aalimah ya san da soyayyar Aboubacar da Basma, ba Mama kadai ba. Sai dai cikin su duka babu wanda ya zura jiki cikin al’amarin a bisa dalilai kwarara da dama. Ido kawai suka zuba musu, suna ganin da ta koma shi kenan za su manta da juna.
Sun dawo Massachusetts ranar asabar, litinin suka koma makaranta.
6/28/21, 7:36 AM – Buhainat: â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©â‚©
💙💙💙💙💙â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤â¤ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’›ðŸ’•💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💓💓💓💓💓
Haka Aalimah ta ci gaba da karatu a gidan Kawunta a Boston (Massachusetts) duk shekara suna zuwa gida su yi hutu su koma. Duk kuma zuwan da za su yi da Basma suke zuwa, inda suka girka wata irin soyayya ita da Yaya Aboubacar, yayan Aalimah. Wadda labarinta har Niger, har kunnen Malam Raazee. Da fari bai ce komai ba, don shi ba irin kakannin nan ba ne masu katsalandan cikin maganar auren ‘ya’yansu ko jikokinsu. Aalimah tana shekarar karshe, ita kuma Basma ta gama saboda karatun Aalimah na shekaru biyar ne, Aboulkhair ya kammala shekarar da ta gabata ya fito a cikakken likita mai kwalin MBBS. Ya tafi speciality a kan kwakwalwa a shahararriyar jami’ar da ta yi fice a duniya a kan ilimin psychiatry (wato John Hopkins University), wadda ke garin (Baltimore, Maryland).
Duk kawaicin Malam Raazee wannan lokacin ya yanke shawarar tsawatarwa ga ‘ya’yansa biyu kan wannan zuzzurfan ilmin boko da suka dora ‘ya’yansu akai, daga mazan har matan babu mai tunanin yi musu aure a cikinsu. An gaya masa batun Aboubacar da Basma, amma har gobe bai taba jin komai a kan Aalimah da Khaleesat ba, wadda ke aji biyu a jami’a yanzu haka. Idan sun ce karatu, to shi wannan karatun ba shi da iyaka ne, ko ko ba shi da madakata? Kada dauke idonsa ya sa a shiga keta haddin Allah.
Aunty Gumsu ta haihu shekaru biyu baya, ta haifi ‘ya mace Nurat. Don haka wannan zuwan da suka yi Niger har Mummy Zulaiha, ya ce a kira masa Mansour yana son ganinsa, ya zo su hadu da sauran ‘yan uwansu a yi ta ta kare kan ‘ya’yansu, ya gaji da ganinsu babu aure bakidaya. Cikin shekarar nan yake son ganinsu a dakin aure bakidaya, daga matan har mazan. Mu’azzam kuma sai sun gaya masa abin da ya hana shi aure.
Mu’azzam ya dade da sulhunta Mummynsa da dangin mahaifinsa bakidaya. Har nata ‘yan uwan. Tare da ita suke zuwa duk karshen shekara. Tsakaninta da Inna Kasisi yanzu sai sam-barka, da ma matsalar daga gare ta ne, kuma da ta nutsu ta bude zuciyarta kamar yadda dan nata ya shawarce ta, ta tadda abubuwan yadda ya gaya mata su. Ita kadai ta dauka da zafi, su mutane ne masu son junansu da kaunar duk wanda ya shafe su ba tare da nuna bambanci ba. Sai dai in ka nuna musu su ba wata tsiya ba ne cikin rayuwarka za su nuna maka ka yi kadan ka keta alfarmarsu, ko mene ne takamarka.
Don haka wannan zuwan har da Mummy aka zo Niamey. Kwanansu biyu kawu Mansour da Maman Aalimah da kannenta suka iso. Aboubacar bai biyo su ba, sabida aiki. Ba su samu zama da Malam ba sai da daddare. Ya sallami matan ya zauna da manyan ‘ya’yansa maza bakidayansu.
“Oussama kai ne babba, kai ne kuma za ka zame min shaida kan cewa tunda ka fara haihuwa ka ke aurar da ‘ya’yanka ban taba shiga ba, ban taba cewa da kai ga abin da ya kamata ba, saboda kai ka san ya-kamatan, ‘ya’ya mata ba sa wuce shekara sha shidda a gabanka. Kaninka Edrissa ya biyo bayanka da wannan kyakkyawan koyi. Amma wadannan (ya nuna Ishaq da Mansour) guguwar zamani ta debe su tana neman kai su ta baro.
