AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Sanda suka iso karfe goma sha biyu na dare Aboubacar na kofar gida. Kasa fitowa daga motar suka yi dukkansu duk da sanin da suke da shi na cewa Aboubacar zai iya hango su ta glass. Hannunsa ya dora a kan cikinta yana sauraron harbawar jaririn yana lumshe idanu ya ce, “Kin san wani abu?â€
Girgiza kai ta yi, haka kawai ta ji ranta ba dadi, kamar su koma gidan Basman su kwana tare. In ya tafi Niger ita da ganinsa sai nan da kwana goma in an gama bikin Khaleesat, sannan ne zai zo su koma. Ba lokaci daya za su tashi da ‘yan Massachusetts ba, su sai nan da sati biyu. Ko dai ta kyale Basma ne ta bi mijinta ga kyawawan ‘yammatan nan na zuri’arsu da ba ta san iyaka wadanda za su kalle mata shi ba? Wani bala’e’en kishi ya turnuke ta irin wanda ba ta taba sanin tana da shi ba. Sabida a inda suke rayuwa ba ruwansu da irin wadannan abubuwan kowa da life-partner dinshi ba mai shiga gonar wani. Ta girgiza kai, ba tare da ya fahimci tunanin da ta ke ba, ya ce, “In namiji ki ka haifa ‘MU’AZZAM zan sa masa, in mace ce, ‘AALIMAH’ (mai ilmi) yadda zan ji dadin gaya mata how sweet and loving her mum is, how helping and generous she is, how much I truly love her and the long time I spend waiting to marry her. Duka zan gaya mata Aalimah, idan kuma namiji ne zan gaya masa yadda na rayu cikin soyayyar dan uwana mai lalura, yadda nake sonsa da burin samun lafiyarsa. Yadda ya kyautata wa rayuwata, ya tsaya min against all odds. Ya mayar da ni abin da nake a yau; Aboulkhair mai rayuwa da tsayayyun kafafu mamallakin Aalimah. Har ga shi za ta samar da Da a gare mu ni da Mu’azzam…â€
A lokacin ya ankara Aalimah kuka ta ke yi.
“Mon Amour na fasa zama, tare za mu tafiâ€.
Dan tsayawa ya yi yana nazarinta gabadaya ta birkice kamar ba ita ba. Nazarin maganganun da ya furta yake yi, ko akwai na tashin hankali a ciki? Iyakar tunaninsa bai gani ba. Kuka ta ke yi shabe-shabe da hawaye da majina. Janyo ta ya yi jikinsa, ya ce, “Aalimahâ€. Sunanta na hakika.
“Nda’amâ€. Ta amsa cikin rishin kuka, don rabon da ta ji ya kira ta tun zamanin samartaka (‘yammatancinsu).
“me na fada wanda ya bata miki rai?â€
“Babu komaiâ€. Ta amsa da sauri.
“To me ya sa za ki canza shawara cewa sai kin je Niger? You are kidding. Kada ki dauka ban san halin da ki ke ciki ba, ko daga kumburarrun kafafunki. Kina wasa ne ma da ki ke tunanin zan barki ki shiga kujiba-kujibar bikin nan na Niger, ki je kina girkin roti da rawa a wajen cocktail, ki jawo min asarar da ban taba shirya mata ba! Don haka ki saki ranki kawai mu yi rabuwar arziki ko a yi ta tsiya-tsiyaâ€.
Ba ta san sanda murmushi ya kubuce mata ba, ga hawaye face-face a fuskarta. Ba ta yi aune ba ta ji Aboulkhair ya rungume ta, sai saukar harshensa a fuskarta yana dauke hawayen salla-salla daga kan fuskarta. Idanun kuwa har wani side su yake yi.
Aboubacar da ke gefe yana waya da Basma yana jiran Aboulkhair ya sallami Aalimah su tafi, gefen idanunsa ya dan hasko masa abin da ke faruwa. Da sauri ya yi cikin gida yana bai wa Basma labari, ta kai yatsunta ta rufe fuskarta wai tana ji masa kunyar abin da ya gano. Sai jinsa ta yi a nata kumatun yana fadin, “Bari in nuna miki yadda suke yiâ€.
Aboukhair da Aalimah ba su rabu ba sai karfe daya daidai na dare. Tana tafiya zuwa cikin gida tana waiwayonsa da murmushi, yana tsaye jikin motar Aboubacar shi ma murmushin ya ke mata. In ba ta yi kuskure ba ba ta taba ganin irin wannan kasaitaccen murmushin daga gare shi ba.


