AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aboulkhair ya damki hannayenta ya rike, ya ce, “Wuw! Thirty minutes cif ban kama Aalimah ta ba, gaskiya na yi kokari. Lets go tun kokarina bai tashi a banza ba, ya yi mantuwa ya dawoâ€.
Zame hannayenta ta yi, ta ce, “Da na sani ma kiss na yi maka a gabansaâ€. Ta yi gaba da sauri. Ta ma manta da abin da Mu’azzam din ya ajiye mata, ya dauko ya biyo ta da shi yana fadin, “Ka ji ta kamar gaske, alhalin ke kanki zama ki ka yi kamar wadda ta yi wa sarki karya a gaban nasaâ€.
Sai da ya tada motar ya dora mata katin da takardar a cinyarta. Credint card ne na bankin da Mummy ke aiki JP MORGAN CHASE da pin numbers din ya rubuta a jikin takardar.
“Ba ki ya yi, yarinya kin zama Madame, ki yi ta zara ana karowa duk wata. Ga shi ko shopping mall daya ba ki sani ba. In na koma hutu zan zagaya da ke ki ga gari, amma yanzu lalalala, sai na gama honeymoon dinaâ€. Ya fada yana mai winking dinta. Murmushi ta yi, ta ce, “Ka ajiye a wajenka, ni ba abin da zan saya, beside komai nake so zan iya gaya makaâ€.
Haka suka yi ta musu, ta dage ba za ta karba a hannunta ba, ya dage nata ne shi ba zai mata ajiyar kudi ba, in Mu’azzam ya gani a hannunsa ba zai ji dadi ba. In ba abin da za ta yi da su din, ta kwashe ta tura wa Kawu Mansour ko mama Asi. Ta yarda da wannan shawarar.
Har suka zo gida Aalimah is very curious and questioning Aboulkhair a kan rayuwar Mu’azzam saboda al’amuransa bakidaya sun kara rikitata. Sun kara daure mata kai, mutum kamarsa mai cikar mutunci da kamala, ga rayuwar duniya Allah ya ba shi daidai misali, amma babu iyali, babu ranar zancensu? Kallon da ta ke masa daga nesa-nesa da ta zo kusa da shi ta ga ba haka ba ne. ba ta ga annoyance din a tare da shi ba banda ganewa da ta yi shi din is a very serious person, mai matukar tsantseni da lokacinsa. Mai girmama bako, mai tarin al’amuran yi fal a gabansa. Tambayoyin da ta ke yi wa Aboulkhair har ya rasa wanne zai fara amsa mata.
Tambayarta ta karshe ita ce, “Wane magani yake cewa za mu cika masa gida da shi? Maganin me yake cewa zai je ya sha ya kwanta?â€
Aboulkhair ya sanya hannayensa biyu ya toshe kunnuwansa bayan ya kashe motar a ma’adaninta, ya ce, “Baby, ina da nawa matsalolin ki taimaka min in warware su. Sannan in waiwayi naki matsalolin which is MU’AZZAM. Na daya, hundred kiss at mouth, fifty at my nose, seventy at my tongue, eigthty at my eyes and two hundred at my neck. In kin gama wannan ki zo na yi miki alkawarin warware miki rayuwar Mu’azzam bakidaya, tun daga kuruciya har girma. Amma ko daya ki ka tsallake ina kirge da abuna, kin tsallake chapter daya cikin labarin Mu’azzamâ€.
Aalimah ta dora hannayenta biyu a ka tana fadin, “Na shiga uku! Mon Amour ka yi min sassauci, ba zan iya ba, and I really-really want to hear his story, amma haka zan ta binka ina sumbata kamar zan cinye ka? A tarihin gidanmu babu mayeâ€.
Ya hadiye dariyar da ta ba shi, ya yi gaba yana fadin, “Za ki ga maita! Sai ki zaba ko maita ko labarin Mu’azzamâ€.
Ta ciji yatsa ta bi shi da gudu, suka shige gidan nasu. Ta riko hannunsa zai shige dakinsa, “Mon Amour ka saurare ni. Zan yi maka tausa dai kadai, Allah ba zan iya ba ina jin kunyarkaâ€. Ta fada kamar za ta yi kuka.
Kwacewa ya yi ya shige yana fadin, “Ni fa na gama magana, ai it is an option, not a choice, ban ce dole ba, ki rike tausarki, in ita ce ina da injin da zai yi min. I just want to confirm I’m married to Aalimah Mansour, (kawai ina so in tabbatarwa kaina ina auren Aalimah Mansour) saboda har gobe ji nake kamar a mafarki… kamar za ki kubuce min Aalimah… kamar har gobe ban gama mallakarki ba. Kamar akwai wasu sauran gurabe cikin zuciyarki da ban kai ga isa baâ€.
Intonation din da yake maganar da shi, da yanayin da ta gani cikin kwayar idanunsa su suka taru suka sukurkutata, suka rikitata, suka sa ta jin wani irin tsoro na ratsa ta. Sanda ta kankame shi ba ta sani ba… sanda ta soma rufe shi da sumbar a guraben da ya bukata da ma in da bai bukata ba, ba ta yi shawara da zuciyarta ba. Ba ta tuna akwai wata aba wai ita kunya cikin idanunta ba. Tun yana fadin, “Niceâ€. Ya koma, “Sweetâ€. Ya koma, “Splendidâ€.