Babu Allah a ransu sai ilmin nasara wanda iyakarsa duniya babu amfanin da zai yi musu a lahira. Sun aje balagaggun ‘ya’ya maza da mata ba sa ko tunanin yi musu aure. Bayan cikinsu babu wanda ban yi wa auren gata ba, tun kafin ya kama kwalin ilmin bokon don dai in fita hakkin Allah. Nauyin auren bai hana ku zama abin da ku ke son zama ba, don haka ku zama shaida, ko yau na fadi na mutu Ishaq da Mansour su suka yi ajalina.
Sun ki aurar da ‘ya’yansu, sun ki gaya min matsalar Mu’azzam, kullum abin nan na damuna a zuciya, da shi nake kwana nake tashi. Shi ma Mu’azzam din ba ya son na yi masa zancen aure, daga shi har Abulkhair ba su da niyyar yi musu aure, balle kannensu mata. Ga Aboubacar shi ma ya dade yana aiki, amma babu abin da suka yi a kan zancensa da Basma, wanda na dade da ji yana yawo a bakin su Bintou.
Yau ga su a gabanku su gaya mana gaskiyar lamarinsu. Me suka dauki rayuwar duniya? Wallahi ba inda za ta kai ku idan ba ku bi dokokin Allah baâ€.
Ya soma matsar kwallah, duk kuma maganar cikin harshensa Temachek yake yinta.
Shiru ta ratsa a falon Malam Raazee. Daddy Ishaq idanunsa sun kada sun yi jazir. Jijiyoyin kansa sun fito rada-rada. Baban Aalimah bai ce komi ba, ko shi yana son jin mene ne matsalar Mu’azzam. Tambaya ta karshe da ya yi masa shekarun baya zuwan Aalimah na farko hutu, da ya tambaye shi cewa ya yi da shi, Mu’azzam addu’arsu kawai yake so, amma ba abinda yamadidi da lalurar tasa zai amfana masa.
Don haka yau shi ma ya zuba masa ido a qagare da son jin amsar bakinsa. Maganar Aboubacar da Basma ya santa ba tun yau ba, bai taba daukanta da muhimmanci ba ne saboda a ganinsa Aboubacar ba shi da abin da zai rike Basma, kuma ba za ta iya adopting tashi rayuwar ba.
“Kai muke saurare Ishaqaâ€. Uncle Edrissa ya katse masa dogon shirun da ya yi. Ajiyar zuciya ya yi, yau kam ya san ba shi da mafita ban da gaya wa mahaifi da ‘yan uwansa ko wane ne Mu’azzam. In ba haka ba za su yi zaton bai dauke su a bakin komai ba, kuma yana nufin ‘ya’yansa ba nasu ba ne. Mutuncin Mummy Zulaiha a idanunsu yake tattali wanda Mu’azzam din ya samu ya farfado da shi ba da jimawa ba.
Ina ga in sun ji ita ce ta illata wa wannan dan da suke matukar so rayuwa bakidaya? Duk da shi ma da nasa laifin, amma tarbiyya a hannun mace ta ke, ita kuma ba ta zauna a gida ba balle ta zama ginshikin samar da ita. Ta debi al’adun al’ummar da ta samu kanta a cikinsu ta yafa gabadaya babu gaira babu dalili.
Shirunsa ya kular da Uncle Oussama ya soma fada, da ma shi masifaffe ne. Ya fadi kalamai wadanda ba su yi wa Daddy Ishaq dadi ba. Ya ce don su ba su yi ilmin boko ba ne shi ya sa yake daukarsu ba a bakin komai ba; a wadanda ba su da kwakwalwar fahimtar abubuwa. Daddy Ishaq ya rasa inda zai sa kansa, sai ya soma hawaye.
Zuciyar Mansour ta tabu saboda ba ya hada Ishaq da kowa cikin rayuwarsa. Hakuri ya soma ba wa babban Yayansu ya ce Ishaq ba haka yake nufi ba. Zancen ne yake yi masa nauyin fada da alama, ya barshi ya hada zaren maganar da ke bakinsa a hankali.
