AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Pg 100

Alhamdulillah, Halima ba ta mutu ba, amma tana samun kanta ta kafawa su Daddy kuka da tashin hankalinsu maida ita gaban iyayenta. In taga Mu’azzam kamar ta ga mala’ikan daukan ranta. Aka yi-aka yi kuma Mu’azam ya sake ta, ya ce shi yanzu ya fara aure. Ba wanda ya isa ya sa shi sakin Haleemah. Yana zamansa lafiya aka yi masa aure ba da yawunsa ba, sai da ya samu hanyar ajiye temper and frustration mafi sauki, sannan a zo a ce za’a raba aure? Da ya san haka auren yake da dadi ai da tuni ya dade da yinsa. A karshe da result din Mu’az na karshe ya fito, dole Daddy da Mummy suka dauke Halima daga Las Vegas suna kuka.
Result ya nuna bayan aggressive tendencies Mu’az na da lalurar hyper sexuality disorder wanda aka fi sani da compulsive sexual behaviour. Wadanda duka su biyun (aggressive tendency and hypersexuality disorder) alamomi ne na bipolar da kuma hypomania.
Amintaccen likitansa shi ne Dr. Nebrass, wani gawurtaccen neuro-psychiatrist ne da ake ji da shi a Amurka. Shi ke kula da komai na Mu’azzam. Ya gaya wa Daddy cewa, su kwantar da hankulansu ganin yadda suka fita hayyacinsu da jin wannan sabon sakamako na Mu’azzam, wanda duka alcohol ita ce sila, wato giya. Ga wasu victims din kuma drug addiction ne.
Dr. Nebrass ya gaya wa Daddy cewa, kamar yadda aggressive tendencies can be controlled by drugs and other clinical therapies shi ma compulsive sexual behaviour (hypersexuality disorder) can be controlled and monitored, kuma mutum ya zauna lafiya tamkar sauran mutane masu lafiya muddin an kiyaye shan magani. It’s a neurological disorder da za a iya magance ta ta hanyar amfani da kwayoyin ‘Anti-Androgens’, and mood stabilizers medicines, su wadannan kwayoyi na Anti-Androgens, suna kashe tasirin Androgens, wato sex hormones a jikin dan Adam mai fama da wannan lalura kuma suna taimaka wa wajen rage sexual urges, wato sha’awar jima’i.
Mutane masu fama da wannan lalura ta hypersexuality disorder (compulsive sexual disorder) suna amfani da sex as a quick fix to relieve anxiety, loneliness, pains, aggressiveness, frustration and other forms of stress without regard to potential consequences. It’s characterized by abnormal sexual drive and difficulty in forming emotional connections, e.g marriage and family life to the extent that the behaviour interferes with work, health, relationships, family and other normal activities. They use sex as an escape behaviour. They have intense sexual impulse. And the episode have to last over size months before it can be diagnosed. Drinking alcohol triggers the problem and increase aggression. (fasara; mutane masu fama da compulsive sexual disorder suna amfani da sex matsayin hanyar farko ta samun sauki daga tsoro, kadaici, zafin zuciya, radadin zuci, bacin rai da sauran stresses ba tare da la’akari da abin da hakan zai haifar ba. Ta yadda har hakan zai shafi ayyukan neman abincinsu, lafiyarsu, mu’amalolinsu, iyalinsu da sauran abubuwa na yau da kullum. Halayensu shi ne abnormal sexual drive wato yawan saduwa wanda ba a saba da shi ba, ko wanda ya wuce kima, shan wahala wajen gina soyayya a zukatansu (kamar soyayya ta aure) da gina iyali. Abin da suka fi maida hankali a kai shi ne, having sex to relieve their stresses and pains. Sai dai duka wannan ana iya magance shi da kwayoyin Anti-androgens da kuma mood stabilizers medicines, mara lafiya ya zauna lafiya cikin kyakkyawar rayuwa kamar kowa.
To kin ji Aalimah, wannan ita ce rayuwar Yayana Mu’azzam. Yau shekara goma kenan yana rayuwa cikin shan kwayoyi domin danne sexual urges tare da kuskurewa ba. Ko da aka tilasta masa ya saki Halima ya sake tan, amma ya gaya wa su Daddy kada wanda ya kara dosarshi da zancen aure kuma kada wanda ya kara yi masa aure ba tareda saninsa ba. Yana jin dadin rayuwarsa a haka, and he’s making it profitable. Kwayoyin anti-androgen suke hana Mu’az sha’awar aure kwata-kwata. He cannot even develop emotion balle ya ji yana son wata mace a ransa. Bayan gama MBA dinsa ya samu aiki da kamfanin man fetur na farko a Amurka, wato CHEVRONCORPORATION sun barshi a reshensu na Las Vegas inda yake zaune ya kasa barinta. Akwai sanda aka yi masa sauyin wajen aiki zuwa jihar OHIO amma Muazzam bai yi kaura ya koma can ba. Kullum zuwa yake ya dawo a jirgin kasa, ko ya je ya yi sati biyu ya dawo. A cewarsa Las Vegas is where all the memoirs of his adulthood began….. He cannot go far from it.