Daddyn Aalimah, Daddyn Aboulkhair, Aboubacar da Aboulkhair afilin jirgin saman Malam Aminu Kano, fuskokinsu cike da takaici da bacin rai. Wai babu jirgi mai zuwa Niamey a yau sakamakon lalacewar jirgin da suka yi booking din a safiyar yau, yana can Niamey ma bai taso ba ana gyara shi.
Aboubacar ya duba agogon hannunsa, ya ce, “Daddy, da wannan zaman cinye lokacin da muke gara mu je mu bi mota. Tafiyar awanni goma sha biyu cif nan gaba za ta kai mu Niamey. Yanzu karfe takwas na safe, in muka yi sauri muka dauki hanya zuwa tara na safe za mu isa Niamey nan da karfe tara na dare. Za kuma mu samu daurin aure a kan lokaciâ€.
Duk sun yi na’am da wannan shawarar, Daddyn Aboulkhair ya ce, “Aboulkhair is a very good driver, na tabbata kafin lokacin ma mun isaâ€.
A gurguje suka dawo gida suka yi wa Mama bayanin canjin da aka samu. Ba su bata lokaci ba suka dauki sabuwar motar Dr. Mansour kirar Jeep 2015 model, Aboulkhair ya tada ita suka shisshigar da kayansu, sannan Aboubacar ya shiga gaba, iyayen suna baya su biyu. Ko su Aalimah ba su san da wannan sauyin da aka samu ba, ba sa gidan dukkaninsu tun sassafe, ta raka Basma asibiti, Hassana (Zulaiha) na fama da mura, Hussainar sunan mama aka sa mata (Aseeya).
Sai da suka shiga gidan mai suka yi full tank, sannan suka dauki hanyar jamhuriyyar Niger.

Mummunan hadarin motar ya afku ne kafin a kai boarder din da ta raba iyakar kasar Najeriya da jamhuriyyar Nijar, bayan sun tsallake garin Jibiya sun shiga boarder din kasar Nijar.
Wasu gungun fulani ne makiyaya suka koro shanu a kan titin za su tsallaka. Ga direban Jeep din ya kwararo motar da gudu irin na neman biyan bukata. Burinsa su shiga Niger kawai kafin azahar a kalla ya san suna cikin kasar ainahinta, inyaso su yi sallah su ci abinci su durfafi Niamey ba tare da sun bata lokaci ba.
Shanun sun taho fal da gudunsu, shi ma ya shararo motar, sai ya ga bari ya dauke kan motar da azama tunda daya titin babu mota ko daya, ba tare da lura da cewa wata karamar mota ta taho ita ma a guje ta bayansa ba, kawai ta ga motar a kan nata titin ba tare da ta tsammata ko ta ankara ba. Kafin direban karamar motar ya yi tunanin abin yi, ya yi mugun taho-mu-gama da bakar Jeep din wanda hakan ya sanya duka motocin biyu fara katantanwa a tsakiyar babban titin kafin a karshe su duka biyun su hantsila wani katon rami a gefen titin. Ba ka jin komai sai hailala da salatin mutanen da ke cikin motocin cikin mika wuya ga hukuncin mahaliccinsu.


Da asubahin ranar Hassana da Hussaina suka ci gaba da ruda gidan da kuka, wanda suka kwana suna yi suna hutawa. Tun daren jiya sun ki karbar nono. Daga Basma har Aalimah babu wacce ta runtsa, suna fama da yaran nan saboda mama na can dakinta kwance babu lafiya, ta ce kuma takamaimai ba ta san inda ke mata ciwo ba, amma ko hannunta ta kasa motsawa balle ta zo ta taimaka musu. Daga kwance ta ce su dinga yin addu’a suna tofa musu.
Basma gefe ta koma ta zuba tagumi, nonuwa sun mata suntum suna ta sukarta suna kuma diga, duk sun jika gaban rigarta. Aalimah na so ta yi sallar asubah don har masallacin kusa da su sun idar, yaran duka biyu suna hannunta tana jijjaga su, ta san in ta ajiye su Basma ko taba su ba za ta yi ba. ta zama dumm! Kamar wadda ta samu ciwon kurumta na lokaci mai tsawo.
Aalimah ta ajiye daya ta goya daya. Rabonta da goyo tun haihuwar Aunty Gumsu. Tunda aka sallamo Basma Mama ke goya su, ta zura hijabi ta tada sallah zuciyarta na harbawa da kukan da yarinyar ke zubawa a bayanta. Ga wadda ta ajiye ita ma ba ta fasa ba. Kawai ita ma sai ta soma kukan tausayin Basma, ta san tsananin damuwa ne ya sa ta daina tabuka komai a kansu. Allah-Allah ta ke ta idar su tafi asibiti, tukin motar da Aboulkhair ya nace ya koya mata duk da ba ta so yau zai yi mata amfani. Da safe ma ita ta kai su asibiti aka duba yarinyar aka ce mura ce kawai, suka sayo magani suka dawo.
