AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Watanni uku cif! Da auren Aboulkhair da Aalimah, Mu’azzam ya yi kokari ya samar mata aikin da ya yi alkawari a asibitin da mijinta yake.Sabida tana zaune a gida bata komai. Wani pharmacy suka tura ta a babban reshensu wanda shi ba asibitin kwakwalwa ne kawai ba, babban asibiti ne General hospital da ya kunshidepartments na kowanne bangare. Sun tura ta wani pharmacy dinsu a Ophthalmology department (bangaren harhada magunguna a tsangayar ido). Kowanne bangare na asibitin akwai pharmacy a cikinsa, don haka duk inda ka ke so a nan za ka sayi magani cikin katafaren asibitin.
Don haka kullum Aboulkhair sai ya fara sauke ta, ya raka ta har cikin ofishinta, ya cire mata abaya ya dora mata farar rigarsu damini hijab dinta da ba sa hana ta sakawa sabida kare martabar addininta, ya rungume ta ya sumbace ta, sannan yake tafiya.
Idan ya riga ta tashi zai zo ya jira ta har ta tashi, sannan su tafi gida. Idan akwai abin da za su saya su biya kasuwa, sannan su karasa gida. Idan kuma ita ce ta riga shi tashi komai dadewar da zai yi haka za ta zauna ta jira shi. Son juna suke kamar su hadiye junansu, ba sa taba gundura da juna. Soyayyarsu mai ban sha’awa da tsafta, wadda duk inda suka zauna sai ta fallasa kanta.
Tun zuwanta gidan Mu’azzam na farko, ba ta kara yarda ta bi Aboulkhair ba, shi kadai yake zuwa. Ta yarda kin mutane da Mu’azzam ke yi, yana da nasaba da mental state dinsa. Da ace za’a bata dama, da ta zauna dasu Basma ta fahintar dasu wanene Yayan su Mu’azzam? A yanzun sun mallaki hankulan kansu sunyi ilmi mai zurfi, sosai zasu yi masa uzri, su bude zukatansu su bashi gurbi. Gurbi na dan uwa mai tsananin kirki kamar Aboulkhair. Maganin wata guda Aboulkhair ke kai masa. Har ta haddace magungunan Mu’azzam don ita ke hadowa ta ba shi. Dose da mgduka ta rike. Rannan yake gaya mata babban likitan Mu’az ya ce zai kara karfin mood stabilizers dinshi, don a samu ya riki wasu al’amuran na social life bayan aiki da ya kwallafa kafatanin rayuwarsa a kansa. Ba ya tunanin kowa, ba ya tunanin komai, babu kowa babu komai a zuciyarsa sai proffession dinsa.
Mummy Zulaiha hankalinta ya dada kwanciya ganin cewa, Mu’azzam ya samu ‘yan uwa a garin da yake, duk da ba gidansu daya ba, ta san ko ya ya ne za su taimaka masa ta wani fannin. Ba zasu barshi cikin ragaita da zaman kadaicin nan nasa ba koda baya so.Ta san cewa, kulawar lafiyar tasa bakidaya ma yanzu a wuyansu ta ke ba.
Aalimah Mansour, na tsaye tana kare wa dan kyakkyawan ofishinta kallo, tana kuma kallon alert na damin kudin da ya shigo mata daga bankinta WellFargo, wai duk wannan albashinta ne na farko. Iyayenta ta shiga yi wa addu’a ba ji ba gani, har Daddy Ishaq ba ta cire cikin addu’arta ba. Wadanda suka tsaya tsayin daka tayi ilmin da ya bata wnnan matsayin. Fitowa ta yi ta rufo ofishin zuwa Atm mafi kusa ta yi wa Daddy transfer na gabadayan kudin, ko dala guda ba ta rage ba, ta hanyar western money transfer. Kudin na shiga Dr. Mansour ya kira Aalimah.
