AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@

Suna tafe a hanyarsu ta zuwa gida, Aboulkhair ya ce, “Me ya sa ki ka gaya masa ba kya amfani da kudin da yake ba ki? Ai ba zai ji dadi baâ€.
Ta gyara zamanta da lullubin kanta, ta ce, “Saboda ya san ba ni da matsala ni, kada in zamo mai hadama. Ga aiki ya sama min ana biyana albashi mai tsoka, kuma yana bina da kudi kusan kamarsu duk wata, ai na zama mara godiyar Allah. Zai yi tunanin me nake yi da su, ga mijina bai rage ni da komai baâ€.
Girgiza kai kawai Aboulkhair ya yi, har yau Aalimah ba ta san Mu’azzam ba. Bai kuma san irin bayanin da zai mata ta fahimce shi ba. Ba ruwanshi da abin da kowa ke ciki ko me wani ke gudanarwa a rayuwarsa. Shi kansa bai damu da rayuwar da yake ciki ba. Ba komai cikin ransa sai kwarewa da aikinsa na hakowa da tace man fetur (Exploration and refining petroleum). Tana wahalar da kanta wajen son ya fahimci me ta ke ciki, ba fahimta zai yi ba. Wani saint (waliyyi) ne shi a cikin turawa, kowa ya je ya yi abin da ke gabansa.

A karshen sabuwar shekarar da ake ciki sun yi shawarar za su dauki hutu lokaci daya saboda su samu zuwa Nigeria daidai lokacin haihuwar Basma. Kuma watan haihuwarta ne watan bikin Khaleesat. Duk da rashin wadatacciyar lafiyar ita Aalimahr ita ma tana fama da laulayin ciki wata hudu, boye rashin karfin jikin nata ta ke ga Aboulkhair tana kwarara kanta a gabansa, don kada ya hana ta zuwa. She missed Basma so much yadda ba za ta iya bayyanawa ba duk da suna waya a kowanne karshen sati, ga dokin ganin abin da za ta haifa mata tunda kuwa dan Yaya Aboubacar ita za a haifa mawa halak-malak. Fatanta ma a nan gaba in za su amince su bata ta hada da wanda za ta haifa ta rike a nan Las Vegas.
Mu’azzam ya samu karin ‘yan uwa masu kula da walwalarsa, ta san in ya hana kowa damunsa ba zai hana ‘ya’yansa ba. Tun daga lokacin da ta san wanene shi, ta damu da al’amarinsa sosai.

KANO-NIGERIA
Sun sauka a birnin Kano ranar alhamis. Ba matar ba, ba mijin ba, kowannensu ya yi ‘yar kyakkyawar kiba kib-kib ga kumatu luwai-luwai a fuskar Aalimah wanda a da ba ta da shi. Yaya Aboubacar ne ya zuba su Sabrina a mota suka je filin jirgin saman Malam Aminu Kano suka dauko su.
Basma na ta kiran waya tana ita a wuto mata da Aalimah ba ta yarda ta fara zuwa sultan road a bata mata lokacin ganinta ba. Aalimah na ba ta hakuri tana gaya mata ba za ta iya kara minti goma ba ta ga Mama ba alhalin tana cikin Kano, ta mata alkawarin har kwana za ta yi a gidanta in ta huta, saboda an hana basma fita saboda ta shiga EDD ga cikin mai wani irin girma.
Sun yi waya da su Mummy su sai bikin Khaleesat saura sati daya za su samu tahowa, yau kuma saura sati biyu.