Nan Mama ke gaya musu tafiyar su Daddy a mota sakamakon rashin jirgi. Duka addu’ar sauka lafiya suka yi musu, suka ci gaba da hidimar yaran.
Tun bayan maghriba kuma suka bude makogaro suke zunduma kuka. Wanda shi ne har yanzu suke fama. Tana idarwa ta fito goye da Husainar ta je dakin su Sabrina ta rufe su da duka suna barci. A tsorace duk suka tashi suna tambayarta me ya faru? Kuka ta hau yi a gabansu tana fadin, sai barcinsu na tsiya ya jawo musu masifa, uwarsu na kwance babu inda ta ke iya motsawa tun dare suna nan suna barcin asara, duk kukan da ‘yan biyu ke yi ba su san ana yi ba ko me? Rantsuwa suka hau yi mata suna dirgowa daga gado suna fadin, wallahi ba su sani ba, kuma su ba su ji kuka ba. Ta ce su je su kula da Mama ita da Basma za su je asibiti a duba yaran.
Wata na ture wata haka suka fita a gigice, ta bi su da harara da idanunta da suka yi jawur. Lokaci-lokaci gabanta na tsinkewa ya fadi, har sai ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ta ambaci sunan Allah. Dan cikinta sai wani irin juyi yake kamar ya wuce watanninsa. Ta dawo tana rarrashin Basma, ta canza riga su tafi asibiti, amma ta yi gumm! Kamar ba da ita ta ke ba, gani kawai ta ke rasa yaran za ta yi, don haka ba ta ga amfanin su je wani asibiti ba. ga Aboubacar tun kafin azahar rabonsa da kiranta, ita kuma in ta kira shi wayar ba ta shiga. Dalilin damuwarta kenan.
Aalimah ta yi rarrashin duniyar nan, Basma ta ki tashi, kawai sai ta fashe da kuka mai karfi.
Ta ce, “Basma, ya ki ke so in yi da raina? Kina so na zauce? Ga Mama can ba ta san wanda ke kanta ba, ni ma zuciyata tsinkewa ta ke yi, karfin hali kawai nake yi, su kuma da gani akwai abin da ke damunsu. Jarirai su kwana ba su sha nono ba ki ce haka za mu ci gaba da zama da su muna kallonsu?â€
Basma ko gezau! Sai ta rabu da ita ta sanya hijab din sallarta ta dauki mukullin motar Aboubacar da ya bar musu don irin hakan, kamar ya san za su bukace ta. Ta nade Hassanar a shawul mai kauri, ta dauki katinansu na asibiti ta tafi, Suhaima ta biyo ta da gudu ta karbi ta hannunta tana fadin, “Muje na raka ki in ji Mamaâ€.
Da suka je asibitin a sashen sababbin haihuwa aka karbi jariran (Day old), likitoci suka hau bincikarsu. Suka samu wuri ita da Suhaima suka zauna. Sai a lokacin nutsuwa ta soma dawo mata jin ta daina jiyo kukansu. Tunanin Aboulkhair ya fado mata. Ta kira shi bayan sun dawo daga asibiti da safe ya ce mata suna Katsina, “in mun shiga Niger I will call you. Take care of yourself and my baby for me MON AMOUR!â€.
Kiran da har yanzu ko kyallinsa ba ta gani ba. Tsabar jiran kiran wuni ta yi rike da wayar a hannunta, in sallah za ta yi a cikinta ta ke soke ta. Da ta gaji da jiran ta yi ta gwadawa ita ya ki shiga. Ta yi tunanin sun shiga sahara sun rasa network, amma har twins suka fara jiniyarsu babu kiran Aboulkhair ko na Aboubacar. Mama ta ce, Daddy ma bai kira ba. A lokacin ya isa a ce ma sun shiga Niamey. To balle yanzu da za a iya cewa sun kwana sun hantse, tunda har ga shi alfijir ya keto.
Ba ta kawo wani mummunan tunani a ranta ba, duk da ta san Aboulkhair yana da layin Niger. Ta sa a ranta bai samu sukunin kiran nata ba ne saboda gajiya duba da cewa, shi ya tuka motar tun daga Nigeria har Niger, har kuma babban birni Niamey. Sai dai wannan tsinkewar na zuciyarta shi yake damunta, saboda ba a son faduwar gaba ga mai ciki. A matsayinta na medical personnel ta san hatsarin hakan, don haka ta koma hailala da salatin Annabi cikin zuciyarta.
