AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Suna nan zaune jigum-jigum kowanne da carbi a hannu, ABoubacar sai safah da marwa yake a cikin asibitin. Mama ta koma gidansu don ta dauko kayan haihuwar da gigicewa ba ta bar Aboubacar ya dauko ba.
Aboulkhair ne kadai mai karfin hali, don waya yake yi da Mummy yana gaya mata ta yi wa Basma addu’a tana dakin haihuwa, kuma an ce ‘yan biyu ne. Sai dai bai gaya mata CS ake mata a halin yanzu ba, kada hankalinta ya zarta. Ya san Mummy sarai a kan son ‘ya’yanta.
Suna cikin wannan hali nurses biyu suka nufo su dauke da jarirai biyu cikin fararen shawul. Haba! In ba ka yi ba ni wuri, kowanne da gudu ya riske su tun kafin ya karaso tsakanin Aboubacar da Aalimah da Mama, Aboulkhair na yi musu dariya, don ya san shi kam ba za su ba shi ba. amma Aboubacar sai ya bi su yana tambayarsu lafiyar uwar jariran, murnar tasa rabi-da-rabi ce. Murmushi daya daga cikinsu ta yi masa, ta ce,
“Nan da minti goma sha biyar za ka iya ganinta a dakin aminityâ€.
Sai da aka gyara Basma aka kai ta daki, sannan aka ba su izinin ganinta. Aalimah ce a gaba, suka yi tozali da juna bayan rabuwar shekaru uku, ga ba damar rungumar juna, Basman na kwance ciki a farke. Sai murmushi ta ke wa Aalimah, ta miko mata hannu ta kama ta matse hannun sosai, sai kuma suka saki dariya dukkansu.
“Welcome to 9jaâ€. In ji Basma.
Da ‘yar siririyar wahalliyar murya, Aalimahr kuma ta ce,
“I congratulate us for becoming mummiesâ€.
Aboubacar ya karaso da Hussainar ya dora mata a gabanta, Aalimah ta karbo Hassanar daga hannun Aboulkhair ta jera mata a gaban ‘yar uwarta. Basma ba ko kunya aka bude ido ana kallon ‘ya’ya, bakin nan kamar zai tsage don murmushi, ko kunyar Mama da ke gefe.
Aboulkhair ya ce, “Kin ji haushi wollah, mutum ba kawaici ko kadan?â€
Mama ta ce, “Kyale ta ta gode wa Allah baiwar da Ya yi mata, kyautar ‘ya’ya mata biyu lokaci daya ma’abota jin kan UWA!â€
Aboulkhair ya ce, “Au abin haka ne Mama? Mata na iyayensu mata ne? Ma cherie ba zan yarda ba, in kin zo taki kihaifo biyuamma mace da namiji kowa ya dauki nasa, ko ki haifi namiji daya, daga baya ki haifo takin. Amma wannan ai wayo neâ€.
Kowa sai dariya har Aalimahr, duk da ta ji kunya. Haka Aboulkhair yake, very friendly to all. Shi ya sa yake da shiga ran kowa. Ba yadda za a yi ka yi zaman minti goma da shi ba ka nemi kun yi alaka ba. Bai da miskilanci, bai da jin kai. Ba za ka taba zaton da consultant ka ke zaune ba, sai dai saurayi dan makaranta.
Sai da suka kwana uku aka sallami Basma, suna ta ja wa Mama kunne ban da wankan ganye, sai na tawul. Murna a wurin Basma ba a magana, da ma ita wannan wankan ganyen da runhu da Mama ta ce in ta haihu sai ta yi mata ba karamin tayar mata da hankali yake ba.
Nan sultan road suka taho, Aboubacar da Aalimah suka je Hotoron suka dauko mata duk abin da za ta bukata.
Aalimah ta dade tana sai wa basma kayan haihuwa, duk abin da Aboulkhair ya sayo ya kawo ya ce ta ajiye saboda babynsu, sai ta saya wa Basma irinsa. Don haka ba kananan kaya ta tara ta taho mata da su ba. har da laces da tsadaddun materials don fitar biki. Ga wadanda Mama ta saya, ga na Aboubacar maigida kan gida. Ba a maganar wanda Mummy da Gumsu za su kawo nan da kwana hudu in sun iso. Don haka Basma da ‘ya’yanta sun ga gata, kuma suna kan gani, don jin cewa ‘yan biyu ne Mummy da Gumsu aka bazama kasuwa aka yi discarding waccan sayayyar aka ce an bar wa Aalimah, komi bibbiyu suke saye, kuma iri daya, ga shi an san abin da aka haifa.