Mama ta fito kofar shiga falo tana kallon Aalimah na fitowa daga mota da dan matashin cikinta tsab da ita cikin wata irin shiga ta doguwar riga ruwan hanta kirar Abu-Dhabi, takalminta ma kalarsa kenan marasa tsayin dunduniya dan kasar Italy. Ta yi wani irin haske mai nuna yanayin rayuwar da ta ke ciki wanke hannu ka taba. Aboulkhair da Aboubacar suna cikin motar ba su fito ba, suna maganar da ba ta san ta mece ce ba (zancen tafiyarsu Nijar suke daga Kano don fara shirin auren kannen su Hamoud da Khaleesat sati mai zuwa idan su Daddy sun iso). Su Suhaima sun rirriko hannayenta kamar sa cinye ta don murna. Shi kansa Aboulkhair din da ta hango ta cikin glass ya yi kyau da kibar da da gani ka san na zaunuwar wadata da kwanciyar hankali ne, fiye da lokacin da yake neman auren Aalimah. Godiya ta shiga yi wa ubangiji a fili tare da binsu da addu’a iri-iri a zuciyarta.
Daidai lokacin da ta ji Aalimah da tattausan jikinta da kamshin jikinta sun rungume ta. Dariya ta yi ita ma ta yi mata kyakkyawar runguma. A yadda Aalimah ta zama matar Neuro-psychiatrist da yawan tu’ammali da patients din Aboulkhair ko duba su da yake tana zaune, da yawan tattaunawa da suke kan cututtukan, ita kanta tana da experience mai dumbin yawa a kan mental health illnesses. Ta fahimci akwai ci gaba sosai da stable treatment a tare da Mamanta fiye da baya.
Shi kansa Daddy da ya dawo nan-nan yake ta yi da Aalimah da maigidanta. Ya rasa ina yaka saka-ina-yaka-aje da su. Kowa ya yi kewar kowa. Shekaru uku cif kenan ba su ga juna ba. Baban da Aboulkhair suna labari, Aalimah da Mamanta da kannenta na yin nasu a daki. Hirar Baban su Aalimah da surukinsa Aboulkhair yawanci kuma kaso tamatin cikin dari ta Mu’azzam ce. Yau Dr. Mansour Raazee ya kara sanin abubuwa masu yawa dangane da Mu’azzam har da wadanda Daddyn su Aboulkhair ya cire a nasa labarin da ya basu a Nijar. Kamar cewa Clearson ya koya wa Mu’azzam kallon fina-finan batsa tun kafin shekarun balaga wadanda su ma suna cikin causes na hypersexuality disorder a shekarun girma. Daddy gefe ya koma yana share hawaye da hankalinsa, ya ce da Aboulkhair wa ya sani ma ko har kwayoyi ya banka masa? Wa ya sani ko ya koya masa ma wata lalatar bayan wannan?
Aboulkhair ya yi murmushi, ya ce, “Daddy ka daina kuka, abin da ya wuce ya wuce. Kuma ni ina tare da su a lokacin na san komai. Na san abin da suke yi da wanda ba su yi ba, duk da karancin shekaruna. Ka ga Clearson bai taba neman Mu’azzam ta wata hanya ba saboda ‘yan wani addini ne wai shi Rastafari, wanda ya haramta musu neman jinsi, sannan ban taba ganin wata yarinya mace ta shiga gidan su Clerson ba, shi kadai ne kwal a wurin iyayensa ya tsoka daya a miya, sannan a shekarun Clearson a lokacin ya san rape shi ne mistake na karshe a kasar Turai, musamman ga su bakin haure. Ya fito ne daga wata kasa Portugal shi da iyayensa. Kwayoyi kuma ba zan iya cewa ba su sha ba, tunda wanda ya sha giya sanda zai sha kwaya ma ba zai sani baâ€.
Daddy sai kuka kamar wani karamin yaro, ya ce da Aboulkhair, yanzu ba don magungunan da yake sha ba, ci gaba zai yi da alcoholic consumption?