“Kudin me ki ke ta turo mana ne kamar wata ma’aikaciya? Kin yi ya kai sau hudu ina shiru, na yau yafi na baya, ina ki ke samu? Aalimah kada ki kasance cikin masu dora wa mazansu hidimar da ta fi karfinsu don ki wadata iyayenki. Mu din we’re contented with our life ba mu nemi komai mun rasa ba, Aboulkhair me ya tara, yaushe ya fara aikin da ki ke kwakularsa wadannan makudan kudaden?â€
Dariya Aalimah ta yi, sannan ta soma yi masa bayani, cewa kudin farko, na biyu da na uku duk Mu’azzam ke saka mata cikin ATM don ta yi lalurorin gabanta ba tare da ta roke shi ba. Ita kuma ba ta da bukata shi ya sa ta tura musu. Na yau din kuwa halak dinta ne, guminta ne, albashinta ne na aikin da Mu’azzam ya samo mata daDesert Parkway Health Center.
Dr. Mansour kasa magana ya yi, akwai matashi mai zuciyar riko da zumunci a duniya irin MU’AZZAM ???
“Yaa Allah ka dubi wannan bawa naKa da tarin alherinsa da jin kansa ga ‘yan uwa da sauran al’umma, Ka ba shi lafiyar da ka ke jarrabtarsa a kanta, ya yi rayuwa mai dadi kamar kowanne dan Adamâ€. Addu’ar da Dr. Mansour ya shiga yi wa dansa Mu’azzam kenan, wani Da mafi soyuwa a zuciyarsa cikin dukkan ahalin Raazee, manyan su da yaransu.
Shekaru guda biyu kwarara kenan da wannan aure mai dumbin albarka, wanda ya zamo wani tubali na hadin kan iyalin Malam Ibrahim Raazee bakidaya. Ya kawo alheri mai yawa ga kowannensu. Duk weekend Aalimah da Basma na rike da juna a kan waya, sabida a weekend din kadai ta ke samun lokacin gaisawa da ‘yan uwa da iyayenta, saboda yanayin aikinta da hidimar Aboulkhair da ba ta karewa. Shagwababbe, cingam, super glue din Aalimah, dan gatan Engnr. Mu’azzam Raazee. A karshen shekarar Aboulkhair ya koma John Hopkins University ya zana jarrabawar part 2 dinsa. Ba da jimawa ba sakamako ya fito, ya cinye komai da wata irin madaukakiyar nasara, ya dawo asibitinsu inda aka canza masa ofis a matsayinsa na cikakken consultant (Neuro-Psychiatrist) a halin yanzu.
A wannan lokacin ne Dr. Nebrass likitan Mu’azzam na shekaru masu yawa da suka gabata ya danka wa Dr. Aboulkhair Raazee kulawar dan uwansa Mu’azzam bakidaya, ta hanyar damka masa file dinsa sabida shi kansa jinjinawa kwarewa da fasahar Aboulkhair yake yi, kamar wanda ya shekara goma yana practicing. Bai sani ba, hakan na da alaka ne da zuciyar ‘yan uwantaka da shakuwa wadda aka gina karatun kacokam a kanta, sannan shi din shekarunsa na komawa gida ya huta (retire) sun cika.
Zuwa wannan lokacin Daddy Ishaq ya gama komai na shirin komawarsa gida Niger da iyalinsa mata bakidaya. Abu daya yake jira su ajiye ayyukansu su koma (takardar daukarsa aiki da ministere des affaires etrangeres), wato ministry of foreign affairs, hukumar hulda da kasashen waje ta kasar Niger mai location a babban birni Niamey, wadda wani tsohon abokinsa ma’aikaci a wurin da suka yi aiki tare tun a Niger Consulate America yake ta kokarin nema masa.