Daidai lokacin likitan da ya karbi yaran ya fito. Tambayarta ya yi, ina uwarsu? Ta ce tana gida.
Da mamaki ya dube ta, sai kuma ya basar ya
ce ta je ta zo da ita za a debi nonon a ba su ta hancinsu, masassara ce ta cika musu makogaro.
Ta ce da Suhaima ta zauna ta je ta zo da Basma, ba za ta jima ba. Har Mama za ta dauko.
Tun daga nesa ta hangi bakar motar ‘yansanda fake a kofar gidansu. Tsinkewar da gabanta ke yi ya fadi da ta samu ya lafa sabida karfin hailala ne ya sake faruwa da ita. ‘Yansanda biyu na tsaye tare da maigadinsu Bilyaminu.
A hankali ta ke rage gudun motar ta wuce su ta nufi gate tana danna wa Bilyaminu horn da nufin ya zo ya bude mata ta shige.
Bilyaminu ya karaso da sauri, maimakon ya bude mata sai ya tsaya yi mata bayanin wai ‘yansandan gidan suka zo. Wani babba a gidan suke son gani. Ba halinta ba ne raina babba ko na kasa da ita, amma ba ta san sanda ta sakar wa Bilyaminu harara ba, “Amma dai ka san daga Daddy har Yaya Aboubacar ba sa nan ko? Don me ba za ka gaya musu ba da za ka tare ni kana gaya min? Ka san uzurin da ke gabana? Tunda ka ga na fita da asubah na dawo yanzu ba sai ka bude min kofa ba ka san ya zaka yi da su ba, tunda ba sata na yi ba?â€
Daya daga cikin ‘yan sandan ya karaso ganin ta ki kula su, kuma ta rufe dattijon da fada, “Excuse me Madam!†Ya fada da kyakkyawar siga.
Dole ta yi shiru ta bi shi da ido.
“Muna neman gidan Dr. Mansour Raazee, lecturer a jami’ar Bayero, tsangayar Mass Communication, da gidan Aboubacar Raazee, accounter GTBank Hotoro Branchâ€. Ya fada cikin harshen turanci.
A sanyaye ta ce, “Nan ne!â€.
“Ko za ki turo mana namiji ya bi mu ofishinmu? Akwai bayani a kansuâ€.
Girgiza kai ta yi, abin gwanin ban tausayi ta ce, “Ni ce babba a gidan, babu namiji bayan su, uwata kuma ba ta da lafiyaâ€.
Tsayawa ya yi yana tunani, bai kamata ya tafi da ita ba ya gaya mata al’amarin da ke tafe da shi, ga ciki yana gani tare da ita, kuma ga dukkan alamu dukkaninsu ‘yan uwanta ne. A hotunan da aka turo musu babu wanda bai yi kama da ita ba.
“Madam, daure ki turo min namiji ko makocinku ne, zan fi son magana da shi a kankiâ€.
“Ka yi hakuri Officer, ni ma bakuwa ce a unguwar ban san kowa ba. Ka yi hakuri ka bar ni in wuce in ba za ka hanzarta fadar uzurinka ba. Na baro jarirai a asibitiâ€.
Kawai sai ta soma hawaye a gabansu, zuciyarta ce ta tsinke, jikinta ya gama ba ta wani tafiyayyen labari ne suke tafe da shi, wanda zai kawo karshen duk wani farin cikin rayuwarta. Wanda suke shakkar tattauna shi da ita, ganinta mace, kuma mai ciki.
“Ok, since you insist (tunda kin dage), za ki iya biyo mu ofishinmu?â€
Ta zuki numfashi da kyar, amma ta kasa furzo shi waje. Yau ita ce a ofishin ‘yan sanda a kan laifin da ba ta sani ba! Kodayake sun ce abin da suke tafe da shi din ya shafi babanta da yayanta ne. To ko laifi suka yi? Ko kama su aka yi a hanyar Niger din? To su kuma sauran da ba’a ambata ba ina suke?
Ba ta da amsa ko daya, don haka ta share hawayen da suka cika mata fuska ta ce su ba ta minti goma ta fada a gida, ta dauko ‘yar uwarta ta kai ta asibiti, sai ta same su a inda suka ce.