Daddy Ishaq ya ji dadin abin da kaninsa ya ce, ya ce su yi masa alfarma ya kirawo Zulaiha a yi zancen nan a gabanta, amma yana rokon alfarmar abubuwa guda biyu kafin ya fada musu komai. Na daya, su yi wa Zulaiha uzuri su yafe mata kamar yadda ya yi mata uzuri, ya kuma yafe mata. Kowa rai ya yi wa dadi baran mai shi ne. Ta fi kowa kasancewa cikin damuwa da yanayin rayuwar Mu’azzam, kuma da tana da yadda za ta yi da tuni ta fitar da shi daga halin da yake ciki. Na biyu ba ya so zancen nan ya je kunnen mata har Inna Kasisi da Inna Bintou. Malam ya ce yana sauraronsa, kuma ya amince zancen zai tsaya a tsakaninsu su kadai.
Mikewa ya yi ya fita, ya tura yaro cikin gidan ya kira Mummy Zulaiha.
A nutse Mummy ta shigo falon, ta ratsa ta tsakiyarsu ta wuce ta nemi wuri can nesa da su ta zauna. Malam ya maimaita mata makasudin taron da bukatarsa na aurar da ‘ya’yansu bakidaya a lokaci guda, har Mu’azzam. Idan kuma sun ce rashin lafiya ya hana shi aure, to yau yana bukatar su fayyace masa wace irin rashin lafiya ce da abin da ya raba auren da ta yi masa shekarun baya.
Mummy kuka ta saki, a hankali ta rufe fuska da mayafinta. Daddy Ishaq ya ce, “Zulaiha yau zan gaya musu, don ba ni da wanda ya fi su. Dukkaninmu ni da ke masu sakaci ne, amma naki ya fi nawa yawa. Idan Allah ya ce haka Mu’azzam zai kare rayuwarsa babu tsimi babu dabaraâ€.
Tiryan-tiryan ya soma ba su labari tun barinsa Nijar zuwa Amurka tare da maidakinsa da dansu guda daya da suka haifa a nan Niamey, wato Ibrahim-Mu’azzam, wanda sunan Malam Raazee na gaskiya ya ci. Shekaru talatin da uku a baya, da duka abin da ya wakana cikin shekarun har zuwa yau shekarar da muke ciki.
Falon ya dauki shiru, sai shesshekar kukan Mummy Zulaiha kadai. Jikin Uncle Oussama ya yi sanyi da fassarar da ya yi wa dan uwansa a baya.
Uncle Edrissa ya nisa ya ce, “To ku ne kun gama yin amanna da maganar bature da maganinsa, ban da haka ai babu cutar da ba ta da magani sai mutuwa da tsufa. Kuma ni ban yarda wannan cuta ba ce a nahiyarmu, can a kasashenku kadai ake wannan ciwace-ciwacen a ce ba su da magani. Mu a addinin musulunci mun yarda cewa babu maganin da babu a cikin Alkur’ani. Shi din (Alkur’ani) waraka ne, kuma magani ne na kowacce irin cuta.
Mu’azzam ya dawo gida, ya rabu da wannan maganin da yake sha, mu yi wanda muka gada iyaye da kakanniâ€.
Uncle Oussama da ke kallon Mummy a hasale babu ko digon tausayinta a ransa sabanin sauran kannensa ya ce, “To kukan me za ki damu mutane da shi yanzu? Wanda ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka. Ni ban taba ganin mace irinki ba, kawai don kin je kasar turawa sai ki dauki kanki jinsinku daya, ki kasa bambance mai kyau da mara kyau, ki saki koyarwar addininki ki kama ta wadanda tun a duniya Ubangiji subhanahu wata’ala ya gaya mana makamashin wutar jahannama ne su (yahudu da nasara).
An yarda babu inda neman abinci da yanayin rayuwa ba ya kai mutum, amma musulmi ya dinga tunawa shi musulmi ne a duk inda ya tsinci kansa, ya kiyaye martabar addininsa da koyarwarsa. Rayuwa cikinsu da cudanya da su (ahlil kitabi) ba laifi ba ne a musulunce, amma ‘ya’ya amana ne a hannun iyaye da ya zama dole a dora ido a kan mu’amalarsu da rayuwarsu, a tsawatar a inda yake bukatar tsawatarwa.