Sun hadu ita da su Mummy a Massachusetts sun je wa Aboulkhair jami’ar John Hopkins har can garin Baltimore (Maryland) ranar da ya karbi shaidarsa ta zama consultant, tare da shi suka taho Boston. Kwanansu biyu da iyayen nasu da kannensu su Khaleesat wadda ta gama karatunta ita ma a wannan shekarar, suka koma gidansu.
Kafin su shiga gida ya ce, lallai wannan karon sai sun je ta gaida Mu’azzam. Zuwanta daya a kulliyar zamanta cikin garin da yake, sai dai in suna waya da Aboulkhair yakan ba ta su gaisa a gajarce. Ita girmansa da respect dinta gare shi ke hana ta sakewa da shi, a wani bangaren kuma tausayinsa bakidaya. Yayin da shi kuma a nasa bangaren da ma ba ya sakewa da kowa sai Aboulkhair, sai kuma Daddy da kaninsa Mansour Raazee, da kuma kakansa mai ran karfe. Ko Mummy ba ruwanta da rayuwarsa. In ka ji suna magana mai tsawo, to nata matsalolin ne da ta ke neman ya taimaka mata ta fita daga cikinsu. Da shawarwarin Mu’azzam ne ta tabbatar a yanzu ta zauna lafiya cikin sukunin zuciya da kyakkyawar mu’amala da kishiya da dangin mijinta, mutuncinta ya dawo cikin idanunsu.
A halin yanzu ma ta neme shi kan babban kalubalenta na yanzu (barin aiki da Daddy ke so ta yi su koma gida). Tana cikin damuwa da hakan matuka. Abin da Mu’azzam ya ce da ita shi ne, “Mummy me kuma ki ke nema a rayuwa? Kin aurar da duka manyan ‘ya’yanki bayan kin ba su wadataccen ilmi, nan da shekara daya za ki aurar da wadda ta saura. Kudin da ki ka tara shekaru masu yawa ki ka ba ni, ki ka ce in sayi gida in bar rent, gaya miki ne ban yi ba, hannayen jari na siya miki da su a manyan bankunan Nigeria da Niger. A yanzu haka gidan nan da nake ciki mallakina ne, na dade ina biya da kadan da kadan na kuma hada da wani kaso kadan daga wanda ki ka ba ni. Don haka don Allah Mummy ki yi wa mijinki biyayya kamar yadda ki ka saba, ke ma ki zauna waje daya ki huta kamar kowacce matar aure ki fara rainon jikoki da tarbiyyarsu. Aboulkhair ya gaya min Basma ta kusa haihuwa, shi ma tashi matar ta samu yanzu, ga Khaleesat za ta shiga daga ciki ita ma. Mummy you are blessed ki kara gode wa Allah, ki koma neman lahira. Na yi miki alkawarin 40% na albashina duk wataâ€.
Kuka Mummy Zulaiha ta saka, abin da Mu’azzam ba ya so daga gare ta.
“Mu’azzam ban san da wane harshe zan daina cewa ni na jawo rushewar farin ciki da cikar rayuwarka ba. Ba zan iya daina cewa ka yafe min ba! Ka ambaci kowa zai haihu ban da kai, Mu’azzam naka na fi son gani. Mu’azzam ka taimaka min in sake yi maka aure ko me zai faru. Ni ban yarda da kafiran nan ba, namu addinin ya ce kowacce cuta tana da magani, Malam Raazee da kawunka Edrissa sun ce za su nemo magani…â€
Ta ci gaba da kuka sadidan fiye da wanda ta ke yi a baya.
Mu’azzam ya dafe kansa da hannun damansa, jijiyoyin kansa na sarawa. Da kyar ya ce, “Mummy ki daina maganar nan don Allah. Na riga na karbi kaddarata da hannu bibbiyu. Mummy I don’t have a feeling to give to a woman. Mummy aure is not about having sex and children only, there’s a matter of LOVE and AFFECTION. And Mu’azzam don’t have any, not even a remnant. Ki sa a ranki ‘ya’yan Aboulkhair da Basma ‘ya’yana ne da na haifa tunda in an tsaga jikinsu za a ga jinina. Mummy please….. ki daina kukan nan, kina tayar min da hankali. In Aboulkhair ya san abin da ki ke gaya min zai hana ni yin waya da ke…â€.