Kwanan Basma bakwai cif! Da haihuwa wanda ya yi daidai da saura kwana biyar daurin auren Khaleesat saboda su Niger sai an fara daura aure ake shiga shagalin biki. Su Mummy suka iso Nigeria ita da Daddy da amarya Khaleesat da sauran ahalin gidan su Gumsu da kananan ‘ya’yansu Yesmin da Nurat. Kodayake yanzu ba mai kiran Yesmin yarinya, tunda kuwa shekarunta goma sha biyar.
Gida ya kacame da hidima ko ta ina, Mama da Gumsu nata jajircewa wajen kula da maijego da ‘ya’yanta. Sun so su yi taron suna a ranar ba zai yiwu ba, kasancewar duka ‘yan uwansu na nesa daga na Mama har na mahaifansu maza sai ‘yan uwan mummy Zulaiha ne suka zo, da yake su ‘yan Kano ne, su ma ba dukkansu ba saboda ba a gaya musu da wuri ba. Don haka su-ya-su suka yi get-together dinsu. Aka ce in ta yi arba’in ta je Nijar da maid. Amarya Khaleesat ta sha ado, maijego da Aalimah sun yi anko na wani masifaffen leshi baki mai fararen duwatsu da Mummy ta taho musu da shi a dinke. Daga wani kwararren gidan hoto na kano Aboubacar ya dauko mai daukan hoto ya zo ya yi ta daukarsu. Shi da Aboulkhair ma sun shigo an yi hotunan da su, kowanne kuma ya yi da matarsa a falon Daddy kamar wasu sababbin aure a yanayin da suka firfito cikin hotunan.
Basma ga bikin zuwa, amma babu zanen daurawa, wai bikin Khaleesat amma an ce ba ita za a yi saboda kawai ta haihu, kuma yanka ta aka yi. Ta turka kuka da magiya, amma babu wanda ya bi bayanta har Mummy mai gudun bacin ransu. Fada ma ta hau ta da shi tana fadin, ba ta da hankali, wadannan jariran sabuwar haihuwa za ta zuba a mota zuwa wata kasa biki, saboda ba ta da imani? Idan ba ta tausayin kanta, kuma ba ta san muhimmancin lafiyarta ba? Mama saboda ita ta ce ta hakura da bikin. Amma duk ba ta gode ba.
Aalimah ce kadai ta ke rarrashinta, a karshe ta ce, tunda Basma ba za ta ba ita ma ta hakura, da ma aiki zai wa Mama yawa, tunda ita ke kula da su ita kadai, masu aiki aikin gida kawai suke yi, amma har girkin abinci a wuyan Mama yake.
Khaleesat kuma sai ta sa kuka ita ma ba ta yarda ba, aurenta guda babu manyan yayyenta mata ba a yi mata adalci ba.
Karshe Daddy Ishaq ne ya raba wannan rigimar. Ya bai wa Khaleesat hakuri soslai, ya ce ta gode wa Allah da kyautar da ya yi mata ta ‘ya’ya har biyu, ta bar Aalimah ta zauna da ‘yar uwarta. Babu abin da za a fasa, a can Niger ma wasu tarin yayyen na jiranta za su yi mata komai.
Gumsu ta ce, “Ba ga su Balkeesa ba? Kuma ita Aalimah sai ta raka ki har Japan insha-Allah (Khaleesat a kasar Japan za ta zauna inda aka tura Hamoud ya karo wani course duk dai a kan sojancin ruwa kafin ya kammala ya dawo ya yi wa kasarsa Niger Republic aiki na din-din-din)â€.
Aka samu Khaleesat ta hakura, sai suka koma tsara yadda tafiyarsu Niger za ta kasance.
Daddy ya ce amarya da su Mummy za su wuce jibi, kwana biyu da suna kenan. Su kuma sai ana i-gobe daurin aure za su yi asubanci. Mu’azzam ma sai ana i-gobe daurin aure zai shiga Niger. Ya yi musu booking Niamey Flight bakidayansu, har kannen Aalimah mata amma dole sai sun je Abuja babu jirgin Niamey daga Kano.