Makauniyar soyayya ga ‘ya’ya ba gata ba ne a gare su, don haka za ki yi ta kuka fiye da Mu’azzam tunda ke uwa ce, kin fi shi son kansa da kansa, babbar banza kawai! Ashe matan ma Aalimah ce ta gyara su inji Balkissa amma ai da dan wando da ‘yar riga suke yawo, kai ba kallabi kamar akuyoyiâ€.
Haka Uncle Oussama ya karewa Mummy tanadi tas ko dagowa ba ta yi ba. Malam dai ya kasa magana, tausayin Mu’az ya kashe bakinsa da zuciyarsa. Sai da Oussama ya yi shiru sannan Baban Aalimah Dr. Mansour ya yi gyaran murya, ya dubi Uncle Edrissa, ya ce,
“Ban musanta batunka ba Yaya Oussama. Kuma ban hana a nema wa Mu’azzam magani namu na gida ba. Amma zancen ya bar treatment dinsa ya daina shan maganin likitocinsa bai taso ba. Da gaske wannan cuta ce mai zaman kanta na taba cin karo da ita a wani bincike da muka gudanarwa world health organization (WHO) a kan hanyoyin da za a bi a rage cututtukan kwakwalwa a cikin al’umma. Kuma ba bugun aljannu ba ne, sannan ba a America kadai ake samun masu fama da ita ba, wallahi har nan Nigeria inda nake, kawai dai Society dinmu ba su dauke shi mental health deficiency ba ne, sun fi daukarsa a DABI’A. Don haka ni shawara ta ita ce a jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato Mu’azzam ya ci gaba da shan maganin asibiti, sannan ku ma ku yi irin naku kokarin, a taru a roki Allah ya yaye masa bakidayaâ€.
Kowa ya yi na’am da shawarar Dr. Mansour, ko da ma can duk ya fi kowa a gidan kaifin hikima.
“Don haka mun ajiye batun Mu’azzam a gefe, za mu dawo kansa daga baya in mun samu nutsuwa. Yanzu muna kan na masu lafiyar. Ishaq, me kake ciki maganar auren ‘ya’yanka? Kai ma Mansour me ka ke ciki kan Aalimah da Aboubacar?†In ji Uncle Oussama.
Daddy Ishaq ya muskuta ya ce, “Ba kin aurar da su na yi ba. In don ta ni ne da tuni na dade da aurar da su. Sun dade da hada kansu shekaru biyar a baya. Bana so ne in shiga gonar Mansour, ina so ya samu cikar burinsa shi da Aseeya a kan Aalimah, kada ya ga kamar na so kainaâ€.
Ido sosai Dr. Mansour ya bude yana kallon Yayansa cikin rashin fahimta. Edrissa ya ce, “Kamar ya ya? Su waye suka hada kan nasu?â€
“Aboulkhair da Aalimahâ€.
Fuskokinsu suka bayyana dadin da zancen ya yi a zukatansu. Malam ya ce, “Da ma aure yana hana wani buri cika ne, ko dai ya taimaka masa ya kai ga ci? Tukunna ma wane buri ne Mansour din da maidakinsa suke da shi a kan Aalimah? Da ma ana ci wa ‘ya mace alwashi a hana ta aure ne?â€
Nan Daddy Ishaq ya warware musu komai kan ba shi ya dauki nauyin karatun Aalimah ba. Ya gaya musu duk abin da ya wakana.
Dr. Mansour Raazee ya dubi yayansa kamar zai yi kuka, “Ba ka kyauta min ba Yaya! Shekaru biyar Aboulkhair na dakon soyayyar Aalimah bayan kai kanka mai daura mata aure ne. Aseeya ke son karatun nan ba ni ba, kuma ita ma in ta san Aboulkhair ne zai auri Aalimah ba za ta hana ba. Shekara biyar Yaya? Ban ji dadi ba ko kadan. A kalla da ka gaya mini ko shawara ce mu yi,. Idan har yanzu Aboulkhair na son Aalimah bai canja shawara ba sabida nisan shekarun da aka sanya shi jira, na ba shi ita duniya da lahira, kuma ban da sadaki ban dora masa komai ba. Sadakin ma in an amince min, zan biya masaâ€.