Aboulkhair ya girgiza kai, “Daga shekaru goma sha tara Mu’azzam ya san cewa, Clearson ya illata masa rayuwa. Daga wadannan shekarun shi da kansa ya daina sha’awar giya. Daga lokacin da ya tabbatar wannan aggressiveness din nasa da ke sa shi ya illata lafiyarsa ya ji wa kansa ciwo, ya yi wa Daddy asarar komai na gidansa giyar da ya sha ce sanadi, ko a boye bai kara kallonta ba. Daddy ya dauke Mu’azzam daga America tsayin shekaru uku ba tare da yardar Mummy ba, bayan mun bar garin da Clearson yake babu wanda ya san inda ya kai shi sai ni, har gobe. Kuma na tabbata kuma bai gaya muku ba. Daddy you are Mu’az’s father also, ina gaya maka Wadannan sirrukan na Mu’azzam ne saboda haka kawai jikina ke gaya mini watarana za ka taimaka masa sabida dumbin kaunarka gare shi. Ina raye ko ba na raye, and Daddy will not tell anybody wasu muhimman abubuwa irin wadannan da suka shafi Mu’azzam saboda daga shi har Mu’azzam din yanzu ba sa son tunawa.
Ya kai shi birnin Medinah shekaru uku a wani gari wai shi YAMBOU hannun wani shehin malami dan asalin Hijaz (Madinah) ya sanya shi a wata makarantar mmalamin a wani kauye Yambou. A can ya yi sauka, ya yi hadda ya manta da rayuwar da ke cikin America bakidaya da zaman da ya yi da Clearson, yana kuma zuwa duk bayan wasu watanni yana kai masa magungunansa. Bai dawo da shi ba sai da ya ga zai zarce shekarun shiga jami’a. Bayan ya dawo kememe ya ki zama tare da kowa, ya zabi zama nesa da gida, wato birnin Nevada (Las Vegas) inda muke gabadayanmu yanzuâ€.
Dr. Mansour ya saki baki da kunnuwa yana jin Aboulkhair, ba Mu’azzam kadai ya ji tausayi ba wannan karon, har da dan uwansa (Ishaq), su suna nan suna ta jin haushinsa ba ya kula ‘yan uwa sabida ya samu duniya, shi yana can yana fadi-tashi don gyara rayuwar dansa da aka lalata masa. ko zaryar zuwa Madinah daga America wani hanzari ne mai zaman kansa. Ko a ina ya samo Balaraben da ya kai wa Mu’azzam din? Oho!
Aboulkhair ya ce, “Through internetâ€.
Sheikh Bahari Limamin babban masallacin Yambou ne. A wata lecture da ya saki a yanar gizo ne ya ce, yana da maganin raba matasa da shan giya da drug addiction komai tsananinsa in dai za a iya yin tattaki a same shi har inda yake. A nan ne Daddy ya samu email dinsa suka tattauna ya taimaka musu da yadda za su samu visa kai tsaye zuwa Yambou ba ta umrah ba. Saboda in ta umrah ce ba za ka iya shiga Yambou ba, ta karatu aka yi wa Mu’azzam. Makarantar kuma mallakinsa ce mai zaune da lasisi daga gwamnatin Saudiyyah. Mu’azzam ya shiga ransa daga ganinsa na farko da shi kuma da bakinsa ya gaya masa yana so ya bari, ba ya son ganinta ba dadinta yake ji baâ€.
Daddyn Aalimah sai karin hawaye.
Aboulkhair ya ce, “Wallahi Daddy bayan dawowar Mu’azzam daga Madinah ko sallarsa abin kallo ce, saboda hakkinta da yake ba ta, a wajensa na koyi gyara sallah ta, a wajensa na koyi komai na ibada na gane su kansu Malaman da ke koyar da mu a America duk rabi baragada ce, ilmin musulunci bai wani ratsa su baâ€.
Daddy ya girgiza kai ya fyace hanci, ya ce, “To wai ni shi kenan haka zai dauwama? Aure da haihuwa sai dai ya gani wurin kannensa?â€
Aboulkhair ya ce, “Daddy mu yi sirri mana ni da kai?â€
Murmushi Dr. Mansour ya yi, ya ce, “Mu yi Aboulkhair, ko Ishaq bai isa ya ji ba idan ba kai ka yarda ya ji baâ€.