Tana shiga gida ta tarar da wani tashin hankalin. Basma ce a sume, su Sabrina na ta sheka mata ruwa. Duk tsananin da Mama ke ciki ta sa sun tayar da ita sun jinginar a jikin filo. Sabrina ke gaya mata tunda aka yo mata waya daga Niger aka ce su Daddy ba su isa ba tun jiya kuma an kasa samun kowannensu a waya ta ke suma tana farfadowa. Ta dubi Mama a firgice sai Mama ta lumshe ido, ta ce, “Ku hada karfi ku sa ta a mota, ki kai ta asibitiâ€.
Jikinta na rawa ta ce, “Mama har ke zan kai, wallahi ba zan barki a gida ba. Kuma yanzu zan yi wa Mummy waya har Niger din in gaya mata ga halin da ku ke ciki dukkanku, ni kadai ba zan iya ba, kwakwalwata kamar ta zauce. Yanzu haka ‘yan sanda ne a bakin gate sun zo tafiya da ni. Ba su je Niger ba, ina suka je? Na shiga uku ni Aalimah, ko dai ‘yan fashi ne suka tare su?â€
Dukkansu babu wanda ya kawo wani abu a zuciyarsa bayan wannan, Mama ta ce ba za ta iya fita zuwa mota ba. Aalimah na kuka ta ce, “Ko a goye ne sai na kai ki asibitiâ€.
Ita da kannenta biyu suka ciccibi Mama, rabi kuma da kafarta suke janta a kasa zuwa mota. Suna fitowa harabar gidan Tabawa da Sabira suna shigowa (masu aikin Mama), wadanda ba aikin kwana suke yi ba.
Wata ajiyar zuciya Aalimah ta yi, da hanzari suka taimaka mata ta sa Mama a mota, ta gaya musu saura Basma, Tabawa ita kadai ta ciccibo Basma sabida kakkarfa ce. Gabadayansu suka duru a motar har su Sabrina, su biyu a gaba, ta ja su zuwa asibitin da ta kai su Hassana da Hussaina.
Dukkansu an karbe su ba bata lokaci, da yake asibitin na kudi ne, international. Ta gaya wa Mama za ta je ofishin ‘yan sandan ta dawo, Mama na daga kwance ta ce ba ta yarda ba. Ta kara gwada layin Aboulkhair, in har yanzu ba ta same shi ba, ta kira Uncle Oussama ta gaya masa, ko kofar asibitin ba ta yarda ta taka ba.
Hakan kuwa ta yi, duk da cewa ta so Mama ta barta ta je, don idan reality bai kassara ta ba, fargaba da zullumi dake zuciyarta za su haifar mata da hauhawar jini, wanda shi ma ba’a sonsa ga mai ciki.
Jiya-i-yau. Ba ta samu Aboubacar ko Aboulkhair ko Daddy ba. Don haka tana kuka ta kira Oncle Oussama wadanda ke can zugum-zugum sun kasa daura aure bayan sun tara jama’a makil daga birni da kauye, tunda babu labarin iyayen yaran bayan kowa ya tabbatar da tahowarsu tun jiya.
Kukan da ta ke yi bai hana shi gane me ta ke cewa ba. Duk halin da suke ciki tun jiya ta warware masa. ta gaya amsa yanzu haka duk an ba su gado daga su har jariran kuma Mama ta hana ta zuwa police station din.
“Za mu zo a yau, kada ki sake kije police station dinnanâ€. Abin da ya ce mata kawai kenan yana mai jin wani irin tsoro da tashin hankali na shigarsa.
Ango Hamoud da ya yi zugum a gefe, da Mu’azzam da ya iso tun jiya ya ja gefe ya ce su je su nema musu ticket yanzu-yanzu mai zuwa Abuja, shi da Edrissa da Mu’azzam da angon da Malam kansa. Bayan wannan bai kara musu bayanin komai ba. Ya karbi sadaki daga hannun kaninsa babban dan Inna Bintou ya daura auren Khaleesat da Hamoud ba cikin dadin rai ba, sai don ba yadda za su yi da jama’ar da suka tara. Tun ba a gama watsewa ba ya ja Malam gefe ya gaya masa duk bayanin da Aalimah ta yi masa a waya, ya kara da cewa, yana tsammanin suna hannun ‘yan sandan da suka je neman wani nasun, ko dai sun yi wani laifin ne an kama su, ko ‘yan fashi ko hadari. Abin da yake zato kenan.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’unâ€. Shi ne abin da Malam Ibraheem Raazee ke ambato, babu kakkautawa. Zufa na keto masa ta ko’ina a jikinsa a lokacin da ya daga kai ya hangi Mu’azzam na fitowa daga mota.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button