Alamun zaman mutum ya ji a kusa da shi, ya daga idanunsa da suka rine da sauri ya dube shi, Aboulkhair ne.
Gabadaya yanayinsa ya canza, bacin rai da tashin hankali sun bayyana karara a kyakkyawar fuskarsa. Idanunsa sun kada sun yi jazir. Mummy ba ta kyauta masa ba. Yana tufka tana warwara, maimakon ta shanye damuwarta ita kadai, ko shi ta kira shi ta yi masa. Me Mu’azzam zai maganta mata ban da ta kara masa damuwa, yana fama da jinyar tashi zuciyar da kwakwalwar? Mu’azzam din ya kamata ta gaya wa halin da ta ke ciki a kansa?
Mikewa ya yi zai fita, Mu’azzam ya rike shi yana daga zaune. Bai iya ya juyo sun hada ido ba saboda idanunsa da suka cicciko da hawaye. Murmushi Mu’azzam din ya yi duk da idanunsa sun kada, ya ce, “Ina ruwanka da hirata da uwata? Wato labe ka koma? Kuma meye laifi don ta yi sharing damuwar zuciyarta da ni?â€
Ba tare da ya juyo ba ya ce, “I’m your doctor. Not a brother. I’m responsible for all the progress and the downfall of your health. Da ni ya kamata ta tattauna abin da ta ke tattaunawa da kai. Mummy ba ta kyauta min ba! Damuwa da tunani suna hana mood stabilizers aiki yadda ya kamata. Kuma na san abin da zan yiâ€.
Ya kwace hannunsa zai fita. Mu’azzam ya daga murya ya ce, “Aboulkhair uwata ce fa! Za ka hana ni magana da ita ne? Ka shiga hankalinka kai da likitancin naka. Rayuwa da ciwo duka a hannun Allah suke. Idan Allah ya ce ma mutuwa zan yi dukkaninku ba abin da za ku iya. Ni gara ma in mutu in huta da wannan rayuwar…!â€
Da gudu Aboulkhair ya dawo ya rungume shi. Hawaye ya soma yana fadin, “Insha Allahu kai za ka binne ni, ba dai ni in ga kabarinka ba Mu’az, ba zan iya jura ba. Zan yi abin da ya fi hauka, ba zan iya rayuwa ba, na roke ka kada ka kara yi min wannan fatanâ€.
Ya dago shi ya zaunar kusa da shi, yana bubbuga bayansa.
“Na ji ba zan kara ba. Amma kada ka kara fadin in ba ni ba za ka iya rayuwa ba. kowanne rai sai ya dandani mutuwa Aboulkhair. Abin fatan shi ne mu cika da kyau da imani. Ka yi wa Mummy uzuri kada ka ce mata komai a kaina.
Ta hanyar expressing griefs and sorrows dinta (bakin cikinta) a kaina ne kadai za ta samu sassaucin tata zuciyar. Ni ne mai ciwo Aboulkhair, amma UWA ta fi ni ji a jikinta. Yanzu tashi mu je kasa in ba ka Sangria Mocktail (Non-Alcoholic fruit drink) ka sha, ka kai wa matarka ita ma. Dazu na yi order dinsaâ€.
Murmushi Aboulkhair ya yi, kaunar Yayan nasa na kara keta zuciyarsa. Ya san so yake ya gusar masa da bacin ransa. Sai a lokacin ya tuna tare da Aalimah yake ya barta a falon kasa.
“Tare ma muke da ita, mu je ka bata da kankaâ€.
Suka sauko tare.