Uncle Oussama ya ce, “To ba a amince maka din ba. Shi zai biya ni daga aljihunsa. Aboubacar da Basma fa? Me suke ciki? Shin zancen da Inna Bintou ke fadi cewa sun hada kansu gaskiya ne?â€
Shiru Dr. Mansour ya yi, sannan a sanyaye ya ce, “Na san zancen, sai dai ban taba ba shi muhimmanci ba, a bisa hujjojina kwararaâ€.
“Wane Aboubacar din da wace Basman?†Daddy Ishaq ya tambaya cikin mamaki da kuma dokantuwa da a fidda shi cikin duhu.
Nan Malam ya gaya masa shi ya dade da sanin zancen a bakin iyayensu mata. Ya yi zaton ya sani shi ya sa ya yi ta zuba ido yana jira su zo masa da zancen. Da ya ga suna nufin sai bayan ransa shi ya sa yake so a yi ta ta kare a yau. Ko bai ga ‘ya’yansu ba, ya shaida aurensu ya gode wa Allah.
Daddy ya dubi kaninsa zuciyarsa na ninkaya cikin farin cikin da ya gaza boyuwa a kan fuskarsa.
“Ba ka bai wa zancen muhimmanci ba sabida wadanne hujjoji naka? Da ni da kai wa ya fi rashin kyauta wa dan uwansa?â€
Murmushi ya yi ya sunkuyar da kansa, “Ku fahimce ni bakidaya, dukkaninsu ba mai iya zama a kasar da dan uwansa ke zaune. Kowanne yana da tsararriyar rayuwa a inda yake. Sannan abu ne mai wahala Basma ta iya baro iyaye da ‘yan uwanta ta zauna da mu a Nigeria. Sannan ina tunanin kamar karfin samunsa bai isa ya rike ta ba in aka yi duba da irin rayuwar da ta taso a cikiâ€.
Murmushi Daddy Ishaq ya yi, kanin nasa na kara shiga ransa. Idan zai yi abu sai ya duba shi (from every sphere, he leave no stone unturned),
“To ai ni kaina na kusa barin Americarâ€.
Ba Mummy Zulaiha kadai ba, kowa a falon sai da ya juyo ya dube shi. Gyada kai ya yi don tabbatar musu da furucinsa, sannan ya ci gaba da bayani yana kallon matarsa.
“Saboda Mu’azzam na kai wannan lokacin a America, saboda yana karbar proper medical treatment, kuma bana so mu taho gabadaya mu barshi shi kadai, ga aikinsa ga yanayin da yake ciki, a ce ba shi da kowa a kasar da yake zaune. Amma ni tun farkon faruwar matsalolin nasa kasar Amurka ta fice min a rai. Ina ta dakon damuwar Mu’azzam. Yau da na fayyace muku sai na ji kamar an dauke min wani nannauyen dutse daga kirjina. A kalla nasan ba ni kadai nake jigilar damuwar ba, ina da masu taya ni ko da da addu’a ne. Target dina na yanzu shi ne, Aboulkhair ya kama aiki, ya yi aure ya zauna kusa da shi, ni kuma in nemi aiki a nan Niamey in dawoâ€.
“Allah ya yi maka albarkaâ€. Inji Malam Raazee, “Shi kuma Allah ya ba shi lafiyaâ€. In ji Uncle Oussama da Uncle Edrissa.
Ba su tashi daga wannan zaman ba sai da suka yanke lokacin auren yaran nasu hudu. Daddy ya gaya musu ita Khaleesat yana da buri a kanta, ya dade da gane shirin da ke tsakaninta da Hamoud kafin ya tafi Japan, inda yake kwas din aikin sojan ruwa, shekara mai zuwa zai kammala. Uncle Oussama rasa me zai ce ya yi, danshi yake wa tanadinta, amma ya gaya masa maganganu marasa dadi dazu. Matsar kwalla ya shiga yi yana cewa, “Pardonne-mon frereâ€. Wato (ka yafe min dan uwa da harshen faransanci).
“Ni ba ka yi min komai ba Yaya. Kauna ce ta saka damuwa da lamarin Mu’azzamâ€.
Addu’a mahaifin nasu ya daga hannu ya yi musu bakidayansu. Ya sa musu albarka, ya roki Allah ya sa su gama da duniya lafiya, ya kara musu kaunar junansu.