Su Mummy suka tashi zuwa Niamey suka bar masu jego, Aalimah da dukkan zuciyarta da lafiyarta ta ke hidimtawa Basma da jariranta. A gefe ga takurar Aboulkhair wanda kawaicinsa ya fara karewa, zaman ya fara gundurarsa shi da matarsa sai daga nesa. A gidan Aboubacar suke zaune shi da Aboubacar din. Cin abinci kadai ke shigo da su gidan. Har bankin GT Aboulkhair ke bin Aboubacar yana ganin yadda suke gudanar da ayyukansu, inda Aboubacar yake a branch dinsu na Hotoro. System din aikin Nigeria yana ba shi mamaki, ka wuni kana aiki amma albashin bai fi ka kashe shi a sati daya ba. Wai ma banki kenan, bankin ma mai daraja irin Guaranteed Trust.
Aboubacar ya ce, “A wurinka kenan. Mu kam ai mun san yadda muke tattala kayanmu ya kai mu karshen watan. Basma ma a nan ta ke aikin, saboda jami’ar da ta fito da na kawo wa manajanmu takardunta da gudu suka dauke ta ba tare da la’akari da abin da ta karanta baâ€.
Irin hirarrakinsu kenan na matasa masu jini a jika, ‘yan uwan da suka san muhimmancin junansu.
Ana i-gobe za su tafi Niger bayan sun zo sun ci abincin dare wanda Aalimah ta dafa ta yi serving dinsu a dining ta koma gefe tana cin nata. Tunda suka zo suka raba plate saboda idon iyaye da sanin ya-kamata. Amma a nasu gidan bayan plate guda ma da one spoon suke amfani. Aboubacar ya riga gamawa ya tashi ya nufi wurin iyalinsa, wadanda suke a dakin Aalimah na gidan. Kamar jira Aboulkhair yake ya tashi, ya ajiye cokalinsa ya mike. Ya juya kofar dakin Mama da alama ta kulle ta ciki duk da dai ya san ba ta yi barci ba. Hannun Aalimah kawai ya kama ya mikar da ita. Za ta yi magana ya dora yatsa a baki, “Zo mu je, sako zan ba ki, yanzu za ki dawoâ€.
Aalimah ba ta gane Aboulkhair so yake su bar gidan ba, sai da ta ji ta a motar Aboubacar, ya tada motar da gudu, suka harba kan titi.
Kasa magana ta yi har suka iso gidan Basma. Ya shigar da motar cikin gate maigadin ya rufe ya wuce ciki ba tare da ya bari sun hada ido ba. To amma ai ita ta san kan kayanta, a kwayar idanunsa ta ke gano komai nasa. Kuma a yadda ta san halittar mijinta ta san ya yi kokarin da bai taba yi ba tun bayan aurensu. Sai ko komawar saJohn Hopkins yin part two exams dinsa da suka jima ba sa tare. Ranar da suka hadun kuwa, har gobe ba za ta manta yadda ranar ta gudana gare su ba, with a fondest thought!
Girgiza kai ta yi cike da tausayin mijinta, ta fito ta bi bayansa. Tun a falon Basma al’amuransa suka soma ganar da ita kewar tata da ya yi ba ‘yar kadan ba ce. Ba ta hana shi komai ba, karewa ma samun kanta ta yi da ba shi hadin kai da zuciya da gangar jikinta bakidaya fiye da na kowacce rana cikin rayuwar aurensu. Da wani irin feeling a zuciyarta da ruhinta da ba za ta iya kwatantawa ba.
Gare shi jin ranar yau yake kamar ranar da ya bare ta a ledarta, komai nata ya kara canzawa fiye da baya, sakamakon matashin cikin jikinta. Aalimah, na cikin sahun matan da ba sa taba gundurar mazajensu sabida baiwar ni’imar da Allah ya yi musu, wanda ita kanta ba ta sani ba, shi kuma ba shi da bakin furta mata hakan sai dai ta gani practically daga yanayin da yake kasancewa a kullum suke tare, wanda ke kara mata kaunarsa.
Dukkaninsu ba su san sanda wani irin barci ya sure su ba, wanda ba shakka na gajiya ne, saboda dukkaninsu sun taimaki juna ne ta hanyoyi da dama da ba su taba samun kansu a ciki ba.
Karar wayarsa ce ta tashe shi, ya janye Aalimah daga kafadunsa ya ga Aboubacar ke kiransa.
“Ban tambaye ka inda ku ka tafi ba, kawai ku yi zamanku da asubah mu biyo mu dauke ka, ita kuma ta dawo da kanta, ai ta san gariâ€.
Dariya Aboulkhair ya yi, wadda ta tada Aalimah daga nata daddadan barcin, suka soma shirin barin gidan.
6/30/21, 11:09 AM – Buhainat: I’m writing this chapter with heartfelt TEARS ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