Ta canza shi daga spoilt, drunkard Mu’azzam, zuwa matashin da ya san ciwon kansa, ko kusa Mu’azzam ba ya son shiga mutane, har family dinsa kuwa, ya fi son rayuwar da yake yi ta kadaici da maida hankali ga ibadah wadda a shekarun teenage dinsa bai samu alfarmar yi ba sai shan giya. Sai kuma dedication ga aikinsa, saboda bai da wani abin yi mai muhimmanci bayan shi. Kamfanin chevron na ji da Mu’azzam fiye da zatonki, saboda yana daga cikin masu habbaka su da kawo musu innovations.
Tunda na shiga shekarun da na fara hankali, na kuma kai ga fahimtar matsalolin Yayana Mu’azzam na yi kudurin zama neuro-psychiatrist saboda in kula da shi a sauran rayuwarsa… Ina so in canji Nebrass in zamo ni ne mai kulawa da shi ba wani ba. Mu’az bai fiya zuwa Boston ba (Massachusetts) mu muke zuwa inda yake. Mummy ta fi kowa zuwa akai-akai, saboda a yanzu tana jin kanta culprit na duk irin rayuwar da Mu’azzam ke yi a yanzu, tana zuwa ta yi kwanaki tare da shi, a kan idonsa aka haife su Basma daya bayan daya, amma babu wata shakuwa a tsakaninsu, ba ya jansu a jiki, ba ya shiga sha’aninsu, tun suna damuwa har sun daina, sun fidda shi a jerin ‘yan gidan. Khaleesat kan ce ba iyayensu daya ba, he’s adopted. Wato dan tsintuwa ne. Sai dai duk da haka har gobe ba su san matsalarshi ba an barsu a yadda suka dauke shi din saboda a shekarunsu da matakin ilminsu ba za su taba fahimtar matsalarsa ba.
Ki taya ni addu’a Aalimah, Allah ya cika min burina in zama ni ne consultant din Mu’azzam Raazee, in ci gaba da zama tare da shi har karshen rayuwa ta…â€
Sai a lokacin Aboulkhair ya lura matarsa Aalimah kuka ta ke yi, tunda ya yi nisa a ba ta labarin Yayansu Mu’azzam. Kukan kuma ba na komai ba ne, na tausayin Mu’azzam ne.
Murmushi ya yi ya ciccibe ta ya yi dakin barcinsu yana fadin, “My easily crying wife, da na san labarin hawaye zai fiddo daga idon matata da ba’a fara shi baâ€.
Rungume shi ta yi sosai tana ci gaba da kukan, ta ce, “Insha Allah kai za ka koma kula da Mu’azzam, ina rokon Allah Ya cika wannan burin nakaâ€.


Sabida yadda labarin Mu’azzam da tausayin shi ke tsunkulinta a zuci, kwananta uku ba ta walwala.
Jin labarin nasa maimakon ya kwantar da kishirwarta a kan saninsa, sai ya tafi ya bankado wasu sababbin inquisitivities din cikin zuciyarta a kan rayuwarsa. Sai dai tana ganin ya kamata ta kyale mijinta haka a kan dan uwan nasa kada ta wuce makadi da rawa. Ya gaya mata abin da zai iya kuma a matsayinsa na likita akwai abin da ba zai iya fada ba a kan patient dinsa, wani abin sirri ne tsakanin likita da patient dinsa kadai.
Ranar da Aboulkhair zai koma aiki ya ce da ita ta sake yin tuwo in ya dawo ya kai wa Mu’az, tunda ya nuna ya yaba, kuma yana so. Da karsashi da karfin gwiwa ta yi sallelen tuwon semo da miyar kuka wannan karon, yana dawowa ko hutawa bai yi ba ya dauka ya kai masa. Da ya dawo yake ba ta labari Mu’azzam ya ci tuwonta sosai fiye da na ranar da suka je, ya ce ya yi mata godiya, amma ya daina wahalar da ita ya barta ta dinga hutawa. Saboda shi ya dauki girki wajen mace wani abu mai matukar wahalarwa a gare ta ya fi dacewa da maza (a cewarsa).
Dariya ta yi, ta ce, “Ashe da zai yi aure da matarsa ta hutaâ€.
Ya ce, “Sosai ma kuwa, in dai ta fannin girki ne, ko Mummy ba ki ga yadda suke kai ruwa rana ba in ta zo, she want to cook for him, a wurinta abincin gida ya fi na restaurant gamsarwa, a wurinsa hakan bautar da mace ne, musamman ita da shekarunta suka soma turawaâ€.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button