Tun daga nesa ta hango su don haka ta kara nutsuwa ta ajiye littafin da ta dauka na Mu’azzam, wanda ta fahimci dubawa yake yi ya ajiye ya tashi, ‘The Danger Of Hypersexual Disorder (By Dr. Martin Kafka, 4thEdition)’.
Da sauri ta ajiye ba tare da kowannensu ya lura ba. Aboulkhair ya zauna a kusa da ita, Mu’azzam ya wuce firjinsa ya zuba mocktail din a manyan kofunan glass guda biyu, ya sanya straw a kowanne ya iso gare su. Aalimah ta sa hannu tana ture Aboulkhair daga kusa da ita, shi kuma ya ki turuwa har Mu’azzam ya iso. Karshe ita ta tashi ta matsa gefe, Aboulkhair ya bi ta da harara.
“Koma wajenki ki zaunaâ€. In ji Mu’azzam da muryar manyantaka irin tashi in yana magana da ita, wadda ta dade da lura ba da irinta yake yi wa Aboulkhair magana ba.
Aalimah ta sunkuyar da kai tana murmushi, a kunyace ta ce, “Shi ya ce in mun zo gidan nan kada in zauna kusa da shiâ€.
Aboulkhair ya hangame baki, ya ce,
“Yaushe aka yi haka???â€
Mu’azzam ya mika mata kofin, hannu biyu tasa ta karba ta yi godiya ya samu kujera mai fuskantarsu ya zauna. Ya dubi Aalimah ya ce,
“Kin ga kuma ni din, sanda ya fara sonki sai da na yi da gaske ya tsaya ya yi karatu. Sai da na ce zan aura masa mata hudu in ya dage ya zama Psychiatric dina. Yanzu haka yana min tunin ukun da suka yi saura ne a sama kafin mu saukoâ€.
Aboulkhair ya sake kwalalo idanu ya sake hangame baki, ya ce, “Yaushe aka yi haka???â€
“To mu duka ka mana tambaya iri daya, wadda ke nufin dukkanmu kana nufin mun yi maka karyaâ€.
Mutsu-mutsu ya hau yi da baki yana rokon Mu’azzam da ido ya warware masa gadar zaren da ya kulla masa ba tare da ya ce da ita ya yi karya ba.
Aalimah ta fahimci halin da Mu’azzam ya jefa mijinta, har gumi yake yi, duk da sanyin garin Las Vegas, ta ce, “Yaya Mu’azzam ai addini ya bashi damaâ€.
Mu’azzam ya zuba mata ido na ‘yan dakiku, ba tun yau ba ya fahimci yarinyar tana da hankali, ga nutsuwa da girmama na gaba. Ya ce,
“Haka ne Aalimah! To amma me ya sa ya ce kada ki zauna a kusa da shi a gidana?â€
Da sauri Aboulkhair ya ce, “Ni fa ban san an yi ba Aalimah, ban sanki da karya ba!â€.
Dariya ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, ta ce, “Yaya Mu’azzam ka san ko zan yi karya kai ba zan yi maka ba. Wai kunyarka yake jiâ€.
Murmushi Mu’azzam ya yi, murmushin nan nasa ingentleness,ya juya yana kallon Aboulkhair da kyawawan idanunsa cike da kauna, bai ce komai ba. Duba agogo ya hau yi, Aalimah ta ce a ranta, “Mun shiga lokacinsaâ€.
Tun kafin ya ce, “Ku je na sallame kuâ€. Dinsa tayi buzut ta mike ta ce,
“Mun tafi Yaya Mu’azzam, sai mun sake shigowaâ€.
Yana mai kara yaba hankalinta ya ce, “Tun ban sallame ku ba? To na gode, kuma ki je ATM.I’ve nothing to give youâ€.
Murmushi ta yi ta ce, “Muna godiya ni da wadanda nake aikawa kudin. Allah Ya kara budiâ€.
Juyawa ya yi ya haye upstairs dinsa.
6/30/21, 11:09 AM – Buhainat: 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€