Aboulkhair ya matso jikinsa sosai kamar zai shige jikinsa, ya ce, “Daddy sabida Mu’az na karanci Neuro-Psychiatry, saboda in san wannan lalurar ciki da bai dinta, saboda a yadda na fahimta su kansu likitocin Mu’azzam ba su da magana kwaya daya game da warkewarsa, ko rashin warkewarsa. Bakunansu sun rabu. Na zabi John Hopkins saboda duk duniya ita ce lamba daya a ilmin Psychiatry, Daddy har gobe bincike nake ban fasa ba, ko bayan zamowata consultant. Aalimah shaida ce kan cewa sai in kwana uku a asibiti ba ta gan ni ba, amma ko kusa ba ta damuwa. A gida ma na kan kulle kaina a study room dinmu yini guda in ce ko abinci kada ta ba ni sai na nema da kaina. Ta kan ce ba ta taba ganin mai son dan uwansa irina ba, tana fatan wannan zumuncin ya kai mu aljanna ni da shi bakidaya, saboda ta lura nawa kadan ne a kan nasa. Kowa ya je masa gida damunsa yake ban da ni. Kowa kamar a kansa yake in dai zai masa awanni cikin gida, amma ni in ya yi kwana daya bai gan ni ba sai ya neme ni. Akwai sanda na kashe waya tsayin kwana biyu ina bincike, ta ce fada yake mata kamar zai doke ta kan ta turo masa ni, ba ruwanshi da wani bincike na.
Daddy duk ina gaya maka wannan ne saboda ka gane irin son da nake yi wa Mu’azzam, Daddy dama ni ne wannan lalurar ta ke a kaina… In dai zan ga ‘ya’yan Mu’azzam da fararen hakoransa a waje yana dariya kamar kowa. Ranar da na dauki hutun tahowa na gama wallafa littafina na farko;A Psychometric Investigation Of The Hypersexuality Disorder- Aboulkhair I.R’, kuma har na yi submitting dinsa a sashenmu na Neuropsychiatry a John Hopkins, tsofaffin malamai za su sake duba shi kafin a sake shi a duniya da sauran jami’o’in America. Kuma Proffessors na tsangayarmu bakidaya da tsofaffin likitoci na asibitocinmu daban-daban, da wadanda suka shude kafinsu a fannin sun tabbatar da cewa, wannan shi ne dependent kuma tsaftacciyar magana ta karshe a kan aggressive tendency and Hypersexuality Disorderâ€.
Dr. Mansour Raazee ya kama hannunsa ya rike tamau cike da fargabar abin da zai fito daga bakinsa… wanda shi ke determining future din rayuwar Mu’azzam, sai dai kafin shi ko Aboulkhair su ce komi Aboubacar da Aalimah sun yi sallama sun fado dakin a hargitse, wai basma Aboubacar ya kai asibiti yanzun nan za ta haihu, kuma haihuwar ta zo da tangarda. Likitoci sun tabbatar musu ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ‘yan biyu ne, kuma haihuwar fari, ga shi ba ta exercise duk karfinta ya kare. Ana bukatar ya saka hannu kafin a yi mata aiki, shi ne ya zo su tafi gabadaya.
Fada Daddyn ya hau shi da shi, kan me ya sa ya taho ya baro ta ba tare da ya saka hannun ba? cikinsu wa ya fi dacewa da sanya hannun? Ya kasa ganewa Aboubacar a rude yake ba abin da zai iya kulla wa kansa a wannan lokacin.
Dukkansu suka dunguma zuwa asibitin standard inda a can ne Basma ke awo, Aboulkhair ya taimaka masa ya sanya hannun aka shigar da Basma dakin tiyata.
Aalimah ban da kuka ba abin da ta ke yi. Damuwarta shi ne, ko tozali da juna ba su yi ba. Ba yadda Basma ba ta yi ba kan ta zo ta ganta ko na minti goma ne ta koma, ta ce ita sai gobe. Da ta san haka ce za ta faru da ta je din, ta san Mama ba za ta hana ta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button