Al’amarin da bai tuke a ko’ina ba sai a gadon barcinsu. Wata irin soyayya mai zafi da tsanani wadda a yau ba ta Aboulkhair ba ce shi kadai, 80% ta Aalimah ce da hobbasarta. Aboulkhair ya yaba, ya yi tukuici yadda ya kamata. Saida suka dawo hayyacinsu ya soma kyalkyala mata dariya. Ya ce ba wuya za a sayar da kanta a Las vegas. Shi duk abin da ya fada don ta yi masa abin da yake so ne, kuma ga shi ta yi.
“Ban da rashin wayo irin naki, wane gurbin ne ban kai ga isa ba? Yana ina? Nuna min shiâ€.
Hannayenta biyu ta kai ta rufe fuskarta, ya rungume ta tsantsan, ya ce, “Aalimah, Allah ya yi miki albarka, ya albarkaci rayuwarmu da ‘ya’ya masu irin tarbiyyarki, ba wata kubucewa da na yi tunanin za ki yi min banda ina so in koyar da ke yadda za ki tafiyar da ni. Kunyarki is too much… Ni kuma… ni kuma…â€. Ya soma zagaye dan bakinta da yatsansa ibham, “…Ina so kullum in ji sulbinshi da sanyinshi da taushinshi kan fatar jikina. In ki ka yi min wannan kin gama min komai, kin kauda hankalina daga kowacce diya mace. Kin zama ni na zama ke, mun zama sirrin juna. Bude kunnuwanki in gaya miki ko wane ne MU’AZZAM???
LABARIN MU’AZZAM.
Wato tunda muka taso daga shekaru biyar a duniya zuwa sama, mahaifiyarmu ta dora mu a kan turbar duk abin da muke so sai mun same shi, kuma za ta iya samar da shi gare mu ta kowacce hanya in har hakan zai sa mu farin ciki. Tun muna kanana Mummy ta lalata mu da kashe kudi, a kullum tana gaya mana don mu ta ke aiki, burinta mu samu duk abin da muke so a rayuwa mu ji dadi a kasar da muke zaune, mu zama daya da ‘ya’yan turawa, mu manta da ‘yan kauyen dangin Daddy don ba kaunarmu suke yi ba. A cewar ta da ba su bar Nijar ba, da tuni sun raba ta da Daddy, saboda rashin son da suke mata. In za mu tafi makaranta haka ta ke damtso kudi ta ba mu, ta ce mu kashe duk da ga lafiyayyen abinci da abin sha ta cika mana lunch box da shi. Mu kuwa mu yi ta bushasha da abokanmu.
Duk kokarinta na hana mu yin abokai tana cewa, mu zama abokan junanmu kadai, abokai suna cutar da yaro ne kawai su canza masa tarbiyya. Wannan tsoratarwa ta Mummy ba ta yi wani tasiri sosai a kanmu ba, saboda muna neman wadanda za su taya mu cinye tulin kudin da ta ke ba mu ne, ba mu kuma san ya za mu yi da su ba. Abinki da makarantu na nasara masu tsananin kula da sanya ido, ba a dade ba school authority ta fahimci irin kashe kudin da muke yi a sayi banza sayi wofi, da irin abubuwan almubazzarancin da muke zuwa da su, ta yi wa Daddy magana. Ya kuma bincike mu kan inda muke samun kudi, inda ba tare da bata lokaci ba muka gaya masa Mummy ce ta ke ba mu. Don haka ya yi mata magana, ya kuma gaya mata tsawatarwar hukumar makaranta. Sabida haka Mummy sai ta koma sanya mana a jaka ba tare da sanin Daddy ba, ta kuma ce mu daina kashewa a makaranta sai mun dawo gida kafin ta dawo daga aiki.
Zancen nan da nake miki, lokacin mahaifinmu na aiki da consulate of Niger ne, ainahin aikin da ya kawo mahaifinmu kasar Amurka. Muna zaune a Washington D.C. Daddy ba wani babba ba ne a consulate din (diplomat officer) ne kawai, amma albashinsa dai mai tsoka ne, don a haka ya yi sponsoring karatun Mummy, har ta gama ba ta jima ba kuma ta samu aiki da daya daga cikin manyan bankunan kasar, wato JP Morgan Chase, matsayin akawu (Accountant) domin ta fito da digiri mai daraja ta farko, kuma a wannan zamanin samun aiki ga bakin haure bai yi wuyar da yake da ita a yanzu ba. Namu karatun kuwa ni da Mu’az ba shi yake daukar nauyinsa ba, ofishinsu ne. Don haka rayuwa muke cikin rufin asiri, ba mu nemi komai mun rasa ba. Da Mummy ta soma aiki sai muka koma cikin wadata fiye da baya, saboda duk albashin nata a kanmu yake karewa ni da Mu’az, suttura, kekuna, ciye-ciye da duk wani abu da yara maza masu shekaru irin namu za su bukata. Mummy ta sakar mana dukkan bakin aljihunta. Sai dai kuma aiki ya sa mun nesanta da juna, ita dai za ta ba mu kudi, ba ta damu da duk abin da muke ciki ba, ba ta san wace irin rayuwa muke yi ni da Mu’az ba idan ba ta nan tunda ta daukar mana house maid mai dafa mana abinci da kula da tsaftar jikinmu.